Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 31 Book 2 Complete Novel

Hannah gaba daya kanta ya kwance bata taba tsammanin abubuwa zasu kwabe mata haka ba, wai me yakawo Jalila a gabar da takeso kulla wannan gadar Zaren, da komai ya tafi dai2, Jalal baze taba tsallake shirinta ba, wayarta ce ta fara ringing amma Hannah tayi biris da ita, an kirata ya kai sau shida sannan ta dauka a fusace tace

“dalla waye haka?” 

“ke dalla zizo ne, za’a miki abun Arziki amma kina wa mutane hauka, ki tattara kayanki tun wuri kisan inda dare yayi miki wallahi” 

“kamar yaya? Saboda me?” 

“Allah ne yake sonki da rahama, Wallahi Jiya na raka wani me gidana Unguwa, ya tsaya gurin wani me gidansa dan sanda ne babba, naji me gidannan sa yana waya, bayan ya gama yake gayawa maigidana, wai wani yabada izinin a kamo masa wata yarinya a ajiye masa ita har seta haihu, ta yaye yaron ya shekara biyar sannan a saketa, idan kuma ba tada ciki aita ajiye ta kar a saketa, kuma yadda mutumin nan yake kwatantawa na gano kaman kece, ban gasgata hakan ba se jiya da naje palace, wallahi cikin dare ‘yan sada sukazo nemanki, dan haka in kin san da wata cakwakiyar da kika kulla tun wuri ki kama gabanki wallahi “

Hannah ta hadiyi wani mugun miyau ta ce 

“Shikenan nagode sosai zizo”

Ta katse wayarta ta mike tsaye tareda fadin

 “kan bala’i banga ta zama ba, ni Jalal zewa haka? Wallahi yadda ya fada din nan aka kamani kashina ya bushe, Amma wallahi in yasan besan wata besan wata ba, ni zesa akama, nizewa hauka? Banga ta zama ba” 

Ta mike da sauri ta  janyo Akwati tafara zuba kayanta tanayi tanayin surutai. 

Jalila tattar komai ta ajiye a gefe ta maida hankali akan karatunta, dan yadda takeji in bata dena yawan damuwar nan ba zuciyarta zata iya bugawa, sosai Maama ta rage wannan gabar da takeyi da Jalila, tana dan sakewa da Jalila har suyi hira, suna shirye shiryen yadda biki ze kasance, Jalila bata taba nuna mata tana fushi da ita akan abubuwan da tayi mata a baya ba, Maama har mamaki takeyi, wani lokacin yanayin halinta daya da Jawwad, ka musu laifi amma su nuna basu san kanayi ba, ita kanta Nana tayi mamakin yadda Maama tayi saurin karaya da Al’amarin da yafaru. 

Jalila tana kitchen tana aiki Nana ta sameta 

“sannu da aiki Jalila, har tausayi kike bani, ke ba kya gajiya da aiki, da ke zaki rigani Aure ai ban san ya zanyi da aikin gidan nan ba, dan ma su Yaya Jawwad basa nan, aikinsu sam baya karewa” 

Jalila tai murmushi tace “Nana uwar son jiki, keda zakiyi Aure ai son jiki banaki bane, madam get ready to face the challenge, Ba sauki a Aure” 

“Nasani amma gaskiya bazan iya yadda kikeyi din nan ba, tabdijan shikenan kai bawa baka da hutu” 

“Aikuwa mukayi miki aure kikaje kikayi shirme, in yace ze kar Aure Addu’a zamu taya shi, mu fidda anko mu sha biki” 

“Kan bala’i ji muguwa, to ta Allah bataki ba” 

“Kai Nana sarkin kishi” 

“ke ba dole inyi kishin sa ba, ke har mamaki kike bani, ainaga kokarin ki da zaki auri Ahmad din nan, inajinki Hanan tana gaya miki matarsa bata da kirki” 

Jalila ta murmusa tace 

“Nana kenan, macen da ta amsa Sunanta mace, wadda ta yadda da kanta bata batawa kanta lokaci akan wani kishi, duk rashin kirkin matarsa ai ba akanta zan zauna ba, zan maida hankalina ne akan mijina, zanyi kishine da matar da nasan ta fini Ilimi, kyau, dukiya da asali, se matar data hada wannan abubuwan lokaci daya itace watakila zan kalleta a matsayin kishiya”

jinjina kai Nana tayi tace

“Sannu Jalila, Aini ko Kaza za’a aajiye ace kishiya ta ce to hankalina baze kwanta ba, yaushe zan kashe kaina, ke masu irin wannan zuciyar taki bau da yawa”

A tare sukayi dariya, Sannan Nana tace

“Yawwa Jalila nikam nace ya akayi kika amso qur’anin nan daga hannun Ilham? Na ganshi a karamin drwower” 

Dan murmushi Jalila tayi tace “Nawane ai ba nata ba, dan haka tunda ya tafi dole ya dawo” 

“Amma dagaske yaya Jalal ne ya baki shi? Kamar yadda Ilham ta fada?” 

“watakila shi yabani dan bani da tabbas” Jalila ta fada ba tareda ta kalli Nana ba

“Kamar Yaya baki da tabbas?” Nana ta tambayeta cike da mamaki

Jalila ta juya ta cigaba da aikinta sannan tace 

“Kamar yadda nagaya miki mana, bani da tabbas na shi yabani koba shi bane ba” 

Nana tace “Kai Jalila kin fiye rainin hankali, mutum yayi miki magana ki raina masa hankali, in tai wari dai maji, Ke Jalila ban gaya miki ba” 

“Ina jinki hajiya Nana jarida” 

Nana ta dan hade rai tace “kefa ‘yar wulakanci ce, wace irin Jarida kuma?” 

Jalila tayi murmushi tace “Allah yabaki hakuri” 

Nana Ta dan saki fuskarta tace “Wai bakiga kwana biyun nan Maama duk tayi sanyi bane” 

Cikin ko in kula Jalila tace “Ban lura da hakan ba, tana komai nata kaman yadda take a baya” 

“Shikenan tunda haka kika ce amma Anjima zaki rakani wani guri” 

“Ina kenan?” 

“In munje zaki gani, saura daga baya kice min bazaki ba” 

Jalila tace 

“zan raka ki Insha Allah, Amrya ba kya laifi” 

“kai Jalila har kinsa naji dadi” Nana takarasa fadar hakan tareda fita daga kitchen din. 

Koda Jalila ta kammala aikinta ta koma daki, ta tarar da missed calls a wayarta, ta dauka ta bude don duba waye ya kirata haka? Kiran na Jawwad ne da kuma Ahmad, tana kokarin kiran Jawwad ne kiran Ahmad ya shigo wayarta, dan haka ta fasa kiran Jawwad ta amsa kiran Ahmad, Jalila ta shafe lokaci me tsawo suna waya da Ahmad, Sosai Ahmad yake bawa Jalila kulawa, dan tana iya shafe lokaci me tsawo suna waya ba tareda ta kosa ba, sukanyi kwanaki basuyi waya ba, saboda yanayin Aikinsa, dan haka duk lokacin da suka samu dama suna daukar dogon lokaci suna tare a waya, tana cikin wayar ne kiran wayar Jawwad ya dinga shigowa, dan haka sukayi sallama da Ahmad, ta kira Jawwad, tana bugawa ya daga 

Jawwad yace “Baby dawa kike ta waya hakane? Da farko na kira baki daga ba, Nakuma kiranki busy busy, for more than hour” 

“Am sorry Yaya Jawwad , Ahmad ne ya kirani, shine.. sekuma tayi shiru

Jawwad yace

“Hmmm to shikenan nagane, dama munyi magana da Hanan tace; zasuyi magana da Nana irin kayan da zasu saka na dinner, za’a turawa Abba, A dakko musu, kayan sun iso, ta kira layin Nana baya shiga” 

Dan zumbura baki Jalila tayi kaman yana ganinta  tace

“suka dai za’a siyawa nikuma fa? Ko tun yanzu anfara ware ni” 

“Waya isa ya wareki babyn Abba, A sekin zaba sannan za’a basu su zaba suma” 

“to shikenan zan musu magana Insha Allah, ya Aikin kuma?” 

“Aiki Alhamdilillah gashi muna ta fama” 

“To Allah yabada sa’a” 

“Ameen Babyn Abba” 

“Ina Jalal? Ya nasa Aikin?” Jalila taji tayi maganar ba tareda ta shirya yinta ba. 

Jawwad yace “Kinfara missing dinsa ne?” 

Sekuma taji gaba daya ta dirirce tarasa me zatace

“Amm a’a kawai na tambaya ne, don’t mind me, yaushe zakazo” 

Jawwad yace

 “A’a tsaya, naji dadi da kike tambayarsa, dama be kamata ya samu aiki ta hanyarki, yakama hanya ya tafi nesa da gida kuma ace bakya bincikar ya yakeba, Jalal dai yana nan lafiya, kuma yadda yake nunamin yana jin dadin Aikin nasa, Alhamdilillah ana samun cigaba a rayuwarsa, muna godiya kanwar mu, Allah yabiya ki ladan wannan dawainiya damu da kike”

“Ameen Yaya, to shikenan,  naji kaman Maama tana kirana”

Jawwad yace “to shikenan munyi waya da Maaman dazu da safe, Amma in cewa Jalal kina gaisheshi?” ya tambayet cikin zolaya

Da sauri tace

“A’a karka fada, ni bana gaisheshi” 

Jawwad yai murmushi yace “Shikenan se anjima” 

sukayi sallama, ta danyi Ajiyar zuciya, sannan ta mike, ta tafi bandaki dan daura Alwala anata kiran sallar Azahar. 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Da la’asar Nana ta uzzurawa Jalila suka dau mota fita, seda suka tsaya a kasuwa sukayi siyayya, Sannan Nana tace ta rakata Asibiti dubiya, Sam Jalila bata kawo komai a ranta ba ta raka Nana Asibiti, suka shiga female ward, Nana ta tambayi wani daki, aka nuna musu, Seda suka shiga  dakin sannan Jalila ta lura da suwaye a dakin, Su Yaya mairo ne a dakin, se Naja dake kwance kaman gawa, ana samata ruwa,

da Jalila tasan gurinsu Nana zata janyo ta, da bata biyota ba, Amma me sukeyi a Asibiti? Ta tambayi kanta, Sallamar dasu Jalila sukayi ne yasa su juyowa suga su waye, Ganin Nana da Jalila yasa su hade rai, Jalila ta samu guri ta tsaya, Nana ta karasa ta zauna, tace 

“Yaya Mairo ina wuni” 

Rai a hade yaya mairo tace “lafiya” 

“Yame jiki kuma?”  Nana ta kuma tambaya

A fusace Yaya mairo tace

“ban sani ba gulayya, uwarki ta gaya miki shine kikazo ganin kwaf, hadda dakko wannan annamimiyar shedaniyar, to da dan uwanki ya fasa Auren Naja bata mutu ba tana da rai, sannan ki gaggauta dauke wannan tsinanniyar yarinyar ku bar gurin nan, dan na tsani yarinyar nan bana kaunar ta, Yarinya sekace mayya, wayasani ko bayan Kafirci ta gaji maita, kila ta sha a Nono, kiri2 tana kokarin rabani da ‘yar uwata, za’ ayi Auren nan amma ta shiga ta fita ta hana, makira sedai kici kanki wallahi, kurwarmu tafi karfinki” 

Jalila dake gefe tace “kinga nifa ban san nan zamuzo ba, dana san nan zamuzo da bazan biyota ba, ni ban san Naja bata da lafiya ba, dan haka kidena zagina, wallahi kika kuma zagarmin uwa sena rama, ko ina maita zanci naman kune? Me zan ci ajikinku jikin matsiyata, Azzalumai” 

Sa’adah ta taso a fusace tazo gaban Jalila ta nuna ta  tace “ke karki kuskura ki zagarmin uwa” 

“in aka zagetan me zakiyi?” 

Jalila ta tambayeta tareda sauke hannun sa’adah tace 

“uwata da aka haifa a cikin Arna, da ita nake Alfahari, dan haka duk wanda ya kuma Yunkurin zaginta se inda karfina ya kare” 

Nana ta mike da sauri taje tsakaninsu ta tsaya tace

“haba dan Allah, nifa ban kawo Jalila gurin nan dan kuyi rigima ba, nazo in duba Naja ne nace ta rakoni, me yakawo zancen maita,  yaya Jalila tayi hakuri a lokuta da dama da kuke cin mutuncin ta, Yaya mairo a rayuwa mussaman idan kanada ‘ya’ ya bakayi wa dan wani gori, kokuma mummunan baki, ……

 

“rufemin baki ko in gaureki da mari, kema ta shanye ki, shine zakizo kimin rashin kunya, na rufe kofa in muku dukan tsiya a gurin nan” 

Jalila tace

 “Wallahi babu matar da ta isa in tsaya ta dakeni, wallahi Nana dana san nan zaki kawoni bazan biyoki ba, kuma ki kyalesu karsu fasa zagina, bacin ranki akan an fasa aurar ‘yarkine, badan anyi yunkurin likawa Yaya Jawwad ita ba ba abunda zesa in fadi wani abu a kanta, tunda tun ba yauba nasan halin yaranki kaf, nasan Naja tana shaye2, an gayamin Sa’adah na bin maza kuma kowanne inada tabattaciyar hujja akan hakan, kuma bari kiji ni ce nan nagayawa Abba yayi bincike akan Naja, kuma bincike ya tabattar masa da ba mutuniyar kirki bace, nan gaba in zakiwa dan wani gori ki duba gaba da bayanki ki tabattar bakida abun gorin tukuna, Allah ne ya sa kamin cin mutuncin da kikemin nida uwata, kuma kadan kika gani wallahi, kekuma Nana ingo key din motar kya taho, ni zan hau ta haya in koma gida”

Jalila tayi ficewarta, da sauri Nana ta biyo bayan ta, da kyar ta lallaba Jalila ta hau motar suka nufi gida, harsuka je gida Jalila bata kula Nana ba ta cika tayi fam, suka shiga da kayan siyayyar da sukayi daki, Jalila ta hade rai sosai Nana ta nisa ta zauna a kusada ita  tace

“Jalila nasan zakiji ba dadi abunda nayi miki, na kawoki anci mutuncinki, Jalila nasa ki rakoni ne dan kiga sakayyar hakurin da kikeyi, Jalila me hakuri ba a taba ganin bayansa, duk takurar da sukayi miki abaya zagi da cin mutuci, Amma abun Allah agaban Maama cikin jikin Naja ya zube, Jalila sadaukarwarki da jajircewarki akan samarwa wasu farinciki, Allah baze taba barinki ki wulakanta ba, Jalila duk lokacin da naga hawayenki ina shiga matukar damuwa, amma dayawa kikanyi kukane idan kika kasa samarwa wani farinciki, kokuma wani yayi hurting dinki, amma hakan baya hanaki kokarin ganin kinsa nakusa dake farinciki, shiyasa na kaiki kiga sakayyar da Allah yayi miki akan makiyanki, masu saki zubda hawaye, Jalila ina sarawa kokarin ki, masu irin zuciyarki kadan ne a cikin al’umma, Allah ya dawwamar da haske a cikin rayuwarki”

Jalila ta rungume Nana, tana zubda hawayen da bata da tabbacin na farinciki ne kona bacin rai, tace “Nana nagode da addu’ar da kikayi min, dukda kasancewar su yan uwan mahaifiyarki baki juyamin baya ba, Amma Nana har cikin zuciya ta bana murna da abunda yasamu Naja, duk abunda yafaru da mace daya a society makamancin wannan, gurba cewa ce ta al’umma, da Yaya mairo tayi musu tarbiyya me kyau, Allah ka dai yasan mutanen dazasu amfana dasu, kuma da bazan taba adawa da Aurenta da Yaya ba, Amma ina fatan Allah ya shiryesu, yabasu mafita “

“Ameen Jalila “

Tunda Jalal yayi wannan tafiyar be kara dawowa ba, sedai suyi waya da daddyn sa ko Jawwad, Amma Jawwad yaje sau biyu lagos gurin Jalal, dukkan wani shirye2 suna yinsa ne ta waya shida Jawwad, tunda sukayi wannan rabuwar da Jalila basu kara haduwa ba. 

Jalal yayi kalau dashi, bashi da tension sosai, sena tunanin irin missing din Jalila da yayi, ‘yan kwanakin da yayi tareda ita, suna shiri ya tsaye masa, amma da zarar ya tuna maganar ta na babu shi babu ita gaba daya se yaji abun duniya ya dame shi, shi kansa yasan Jalila halitta ce me matukar mahimmanci a rayuwarsa, a yanzu yana kokarin yin salloli biyar a rana, dukda ba kowane lokaci yake yinsu akan lokaci ba, yana kokarin yaki da zuciyarsa yaga yayi salla. Amma duk lokacin da yaji abubuwa sun da meshi, yana zama yayiwa kansa caji da giya yadda yakamata. 

Sannan Jalal yasaka a nemo masa Hannah duk inda take, se yaga waye gatanta, dan yayiwa kansa alkawarin se yasa an ladabtar da ita, seta gane shiba sa’anta bane da zatayi masa hauka. 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Bangaren Jalila ma tana son sanin halin da Jalal din yake ciki, tana son sanin ko har yanzu yana shaye2? Wace irin rayuwa yakeyi zamansa a lagos? Tana tausayin Jalal sosai, musamman idan ta tuna da labarin rayuwarsa da kuma amanar da Antynsa ta bata, ko ba komai dukda fadan da sukeyu takan tuna Alkhairan sa, Amma da ta tuna abunda Mummy da Ilham sukayi mata, gaba daya se ranta ya baci, se taji bata sha’awar kuma shiga shirgin rayuwar Jalal, dama saboda Jawwad suke haduwa, in Jawwad yayi Aure ko ganinta baze kara yiba balle mahaifiyarsa ta zargi wani abu. 

Rana bata karya, sedai uwar diya taji kunya inji hausawa, Duk abunda aka sama sa rana inda rai da lafiya zezo, Shirye2 sunyi nisa game da wannan bukukuwa da wadannan iyalai ke tun kara, Jawwad yayiwa Hanan saiti uku na kayan lefe, be cika mata tarkace ba, sedai yazuba mata kaya masu matukar tsada da kyau, haka Nana ita set hudu mahmud yayi mata, itama an zuba mata dukiya (kunsan family su Jalal akwai masu gidan rana) gaba daya kayan lefen bauchi aka kaisu, a can aka karba kayan, na Abdallah ma aka kai kaduna gidansu siyama, gaba daya Basa zama, koda yaushe Hanan tana yawan zuwa kano saboda siyayyar biki. 

Duk wani shirye2 Jalila ce kan gaba gurin tsara yadda abubuwa zasu gudana, An shirya gaba daya bikin zasuyi shi a garin bauchi ne. 

Saura sati daya a fara biki, su Nana suka tafi garin bauchi inda acan za’ayi dukkan wata hada2 ta biki, 

Jawwad da Jalal tare suka je har maiduguri suka kai musu katin bikin Jawwad, dama ga abun dai2 da bikin Nana, rabon da Jalal ya taka kafarsa garin maiduguri har ya manta, Amma bisa ga mamakinsu sega Jalal, dangin Daddy sunyi matukar farincikin ganin Jalal, ya nutsu ba kamar da ba, yasa manyan kaya hada hula, gashi suka samu labarin har aiki yake, sunyi farincikin ganin sa, sun samu kyakyawar karba daga dangin Jalal, dama Jawwad ma dan gida ne, seda suka kwana biyu a garin maiduguri suka wuce bauchi shida Jawwad, sam Mummy bata san batun Jalal yaje maiduguri ba. 

Shirye2 sunyi nisa sosai ana ta hada2, za’a shiga satin biki, Jawwad da Jalal sun kwana biyu a bauchi suka koma kano domin rabon invitation ga abokan Jawwad, Amma har suka tafi Jalila basu hadu da Jalal ba, duk inda amare suka shiga Jalila na biye dasu, tare sukaje gyaran kai, da kunshi na amare, hatta gyaran jiki da Jalila ake, se sheki take kamar itace Amaryar, in kaga yadda take zakewa kai kace itace amaryar, Ana gobe za’a fara bikin ‘yan uwansu Jalal daga maiduguri suka zo (dangin su Mahmud) lokacin da suka zo su Jalila sun tafi gurin kunshi, tunda suka zo Antyn Jalal ke cigiyar Jalila, Amma aka sanar da ita sun tafi gurin kunshi, guri na mussaman aka tanadarwa dangin mijin Nana. Ana gobe a fara bikin su Jawwad suma suka dawo shida Jalal, duk inda zashi kafarsa kafar Jalal. 

‘yan uwa wanda sukazo daga wasu garuruwan, Inna ta dinga nuna musu Su Jalila Da Nana, tana gaya musu ga’ ya’yan da jikokin kanwarta. 

Yaya mairo kam da zuri’ar ta kaf babu  wanda yazo taron nan, sedai sauran ‘yan uwa da abokan Arziki. 

Se dare su Jalila suka dawo daga gurin kunshi, kallo daya zakayiwa fuskar amaren zaka gane yadda suke cikin farinciki, gashi sun dau kyau Masha Allah, suka tafi part din Anty fido a can suke kwana saboda estate din ya fara daukar harami da baki, kasancewar daddyn Hanan babban mutum ne asanshi sosai. Hakama Abba yanada mutane sosai, ga dangin su Jalal, dan haka estate din cike yake da mutane. 

Koda su Jalila sukayi sallar magariba, Hanan tace 

“gaskiya sena kira Haidar yazo ya ga kunshin nan” 

Jalila tace

“ke zumudin me kikeyi? Kwana nawa ya rage?” 

“dan kwana nawa ya rage, se indena kula dashi? Se yaga kunshin nan, in yamasa ayi biki da shi, in yace be kyau ba a dirje shi a daren nan” 

Gaba daya sukayi dariya, Nana tace 

“ni dama muna gurin kunshi Mahmud yacemin; sunzo dazu suna tareda su Yaya Abdallah, ina son mu hadu da shi, inji ko yaci Abinci?” 

Jalila kallonsu kawai take tana murmushi, tana mamakin ya sukeji a ransu game da soyayya haka? Ita dai tasan tana son Ahmad, Amma bata tunanin zata iya wannan rawar kafar akansa kamar yadda su Hanan sukeyi, ko lokacin da take son Yaya Jawwad bata tunanin zata iya abunda su Nana sukeyi, tana kallonsu suka canza kaya, sukayi waya da su Yaya Jawwad suka fice babban palourn part din. 

Itama sallolinta tayi, tai wanka ta canza kaya, ta samu ta nutsu tana cin Abinci, ta nayi tana chatting da Ahmad, yana ta mata magiya akan ta fito yana son su hadu amma taki, se wasa take masa da hankali. 

Maama ta kira Jalila a waya tace taje main part ana neman ta, haka ta tashi ta tafi, da ita so take ta samu ta kwanta ta dan huta, ta fita ta kofar kitchen yadda su Hanan bazasu ganta ba. 

Koda taje, da kyar ta gano Maama saboda cikar da akayi a gidan, Maama tace 

“dangin mijin Nana ke nemanki, Antyn Jalal tunda sukazo take cigiyar ki fa” 

Jalila tace “Ai ban san sunzo ba, suna ina?” 

Maama tayi mata Jagora har masaukin da aka basu, Jalila na shiga Antyn Jalal ta fadada murmushinta tace ” ‘yar halak taki ambato, tun dazu nake cigiyarki” 

Cikin fara’ a Jalila tace

“Anty sannunku da zuwa, munje gurin kunshi ne shiyasa, ya kukazo? Ya hanya?” 

“Alhamdilillah Jalila, Allah yasanya Alkhairi, ya kaimu lokacin naki Auren, kalli yadda kike sheki kamar Amarya” 

Sunkuyar da kai Jalila tayi, alamun kunya, ta gefen Antyn ce tace 

“Masha Allah itace Jalila kenan, kai Jalila Allah yasaka miki da Alkhairi, muna godiya da nuna kulawarki ga danmu, last week sega Jalal a maiduguri, babban farinciki danayi, wai aikin dayake ta silarki aka same shi, mungode Jalila” 

Gaba daya Attention din sauran da suke dakin ya dawo kanta, wasu suna magana da hausa wasu nayi da yare, suka dinga yi mata Addu’a, tarasa Addu’a mema suke mata haka? Kamar wadda ta basu wata gagarumar kyauta. 

Dangin Jalal suna da matukar kirki da karamci, nan Antyn Jalal ta dinga nuna mata dangin Jalal, tana gaya mata kowacce mecece a gurin Jalal, ‘yan gayune, kuma kallo daya zakayi musu kasan suna hutawa, gasu kyawawa abunda ta lura da shi shine, gaba dayansu babbar shedar da zaka gane family dinsu da shi, shine wannan dogon hancin irin na Jalal, mazansu da matansu haka suke kayan dogon hanci, Kamar sun saba da Jalila suka dinga yi mata hira, gaba daya Jalila jinta take a takure, Anty ta lura da hakan dan haka tayiwa Jalila sallama, tace seda safe. 

Jalila na fitowa tana sauri takoma part dinsu ta hadu da Yusuf a hanyar shiga babban parlour, yace 

“Yawwa Alhamdilillah, naji dadin ganinki a yanzu, zomuje kimin wani dan aiki” 

Jalila tace

 “to Yaya” yana tafe tana binsa a baya, ya shiga inda ake ta hada2 dafa Abinci, ya dakko wani kwando da manyan warmers akai da plates, da spoons da serving spoons, yabawa Jalila ta karba ta rike, shikuma ya dakko cartons na ruwa da lemuka, yace 

“muje Bakinmu nasa akayiwa girki, dare yayi Abinci ya kare

” Jalila ba tace komai ba ya shiga gaba ta biyo bayansa, wani part din suka nufa, ita  bata taba sanin da gurin bama, saboda parts din da suke bangare daya na estate din ma dayawa, tundaga waje harabar part din ake iya juyo hayaniya na tashi da dariya na ‘yan maza, Yusuf ya shige gaba yasa hannu ya bude kofar ya shiga, ya juyo ya ce mata 

“Shigo Jalila”

 ba musu ta bishi da kayna a hannunta, kallo daya tayi musu ta sauke kanta, mazane sun kai su bakwai a cikin palourn, inma basu fiba, dan haka duk taji ta takura, kanta a sunkuye ta dan risina ta gaishesu, suka amsa mata gaba daya, dayan yace “A’a wannan kaman Hanan” 

Taji muryar Abdallah yace

 “Ba Hanan bace, sister dinta ce, Amaryar Ahmad to be” 

Ahmad yace 

“Tun dazu nake magiya ki fito in ganki kika ki, cikin sa’a sega Yusuf ya kawomin ke, amma dan mugunta ya hadaki da wannan kayan nauyin, memakon shi ya dakko” 

Sunkuyar da kai Jalila tayi tana sauke kwandon hannunta, Yusuf yace 

“Au ban maka abun Arziki bako? Nida yakamata ka godemin” 

Ahmad yace 

“nina isa in fadi haka, ince bakayi min abun Arziki ba, Kamin abun Arziki sirikina, wallahi Yusuf ji nake kaman a daura namu auren nida Jalila” ya dan kalli Jalila yace 

My Queen yakamata muyiwa Daddy magana, yadda kikayi shar dake haka kamata yayi kawai muma ayi namu”

Jalila ta sunkuyar da kai cike da jin matsananciyar kunya. 

Daya daga cikin Matasan yace

“dan banza uban zumudi, dole kayi zaman jiran shekara guda, kacigaba da lallabawa da Ameera, kokuma kayi biyu babu” 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Gaba daya kunya suke bawa Jalila, tayi kokarin mikewa domin tabar dakin, ta mike kenan kawai idonta ya sauka ana Jalal da tunda ta shigo bata kula da shi ba, farar Jallabiya ce a jikinsa fara kal, sumar kansa ta sha gyara se sheki take, watanni hudu kenan bata ganshi ba, amma ya kara kiba, gaba daya ya tattara hankalinsa akan danna waya da yakeyi amma gaba daya idonsa akan Jalila yake, yana mata wani irin kallo da takasa gane na menene? Tuhumace, kokuwa meyake nufi? 

Muryar Abdallah taji yace

“Queen kin san kuwa ranar dinner, Siyama zasuzo ayi dinner anan, ranar daurin aure in angama da nan, zamuje kaduna a can gidansu za’a daura namu” 

Cikin sakin fuska ta juyo tace “Dagaske Yaya Abdallah, zanga Siyama? Rabon da in ganta tun ranar dana bar kaduna” 

Ahmad yace “tasan Amaryar taka ne?” 

Abdallah yace

“tabdijan Aminiyarta ce ta kuruciya, wadda take Jawa duka, kai Jalila ai an girma an dena neman magana, Siyama tana bani labarin wahalar da ta sha saboda ke, gaskiya badan badan ba sena rama mata” 

Jalila ta dan zumbura baki sannan tace “Seku rama din ai” 

Ahmad yace “Ka rama me? Munci bulus ko queen?” ta dan jinjina kai tana murmushi. 

Koda aka bude warmers din nan, jallof couscous ne, ya sha nama da kayan vegetables, ta dan kalli Jalal ta kalli Abincin tasan Jalal baya cin Couscous kome zeci oho? 

Kai bazakace Jalal yayi existing a dakin nan ba, duk hayaniyar nan da’ake yi, kala bece ba, shida kujerun gurin kusan daya, dan ko uffan baya cewa, ko abun dariya sukayi fuskar nan tasa murtuk take babu alamar wasa. 

Kallon da yake wa Jalila gaba daya yasa ta tsargu har taso ta diricice, dan haka tace “seda safenku” 

Ahmad yayi farat yace

“tsaya in rakaki  zamuyi magana”

Yusuf yace 

“Sena gayawa Amira, wannan rawar kan da kake yi” 

“Karka fasa gaya matan” 

Jalila ta nufi hanyar fita, dan gani take kaman Jalal ze iya tashi ya dizgata agaban mutane, tana kokarin wucewa tayi tuntube da kafar Jalal kasancewar ya mike kafafunsa kuma takusa da kafafunsa zata wuce, ga shi a rude take dan haka ta kusa faduwa, Allah ya temaketa bata fadi ba tace “Subhanallah” shikam Jalal ko a jikinsa dan ko kallon inda take beyiba, Ahmad yace

“Haba ya haka? Kana kokarin nakasa min mata, ka baje kafafunka akan hanya, at least yakamata ka bata hakuri” 

Wani irin kallon baka isaba Jalal yayi masa ya maida kansa kan wayarsa ya cigaba da abunda yakeyi, ba tare da ya furta koda harafi daya ba Jalila tace 

“No karka damu, base yabani hakuri ba, wannan ai besan yayi laifi yabada hakuri ba, da na fadi kafar zan take inga ta tsiya” 

Kallon da Jalal yayiwa Ahmad ba karamin batawa Yusuf rai yayi ba, dan da’a waje ne wani civilian din yayi musu haka, seya gane shayi ruwane, shibe ma san daga Ina wannan mugun dan jiji da kan yake ba. 

Abdallah yace

“Yusuf kabi a hankali, wannan da kake yabata hakuri, in yaso se ya hana abaka Auren nan, sirikin kane ka bishi a sannu, yayan Mahmud ne daze Auri kanwarku Nana, kuma babban Aminin Jawwad” 

Yusuf yace 

“wannan din”? 

“Kwarai Shidin” 

Jalila dai ta fice waje, Ahmad ya biyo bayan ta, 

“Jalila wai me wannan mutumin yake takama da shine da yakewa mutane kallon basu isa ba??” 

Jalila tace

“ba kallon mutane basu isa bane, haka yake, haka halayarsa take, ka lura ko Mahmud da yake kaninsa baya kulashi sosai, Yaya Jawwad da Abdallah kawai yake shiga shirginsu” 

“Amma meye hadinki dashi da ze dinga kallonki haka?” 

“Ba wani kallona da yake, kaika ga hakan, bani da Abunda Jalal ze tsaya kallo, A lissafin Rayuwarsa baya shiga shirgin mata, koda ‘yan uwansa ne, muna gaisawane kawai saboda Aminin Yaya Jawwad ne” 

“Kai queen, duk taurin kai da dagiyar namiji, baze iya dauke kai akanki ba, Amma me ya kai Jawwad abota da wannan bahagon mutumin”. “Amintarsu hadin Allah ce” 

“to shikenan, abar maganar ya gajiya,? naga kunshi ki yayi kyau, kamar in saceki in gudu” 

Murmushi tayi tace

“Tabdijan kaida Daddy kuwa, inka gudar masa da ‘ya” 

Haka suka cigaba da hira, ya rakata har kofar part din Anty fido, sannan ya koma. 

Tana shiga part din tabi ta babban parlour, bakowa a ciki ta nufi makwancinsu, tana shiga Hanan ta kalleta tace “daga ina haka?” 

“Naje cikin gida ne, Yaya Yusuf yasakani aiki” Hanan bata kuma cewa komai ba, Maimakon su kwanta suka zauna sukayi ta hira, seda suka raba dare sannan kowacce ta nemi guri ta kwanta. 

Washegari yakama ranar daza’a fara biki, ranar ne za’ayi kamu, iya mata da yamma, ko Angwaye bazasu gurin ba, iya mata ne a gurin kamun, , a wani katafaren dakin taro,

karfe biyar na Yamma, Amare suka iso dakin taron sanye da shiga irin ta fulani, Suka fito a ainihin usulinsu na fulani, ‘yan matan ma, duk kayan fulani suka sa, se manyan iyaye da suka saka Atamfar anko na kamu, karshen haduwa kam sunyita ba’ a magana, Sunyi kyau, Amara kirjin biki ma wato Jalila tayi kyau, ammata simple make up, gashi anmata ado da gashin kanta, sosai kayan suka karbeta, Anyi raye raye, anci an sha, an lika kudi, anyi hotuna da ‘yan uwa da abokan Arziki, anyiwa Amare kamu, ba’ a tashi daga gurin ba se karfe goma na dare, motoci sukazo suka kwashesu zuwa gida. A motar Ahmad Jalila ta koma gida, Jalila banda motar Jalal bata taba hawa motar wani ba se Ahmad, suna tafe yana yaba irin kyawun da tayi. Da suka koma gida ma a idon Jalal suka dawo, Jalila tayi kyau se hirarsu suke ita da Ahmad. 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Tunda suka koma, Jalila bata tsaya tabi takan kowa ba, ta tafi part dinsu, Mummyn Hanan ce tazo ta samesu a dakin da suke zama, tace “Kuyi maza kuzo, Uwar mijin Nana tazo, kuzo muje ku gaisa” 

(wato Salma uwargidan daddyn Hanan) 

Jalila najin haka tace “nima bari in biku” 

Ko kayan basu canza ba, suka bi bayan Mummy. 

Koda suka shiga masaukin da’aka bawa Maman Mahmud kamshin turare ne ya gauraye dakin, tana zaune akan kujera, Jalal na zaune a kusa da ita, se wasu ‘yan mata, da kuma Antyn Jalal tana salla, da alama hira sukeyi da Jalal, kamarta daya da dan nata Mahmud, haka kuma tana dan yanayi da Jalal din, suka shiga da Sallama, ta dago cikin fara’ a ta amsa, Mummy Hanan tace “to Hajiya Salma ga yaran naki nan, sune Amaren” 

Ta kallesu daya bayan daya, ta kalli Nana tace “ga sirikar tawa nan, ita nasan ta ai” 

Sukayi murmushi suka durkusa suna gaisheta. 

Jalal ya kalli Jalila tayi kyau sosai, Se murmushi takeyi, Hajiya Salma tace “Jalila baki sanni ba ko?” 

Jalila ta Kalle ta ta jinjina mata kai, Hajiya Salma tace 

“ni na sanki ai, kamar ki daya da mamanki, Amma kuma kusan duk kamaninku daya keda Amaren” 

Jalal ya juya harshe sukayi magana da Hajiya Salma. 

Nan ta shiga yi musu Nasiha akan Aure, da mahinmancin biyayyar Aure. Tana cikin yi musu ne Maama ta shigo, ta kawowa Hajiya Salma Abinci, nan suka hadu aka cigaba da yiwa Amare nasiha, Jalila kam ta kame tana sunkuyar da kai sekace itace Amarya. Jalal ma yana kusada Hajiya Salma ake musu wannan fadan, ko a jikinsa, be kula Jalila ba haka itama bata kulashi ba, tsakanin ta da shi se kallo. 

Jin da Jalila tayi Hajiya Salma tana bayani da manyan bakake, Mummy Hanan ba ruwanta suka dinga yiwa amare fada, da koyar dasu zaman takewar Aure, ba shiri Jalila ta mike zata fice, Maama tace “Ina zaki kuma?” 

“Amm… Zanje inci Abinci yunwa nakeji” 

Sosai Jalila ta bawa Hajiya Salma dariya, 

Tace 

“dawo ki zauna, ina da magana dake dama” shiko gogan har akayi aka gama ba inda yaje yana zaune, daga karshe ma Abincin da aka kawowa Hajiya Salma ya zuba yafara cin Abunsa. 

Yadda Jalal yake wa Hajiya Salma kamar irin dan Autan nan nata, kuma ga dukkan alamu tanaji dashi. 

Seda aka gama yiwa su Nana fada, Aka sallamesu amma tace Jalila ta tsaya, suka tafi Maama ma komawa tayi, dan Akwai Ayyuka sosai a gidan, Maama na fita Jalal yabi bayanta, yace dan Allah yanaso a bashi tea. 

Ya rage daga Jalal se Mummyn Hanan, Jalal da Hajiya Salma. 

Hajiya Salma tace “Jalila me dana yayi miki ne?” 

Jalila ta kalleta da alamar bata gane ba. 

Hajiya Salma tace 

“ABDUL JALAL mana babban dana kuma ďan Auta, kince bake ba shi, me yayi miki ne? Ba laifinsa bane, nasani laifin Mummyn sa ne, Amma kiyi Hakuri, Daughter Jalal yana jin maganar ki fiye da yadda kike tunani, Jalila Taimakon Rayuwar Jalal kike, Jihadi kikeyi, Allah ne kadai ze biyaki, karki duba abunda mutane zasu fada, kedai kiyi dan Allah, duk yadda muke da Jalal bana masa fada, idan nayi masa fada se yafara gaba dani ko wayarsa na kira baze daga ba, Amma da yake Allah ba yadda baya lamarin sa, kinga dake da Jawwad, musamman ke yanajin maganar ki, ban san me kikayi masa haka yake jin maganar ki ba” tai maganar cikin zolaya, sannaan tace

“Naji dadin ganin cigaban da aka samu a rayuwarsa ta bangarenki, ko danginsa babu wata wadda yake sakewa da ita kamar ke, yana jin maganar ki dukda shirin naku na Tom and Jerry ne”

Jalila ta sunkuyar da kai, Mummyn Hanan tace 

“gaskiya nima yadda na lura da shi, baya son. Mutane sam, mussaman ranar da suka je mana can Kaduna, Amma dukda haka a nutse yake”. Hajiya Salma tace  

“Wallahi sister badan kaddarar Rayuwa da ta faru da shi ba, yarona mutumin kirki ne, ki tambayi Jawwad kiji, Wallahi banga abunda bazan iya mallakawa Jawwad ba saboda dawainiyar da yayi dashi ba” 

Mummy tace 

“ke kika haife shine?” 

Hajiya Salma tai murmushi tace

 “Dan ex-husband dina ne?” 

Zare ido Mummy tayi “Haba dai, duk abun nan bake kika haifeshi ba?” sukayiwa Jalila nasiha sannan, Hajiya Salma ta sallami Jalila, sannan suka cigaba da hira ita da Mummyn Hanan. 

Tunda Hajiya Salma tazo, duk abunda take bukata sedai ta kira Jalila, duk inda zatayi kuma seta kira Jalila, kamar dama can sun san juna, Mafi yawan tattaunawarsu akan yanayi na Rayuwar Jalal ne, Sosai Hajiya Salma taji kaunar Jalila a ranta, Jalila tanada biyayya, da girmama mutane, ga kuma namijin kokarin da take akan yaransu Jalal. 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Washegari yakama ranar daza’ayi dinner, tun safe ake shiga ana fita a gidan nan, gida yacika da mutane,

Shabiyun Rana Siyama ta iso itads ‘yan uwanta, Labari na ishe Jalila Siyama ta karaso aids gudu ta nufi cikin gidan tana zuwa suka Rungume juna, Maama tace

 “Jalila kiyi a hankali, karki ji mata ciwo mana” 

Jalila tace “Siyama ta, dama zan kuma ganinki?” 

Siyama tace “gani kuwa kin ganni” Jalila ta janye Siyama, Zuwa bangaren Anty fiddo, Hanan Ma na ganin Siyama ta rungumeta itama tace “Na dauka tun ranar kamu zakizo, Amma shine baku zoba se yau” 

Siyama tace “Ai muma munyi kamu da party a can ne, saboda wanda bazasu samu damar zuwa nan ba” 

Suka gabatar da Siyama ga Nana, dan  basu san Juna a zahiri ba, Amma sukanyi waya saboda Jalila, 

“Nana tace, Sannu da zuwa Siyama, ya hanya?” 

“lafiya kalau Nana, ya taro?” 

“Alhamdilillah” 

Suka zauna suka dinga hira, suka shantake a gurin, suka dinga hira suna tuna kuruciya da shiritar da sukayi, Nan Jalila ta dinga basu labarin Artabun fadanta da Jalal, har lokacin daya taba yi mata duren hayakin taba. Sunsha dariya, Nana sam bata san rashin jituwarsu ta kai haka ba, Amma bata gaya musu fadi tashin da ta dinga da kokarin ganin ya shiryu ba, har labarin su Hannah da Jeje bata gaya musu ba. Suka shantake suna ta dariya. 

Anty Fiddo ta shigo ta samesu a zaune suna hirarsu suna ciye2, kaman karsu rabu, Anty fiddo tace

 “waikuna nan a zaune, kamata yayi ku hanzarta ku fara shiri, ku tafi gurin kwalliyar nan, kar a bata lokaci” seda ta kai aya ta lura da Nana, taana ganin Siyama 

“Tace Amryarmu, gaskiya Abdallah ya iya zabe, Jalila ke Alkhairi sanadiyar kawancenki da Hanan, mun gano ‘yan uwanmu, kuma sanadiyar ki Abdallah yayi mata shima, Allah ya kaimu Aurenki da Ahmad” 

Hanan tayi farat tace

 “ba Ameen ba” 

Anty fiddo tace

“Saboda me?” 

“nifa bana son Auren ta da wannan Yaya Ahmad din wallahi, matarsa bata da mutunci, wannan Ameeran tab, ni wallahi bana son Auren su” 

“ina ruwana da rashin mutuncin matarsa, dai dai da ita nake, ai dani ze zauna ba dake ba” 

Siyama tace 

“Nikam Jalila ina Jalal, ina son in ganshi” 

Tsaki Jalila tayi tace “ina nasan inda wani Jalal yake” 

Hanan tace “Karya takeyi, yana nan Haidar ya gayamin, suna tare” 

Nana tace “Too Siyama kema kin san Jalal, ai dole ki ganshi, nasan watakila anjima yaje gurin dinner zaki ganshi” 

Anty fiddo tace “kunga abar surutun nan haka, ku tashi ku fara shiri” 

Haka su fara shirye2, karfe hudu suka tafi gurin kwalliya. 

Karfe tara na dare Jalila tana tareda Amare an musu kwalliya me daukar hankali, kayansu iri daya, sea green din material, da takalmi da purse, Jalila kuma tasaka blue-black na material kaman yadda shine yazama ankon dinner, Tasaka bakin takalmi da jaka, jikinta babu mayafi, Su Jalila ne ‘yan shigo da Amare, masu shigo da amare kowacce gefenta da namiji da, Amare da Angwaye, Jalila Ahmad ne a gefenta, suka shigo da Angwaye, ana musu hotuna tareda likin kudi, suka kai su har kan high table, nan aka tsaya aka fara hotuna, Ba zato ba tsammani Jalila taga Jalal, sanye da shaddarsa coffee colour, me tsadar gaske, ta sha aiki da bakar hula da takalmi sau ciki, tsinstiyar hannunsa dauke da wani dankareren Agogo, fuskarsa ba yabo ba fallasa, ya durkusa gefen Jawwad yana masa magana a Kunne, nan aka shiga hotuna ‘yan uwa da abokan Arziki, Jalila anyi hotuna da ita ba Adadi, nan Hanan ta nunawa Siyama Jalal,

Siyama tace “Yadda Jalila ke masa rashin mutunci bazakace haka yake ba, hadadde dashi” sukayi dariya 

ba karamin kyau Jalila tayi a idon Jalal ba, Amma ganinta ba mayafi yasa duk yaji ransa ya baci. 

Nan aka fara gudanar da taro kaman yadda aka tsara, dukkan bangarorin sunyi bajinta gurin lika dukiya kaman ba’a san dadinta ba, Hajiya Salma ba’a barta a baya ba gurin yin wannaan hidimar, tunda ta hau kan stage  Jalal ya fito ya dinga lika mata kudi, kamar be san ciwonsu ba. Aka dinga mata kirari, ko Mahmud da ta haifa bata masa likin da tayiwa Jalal ba, ta koma gefe, takira Jalila tasa me hoto ya dinga daukarsu hoto itada Jalila da Jalal. 

Hakama Sunsha hotuna Jalila da Maama, Jalila tayiwa Maama likin kudi sosai ta dinga rungumeta suna hoto a wayar Jalila, kamar ba Maaman da take gallaza mata ba. 

Lallai halayar Jalila daban take, sam bata riko. 

Aka jima M. C ya kira Amare da Angwaye kan stage, suna dan takawa, yasaka wakar da Jalila ke matukar so, dan haka stage din nan ba kowa se Amare da Angwaye, Jalila ta fito, tafara Rawa itada  Su Hanan Jalila Rawa take me cikeda daukar Hankali, ba wani girgiza jikinta take ba, Amma ta dau hankalin mutane, Ahmad ya fito ya dinga mata barin kudi, ana musu hotuna. 

Jalal ya kai karshe a bacin rai, Ga jikinta ba mayafi, ga dinkin yayi fitting dinta, gata tubarakallahu tana da diri me daukar hankali bawata rawa take ba, juyi kawai take Amma Jalal ya kule musamman yadda Ahmad ke mata barin kudi, yana mata wani irin kallo, wayar Jalila ce tafara ringing dan haka ta sakko daga kan stage din ta fita daga hall din domin amsa wayar, tana fita Jalal yabi bayan ta. 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Tofa Fans Oga Jalal ya dau Zafi, A tunanin ku mezeyiwa Jalila? 

Nayi muku dogon typing dan haka ina bukatar Comments 

Back to top button