Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 25 Book 2 Complete Novel

Gaba daya sukayi shiru suna sauraranta, tareda kallon mamaki, tacigaba da cewa “Sannan kuma zan tabattar maka da zarginka Nice kuma nasaka aka dauke Jalal ranar birthday dinsa” ta juya ta kalli Suleiman tace “Yallabai gashi nan, ku tambayeshi” 

Suleiman ya janyo kujera gaban gadon Jeje ya zauna, ya kalli Jeje yace “Ya jikin naka dan uwa” da kyar Jeje ya motsa baki yace

“Da sauki” 

suleiman ya gyra zama yace “Inbazaka damu ba, zamuyi maka tambayoyine gaskiya muke bukatar ka gayamana in kayi karya, zamu daukeka a haka mutafi da kai office ka warke a can, mecece Alakarka da mutumin daya yi maka wannan raunukan?” 

Jeje yace “Ubangida nane, ni yaronsa ne” 

“Ubangidanka kamar yaya? Aikin me kake masa, A ina kuka hadu? Yaushe kafara masa Aiki?” Jeje ya juya ya kalli Jalal ya sunkuyar da kai kasa, a fusace Suleiman yace “magana fa nakeyi maka, kabani Amsa kuma in kayimin karya seka gane kuskuren ka” Jeje ya juya ya kalli Jalal yace

“Jalal ina fatan zakamin Afuwa jin abunda ze fito daga bakina, Asalina nidan garin Azare ne, a cikin wani kauye, mahifina ya dakkoni yakawoni Almajiranci lokacin inada kananun shekaru dabasu fi takwas ba, tunda aka kawoni bawanda yakuma zuwa inda nake, balle susan halin danake ciki, sedana shekara goma shahudu sannan naje gida, kodanaje gida mahaifiyata ta rasu, nayi bakin ciki me tarin yawa nadawo kano, Rayuwar Almajiranci Rayuwace me matukar matsi da wahala, ba kula ba Abinci sabulun wanka wanki, balle magani komai kai zakayiwa kanka Rayuwa tayimin Zafi nafara shiga kasuwa domin neman na kaina, na gudu daga makaranta a haka na shiga makarantar boko, a kasuwar nan nasamu aiki a gidan karuwai nake musu aiki, a haka nakoyi shaye2, neman mata tunda kananun shekaruna, Jagaliya da bangar siyasa ba wadda ba’adamawa dani, mun hadu da Alhaji Kabiru a gurin campaign din wani ubangidansa, ninake jagorantar group din jagaliya da ‘yan daba, Alhaji Kabiru ya gayyaceni gidansa da zummar yanaso inmasa wani Aiki zena biyana, na yadda na Amince, ya nunamin hoton Jalal yace akansa yakeso inmasa Aiki, nace kamar yaya, yace soyake Jalal yazama mugun dan shaye2 dan Jagaliya kamar ni, nace masa amma tayaya hakan ze faru yacemin inyi duk yadda zanyi zena biyana duk wata dubu Ashirin, idan har burinsa yacika Jalal ya lalace ze bani wasu kudi masu yawa, Na amince na karbi Adress din Jalal nafara zuwa unguwar su, na lura yanada saukin Kai dayawan kyauta, dukda na girmeshi haka na dinga kokari ina shiga jikinsa, ina turamasa Akidar shaye2, dabe amince ba har sabani muka samu, amma daga baya bansan ya akayi ba ya Amince da kansa, Abokinsa Jawwad yayi kokari yaga ya rabamu amma abu yaki, haka nakoya masa zuwa clubs daban2 kasancewar yanada kudi kayan maye se wanda mukeso zamu sha, Nayi kokarin in koyamasa bin mata amma yaki, sam hankalinsa baya kan wannan shidai kawai yayi shaye2 Alhaji Kabiru yacigaba da biyana makudan kudade kafin daga baya ya nunamin sana’ar dayakeyi ta saida miyagun kwayoyi da makamai ta barauniyar Hanya, idan Jarinsa yai kasa senazo nasan yadda nayi na karbo masa kudi masu yawa a gurin Jalal seyaraba yabani kasona, nazama babban Aminin Jalal, Alhaji Kabiru yasa nadinga Jan ra’ayin Jalal akan mutafi Dubai semunfi holewa acan bame samana ido, mussaman shi da mahaifiyarsa take takuramasa aikuwa ya yadda, shikuma Alhaji Kabiru yahada baki da wasu ma’aikata za’asaka kwayoyi a kayan Jalal, yadda semunje dubai za’a kamashi, idan mukaje dubai aka kamashi da wannan kayan hukuncin kisa ne, Amma abun mamaki se a Airport Jalal yace yafasa tafiyar nan, Saboda Jawwad. Ba karamin fushi Alhaji Kabiru yayi dani ba, yana ganin sakacina ne, da wannnan ya wuce se muka shigo da Hanna wata karuwa cikin tafiyar tamu, Saboda tasirin mace ga da namiji, Amma duk yadda taso ta janyo hankalinsa kanta yaki, Idan yayi shaye2nsa yayi bacci A gurin wataran Jawwad ne yake zuwa ya dauke shi, muka hada baki aka shirya masa birthday party, da nufin cewa za’ayi party ne imu imu abokan shaye2nsa, Amma abun mamaki muka ganshi shida yan uwansa dasu Jawwad, muka shirya idan aka bashi kayan maye a gurin zamu faki idon mutane mu daukeshi, za’a kaishi wani gida da aka kama Hayarsa na wasu yan awanni, Zamu kai Jalal can, a gidan Akwai manyan makamai, Akwai yara kanana da aka hayo aka saka a gidan, Alhaji Kabiru ya saye wasu manyan “yan sanda da kudi, cewar za’azo akama Jalal a wannan gidan, da wannan kayan za’ace an kamashi da miyagun kwayoyi, da Makamai sannam yana safarar yara mata, Amma shima se akasa aka Sace Jalal a gurin party muka nemeshi muka rasa, shima Alhaji Kabiru yai fushi dani da kyar ya hakura, Sekuma karon karshe da Alhaji Kabiru yakamani da ‘yarsa a gidan Karuwai, da muka dau tsawon lokaci tareda ita, Yallabai wannan shine Abunda ke tsakanina Da Alhaji Kabiru ” gaba daya dakin yayi shiru, Jalal cikin Rawar murya da sanyin jiki yace

” Jeje waye Alhaji Kabiru, Menayi masa haka A rayuwa? Laifin menayi masa yazabi ganina a wannan Kazamar Rayuwar?” Jeje yace” Alhaji Kabiru shine mahaifin wannan Abokin naka Faruk, da mahaifinsa ke yawan yimasa kashedi akanka, sannan kuma shine tsohon Saurayin mahaifiyarka data Yaudara, Yasha alwashin daukar fansa”

“Shine ya zabi Ramawa akaina? Ina ina lokacin dahaka tafaru tsakaninsu? Meye Nawa a ciki? Meyasa kowa akaina yakeson daukar fansa? Meyasa? Jeje nikayiwa haka ko? Kashiga Rayuwata ka lalatamin komai, harda kokarin Rabani da Aminina Jawwad na yadda da kai amma aka hada kai da kai ana hadamin wannan miyagun tarkunan, Yanzu badan Allah ya kiyayeni ba…. Kasa karasa maganar yayi, Hawaye yafara fita a idonsa ya mike yanufi hanyar fita da Sauri, bayansa Jalila itama tabi da Sauri, tana kiran Sunansa amma kafin ta cinmmasa tuni ya hau motarsa ya kunna, ya tasheta da gudu yabar Asibitin.

Haka ta dawo dakin data bar Suleiman, suleiman ya kammala tambayoyinsa. 

Jeje ya kalli Jalila yace “Kin shammaceni fiye da tunanninki, ban taba zaton karamar yarinya kamarki zata iya aikata wannan abunba, kin kassaramin Rayuwa, kisani Babu wanda ze iya daukar mataki akan Oga KB, saboda za’a sakeshi ki Saurari abunda ze biyo baya idan aka sake shi” wani mugun kallo tayiwa Jeje “Duk wani zalunci da kassara Rayuwa yabiyo bayan wanda kukayiwa Jalal, Azzalumi daga kai har uban gidan naka, Kaike min kallon karamar yarinya, duk abunda nasa gaba sena ga bayansa, zamu gani nagama da babinku har gaban Abada, kuma ka saurara kagani ko ansakeku zalincin dakukayi baze barku ba” Ganin Jalila ta dau zafi sosai yasa suleiman yace “Kwantar da hankalinki, ki share hawayenki wanda zan dankawa case din shima wanine, za’adau matakin daya dace, kaikuma ina gurin kake wannan maganganun ko? Ka kara daure kanka zaka gane bakada wayo” sannan ya kalli Jalila yace “Shi waye wannan din? (JALAL) Jalila tace” Yaya nane”

“Gaskiya an cutar dashi Sosai, and he needs counseling, kusa ido sosai akansa sannan ku kuladashi, ajashi a Jiki a dage da Addu’a har Allah yasa a raba shi da shaye shayen nan” 

“Hakane Insha Allah za’ayi kokarin hakan, 

” Yawwa yanzu dai muje in ajiyeki a gida ko? “

” A’a ka ajiyeni a hanya dai” Yai murmushi yace to muje. 

Jalila ta koma gida cike da farinciki jin  kamshin Nasara tana saka ran tunda aka kama Jeje to ko Jalal be dena shaye2 ba ze rage sosai, tunowa tayi a halin da yabar Asibitin 

“ko yana ina yanzu?, Allah yasa yazo gida lafiya” ta shige cikin gida abunta, tana shiga Nana tace “Jalila ina kika tafine?” 

“Hmm kedai bari kawai, gidansu Zahra naje, amma ai gani na dawo” 

“Kinci sa’a Abba baya nan, shiyasa kika samu sake” Murmushi Jalila tayi tace “Aiko yana nan ma baze ce komai ba” 

“kyaji dashi dai, anjima ze dawo yayo waya ya tambayeni kina ina? Nace masa kindan fita” 

“Dagaske anjima ze dawo? Bari inzo inshiga kitchen dole in kintsa cikin Abbana, wannan karon ya dade a lagos” Nana tai murmushi “‘Yar gidan Abba, dama yafi sonki akanmu” Jalila dariya tayi ta wuce cikin daki, ta shiga da Sallama amma Naja bata amsaba sema wani dogon tsaki data ja, Jalila ko a jikinta bata damu ba, dan ita nasarar data samu ta fiye mata duk wani neman magana da Naja takeyi, Jalila tanemi guri ta ajiye jakarta da hijjabinta, Wayar Jalila ce tafara ringing ta duba taga Hanan ce, Murmushi Jalila tayi ta daga wayar, tace “Hanan wai yaushe zaku zone?” 

“ke ba gaisuwa ba tambayar ya nake se yaushe zamuzo, idan munzo mezaki bani?” 

“Ba’abunda bazan baki ba, yau ina cikin farinciki, nasamu Nasarar daban taba zaton samunta ba” 

“Wannan wace irin Nasarace kekuwa kike ta murna haka?” 

“Bazaki gane ba, bakina akwai magana sosai, kedai kawai sekunzo” 

“Gaskiya kifara gayamin yanzu dan zaki barni da tunani” 

“Gaskiya bazan gayamiki yanzu ba, innafara bazan iya gamamiki ba, kuma zakiso kiji komai, kawai se kinzo dai” 

“Amma naso kifara gayamin yau, daddy ya kira Abba, amma yace yana Lagos kifara hada kayanki zebamu ke, tare zamu tafi Bauchi” 

“Eh dama yau ze dawo Abban, Wayaga Jalila a Bauchi, zanga gari inci waina inture” 

“Ji kwadayayyiya, ke burinki kici waina, to bazakici wainar ba” sukayi dariya gaba daya, Hanan tace “Baby, ina Abun kaunata” dan jimm Jalila tayi sannan tace “kinada lambarsa ai, meya hana ki kirashi” 

“Ban niyya ba, ke nakeso ki amsamin” 

“Yana lafiya” Jalila tafada a takaice

“Kimikamin sakon soyayya, kigaya masa kullum yana kawwame a cikin wani bigire me girma a zuciyata, I Love Him, Kaunar Jawwad a jinina take, kigaya masa ina nan zuwa sati me zuwa, in ganshi” 

“Kan bala’i wane Jawwad din, ke banason karamin karauwanci, kobaki San anmasa mata bane?” NaJa ce take masifa daga gefe jin an ambaci Jawwad, dayake duk wayar da suke tana ji, Hanan tace “Jalila se anjima ki isarmin da sakona gurin abun kaunata, ba ruwana da kowace mace ko mata hudu aka masa Wallahi seya saki daya ya Aureni, sannan kigayawa me maganar nan Hanan tafi karfin tayi karamin Karuwanci se babban Karuwanci me lasisi, sati me zuwa Insha Allah zan shigo kano, zan gwada mata nawa salon karauwancin, ki gaida mutan gidan” Hanan ta kashe wayarta. Naja ta hau bala’i ta inda ta shiga bata nan take fita ba, yayinda Jalila ta samu guri ta zauna ta dinga kyalkyala dariya, tace “Allah ya kaimu my Hanan tazo, za’a sha drama, zanga yadda zata kaya, agama mu fece Bauchi in garin dadi in zamana se ankuma ganina” Hakan yakara bakantawa Naja rai, ta tashi fuuuu tabar dakin, Seda Jalila tagama dariyarta sannan ta mike lokaci2 Jalal yana fado mata a rai. Kitchen ta tashi ta tafi, ta tarar an Aiki Nana, ta shiga tafara Kokarin dora sanwa musamman dataji batun Abba ze dawo, tana tsaka da Aiki Jawwad ya shigo ya sameta

“Sannu kukunmu, kullum cikin adanamana cikinmu kike, weldone baby” ta juyo ta kalleshi tana murmushi 

“Allah yatemaki babban Yaya, da girman kujerarka, Nace Yaushe za’a dakkomin Abban, na dade ban ganshi ba fa” takarasa cikin shagwaba, karasowa yayi gabanta yace “Autar Abba saekin rikici anjima kadan zanje dakko shi ai” 

“Yawwa naji dadi sosai, Ina dan uwanka ne?” 

“daga gurinsa nake, bayajin dadi ya kwanta bacci” 

“Meyasameshi haka?” 

“Jalal ba a rabashi da damuwa, be gayamin ba, yace yana bukatar hutu ne kawai” dan jinjina kai, har cikin ranta takejin tausayin Jalal, hawayen dataga yanayi dazu a Asibiti ya tsaye mata a rai, basarwa tayi tace “Yaya Su Hanan zasuzo a cikin next week Insha Allah, zamuje Bauchi in Abba ya yadda” 

“Bauchi kuma? Zasu daukemin ke?” 

“Ai bazan dade ba ai, nima zanga gari sosai” 

“Bawani nan nidai bansoba gaskiya, banason kiyi nisa dani” tai murmushi tace “Hanan tace inmiko mata gaisuwa, tace in gaisheka” 

“nifa nayiwa Hanan laifi Jalila, da tana kirana mu gaisa amma yanzu ta dena” 

“Karka damu Yaya Jawwad, nasan halin kayaya don’t mind her” 

“Kinsan banason in batawa kowa rai ni” 

“Ni zanbada wannan shedar akanka, kai abun sone ga kowa Yaya Jawwad, Irinka basu dayawa ko a cikin mutane shiyasa…….. 

” To maye bita zaizai” gaba daya suka juyo, Maama ce itada Naja a kofar kitchen din, suka karasa shigowa 

“Jawwad ban isa in gayamaka magana kaji ba saboda wannan shegiyar yarinyar ko? Sam kaki saurarar Naja kaki kulata, ka tare a gindin wannan ‘yar macen, to wallahi baka isaba Jawwad, Akan yarinyar nan idan na juya maka Baya sedai kanemi wata uwar baniba” da Sauri Jalila ta kalli Maama, Naja se kara zigata takeyi, Maama tace

“Eh kalleni da kyau, munafuka Mayya za’ a mallakemin da kaman yadda uwarki ta mallake ubanki aka dinga wulakanta ni a lokacin, wallahi baki isaba kinyi kadan, kuma dan uwarka dan ubanka Naja zaka Aura, kekuma kije kinemi mara mutunci mara Asali irinki, ba dana ba dan dangi gaba da baya”

Jawwad yace “Maama dan Allah kiyi hakuri, kidenai gaya mata haka” 

“Wato bakason bacin Ranta, gara batamin Rai akanta ko? Nikae gayawa abunda zanyi, ka kiyayi bakina Jawwad” A hankali Jalila ta tako ta rabe gefen Maama zata wuce, Naja ta kamayi mata Gwalo, bata kulata ba ta wuce daki. 

Tana zuwa daki tasamu gado ta Haye, ta sunkuyar da kanta se Hawaye wani nabin wani, Jalila ba karamin dagawa Maama kafa take ba amma sam ita bata gani, amma lokaci yana zuwa da zata gane kuskuren abunda take mata, amma tayiwa kanta Alkawarin seta koyawa Naja hankali. Koda Nama ta dawo tayi mamakin ganin Ran Jalila a bace, tabarta da fara’arta amma ta dawo ta tarar da ita rantaa a bace, Nana tace “Jalila nasan wasu lokutan zaman gidan nan baya miki dsdi, mussaman da Naja ta dawo gidan nan, amma kiyi hakuri komai me wuce ne, dukkan tsanani yana tareda sauki” 

Murmushi Jalila tayi tace “Ni nace miki ammin wani abunne? Bana jin dadine kawai” 

“Amma ai idonki ya nuna kuka kikayi” 

“Baki yadda dame ma fada ba kenan” 

Nana tace “shikenan Tashi muje, tunda kin kafe, amma idonki ya nuna akwai damuwa, muje mukarasa girkin” Jalila tai kokarin ta danne damuwarta sucigaba da aiki amma abun yaki yuwuwa, ko yaya Nana ta kauce se Jalila zubda Hawaye, ita kanta tasan tana Hakuri da kauda kai akan wasu abubuwan. 

Da la’asar sun kammala komai Jalila tayi wanka ta canza kaya, amma duk ranta ba dadi, tasan Jawwad ma yana nan ransa babu dadi, da sunci karoda Naja seta dinga yar mata da miyagun maganganu, ga Maama agurin babu damar ta rama,

“Ai wallahi Maama mungode Allah, danginmu a tsarkake muke, ai karshen masifa a hada maka zuri’a da Arna” Maama tace

“Godewa Allah kam yarinya, dukkanmu musulmi ne, babu shegu babu Arna” Naja tace

“Maama ‘ya’ yan halak dinma im aka bincika wasunsu shegune, dan Arna da Auren suma bin maza suke” 

A fusace Nana tace “Naja waike dabbar dajin inace? Wani irin hauka… Maama ta katseta ta hanyar cewa

“Rufemin baki ko make miki baki, aiba karya tayi ba kudinma babu tabbas kun hada jini da ita”

ficewa Jalila tayi gaba daya daga cikin gidan tafito harabar gidan. Nanna ta yunkura zata bi bayan Jalila Maama tace “wallahi kika bita sena baki mamaki, wuce ki zauna daga nan inta tafi karta dawo, haka Nana ta koma ta zauna” 

Koda Jalila tafito harabar gidan, taga Manu driver da abokansa, a harabar gidan suna gyran flowers, ta duba taga bataga motar Jawwad ba, dan haka ta wuce part din Jawwad, ko ganin gabanta batayi, ta samu gefen kujera ta zauna ta toshe bakinta tafara kuka, bata son kowa yaganta balle a rarrasheta ta zauna tana kukanta, tanajin yadda ranta yake mata zafi. Tana tunanin meyakamata tayi ta huce yadda Maama ke wulakanta ta, bata son gayawa Abba halin da’ake ciki, tasan hakan ba karamin matsala ze jawowa Maaman ba, tana bukatar wanda zata gayawa damuwarta koba komai ta rage damuwa, tasan Hanan zigata zatayi tayi rashin mutunci, gashi ita bada kowa ta yadda ba, balle tagayawa wani abunda ke damunta,,  tana cikin tunani tareda kuka taji magana

“Meyasaki kuka haka?” bata san da mutum a dakin ba, dan haka ta juya da sauri da doguwar sumarsa ta ganeshi, sam bataga kowa a dakin ba, shiru tayi tacigaba da kukanta, karasowa yayi gabanta ya zauna ya zuba mata ido, ji tayi duk ya takurata a hankali yace

“Meyasaki kuka haka?” 

“dan Allah nika kyaleni, ina ruwanka da kuka na” 

“Inada ruwa da kukanki, kamar yadda kike da ruwa da Rayuwata, now talle me what happens?” 

Banza tai masa ta dauke kanta, yakuma kallonta yace

“Gayamin mana”

A fusace tace “bazan fada ba, meye hadinka da damuwa ta?”

“Nasan kinajin haushina saboda kuskuren da’aka samu, amma…

” kace kuskure? Ba wannan ne karo na farko daka mareni ba, kace na fiye maka shishshigi, nakuma yi Alkawarin na dena yimaka kaikuma meye naka nayi min shishshigi, dalla matsa kabani guri in wuce”

“zan baki guri ki wuce, amma meyasa kika damu dani haka, kike bani wannan kariyar bansaniba, dukda irin halayena? Kinyi kokarin kareni a lokuta daban2 bansaniba meyasa? Gashi kinsan abubuwa dayawa dani ban saniba, at least kin haska wani bangare a Rayuwata da yakasance me tsananin duhu, nesanta Jeje dani hakika haskene me yawa a rayuwata, bansan ya akayi na yadda da Jeje nafara wannan muguwar rayuwar ba, kawai na tsinci kaina a wani yanayi dani ka dai nasan menakeji, amma meyasa kika temakeni, kike kokarin ganin kin canza akalar Rayuwata?” yai tambayar yana kara tsareta da ido,  itama kallonsa takeyi dan bata san mezatace masa ba, wani uban tsaki taja ta wuce ta gefensa ta fice daga dakin.

A hankali ya koma ya zauna yana tunanin abubuwa da dama, abubuwa dayawa ya dinga tunawa, Jalila tayi Rawar gani a Rayuwarsa, yanzu ya gane abubuwa dayawa da a da sam besan dasu ba.

Itakam guri tasamu tai zamanta taki komawa cikin gidan tanata zancen zuci, karar motar Jawwad ne ya dawo da ita hayyacinta, shida  Abba ne ya dakko shi a Airport, da fara’a Jalila ta tashi ta nufi inda suke, Abba yace “Jalila bakida lafiya ne? Naga kin rame haka” murmushi tayi “Haba Abba duk wannan kibar danayi kayana sunmin kadan fa”

“Anya kuwa in yadda? Idonki kaman kinyi kuka fa”

“Abba nikam meze sani kuka yau zanganka? Bacci nayi kawai, kawo jakan in rike maka” tasa hannu ta karbi jakarsa, Jawwad yana ganin dakiyar Jalila daka ganta kasan tana cikin damuwa, amma ta maze tanata kokarin boye damuwar.

Ba karamin murna sukayi ba dawowar Abban nasu, Jalila tasan koba komai zata samu saukin wani Abun, 

bayan sallar magariba suka gabatar masa da Abinci yaci, nan suka sake aka shiga hira da Abba, Maama tanata dan dari2 kar Jalila tagaya masa wani abu, dan ta lura tun dazu Abba yake tambayar Jalila koda matsala amma tace ita ba komai. Sekusan goma na dare suka watse suka tafi dakunansu.

Ilham tagaji da azabtarwar da Jalal yake mata, yakamata sunemi wata mafitar, tsawon shekarun datayi a gidansu Jalal bataga alamar zasu cinma burinsu ba, Jalal mugun baudadden mutum ne, ga tsabar jaraba da masifa, gashi da rashin yadda, kwanan nan ta lura kaman yakara tsanarta batasan metayi masa ba, ta lura yanzu har uwassa ma yakara fita harkarta, ko cikin gidan baya shigowa, mikewa tayi ta tafi palourn mummy, ta tura kofa bako sallama ta shiga ta samu guri ta zauna

Mummy ta kalleta tace “Ke lafiya kika shigomin bako sallama meye haka?”

“Mummy yaushe zaki cikamin alkawari na ne?”

“Wanne kenan?”

“Mummy har yanzu banga alamar Yaya Jalal ze yadda ya Aureni ba, lokaci fa kuremin yake ni macece yakamata zuwa yanzu kiyi wani abu akai, ina sonshi, banajin zan iya Auren wani bashiba, kitemaka Mummy dan Allah kiyi wani abu” Ajiyar zuciya Mummy tayi “Ilham yakikeso inyine? Yaron naan kullum wutar kiyayyata ruruwa take a ransa, kiduba rashin lafiya nayi amma da naje kansa ga yadda ya rikice gana sambatu infita baya son ganina, ya zanyi Ilham? Kaina ya kulle al’amarin Jalal sunfara bani tsoro”

“Kina nufin in hakura dashi kenan?”

“Bahaka nake nufi ba, amma kidan karamin lokaci, nina miki alkawari ai, bakuma zan saba ba”

“Shikenan Mummy seda safe” Ilham ta tashi ta fita ranta a bace, ji take kaman ta shake Mummy, takoma dakinta ta kulle kofa, ta dau waya takira ummanta tagaya mata abunda ke faruwa, tace mata ta kwantar da hankalinta, in tasamu lokaci taje gida, zasu san yadda zasu bullowa lamarin Jalal da Mummy. 

Da sassafe Jalila suka shiga kitchen hada Abinci, bayan sun kammala kowa ya hallara a palour don karyawa, bayan an gama breakfast suka shiga hira, anan Maama ta sanarda Abba ai Naja tazomusu hutune, sannan akwai maganar datakaeso zasuyi da Abba amma ba yanzuba, ba karamin faduwar gaba Jalila taji ba dan tasan be wuce zancem Auren Jawwad da Naja ba. 

Abba nan yashiga rarraba musu tsaraba kamar yadda ya saba in yayi tafiya, Abba yabada zuma a gwangwani yace akai gidansu Jalal, A ajiyewa daddyn Jalal, ya daga waya ya kira Jawwad yace yana son ganinsa, bayan yagama waya da Jawwad ya kalli Jalila yace 

“Baby Babanki yayo waya daga Kaduna (baban Hanan) yace nan da kwana uku zasuzo, yanaso zasuje dake Bauchi yana neman Izinina, nace masa inkin amince ba damuwa amma bana so ki dade a can” Jalila tai murmushi tace “Na yadda Abba, zanje” Nana kam ta hade rai tace “Ni gaskiya ban yadda ba” Abba yace “Jalila nayi mamakin saurin Amincewarki da batun tafiyar nan, iya sanina dake ba kyason barin gida, amma ya’akayi haka, ko akwai wani abu bakyason gayamin ne?” 

“Haba dai Abba, ba wani abu ni kawai inason inzaga inje garuruwan dabantaba zuwa ba” 

“Eh hakan yana da kyau, amma bazan bari ki dade ba kinga ga komawa makaranta” 

Jawwad yai Sallama ya shigo palourn, ya durkusa ya gaida Abba sannan ya gaida Maama, aciki ta amsa masa dan tanajin haushinsa, yakoma gefen Abba ya zauna yace 

“Abbana gani, Allah yasa ba laifi nayi ba” 

“Aini baka laifi a gurina, da dai wannan ce tafi kowa iya laifi” Abba ya fada yana nuna Nana, dariya sukayi, yayinda Nana ta dan hade fuska da sigar shagwaba tace “Abba niko? Aikam bana wani laifi ni” Abba yace “Anya kuwa a tambayi Jalila?” haka Abba yasake ya dinga wasa da dariya dasu, banda Maama da take ta cika tana batsewa, Naja kam dama tuni tabar gurin, Abba ya kalli Jawwad yace “Babban mutum, daddynka yamin magana yace yasamo maka aiki a NNPC amma kace kai A’a, yace in rarrasheka ka karba, meyasa bakason Aikin” 

“Abba ba banaso bane ba, banason tafiyane saboda Jalal, bansan wani hali ze shiga ba, dukda Alhamdilillah ana samun cigaba a daidaituwar lamuransa, amma banason in tafi yacigaba da mummunar Rayuwa tunda……… Ai kafin yakarasa a fusace Maama tace” Jalal din ubanka ne? Kai meyasa bakada tunani ne? Ana nema amaka gata amma kana maganar wani, baka isaba seka karba ka tafi, tunda kagama karatun zaman jiranwa zakayi? Shiru Jawwad yai bece komai ba, a hankali Nana da Jalila suka zame suka bar palourn ya rage saura Maama, Jawwad da Abba, Abba yace “Jawwad tashi kaje zamu karasa maganar” Jawwad ya tashi ya tafi, Abba yace 

“Waime yasa mata wasunku bakuda halaccine? Haba Maman yara, Abunda Jawwad yayi, yai dai2 shine halacci irin kaunar da yaron nan yake masa bekamata kice hakaba, ki kyale shi zuwa wani lokaci tukuna mugani, kinsan kowane dan adam baya wuce rabonsa” 

“Naji, Amma Jawwad ya kai munzalin da a yanzu yadace ya fuskanci Rayuwarsa, ya nemi Aikinyi sannan ya mallaki iyali” 

“Eh gaskiyane, samun Aiki ba wani babban Abu baneba, kuma bacewa yayi bazeyi Aikin daza’a samomasa ba sedai yace abashi lokacine saboda Jalal, Amma kuma aini har yanzu becemin ga wata wadda yakeso ba tukuna, kinsan mutumin nawa da kunya Akwai fulatancin sosai a tareda shi, Allah yasa ko budurwa ma yanada ita” Abba ya karasa zancen cikin murmushi, Maama tace “inma bashida ita se asmomasa, bazan cigaba da zura masa ido se ya tsofe ba Aure ba, dama maganar danakeson yimaka kenan, ga Naja nan ‘yar gidan Yaya mairo da ita nakeso in hadashi, tunda yarinyar itama ba laifi akwai hankali” Abba ya danyi shiru sannan yace

“To banki ta takiba, Amma banason ayi abunda ze zamana an cutar da dayansu, yakamata muji ta bakinsu tukuna” 

“Kamarya semunji ta bakinsu, muba iyayensu bane ba dole subi abunda mukeso, hakan ze kara karfin zumuncin dake tsakaninmu” 

“To Allah ya tabattar mana da alkhairi, ni bari in wuce daki zan dan kwanta, kar amanta akaiwa Baban Jalal wannan zumar” 

“Za’akai” Abba ya wuce daki. 

Jalila tanata tunanin yazata bullowa wannan lamarin, dan in aka hada Jawwad Aure da Naja an zalunceshi, gashi tasan Maama bazata taba barin Jawwad ya Aureta ba, nan duniya tasan inta Auri Jawwad tayi sa’ar miji, salihin bawa da baruwansa da hayaniya”da taga tarasa mafita taje ta janyo trolley dinta ta fara shirya kayan dazatayi Amfani dasu dan tafiya bauchi, taji gara ta dan bar garin tayi nisa maybe ta huta da wannan abubuwan daga wannan se wannan. 

“Kayan me kike hadawa haka?” 

“Kayan da zan tafi dasu Bauchi mana” 

“Jalila bana son kitafi, badan hutunmu next week ze kareba da binki zanyi” 

“Allah sarki my Nana, nikaina zanyi missing dinki da kiriniyarki” 

“Mtseww Allah raka taki gona, inkin tafi karki dawo bakar kaya kawai, daga nan kema kitafi inda uwarki ta tafi” 

Nana ta juyo ta kalli Naja a fusace tace 

“Wai Naja ke wace irin mahaukaciya ce” da sauri Jalila ta dakatar da ita ta hanyar cewa “Ke Nana wayagaya miki in kare yana Haushi ana kulashi, kyaleta dan Allah, innaje Bauchi me kike so in kawo miki” Naja tace “Ke kin isa kice min Karya, uwarki ce Karya baniba” Jalila tai sauri tace

“Nana naji kaman muryar Maama tana kiranki yi Sauri kije” Jalila ta tura Nana waje ta dawo ta zauna ta kalli Naja tace 

“Uwata batada katon baki da zako zakon fika kuma bata haushi kaman uwar wata, ki kiyayi ranar da bomb dina ze tashi dake, Naja har inda Yayarki Sa’adah ke zuwa a zubar mata da ciki nasani, tsohuwar karuwar Alhaji Kabiru ce dayanzu yake can ana shirin gurfanar da shi a kotu ko karya nayi? ” 

zaro Ido Naja tayi

“Karya kike ubanwa yagaya miki haka? Waye yayiwa Sa’adah sharri “

“Kinga bana son wani borin kunya, ganina kawai kike amma bakisan waceni ba, bana zama da mutum ba tareda nasan wayeshi ba, karkiyi mamakin kema nasan komai akanki Jalila ta wuce tunaninki Naja, kibini a sannu im bahakaba zanmiki tonon sililin da sekin kasa hada ido da mutane, tun ranar dana ji kina waya cikin dare da Saurayi kema na fara bin diddigin ki dan haka ki kiyayeni”

Gaba daya jikin Naja ya sanyi, yayinda gumi ya shiga tsatstsafo mata ta goshi, tunani tafarayi ya akayi Jalila ta san wani abu akansu haka, bakowa yasan wannan abubuwan da Jalila ta fada ba amma ita ya akayi tasani, Jalila ta tashi tabar inda Naja take tacigaba da hada kayanta. Tundaga Ranar Naja takejin tsoron yiwa Jalila rashin mutunci dan ta tsorata da kashedin datayi mata. 

Shikam Jalal yakara takure kansa, tun ranar bekuma haduwa da Jalila ba, yana son ya ganta amma baya samun damar hakan, dan ko a waje baya ganinta, Jalal baya son kowa yaje inda yake, baya iya cin Abinci idan ya tuna abunda Jeje da uban gidansa yayi masa saboda laifin da banashiba seyaji duniyar takara yimasa Zafi, ga abunda yaji Da kunnensa Ilham na fada akansa itada mahaifiyarta, Gakuma Jarumatar da Jalila ta gwada saboda shi abun ya dade yana bashi mamaki ya akayi Jalila ta gano Jeje da uban gidansa akansa suke Aiki harta hada wannan gwaramar, yana son jin wasu abubuwan daga gareta, idan yaji duniyar tayi masa zafi, seya sha giya ya bugu sannan yake jin dadi. 

Jalila tashirya kayanta tsaf tun dare, ji take kaman za’acireta daga prison zata tafi kwana biyu ta huta da tension din da suke kanta. 

Tun safe Jalila tayi wanka, tai waya da Hanan tace mata zasu karaso da wuri. 

Jawwad yaje ya takura Jalal yaci Abinci ya dinga yi masa Nasiha akan wannan takura Rayuwarsa da yayi, Jalal yace “Dan uwa, Nayiwa Kanwar ka laifi fa, nikuma tayimin Abunda har in bar duniya bazan manta ba” 

Jawwad yasan Jalila yake nufi yace

“Allah yasa ba wani laifin tayi maka ba? Nasan Halin Baby sarai in wani abun tayi maka Allah yabaka hakuri” 

Jalal yai murmushi yace “Ba laifi tayimin ba, Amma tayimin abunda banida abun biyanta, inajin kunyarta abubuwan danayi mata abaya” Jalal ya karasa maganar idonsa fal kwalla

“Subhanallah haba Jalal, haba ‘yan mazan daddy, hawaye a idonka, kadena damuwa kaji, komai ze wuce banason ganin ka cikin damuwa muje kaci Abinci, Yau Jalilanma zata tafi bauchi” 

“Bauchi kuma?” 

“Eh Jalal, nima ban soba amma tasamu ta huta, zaman gidanmu sam baya mata dadi, Maama tana takuramata kuma Yaya mairo ce take zigata, banajin dadin abunda suke mata, inta tafi ta huta kwana biyu, tashi muje ka karya” 

Jalal be kuma cewa komai ba yabi bayan Jawwad suka fita. Da kyar Jawwad ya takura Jalal yaci Abinci shima kadan yaci yace ya koshi. Jawwad yaita tunanin me Jalila tayiwa Jalal haka har yake cewa baze manta ba?. 

She kusan karfe daya na Rana su Hanan suka karaso kano gidansu Jalila, a guje Jalila ta fito daga cikin gida ta rungume Hanan cikin farinciki, Hanan tace “Nayi missing dinki ‘yat Baba” suka kuma rungume juna suna murna, Jalila ta kalli Abdallah tace “Babban Yaya sannunku da zuwa ya hanya?” 

“Hanya Alhamdilillah, da tuni munzo amma Hanan tasa muka makara” 

“Aina sani ita tahana kuyi sammako” Hanan tace “to mukoma kenan?” 

“A’a ni bance ba, ina Baban yake?” 

Hanan tace “Daddy shida Mummy zasuje su tarar da mu acan, dama zamuyi biki, yarinya har Anko daddy ya dinka mana nida ke” 

Jalila tai musu jagora har cikin gida a palour tabasu gurin zama, taje ta sanarda Abba su Hanam sunzo, dukda wulakancin da Maama takewa Jalila, amma ta sakarwa su Hanan fuska ba laifi, Jalila taje tagayawa Nana su Hanan sun karaso. Naja najin haka ta biyo su dan ganin wai wacece Hanan din nan ne tana zuwa palourn tayi turus, se yanzu ta tuna suntaba haduwa a gidan kamarta daya da Jalila, Amma Hanan takara kyau sosai seda Gaban Naja ya fadi, Hanan tanada kyau sosai gata ta iya gayu, Nana ta fito palour suka gaisa dasu Hanan nan aka shiga hira a palourn, Abdallah yace “Nifa banga Jawwad ba da mutumina Jalal” Nana tace bari inje in kiramaka shi, nasan besan kunzo ba tashi tayi ta fice a palourn Maama da kanta ta kawo musu Abinci, Abba ba ruwansa ya zauna suka dinga hira da Abdallah, Jalila ta janye hannuna Hanan zuwa dakinsu, Nana ta dawo itada Jawwad, Jawwad yashigo da fara’a ya zauna kusada Abdallah suka gaisa daga nan sukayita hira. 

Naja ta babbake a daki, dan haka Jalila bata samu damar yiwa Hanan hirar datake so ba sukayita hirarsu ta rayuwa, Hanan taji muryar Jawwad a palour tacewa Jalila zanje wanke Hannu”

“baga toilet ba kishiga mana ki wanke” 

“Ba wanke Hannu zanba Jawwad nakeson gani” 

Naja tace “Ke mekikace meye hadinki da shi dazaki ganshi?” 

Ko tsayawa Hanan batayi ba tayi waje, amma kafin takarasa palourn ta tsaya ta daidaita nutsuwarta sannan ta fito palour, 

Da sauri Naja ta fito itama, unexpected Jawwad ya daga ido yasauke akan Hanan, takara kyau dressing dinta ma yayi ba karya, gaba daya besan lokacin dayake kallonta ba, tabass Hanan kamarta daya da Jalila a ransa yace “tsarki ya tabatta ga Allah, ba dangin iya bana Baba, amma ya halicci masu kama daya kuma ba twinsa ba, sedai sunada dan banbanci” 

Cikin kasaita ta wuce shi a palour ta nufi kitchen. 

Hanan takuma dawowa zata wuce

Abdallah yace “Auta bakiga Jawwad din naki bane” dan kallon Jawwad tayi, tayi murmushi tace “Naganshi mana” Naja kamewa tayi a gurin musamman dataga Jawwad yana kallon Hanan, da alama beji dadin yadda Hanan taki kulashi ba. 

Abdallah yace “Wallahi Hanan totally dinta se a hankali, duk ta takuramin wai muyi Sauri muzo taganka amma ta ganka ta wani basar” Jawwad yai murmushi yace “Kyaleta Abdallah zamu shirya ne, maybe gajiyar Hanya ne ya hanata yimin magana” 

“Bawani gajiya tsabar wulakanci ne kawai” Hanan ta murgudawa Abdallah baki, suna hada ido da Jawwad ta kashe masa ido daya, gaba daya ya rikice, gani yake kaman kowa yaga Abunda Hanan tayi gaba daya yakasa sukuni,

 ita kam Hanan ta wuce Naja takoma inda tabar Jalila a daki, ba kunya Naja takuma biyota dakin, Hanan tana shiga tace “Ohh God, Jalila Haidar yakara kyau yakuma zama babban mutum, wayyo dadi kasheni, naga farincikin zuciya ta” Jalila tace “Waye kuma Haidar?” 

“So kike indinga kiransa da sunan da kike kiranshi ne, kowa yace Yaya Jawwad nima ince Yaya Jawwad, Haidar dai kaman in sace shi in gudu haaka nakeji, yawwa Queen ranar muna waya dake naji wata namin kashedi akan abunda yake mallakina, wacece dan Allah?” 

“Nice nan, kuma wallahi duk maitarki iyayenmu sun tsaida magana, bashida wata mata in baniba, mayun banza dana wofi marasa zuciya” Naja ce taketa fiffika tana fadan maganganu Hanan taja wani dan tsaki tace 

“Jalila aina dauka wadda take cewa zata auri Jawwad din mace ce, ashe mata maza ce mata ta rako duniya, ke cewa akayi ya Aureki, nikuma Jawwad yana sona ne” , dan saurin kallonta Jalila tayi, lokaci da dama Jalila tana daukar abunda Hanan take a matsayin wasa, dukda tana ganin tsagwaron gaskiyar abunda Hanan din ke nufi a idonta Jalila na cikin wannan tunanin Hanan tace “zan tabattar da hakan anan kusa ba a nesa ba, ke Queen ina mutuminne tunda nazo ban ganshi ba” 

“Wakenan?” 

“kinfini sani, Jalal mana” tsaki Jalila tayi tace “Nifa bana son maganar wannan shirmammen” 

“Jalal dinne shirmamme?” 

“Eh shidin, ke Akwai Labari amma semun je bauchi Lafiya insha Allah” 

“To Allah ya kaimu lafiya” 

Abdallah yace “Jawwad nikam ina Jalal ne naganka kai kadai?” Jawwad yace 

“Yana part dina baya jin dadi” 

“Allah sarki, muje inganshi, muyi salla Azahar sannan mu wuce” 

Suka tashi suka tafi part din Jawwad, suka tarar da Jalal zaune akan kujera, yana kallon TV amma sam hankalin sa baya kan Tv, shigowarsu yasa ya daga kai, murmushi yayiwa Abdallah, ya mika masa hannu suka gaisa

“Jalal ashe bakaji dadi ba? Sannu gaskiya ka rame, Allah ya sawwake” 

“Abdallah aini na warke tuntuni, Jawwad ne da zuzuta abu” 

Jawwad yace “Au ni nake zuzuta abu, dadinta kallo daya za’ayi maka asan baka da lafiya” sukayi Salla, suka zauna sukayi ta hira, Jalal ya sake sosai. 

Can aka jima Abdallah ya kira Hanan a waya yace su fito yanzu zezo su tafi, Hanan tace masa to, Jalila ta nunawa Hanan akwatinta tace “Hanan kaimin mota, bari in sa kaya” Nana tace

“bari inje ingayawa Abba zaku tafi” Hanan ta ja trolley Jalila ta kai bakin mota, amma motar a rufe, tasan Abdallah suna part din Jawwad kanta tsaye ta tafi part din, tundaga waje take iya jiyo hayaniyarsu, shiga tayi da sallama duk suka amsa mata, ta fadada murmushin fuskarta ta Kalli Jalal tace “Yaya Jalal kwana dayawa, Yakake ya gida amma naga ka rame sosai” shima murmushi yayi mata yace “lafiya kalau Hanan, amma aini hakanake dama can ban rame ba, yagida ya hanya?” 

“Alhamdilillah, ina wannan kanwar taka, yama sunanta?” 

Abdallah yace “Kai Aku me magana, daga zuwanki kinfara zuba kaman kanya” 

Dan hade rai tayi “kace mufito kuma ka kulle mota, ga kayan queen can na fito dasu, kazo ka bude in samata a mota” 

“Sedai kizo ki karba kibude, bari mugama hira” 

“Gaskiya Abdallah ka dinga jin tsoron Allah muka katse namu hirar kace mu fito kaikuma ka zauna” 

Taki kallon inda Jawwad yake, balle yasaka ran zata kulashi, Jawwad ya karbi key din motar a hannun Abdallah yace 

“muje in bude miki motar, Abdallah bashida niyyar tashi yanzu” 

Dan murmushi tayi ta juya, Abdallah yace “tasamu abunda takeso, dama ba dan Allah tazo nan dinba, sarkin gulma wani inzo in bude mata mota, kawai kice Jawwad yataso gurinsa kikazo, sewani Iyayi kike” 

Hanan taji kaman kasa ta bude ta shige, Abdallah mugun dan rainin hankali ne Jalal yace “Ahha kai Abdallah ina ruwankane? Yada shishshigi haka?” 

“Auto nayi shiru, tunda ka goyi bayanta” 

Suna fitowa Hanan ta nufi hanyar komawa cikin gida, Jawwad ya kira sunan ta, ta tsaya amma bata juyo ba, ya karasa gabanta yana kallon ta amma ta sunkuyar da kai, 

“Hanan, menayi mikine? Tunda kikazo kin kula kowa amma ni kin shareni” 

“Bakomai” 

“Ban yadda ba komai ba, laifin menayi miki?” 

“Haidar dan Allah ka kyaleni, banason matsala, kace baka sona, gaa nazo na tarar da wata tana gayamin ita zaka Aura ya zanyi? Ina kokarin in cireka a raina amma nakasa, ganinka din nan ma yana karamin pressure ne, na damu da kai sosai kaikuma ka nuna baka sona, base in hakura ba, mezesa incigaba da shishshige maka?” Abun mamaki hawaye ke kokarin fita a idon Hanan, hakan na nuna maganganun da take fada har cikin ranta, Jawwad yace 

“Zannemi wata alfarma daya a gurinki, zakiyi min? “

“Alfarma kuma? Wace iri” 

“Sekinyi min Alkawari zakimin Alfarmar” 

“Inkuma bazan iya bafa?” 

“Bazan tambayi abunda bazaki iyaba ai, abune me sauki” 

“To fadi in zan iya” yai murmushi yace

“Sonake inkuma jin sunan dakika kirani dashi please, yanamin dadi” 

Dan zumbura baki tayi ta noke kafada, “Niba wani suna” 

“Kince fa zakiyi min Alfarma” cikin shagwaba tace 

“ni banyi Alkawari ba ai” 

“Please, ko inyi kuka ne sannan ki fada” 

“Eh to yi kukan in gani tukuna” sukayi dariya a tare, yanayin irin tsokanar Jalila haka Hanan takeyi, amma Hanan bata iya komai ba akan Jalila, Jawwad yace 

“Hanan da bakina ban taba cewa bana sonki ba, ban taba soyayya ba, amma nasan ina son Jalila so ba na wasa ba, kinga akwai alaka me girma tsakanin ki da ita, sannan batun Naja da kikeyi Wallahi Hanan yanzu haka ina dauriya ne kawai, Naja zabin Maama ce, tanason in Aure ta ni inason yiwa Maama biyayya amma bana tunanin zan iya Auren Naja, 

Hanan nasan kinshiga damuwa saboda ni but am very sorry, banason kowani rai ya shiga damuwa saboda ni, ta mussaman ke ce a gurina” Hanan tai murmushin da seda hakoranta suka fito, ta jingina da motar tace

“Kasan meyake kara burgeni da kai Haidar?” 

“A’a sekin fada” 

“A dukkanin maganganun ka kana kokarin fadar gaskiyane, sannan kanada tausayi shiyasa nake kara sonka, Amma bari ingaya maka wani abu, alakar dake tsakanina da Jalila bazan so ta baci ba, saboda ina mata so na gaskiya, bazanyi wani abu in cutar da ita ba, Amma maganar gaskiya kanawa Jalila so ne irin na ‘yan uwantaka ba soyayya ta Aure ba, haka ma zuciyar Jalila tana maka sone na’ yan uwan taka, nasan zakayi mamaki, Jalila bata taba soyayya da wani ba, tanada Samari Amma har yanzu taki yadda zuciyarta akwai wanda takeso saboda taurin kanta, kaima zan baka lokaci zaka gazgata abunda nake nufi”

Gaba daya zuciyar Naja ta gaama tsinkewa, Ganin Hanan taki dawowa yasa ta fito harabar gidan, amma tayi tozali da Hanan da Jawwad se murmushi yake, tunda take da Jawwad maganar minti goma bata hadasu balle yaita wannan murmushin, Nana ma befiye shiga harkarta ba, a da tayi tunanin ko Jalila yake so, wato wannan yarinyar me girman kan bala’i ita yakeso, koma dai duka yake sonsu ne tana tsaye tana kallonsu

Jawwad yafara magana “Hmm Hanan ina kika samo wannan ideology din, yazakice Baby Akwai wanda takeso, kuma munayiwa juna son ‘yan uwan taka?” 

“Ban fada domin in shiga tsakanin ku ba fa, nawa hasashen ne haka, Ita kanta Jalila bata son wa take so ba, bakowane lokaci take yadda da zuciyarta ba tana karbar abubuwane da lissafin kwakwalwarta” 

“Hanan ya akayi duk kika san Jalila haka ne?” 

“Haidar a zaman danayi da Jalila motsi tayi nasan abunda take nufi, nasanta fiye da yunwar cikina”

 kyar yake kallon Hanan ko kyaftawa bayayi yana juya maganganun ta a ransa, ganin yanata kallonta yasa tace “ya dai kona bata maka raine?” 

“Ina so kicigaba da magana ne, komai kikayi kyau yake miki” murmushi tayi tana rufe fusaka, 

yace “masha Allah yanzuma bakiga yadda kika kara kyau ba” 

Abdallah da Jalal suka fito daga part din Jawwad, ba karamin matching Jawwad da Hanan sukayi ba, suka nufosu Abdallah na shirin sukarasa ya tsokane su, shikuma Jalal Jawwad kawai yakson ya titsiye yau, amma kafin su karasa Naja ta rigasu dan Naja ba karamin kulewa tayi ba, dan haka ta taho kaman wata kura, ta nufo su Jawwad, tana zuwa ta rike kugu tace “ke wace irin matsiyaci ya ce haka? Nace miki Jawwad shine wanda zan Aura na meye zakizo kina wani shige masa, kina wani salon karuwanci meye haka?” 

Hanan kaman tayi magana, sekuma ta fasa tace bari inga matakin daze dauka

Aikuwa Jawwad yace “Naja meye hakane wai? Yazaki kirata da karuwa me tayi miki? Wannan wace irin magana ce” 

“Eh dole kace wace irin magana ce mana, kasan ni zaka Aura amma kazo kunfi minti Ashirin a nan gurin alhalin niko hirar minti goma bakayi dani”  

Jalal yace “wai dan Allah meyake damun wasu matanne, yanzu meye hakan kuma?” 

Abdallah yace mata se Addu’a ai, se yanzu Naja ta lura da shi, wancan zuwan ma tare sukazo, ita da Abdallah ze Aureta aida ta hakura da Jawwad 

Abdallah yace “kinga baiwar Allah kiyi hakuri dan Allah, Kekuma Auta, Jawwad fa Ustaz ne, kinzo kin wani kanainaye shi tun dazu, kina kashe masa murya kina fari, Ashe ma ankusa Aurar dashi, ai seki hakura” gaba daya sukayi dariya suka maida Naja kaman wata mahaukaciya,

Hanan tayi murmushi cikin kasaita tace “Macen data kai mace, itace idan tace tanason take samu, ba ragowar muna mata ba” shikam Jawwad ba karamin kunya Abdallah yabashi ba

Sannan Hanan tace “gaskiya Abdallah kai dan hana ruwa gudune, Yaya Jalal ka shiga tsakanina da Abdallah, My Haidar karka damu da Abdallah haka yake da wannan takurar” 

Jalal yace “Inyee ashe har suna aka canza maka abun masoya kai Jawwad, se anyi magana ya dinga sunkuyar da kai waishi kunya, bayan yagama zuba kalamai shima” 

Da sauri Naja ta shige cikin gida, tanata kumfar baki a palour ta tarar da Nana sun fito  Jalila daga part din Abba

“Ni za’ayiwa hauka, ni wannan  yarinya zatayi wa karuwanci, wallahi yau duk bala’in da za’ayi se anyi, shegiyar yarinya a gabana kaman zata hadiye Jawwad kan bala’i, a fusace Nana tace 

“Ubanwa ya hana kiyimusu  can sekinzo mana nan, inkina yiwa Jalila tana kyaleki, ita wannan a yanzu intaga dama wallahi zata saka sojoji sumiki dukan mutuwa, dan ko a ina take a a fadin kasar  nan akwai yaran babanta” 

Jalila tace “Nana, bari inje waje inga meke faruwa, Nasan halin Hanan sarai, ba kanwar lasa bace, dukan sojoji yafiye maka dukan wannan bakin nata, koba komai yau na huta, Anamin maganin karya me remote”

Aikuwa Jalila takara angizo Naja, “ke dan abu ta kazakazanki, nikike cewa karya?” Ai Jalila bata jira taji metake cewa ba ta fito. 

Jawwad duk yarasa ya zeyi dasu Jalal, se tsokanar sa sukeyi shida Abdallah yana sunkuyar da kai, itakuwa Hanan ko a jikinta data fuskanci sun takura masa, se tace

“cwt Haidar don’t mind them, kaga Abdallah aiba a magana shima haka yake zuwa ana kashe masa murya, idan ana masa wannan kashe muryar seka sace shi ka gudu be saniba” seda ta danyi murmushi sannan tace “Kaga yaya Jalal Allah kadai yasan shime ake masa, shima nasan yana zagayewa yaje akashe masa muryar dayake takura maka, kaima ka dinga ramawa amma zanso inga budurwar Yaya Jalal inga in an kashe masa muryar shi ya yakeyi, sweet Haidar sena koya maka magana, adena takuramana” 

Jalal yai dariya yace “Ni Hanan aibana soyayya, ban santa bama balle inje a yimin wasu kalamai,, in aka fara yimin kalaman zan kiraki kizo kigani, sedai fatan Allah ya hadamu da masoyanmu  na gaski….. Jalila ya hango tana sakkowa daga steps, tayi kyau sosai, amma abunda yabashi mamaki ta rame, “ko bata da lafiya ne? Tayi rama sosai, itama tana daga ido sukayi ido hudu, taji gabanta ya fadi “kaddai ace har yanzu Jalal bashida lafiya, wace irin rama yayi haka?” kallonta yake yadda take tafiya step by step, Hanan kam tuni taga abunda yake faruwa tai murmushi a ranta 

Jalila ta karaso tace “Yaya Jawwad ina fatan komai lafiya, naji Naja tanata masifa, Hanan me kikayi mata ne?” 

“meko zanmata? Dan kawai ta ganni da Haidar ne” 

Abdallah yace “karya takeyi tun dazu ta tsareshi anan tana zuba masa kalamai, tun yana jinkunya naga alamar kalaman sun fara shigarsa, murmushin yake Jalila tayi tace” nikam ki lallaba ku rabu lafiya”

“karma a rabu lafiyan ba abunda ya dameni bane, haidar dina ne agabana” 

Abdallah yace “ke Hanan kinfiye zakewa, ance miki anbadashi amma kin nace” Hanan ta lura yadda Jalal ke kallon Jalila, itama Jalila tana satar kallonsa amma bata bari su hada ido, Hanan ta gyar murya tace

“Queen kinga Yayyenki nan biyu sun takuramana, shi Abdallah nasan yadda Siyama ke kasheshi da kalaman soyayya, amma shi Yaya Jalal ban saniba, da nasani da na ramawa Haidar, amma gayamin ko kin san budurwarsa?” hararar Hanan tayi tace “Aiba tare muke yawo ba balle in san budurwarsa, seki tambayeshi ai” 

Hanan ta tintsire da dariya dama tana sane tayi hakan? 

Jawwad yace “Baby ina Abba ne?” 

“Yana cikin gida, yaya Abdallah ku shiga sekuyi sallama da Abban” 

“ok bari muje” 

Jawwad ya musu rakiya suka nufi cikim gida

Jalila tayi mamaki yadda Jalal yake hira bazakece shine ba, Jalila tafara kokarin saka jakarta a mota

Jalal ya dan kara kurawa Jalila ido, yazo kusada ita ya tsaya, ya danyi kasa da muryarsa yace 

“meyake damunki kika rame haka?” bata dago ba tace

“ni ban wani rame ba, dama haka nake” 

“hmm, shikenan tunda kince haka, amma yaushe zaki dawo?” 

“Ka Aike nine, wai ina ruwanka danine?” 

“Aiba abun zafi bane, meye nayin fushin kuma?” 

“idan na tafi bazan dawo ba, idan na tafi zan hutawa raina indena ganin masu ba kanta min rai, kaima ka huta dame yi maka shishshigi, kaci karenka babu babbaka, inka gadama kaima ka gina club din shna giya” 

“meyasa ba kya mantuwane? Abu baya wucewa a gurinki kenan?” Su Hanan ya gani suna fitowa dan haka yace mata

“zaki iya zuwa ki zauna a wani garin, kibar Jawwad din naki da Nana tsawon lokaci?, idan ina ganin ki inajin kwarin gwiwar dena wani abun, dama zan miki sallama ne dan inaga kafin ki dawo, zan koma Dubai da zama, bazan kara dawowa Nigeria ba, har abada, ina fatan kiyafemin kura kuran danayi miki, Sannan Nagode da kokarinki a kaina, keda Ummi bazan tabawa mantawa daku ba, sannan A shekarun baya, wani zuwa da kikayi, Su daddy sun baki kyaututtuka, ciki hada wani Jan Alqur’ani me red din box, nina baki kyautar wannan Alqur’ani sannan Akwai Ajiya ta a ciki. 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

❤️❤️❤️ ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 inayinku irin sosai din nan comments dinku nasani nishadi da bani karfin gwiwa inayinku ina kaunarku nima Allah ya barmin ku 😍😍😍😍

Share please 

I want comments not stickers or just thanks 

Daga alkalamin Aysher cool.

Back to top button