Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 3 Complete Hausa Novel

 

“To wai Yaya mairo me kikeso inyine  yaje ya taho da ita yace anan zatayi Hutu to korarta kikeso inyi ko kuma yazanyi

Kinsan halin Abban su Jawwad yanason Dan uwansa akan yarinyar nan beki yamin wulakanci ba”

Maama tayi maganar cike da damuwa

“Seki hade mata fuska yadda nan gaba in ance tazo miki Gida bazata zo ba akan me azo akoyawa yaranki dabi’un arna kinsan ba kunyace dasu ba har kibarta da danki su kwana daki daya da yarinyarki”

Jikin Jalila a sanyaye ta saki handle din kofar ta koma da baya idanunta na zubda hawaye bazata iya cigaba da jin wannan miyagun maganganun da cin fuskar ba 

Wai itace dangin arna ababen kyama to shikenan su arna ba mutane bane

Kaman wadda kwai ya fashewa a ciki haka taja kafarta ta nufi dakinsu ta shiga ta tarar Nana da wata budurwa wadda batafi sa’arsu ba (wadda sukazo da yaya mairo)

sallama tayi a hankali 

Nana na ganinta ta mike ta rungumeta 

“Oyo yo Jalilana sannu ya jikin”

Murmushin dole Jalila tayiwa Nana Wanda iyakarsa bakinta “

da sauki Nana nasaku wahala sannuku Nagode”

” shhhh meye kuma wahala anan bana son irin wannan zancen gaskiya babu haka a tsakaninmu” 

“To na dena Ashe bakuwa kikayi”?

” baki ganeta ba Sa’ada cefa Yar gidan Anty mero”

“Eyya banganeta bane sannunki”

Jalila tafada 

Sa’ada ta Dan dubeta a yatsine “yawwa sannu”

“Nana bari in Dan watsa ruwa”

“To a fito lafiya kiyi a hankali inda wani abu daba zaki iya ba kimin magana ” Nana tafada cike da kulawa

“Karki damu zan iya komai da kaina”

Towel ta dauka ta shiga toilet dayake toilet din a cikin daki yake

Tana shiga bandakin Sa’ada ta gyara zama cike da gulma 

“Ke Nana yanzu Dan Allah wannan danginsu arna ne?kuma kike zaune tare da ita ko kyamarta ba kyayi?”

A fusace Nana ta kalleta

“Mene haka Sa ada ina ruwanki?

Waima tukuna ubanwa yagaya miki haka karki karamin irin wannan maganar bana so” Nana tai maganar a fusace

“Daga fadan gaskiya se ki kama min jaraba, ai dai kinsan mamanmu bazatayi karya ba ke Yar uwata ce bazanso kishiga wani hali ba ni warin arna ma naji tanayi”

“Ke Yar uwata ce Jalila ma Yar uwata ce ta shi kibarmin daki”

Jalila kam taji komai duk zancen da sukayi taji a bayan kofa ta jingina jikinta tana zubar da hawaye me kona zuciya 

Jiki a sanyaye tayi wanka tafito wankan dabata da tabbacin tafita 

Tana fitowa Nana ta kalli Jalila cike da damuwa zatayi magana saboda tasan taji abinda Sa’ada tafada

Amma Jalila cikin karfin hali da dakewar zuciya tace

“Nanancy yau me za a girkamana ne ne yau?”

“Kinga Jalila Dan Allah………

Jalila katseta tayi ta hanyar cewa

” yau muyi dambu kinsan mutumina ne amma Allah yasa kin iya Dan kinsan nafiki iya girki”

Duk yadda Nana taso suyi zancen maganganun da Sa’ada tayi domin tabata hakuri Jalila taki se ta basar da zancen 

Jawwad kam yakada ya raya Jalal ya bishi suje masallaci yaki yace shi inyaje Gida yayi sallarsa

Haka Jawwad ya tafi massalaccin shikadai

Bayan yadawone yace bari yaje cikin gida yakuma duba Jalila Dan haka ya nufo cikin gidan

Nana ta kalli Jalila tace

“Maama kuwa tasan kindawo”?

“A’a naga tayi bakuwa shiyasa banjeba kar in takuramata” Jalila tabata amsa

” bafa wata bakuwa bace Yaya mairo ce yakamata tasan kin dawo ai “

“Hakane bari inje”

Yana shigowa palourn ya ga Yaya mairo da Sa’ada gefe ga Maama a zaune”Yau manyan baki mukai kenan Anty mairo ina wuni”

“Eh kace haka mana yausha rabonka da gidana baka da zumunci Jawwad Sam wannan halin naka a dangin ubanka ka samo shi Dan mu bahaka muke ba”

Tafada cike da isa

Shikam har ga Allah Jawwad baya zuwa gidan yaya mairo dukda kasancewarta yayar mahaifiyarsa irin matan nanne masifaffu Wanda basa raina abin magana ga ta da mugun Sa ido kuma intana guri kawai so take abinda ta yanke shiza a yi ga shiga abinda ba ruwanta

Shiyasa Jawwad baya kaunar zuwa inda take yanzuma komeye na sako dangin babansa oho?

“To yanzu Dai Allah yabaki hakuri insha Allah hakan bazata sake faruwa ba insha Allah zaki dinga ganina har kigaji da zuwana”

“Kaji dashi dai”

“Maama ya jikin Jalilan kuwa?”

Ya fada cike da kulawa yana basar da zancen Yaya mairo

Maama ta Dan yatsina fuska 

“Wace Jalilan kuma bayan wadda na baroku tare a asibiti “

“Maama to ai tun dazu muka dawo baki ganta bane?”

Har Jalila zata fita daga dakin “

Nana tace tsaya mutafi tare karki fadi a hanya”

“Hh Nana kenan yadda nake jina yanzu ko dambe zamuyi ai sena zaneki yi zamanki bari inje”

Dariya Nana tayi lallai kinji sauki

   “Hmmm kingani ko dan Allah ji yadda yake wani nuna damuwa akanta jikar arna wallahi in baki wasa ba Zainab, yarinyar nan da uwarta se ta shanye miki ya’ya, 

arna ba abun yadda bane karki tona sallar datake ganin idon mutane ne watakila a boye a can inda take ita da uwarta suna zuwa coci”

“Wlh nima bakiga wulakancin da Nana tayimin ba saboda wannan yarinyar hadda in fita in barmata daki”

Sa’ada ta tsoma baki, Sa’ada irin halinsu daya da uwata bata da kunya Sam

Daka ganta zakasan idonta a bude take fuskarta tayi Jawur saboda bleaching

Ran Jawwad ne ya baci matuka

“Haba Anty mairo wane irin cin zarafi ne wannan kuma hada mahaifiyarta wannan…….

” dalla rufemin baki sakarai Wanda besan me rayuwa take ciki ba ina magana kana gayamin wai cin zarafine, Yaya mairo ta katseshi a tsawace

Kingani ko Zainab kinga abinda nake fada miki ko kalli Jawwad ina fada yana fada saboda rashin kunya wallahi ki raba yayanki da waccan Yar arnan in ba hakaba wallahi wataran zaki gansu a church suma

“Kaga Jawwad ta shi kafita jeka”

Maama tafada tana nuna masa hanyar fita

Mikewar nan dazeyi yafita yaga Jalila a tsaye idanunta taf da hawaye alamun taji komai

Girgiza kai yayi yafice zuciyarsa a cunkushe ji yake kaman shi akayiwa wannan cin zarafin

Da gudu Jalila ta dawo daki ta shige bandaki ta rufe kofa 

Abin yabawa Nana mamaki meyafaru haka 

Kofar bandakin tafara bugawa a hankali 

“Jalila meyafaru ne?”

Jalila ta daidaita nutsuwarta tace 

“Ina zuwa”

“OK nagane inkin fito ga abincinki nan”

Nana tafada 

Itakam Jalila gefen bath ta zauna ta dunga zubarda hawaye masu kona zuciya 

  Why meyasa akemin wannan cin zarafin nida ummina ake kiranmu arna naga dai ba Wanda zece kaf zuri’arsa tun saga farkonsu har karshensu musulmaine,

  Ummi meyasa kika auri abina kika haifeni, tun tasowata dangin mahaifina kemin wannan cin zarafin har yanzu basu dena ba yaushe wannan abun ze kare,

Wasu zafafan hawayene suka cigaba da zuba daga idonta 

Bata san tsahon lokacin data dauka a bandakin ba tana wannan kukan har tagaji ta fito, 

Ta canza kaya ta dai daita nutsuwarta ta fito palourn,

Yaya mairo basu tafi ba 

Nana tana parlour tana karanta wani English novel “the wish”

Maama kuma tana kitchen

Kaman kullum har kasa Jalila ta tsuguna 

“Anty ina yuni”

“Lafiya “

Shine abinda ta fada a wulakance

Tashige dakin maama zatayi salla

Jalila kuwa seta nuna ko a jikinta

Nana ta kalleta 

“Ashe Allah yayi miki fitowa daga bandakin, sekace me haihuwa kika shiga kikayi tsit”

Murmushi Jalila tayi

“To wayasani ko itan nayi”

Sa’ada kallon Jalila  tayi a wulakance 

Ta tabe baki 

“A gurin arna haihuwar shege a bandaki ai ba sabon abu bane”

Sa’ada tafa da 

A fusace Nana ta dago zatayi magana 

Jalila ta rigata

“Aikuwa dai ba kunya sukeji ba tunda basa kunyar su raini cikin shege su Haifa su rains

wasu kuwa zubarwa sukeyi

Kinga, gara laifin arna Dana muna musulmi Wanda yasani ya take kodayake wasu aisunan ana musulin cine ba asan ma’anarsa ba”

Tana gama fadin haka ta shige kitchen gurin maama

“Sannu da Gida maama”

“Yawwa ya jikin “

Maama tafada cike da basarwa

“Naji sauki akwai abinda zan tayaki ne”

“A’a jeki abinki”

A parlour kuwa Nana ce ta dingayiwa Sa’ada dariya tace gobe ma kikuma in baki yasan meze fada besan abinda za a mayar masa ba

Jalila kuwa daga kitchen din nan harabar gidan ta fito ta dauki kujera ta tafi gaban flowers ta zauna,,

Tanata tunani zuciyarta sam ba dadi, ga wani Abu da ya tokaremata a kirji Wanda tasan Bacin Raine, gashi rabonta da abinci tun Wanda taci da safe a asibiti Wanda Nana takawo mata dazu bataci ba ko yunwar bataji, saboda Bacin rai

taga hakan baze fishsheta ba dan haka tafara rera karatun Qur’ani cikin sauti me dadi

A hankali taji zuciyarta tana sanyi yanayin yayi mata dadi ga yammaci ga flowers din na dauke da furanni masu kyau Dan haka taci gaba da karatun cike da jin dadi da kwarin gwiwa

A hankali take jin taku ana tahowa inda take bata waigaba kuma bata dena karatunta ba

“Masha Allah “

Taji muryar Jawwad yafada seda ta kai karshen ayar sannan ta tsaya 

Ko ba a gayamata ba tasan tare yake da mayennasa wato Jalal saboda taji kamshin turarensa

Gabanta ya zagayo ya tsugunna

“Dafatan ban katseki ba ya sayyada?”

Jawwad yafada

“A’a  yayana, sannu dazuwa”

” cigaba da karatunki”

“Ai na idar dama Abeena nakewa Allah ya kaimasa ladan kabarinsa,

Babban abinda zamuyi idan iyayenmu na Raye shine muyi musu biyayya kar mu yadda muyi sa’insa dasu ko mudaga musu murya,

Fushinsu masifa ne a rayuwar mu, tunda bamu ISA mu biyasu ba dawainiyar dasukayi damu ba, in sun rasu kuma muyi musu addu’a saboda bamu da tamkarsu”

“Wannan gaskiyane sister lyk no other ina alfahari dake”

Lallai yarinyar nan kullum in muka hadu seta gayamin bakaken magana waini zatayiwa wa’azi

Kijira zakiga yanda zanyi maganinki a karo na gaba

Jalal yayi wannan maganar a zuciyarsa

“Jalila nasan kinji abinda Yaya mairo tafada amma Dan Allah………

” shhhh ni banji komai ba Yaya kamanta kawai” Jalila tayi maganar tana murmushi

“Kai ni nagaji malam Kasan banason jira ka ta shi muje kabani abinda zakabani in tafi seka dawo ka cigaba da shirmen”

Hakan yayi dai² da fitowar su Yaya mairo Maama tayo musu rakiya

“Zainab Dan Allah dubi danki kalleshi ga yadda ya gurfana a gabanta, kaman zata masa gafara wannan shegiyar yarinyar in baki da mataki akanta ba setasaki kika,

Wannan yaronnaki yadda yake rawar kai akanta seta dilmiya shi”

Jiki a sanyaye Jawwad ya mike ita kam Jalila sunkuyar da kai tayi 

“Bahaka bane Anty mairo ina mata sannune”

“Ubanka kake mata ba sannu ba wadda kayi mata a asibitin bata isa ba sakarai kawai ka wani gurfana a gaban ta sekace uwarka”

  Shikam Jalal tuni ransa ya gama baci yana kuma jinjina hakurin Jawwad da shine wallahi babu matar daze tsaya tana masa masifa haka

“Dan Allah Jawwad kaje kabani in tafi nagaji Kasan bana son tsayuwa kuma wannan matar tazo tanawa mutane hayaniya da shirme aka zata sawa mutane ciwon kai

JALAL  yayi maganar cike da masifa

“JALAL itama mahaifiya tace fa yayar maama ce”

Sakin baki Yaya mairo tayi tana kallon ikon Allah

Itakam Sa’ada ganin JALAL seda gabanta tayi mummunar faduwa

Maama tayi shiru saboda bata shiga shirgin abotar su tasan halin JALAL sarai

“To ni Ina ruwana kai ka taba ganin me uwa biyu 

Dalla ka tsaya ana zaginka haifarka tayi meye na zaginka dan tana yar mamanka  haka akeyi?”

“Wannan Dan iskan fa daga ina”

Yaya mairo tafada tana kallon Jawwad

“Emm da…

” magana nake maka kana kame² nace wannan Dan iskan yaron Mara mutunci daga ina Zainab magana nake kunyi shiru kuna kallona”

Itakam Jalila silalewa tayi tabar gurin

JALAL yazo gaban Yaya mairo yatsaya “

fadi da kyau ni dan iska ne Mara mutunci, amma kinfini kama dasu tunda kema kin haifi dan iskan boye da bakowa yasan shiba

Dafa kafadarsa Jawwad tayi

“Bros Dan girman Allah kayi shiru mana Yayar uwata  ai uwace ai yakamata kaimin kara” yafada jikinsa a sanyaye 

“A’a kyaleshi yacigaba da zagina”

Tafada tana zare ido

Jalal ya kalli Jawwad 

“a ganinka duk wannan ba kara nayi makaba,

kai kasan in wanine yagayamin haka da wani zancen ake ba wannan ba

Dalla cikani” ya fizge hannunsa yayi waje

Da kyar Maama ta lallaba Yaya mairo ta tafi se zage² takeyi

Yau dai ansha drama a gidansu Jawwad

Jalal kuwa yana zuwa Gida  dakinsa  ya yatafi 

“Mtseww munafukar mata waini ne Dan iska itama fa tanada yan iskan nan amma ta zageni, wallahi badan Jawwad ba da yanzu hakoranta se dai asaka ranar Samata na roba”

Haka yaita surutai shikadai wayarsa ce ta fara ringing 

Dagawa tayi yasaka a kunnensa 

“To ina zuwa”

shine kawai abinda yafada, ransa duk a bace yake yau, haka ya fito ya nufi cikin gidan

Ilham ce tai sallama ta kaiwa Jalila wayarta da ta Yar a gidansu lokacin data fadi

Sannan taga yamata cewar baban Jalal yana kiranta

“To Allah yasa ba laifi nayi masa ba”

“In munje kya gani”

Ilham tabata amsa

“Nana zo muje ki rakani”

“A’a aiki zatamin sekace za akamaki kije ki dawo”

Maama tayi maganar a takaice

Daddynsa ya tarar da mummy a zaune ba sallama balle gaisuwa fuskar nan ba fara’a 

“Daddy gani”

“Yawwa Dan albarka dama magana nakeso muyi, mummynka tace ka dena zuwa makaranta, kuma wai Dubai zaka tafi? Ya akayi ne?”

Wani mugun kallo yai wa mummyn

“Eh hakane Dubai nakeso in tafi

“Karatun fa mummy tafada a fusace

” bazanba” yabata amsa

“Kaji ko? hakafa nake fama dashi bayajin maganata baya ganin girmana,

Wallahi Jalal kar ka bari ka mutu baka dena abinda kake kana sabamin ba”

Su Jalila tun dazu suka shigo suka tarar  ana wannan fafatawar

Mikewa yayi ya nufi hanyar fita yana masifa idonsa Jawur 

“Ni akayiwa laifi ni yakamata anemi yafiya kece silar komai amma kin rufe idonki laifina kawai kikegani ni akayiw laifi kuma kece kika jamin duk wata kalar rayuwa Dana keyi”

JALAL Yayi maganar cikin karaji

“Bazaka taba canzawa ba, ba adagawa iyaye murya, ba a sa’insa dasu

Amma kai hakan ba komai ne a gurinka ba, ta Yaya zakaga haske a rayuwarka

Se mutane sunce Baka da tarbiyya kaji haushi, anya kanaso kagama da duniya lafiya?”

( Jalila kenan damusar kwali ga tsoro ga ban tsoro)

Aikuwa gadan² JALAL ya nufi inda take idonsa babu alamar tausayi.. 

Gadan² yanufi inda Jalila take,

Kasa kwakwakwaran motsi Jalila tayi, ta kuramasa ido jira kawai take taga hukuncin daze mata

  kawai se ya canza shawara ya koma ya fice daga palourn 

Ajiyar zuciya Jalila tayi dataga be mata komai ba

Ilham ta kalli Jalila cike da bacin rai 

“Waike Dan Allah meyasa kika fiye shishshigine ina ruwanki da shi wannan fa sabgar family ce meye naki a ciki Yar karere”?

Jalila ta kalleta tai maganar kasa²

“Hmm so hana ganin laifi”

Daddyn Jalal ne yayi gyaran murya yace 

“A’a Ilham abinda yayanki yake baya kyautawa abinda takwararsa tafada gaskiyane se dai muyi masa fatan Allah ya shiryeshi”

Wani dam kirjin Ilham yayi takwararsa kuma?

Tai maganar a zuciyar ta

Jalila ta karasa cikin palourn ta durkusa har kasa ta gaishe da daddyn Jalal

Mummy kuwa tuni tabar palourn ranta yana daci game da abubuwan da Jalal yakeyi Sam baya ganin kimarta a matsayinsa na Dan da ta haifa

Fuskarsa a sake ya amsa mata gaisuwar

“Jiya ake gayamin baki da lafiya har an kaiki Asibiti, dazu mummyn su zata je dubaki da safe akace Baku dawo ba, 

“Yanzu ya jikin naki”?

” ai naji sauki daddy “

Tayi maganar kanta a kasa

“To dama kiran kenan in miki sannu

Ya gurin mamanki ?”

“Tana nan lafiya”

“Masha Allah kin dawo nan ne gaba daya”?

“A’a zuwa nayi nakusa komawa”

“Allah sarki in kin tashi tafiya kizo muyi sallama kafin kitafi”

“To daddy nagode”

“Yawwa Allah yabaki lafiya”

“Ameen”

Ta amsa 

“To daddy seda safe”

“Allah ya tashemu lafiya daddy nagode”

“Ameen Yar albarka 

Allah yayi miki Albarka”

“Ameen ta mike ta nufi hanyar fita”

“Daddy dama kasanta ne?”

Ilham tafada tana ya mutsa fuska

“Nasanta Ilham amma tun tana Karama nasan mahaifinta kanin Alhaji Mahmud ne (baban su Jawwad) mutumin kirkine sosai”

Dan tabe baki kawai Ilham tayi

Jalila kam kama hanyar fita tayi

taji an riketa a firgice ta waiwayo taga waye da wannan aikin 

Jalal tagani idon Sa Jawur yana wani irin huci 

Ya daga hannu ya wanka mata mari, ta gigice tana nema ta fadi, ya dagota yakuma wanka mata wani Marin

Hannu biyu tasa ta dafe fuskarta lokaci guda kuma hawaye na zubowa daga idonta,

“Why meyasa kike son shiga rayuwata?

Ina ruwanki dani?

Sa’anki ne ni ko dankinga ina kyaleki  saboda yayanki nake daga miki kafa, amma ki tambayeshi waye ABDULJALAL!!!

ba a shigowa hanyata duk Wanda ya shiga rayuwata se na tabbatar Dana koya masa darasin da har ya mutu baze manta ba,

Kifita daga rayuwata nagaya miki sha³ kawai I hate u!!!”

Yafada yana kuma zazzaro mata ido 

“Bazan fita ba, in har bazaka rabu da yayana ba kuma bari in gayamaka baka isa kamin abinda Allah bemin ba”

Ta fizge hannunta tai tafiyarta fuskarta na cigaba da radadi saboda Marin ya shigeta seda tai gaba ta tsaya ta waigo ta kalleshi

“Ka rubuta ka ajiye Marin nan dakayi min seka biya shi kuma na fada Mara tarbiyya, in kaji haushi kadena abinda kake, sannan ka koma makaranta Dan wannan abinda kake ba alamar Ilimi a tare da kai in kaga dama ka yayyankani ka cinye I hate u too,

Tai ficewarta ta tafi Gida, harta shiga gidan, ta tafi dakinsu bata ci karo da kowa ba,

Nana ma bata dakin, dan haka ta dau wayarta da Ilham ta kawo mata dazu 

Missed calls din Ummi tagani a ciki dayawa sekuma na kawarta siyama

” Allah sarki Ummi na nayi missing dinki, dole ma inzo in tattara kayana in bar garin nan tsakanin Jiya da yau nayi Dana sanin zuwa kano ga cin zarafin da wannan matar tayimin, ga kuma wannan Azzalumin Dan shaye² da yakeneman illatani

In na tafi bazan sake zuwa kano ba insha Allah gobe zanyiwa Abba magana ni Gida zan koma”

Tai dialing lambar Ummi bugu biyu ta dauka

“Jalila meya faru nake ta kiran wayarki tun jiya da daddare amma baki daga ba?”

Ummi tayi maganar cike da damuwa

“Ummi wayace a silent kuma na manta inda na ajiyeta se dazu na ganta”

“Jalila akwai matsalane? Naji muryarki wani iri, ko baki da lafiya ne?”

“A” a lafiyata kalau mura nake ne”

Badan Ummi ta yarda ba ta bar zancen

“Ya gidan ya yan uwan baki?”

“Kowa lafiya Ummi”

“Ina fatan ba wata Matsala dai ko?”

Matsala kam akwaita very soon ma zan dawo Gida amma a zahiri se cewa tayi

“Eh babu wata matsala amma a satin nan zan dawo Gida insha Allah”

“Kin fasa hutun a nan ne?

” Eh nafasa kewarki ce ta dameni Gida zan dawo “

Ummi ta fuskanci akwai matsala Jalila bata son gaya mata ne.

“To shikenan se da safe ki gaida mutan gidan naku”

“Zasuji insha Allah, mu kwana lafiya kyakykyawar uwa”

“Ameen yar albarka”

Tagama wayar kenan Sega Nana ta shigo

“Yar uwa kin dawo Ashe ? Kiran me akayi miki ince ko lafiya”

“Lafiya kalau, dama babansu Jalal ne yamin ya Jiki, sannan yace ranar dazan tafi inzo,”

  “Allah sarki babansu Jalal akwai kirki kaddarace tasa Allah ya hada shi da tantirin da, kodayake yana Dan ganin girman babansa akan mummyn shi”

“To Allah ya shiryeshi in me shiryuwane”

Jalila ta fada tana mikewa domin ta gabatar da sallar isha’i

Bayan sun kwanta Jalila takasa bacci se Juyi take kanta har ciwo yake saboda zafin Marin da ta sha

“NI KIKAYIWA LAIFI YAFIYATA YAKAMATA KINEMA BANI ZANNEMI YAFIYARKI BA KIN SAN GASKIYA AMMA KIN RUFE IDO KINAMIN FADA KECE SILAR KOWACE RAYUWA NAKE A YANZU”

Maganganun Jalal suka dawo mata To me hakan ke nufi lallai akwai wani abu a kasa

Wai meyasa duk lokacin dazan hadu da yarinyar nan se tayi abunda zata konamin rai, seta gayamin maganganun dazasu bata min rai 

Meyasa ta kenema ta Shiga rayuwata, ba Wanda ya isa ya tsaya gabana yana gayamin abinda ya gadama,

Ina daga mata kafa ne saboda aminina,

Ire iren wannan tunanin Jalal ya dingayi ga mummy itama ta caza mai kai ransa yagama baci zuciyarsa a cunkushe 

Dan haka ya yanke shawarar abinda ze fishsheshi Dan haka ya dau motarsa ya tafi mashaya gurin Jeje.

Jawwad ganin abinda yafaru dazu tsakanin Yaya mairo da Jalal yasan 

Jalal fushi yake dashi Dan haka ya yanke shawarar zuwa yabashi hakuri.

Yaje part din Jalal amma bayanan, yashiga cikin gidansu nan ma bayanan

Ya dinga kiransa a waya amma shiru be dauka ba.

Dan haka ya koma Gida har ya kwanta yaji yanaso yasan inda Jalal ya tafi.

Danhaka ya kuma komawa gidansu Jalal don ya duba ko ya dawo,dayake Jawwad yana shiga gidansu Jalal koda yaushene tunda iyakacinsa, part din Jalal be fiye Shiga cikin gidanba se da dalili

Dan haka Jawwad yanazuwa me gadi yake bude masa ya shiga Dan shima Dan gidane.

Har yanzu Jalal be dawo ba

Har had JAWWAD  ya juya ze tafi, seyaga kawai so yake yaga Jalal yaji inda ya tafi haka

Jeje kuwa yakara ingiza Jalal ya dinga tuttulawa Jalal giya, se dayaga yayi mankas ba iya komai ya dauko shi yasahi a mota yadawo dasshi gida.

Rungumo Jalal Jeje yayi ya shige dashi part dinsa saboda Sam Jalal baya hayyacinsa tangadi kawai yake

Tunda Jawwad yaji karar motar Jalal yafito kofar part dinsa ya tsaya yana jiran Sa amma seyaga Jeje rungume da Jalal ko ba a gaya masa ba yasan Jalal a bige yake, Jawwad be kulasu ba,

Hanya yabasu Jeje ya wuce da Jalal bedroom dinsa ya kwantar dashi, yazo fita Jawwad yasha gaban Jeje 

“Me kabashi?sannan daga ina kuke?”

Yayiwa Jeje tambayar ransa a bace

Jeje ya kalli JAWWAD a wulakance 

“Wane irin tambaya ne wannan? Kaima kasan me yasha giya CE meye kuma na tambayata ina mukaje ai kasan inda yake zuwa

” kashedi nawa nayi maka game da Jalal, kai kake kara hure masa kunne meyasa kake bibiyarsa haka?

Why? “

“Bani yakamata in baka wannann amsan ba kajira lokaci”

Daga haka jeje yasa kai yai ficewarsa

Jawwad kuwa ransa a bace yashiga bedroom din, Jalal ya tarar yana ta bacci, hade da surutai cike da maye

Girgiza kai kawai Jawwad yayi Allah ka shiryi bawanka Allah ka nunamin Jalal yazama mutumin Arziki.

Washe gari da safe iyalan gidan sun hadu a palour suna karyawa, kowa ya maida kai yanacin abinci amma banda Jalila wadda taketa juya cokali tana cakalar abincin JAWWAD ne ya kalleta 

“Lafiya kuwa sisy ba kyacin abincin fa ko akwai damuwane?”

Jawwad yafada cike da kulawa

“Nima na lura da hakan bros tun jiya naga bata walwala”

Nana ta fada tana kallon Jalila

Maama kaam Dan kallonta yayi ta tabe baki ta cigaba da cin abincinta

“Duk Ku tsaya Yar albarka gayamin meke faruwa ne”?

Abba yafada cike da kula yana kallon Jalila

Hawaye ne yazu bo mata Wanda bata San zasu zubo ba,

” subhanallah Jalila meyafaru, me akayi miki”

Suka shiga hero mata tambayoyi

Jimin munafukar yarinya wayamata wani abu dazata kama yiwa mutane kuka kalli yadda duk suka bats attention lallai maganar Yaya mairo akwai kamshin gaskiya

maama tayi zancen a zuciyarta

Gaba daya attention dinsu ya dawo kanta suna mata tambayoyi

“Abba ni Gida nake so in koma”

Tafada a hankali

“Wani abun mukayi mikine?”

Nana tafada kaman zatayi kuka

“Kunga Ku tsaya, Jalila anyimiki wani laifinne in wani abun mukayi miki kigaya mana”

Jawwad yayi maganar yana kallon cikin idon Jalila

Abba yayi gyaran murya yace

“Yarinyar kirki meyasa kikeso kikoma Gida? ko mune ba kyasan zama damu”

Girgiza kai tayi 

“a’a  Abba ni ba abinda kuka yimin kawai ina kewar ummi ne, sonake inkoma gurinta”

Maama ji tayi kaman ta kwashe Jalila da mari saboda gulma Dan kawai tanaso takoma Gida shine zata yiwa mutane kuka salon ace wani Abu sukayi mata

(Wato maama taji zigar yaya mairo)

“To shikenan yarinyar kirki yaushe kikeso ki koma gidan?

Tunda kin gaji da zama damu”

“A’a Abba ba gajiya nai da zama daku ba, ba abinda kukayi min,

Gobe nakeso in koma”

Tafada tana sunkuyar da kai

“To kibari ranar juma’a insha Allah se Jawwad ya maida ke gida hakan yayi miki?”

Murmushi Jalila tayi tare da gyada kai

“Shagwababbiya kawai shine seki mana kuka Dan kina kewar Ummi?”

Jalal yafada cikin zolaya

Maama dai batace uffan ba

Haka dai suka kammala breakfast din 

Suna komawa daki Nana ta kalli Jalila

“Jalila me mukayi miki zaki tafi kibarni 

, hutu fa be Kareba

Naji dadin zuwanki meyasa zaki tafi ki barni”?

“Haba Nanancy na nifa bukuyi min komai ba kawai inaso in komane”

“To yaushe zaki kuma zuwa”?

“Zan kuma zuwa Nana karki damu”

“To shikenan zanyi missing dinki”

Nana ko zan kuma zuwa gidanku se bayan dogon lokaci, idan nacigaba da rabar Ku kiyayyar da mahaifiyarku kemin zata fito fili

Ga wannan azzalumin makocin naku abokin Jawwad

Amma a zahiri se ta rungume Nana

Karki damu Yar uwata I will miss you too

Ran Alhamis da daddare Shirin komawa Gida sosai Jalila takeyi ta hada kayanta cif ji take kaman ba itaba zata koma Gida gurin umminta 

Nana ce  ta raka Jalila gidansu Jalal domin tai musu sallama,

Ilham suka Tatar tana shirya abinci a palour

Kaman kullum Ilham se hararan Jalila takeyi kuma har Jalila tai kwanciyar Asibiti bata taba cemata ya jiki ba

“Gurin mummy mukazo ba gurin Jalal ba naga kina hararata”

Jalila tafada  da sigar Neman magana

“In ma gurin nasa kikazo biki isheshi kallo ba Dan ba macen dayake gani bayan Ilham”

Ilham tai maganar cike da tsiwa dakuma gadara

Aikuwa Jalila tafara dariya 

“Shi Jalal dinko, yanzu akansa kike wannan abun hh wani jan idonsa kaman ansa masa tear gas”

Jalila tai maganar tana dariya

Iya kuluwa Ilham ta kulu amma kafin tayi maganar Nana tace

“Dan Allah kuyi hakuri wannan wasannaku karshensa fadane

Ina mummy? gurinta mukazo”

Haka Ilham ta kaisu part din daddy Dan mummyn tana can

Itakuma tadawo palour

Jalila tayi musu sallama  cewa gobe in Allah ya yadda zata tafi

Daddy yace to ta gaida mamanta yayi mata addu’a kuma insha Allah zemata aike haka sukayi sallama da mummy ma

Suna fitowa daga part din Daddy kaman kullum wata dramar ake

JALAL da Ilham se masifa yake zazzaga mata kaman ze dake ta tana bashi hakuri kaman wani ubanta

“Kina abu kaman wata dabba kinfiye naci wallahi inkina da zuciya karki kara zuwa inda nake kokice zaki dafa wani abu kibani, bana so ko ana dolene?”

  Idon Ilham taf hawaye 

  “Dan Allah kayi hakuri Yaya bazan iya dena zuwa inda kake ba”

Aikuwa dariya Jalila ta kwashe da ita

“Tab laila majnun amma gaskiya iska tana wahalar dame kayan kara”

Wannan wace irin mayyar yarinyace tantiriya me bakin naci.

Wannan yarinyar kwai bakar Jarababbiya kome za ayi mata bazata dena magana ba in taga abin magana, kozaka kasheta setayi magana

Kallon ta Jalal ya cigaba dayi yana jinjina bakin taurin kai irin na Jalila

Itakam Jalila dariyarta ta cigaba dayi

“Tab wai akan wannan kike wannan kukan aiki yasamu wata, tab sannufa Ilham kin dorawa kanki wahala wallahi…..”

Jalal kallon Jalila yayi cike da takaici 

Jalal girgiza kai kawai yayi ya fice saboda ya fuskanci in yacigaba da biyewa maganganun yarinyar nan to tabbas bakin ciki ze iya masa illa

“Jalila meye hakane wai ina ruwanki dasu taho mu tafi”

Nana tai maganar tana janyo hannunta 

“Munafukar banza kawai se tsabar shishshigi da Sa ido aikin banza kawai”

Ilham ta fada tana jujjuya Ido

Saboda cusa takaici se Jalila takara tuntsurewa da dariya 

“Allah ya temaki matar Dan giya wannan soyayyar kaman a Bollywood ke kinga wani  kaman ta tsaya agaban director hh mrs. Jalal”

“Na shiga uku nikam Jalila meye haka wai dama haka kike ba dadi fa

Ni dai taho mu tafi”

Nana ta fada tana kuma Jan hannun Jalila 

Ilham kam rasa bakin magana tayi kamewa tayi tarasa abin cewa

Suna fitowa Nana ta kalli Jalila cike da damuwa

“Haba Jalila why? Abinda kikayiwa Ilham be dace ba wallahi bazataji dadi ba”

“Lallai Nana ke bakiga wulakancin da tayimn da farko ba har munafuka tacemin fa”

” haba Jalila da baki kulasu da bazata gaya miki ba “

“Sorry Nanancy kinsan bana gani inyi shirune kawai, in ta kwantar da hankalinta gobe insha Allah zan bar garin nan”

“Jalila dena tunamin banason tuna gobe in Allah ya kaimu zaki tafi duk se inji na damu”

Nana ta fada a sanyaye

“Nima banason barinku amma very soon zan dawo insha Allah”

“Allah yasa da gaske kike”

“Da gaske mana”

Dayake me Hali baya fasa halinsa sukaga Jalal a harabar Gidan yana kokarin bude motarsa

“Wai akan wannan ake kuka, Allah ya kyauta, har ake Neman a zageni gaskiya Ilham Yar wahala CE”

“Na shiga uku ni Nana, Jalila haka kike dama?” 

“Ai ni nafi haka ma duk abinda nasan ba a so ko akemin gadara akansa to nikuma shi nakeyi”

Jalal da ya riga ya shiga mota yana jinsu dayake suna daf dashi tayi maganar shiru yayi bece uffan ba

Sema kokarin tada motarsa da yake

Washe gari da safe Jalila ji take kaman za asa ta a Aljanna yau zata koma gida gurin umminta,

Kuma zata rabu da wannan mugun, kuma se yaya mairo taganta zata kuma cin zarafinta, 

se shirinta takeyi amma  lokacin kanta yana mata ciwo tunda Jalal ya mareta kanta kemata ciwo

Nana tana wanka Jalila ta hada kayan ta cif Jawwad

 ya shigo dakin yasameta tana kallon akwatin ta 

“Yar gidan Ummi kingama shirin kenan?”

Jawwad yafada yana zama a gefen gado

“Eh Yaya nagama”

“To insha Allah in an sakko daga masallaci zamu tafi kizama cikin shiri in ma dawo zamu tafi”

“Aini ko yanzu kace mu tafi na shirya,”

“Eh kyace haka saboda kin gaji da zama damu ko?”

“A’a nifa nace muku bahaka bane”

Ta fada a shagwabe 

“To shikenan naji kar kimin kuka”

Jawwad yayi maganar da sigar tsokana

Daga nan ya tashi ya tafi 

Bayan fitarsa da ba dadewa Ilham ta shigo hannunta dauke da ledar bagco, ta tarar da Nana da Jalila su suna cin abinci suna hira 

Jalila tana ganinta ta sunkuyar da kai tana dariya kasa²

“Mtseww”

Nana taja uban tsaki ta direwa Jalila bagcon a gabanta “gashi nan Inji mummy, sakon daddy ma yana ciki”

Ta fada tare da juyawa zata tafi 

“Haba Ilham kya tsaya kuyi sallama fa yau zata tafi”

“Ta sauka lafiya “

Shine abinda kawai Ilham tafada tai ficewarta

Itakam Jalila ta kudure a ranta seta tsokani Ilham amma tasan in tayi a gaban Nana mita zatayi mata Dan haka se cewa tayi

“Nana ina zuwa”

“Ina zaki?”

“2mint yanzu zan dawo”

Ta biyo bayan Ilham se ta hangeta ta tsaya  tana waya a wajen flowers din gidan

Seta nufi inda Ilham take amma kafin takarasa taji tana waya

“Wallahi mami nafara gajiya wulakancin yau daban na gobe daban Sam Hankalinsa baya kaina jiyama bakiga wulakancin da yayimi ba am tired wallahi”

Jalila Batajin me akace daga daya bangaren

“Hakane mami, Allah ya nuna mana lokacin da burinmu ze cika zan cigaba da hakuri in cigaba da kokari se burinmu ya cika akan Jalal da mummyn Sa”

Buri kuma, Wane irin buri ne haka hasashe na ze zama gaskiya kenan

Jalila tayi maganar a zuciyarta 

Fasa abinda tayi niyya tayi takoma cikin Gida 

Kayan da aka aikomata daga gidansu Jalal taga Nana tana budewa 

Less ne me kyau da agogo se turare da wani Dan karamin kit Ja anyi rubutun larabci a jiki Qur’ani ne izu sitting a ciki me matukar kyau

Se envelope da akasaka kudi dubu goma

A jiki aka rubuta 

safe journey from daddy

“Yanzu duk wannan nawane?”

“Ai Jalila indai kyauta ne babansu Jalal akwai kyauta yana da kirki sosai”

“Nana ni duk Qur’anin nan yafi min kyau bazan dinga bude shi ba ajiye shi zan in dinga kallonsa yayi kyau sosai ajiya zan masa me kyau”

Nana ta kwashe da dariya 

“To ai saboda  ki karanta akabaki shi sekuma yazama abin kallo”

“Eh mana koba komai zan dinga tuna baban zalimu ne yabani”

“Me kikace Jalila?”

“Ba komai, bari inje in nunawa maama kayan”

Zuwa sukayi suka nuna mata ba fuskarta ba yabo ba fallasa tace yakamata taje tayi musu godiya

Sannan itama tabata abinda zata bata

Abba yayi mata nasiha sosai sannan yace university a kano zatayi in lokaci yayi zezo a Dakota daga Kaduna

Jalila ko a jikinta bata dauki abun serious ba ita dai babban burinta taga sun kama hangar Kaduna

haka yaimata alheri shima tare da yimata nasiha akan hakuri da rayuwa ta kula da tarbiyarta sannan tayi karatu.

Misalin karfe biyu tagama shirinta tsaf JAWWAD kawai take jira

after dress ce a jikinta baka se mayafin After dress din data yafa akanta tayi kyau matuka 

Taje gidansu Jalal tayi musu godiya 

Daddyn Jalal shima haka yayi mata nasiha tai musu godiya ta fito taga Ilham ta dawo maybe wani gurin taje

“Juliet INA romeon naki,?

Tafada cike da tsokana

Nikam yau zan koma inda na fi wayo nasan na bata miki a Dan zaman damukayi kiyi hakuri Ilham ni duk abinda na miki wasa ne”

Mtsewww Ilham taja wani dogon tsaki

“Ke kikasani ma gulmaciyar banza kawai”

Ilham ta fada tana ma Jalila kallon up and down

Jalila tayi wani kasaitaccen murmushi

“Nagode Yar wahala nice ma ke, let me tell u something ur mission will fail u will never succeed”

Tafice daga gidan tabar Ilham tsaye tana juya maganar Jalila

“Ur mission will fail”

A harabar gidan taga Jawwad da mayensa 

Jawwad yasamata trolley dinta a boot 

Jawwad na ganinta yace 

“Masha Allah  looking so gorgeous sisyna let’s take a pic”

Kusa dashi Jalila taje ta tsaya sukai ta hotuna hada Nana

Shikam gogan wani uban tsaki ya dinga Ja ganin yadda JAWWAD yake biyewa wannan fitsararriyar yarinyar 

Nana ce ta rungumo Jalila tana share kwalla “Dan Allah kikuma dawowa”

“Insha Allah karki damu Nanancy na zankuma zuwa insha Allah”

Suka shiga Jalila suka kuma sallama da maama sannan ta fito

Jawwad ya Riga ya shiga ya kunna mota yana jira ta karaso ta faki idon Jawwad 

Tacewa Jalal to yau zan tafi se hankalinka ya kwanta bame kumayi maka shishshigi amma zan tuna maka ne ban yafema cin zalina da kaiba mugu kawai kuma insha Allah se……

Bige mata baki yayi 

“Ki barni da Wanda akayi min a baya yake wahal dani, in kika sake kikamin mummunar addu’a a sena baki mamaki

A cikin gidan naku a gaban yayan ki zan tattakaki in koya mini hankali dama namiki alkawarin maida ke Irina amma tunda tafiya zakiyi yayanki zan mayar Irina, in ya aureki se aji dadin fada matar Dan giya

wuce ki bani guri ko in barar dake anan Mara kunya sha³”

Kaman munafuka haka ta wuce tana shafa baki taga ko Jini ya fito

Nana tafito da karfi race 

“Jalila safe journey I will miss u”

Daga mata hannu kawai Jalila tayi ta shiga gaban motar saboda bakinta ji take kaman banata ba

Jalal ne yazagayo inda Jawwad yake dan uwana a sauka lafiya, ka dawo da wuri Dan Allah, akwai wani zazzafan guri dazaka rakani

Jalila ta dago da sauri tana kallonsa 

Allah ka tsaremin yayana

“Ta Allah bataka ba “

Tafada a fili

“Ya dai magana kike ne”

Jalal yai mata tambayar

“Bakina ne a haka tabashi amsa”

“Na fuskanci dai ba kwa jituwa, Jalal ma fa yayankine”

Jawwad  yai magNar yana kallon Jalila

“Allah ya kiyaye”

“Dan uwana ina dawowa zan raka ka insha Allah idan na dawo”

Jalal yafada yafara Jan mortar

“To seka dawo”

Sun hau kan kwalta sosai Jawwad tuki yake a hankali cikin kwarewa 

Jalila tayi nisa cikin tunani

“KE YAKAMATA KINEMI YAFIYATA , DUK WANI ABU DANAKE AIKATAWA KECE SILA,

KINSAM GASKIYA AMMA KIN RUFE IDONKI KINAMIN FADA”

“ZANCIGABA DA HAKURI HAR BURINMU YA CIKA AKAN JALAL DA MUMMYN SA”

“KARKI SAKE KIMIN MUMMUNAR ADDU’A KIBARNI DA WANDA AKAYI MIN ABAYA YAKE WAHAL DANI”!!!!!!

Gaskiya akwai abubuwa masu rikitarwa game da rayuwar Jalal haka nan taji tana son Sani

” sisyna”

“Na’am yayana”

“Nasan abinda yasa kikeson komawa gida, yana da nasaba da abinda Yaya mairo taimiki, Amma Dan Allah kiyi hakuri ki dena bari irin wannan maganganun suna tasiri a zuciyarki kowa yasani dagake har Ummi mutanen kirki ne

Ni kaina banji dadinin abinda tayi ba”

“Yaya na nifa ba hakane yasa zan koma Gida ba kamanta kawai”

“Kin tabbata?”

“Eh na tabbata babban Yaya”

“To yanzu se yaushe zaki dawo?”

“Se wataran”

“Se wataran kuma ba rana kenan”

“Hhh da wataran zan dawo”

“Hmm to shikenan”

Shiru ya Dan ratsa 

“Yaya Jawwad”

“Nana’am Anty JALILA”

Murmushi tayi

“Wadan dan Allah wace Ilham a gurin Jalal”

“Yaya JALAL dai shima yayanki ne”

Allah ya kiyaye Amma a fili se tace

“To naji zan dinga fada”

“Yawwa sisyna 

Yadda muke dake cousins haka ILHAM take da Jalal da mummyn Jalal da mamann ILHAM ubansu daya

Gyada kai Jalila tayi

” to meyasa Jalal yake haka, meyasa kuma ka

ke abota dashi,? Gashi ya raina mamansa kaga abinda yake mata kuwa?

“JALAL ko?”

JAWWAD yafada yana kallonta

“Au namanta Yaya JALAL”

Ajiyar zuciya yayi yace

“Se randa kika dawo kano zan baki amsoshin tambayoyinki”

“Why not now?

Ta tambayeshi

” kawai sekin dawo Kano zan gaya miki ke dai in kinyi sallh kidinga Sa shi a addu’a

Gyada kai kawai tayi 

Amma a ranta cewa tai tabdij nida kano ai seda wani babban dalili 

A gefe data kuma zuciyarta na kwadaita mata son sanin waye Jalal

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Share please

More comments more typing…….

Back to top button