Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 22 Book 2 Complete Novel

Haka khadija tacigaba da wasa da hankalin Saudat ba tareda ita Saudat din tasan me khadija take shiryawa ba. 

Khadija ta karbi kudade dayawa agurin Kabir da sauran kudaden data damfara a gurin samarinta tafara business na atamfofi da kayan sawa, gurin manyan masu kudi, saboda tace in Allah yasa lokacin bikinta kece raini zatayi bazata barima azo ayi wani abu  a wannan gidan nasuba, biki za’ayi kaman na diyar sarakuna, dan jikinta yana bata zatayi galaba akan Habib saboda alamun sun nuna yanada saukin kai da tausayi. 

Ranar da habib yadawo Nigeria me gadinsa yakira khadija a waya yasanar mata, taimasa godiya take ta turamasa katin 5k saboda albishir din dayayi mata, shi habib har yamanta da batun me turomasa messages, se bayan kwana biyu yamaida layinsa na Nigeria messages din khadija yafara cin karodasu ba adadi, tsaki yayi ya aje wayar yashiga sabgoginsa, kwanan sa uku da dawowa yakoma gurin aikinsa, yana zaune a office aka kirashi a waya, bakuwar lamba ne dan haka beyi tunanin komai ba ya daga wayar, tana sallama ya gane wacece, amma yarasa meyasa duk lokacin dazata kirashi baya iyayimata rashin mutunci. Yana cikin wannan tunanin yaji muryarta tana cewa “Rayuwata, barka da dawowa kasa Nigeria, ina maka barka da zuwa nayi kewarka matuka, nayi rashin lafiya sosai bayan tafiyarka, ina fatan kundawo lafiya” Abun mamaki taji yace “ya jikin naki?” seda tayi murmushi ta wani lumshe ido “Jiki ina samun sauki Alhamdilillah” 

“me yake damunki?” takuma kashe murya “hayatee komaima yana damuna, nikaina narasa meke damuna, amma jigon rashin lafiyata soyayya ce, at least zansamu relief tunda ka dawo, bari in barka ka huta, I love you hayatee” ta kashe wayarta, tunda habib ya dawo Nigeria tafara shawo kansa saboda koyace katta kara kiransa bata fushi, kullum cikin nuna masa soyayya take, ta lura ya dan damu akan maganar rashin lafiyarta, hakan yasa tafara ji ajikinta burinta yana daf da cika. Tacigaba da kokari tana dauke hankalin Saudat daga kokarin zuwa gidan habib. 

Seda khadija ta lura habib yafara bata kulawa, seta dena tura masa message ta kashe wayar da take kiransa da ita domin ta tabattar da ko yafara sonta, haka ta danne zuciyarta tsawon sati biyu bata kirashi ba kuma bata turamasa message ba. 

Ranar da sati biyu ta cika khadija ta kunna wayarta, messages ne suka shigo wayarta, data bude duk na habib ne sekuma kamfanin layi, dayake shikadai take kira da layin, duk messages din yana tambayarta ina tashigane layinta baya shiga Allah yasa lafiya, bata san lokacin datayi wani tsalle ba tayi ihu a daki, mamanta ta shigo dakin da sauri “ke lafiya meyasameki?” 

“bakomai mama bansan nayibane” 

“to Allah ya shiryeki auta” mama ta fice khadija ta mike tsaye hada rawa a cikin daki. Bayan sallar magariba kabir ya tura yaro yace yayi masa sallama da khadija, tace yaron yace tana zuwa, ta shirya zata fita gurin kabir sega kiran Habib. Nan da nan ta tashi ta kulle kofa tazo tanemi guri ta zauna akan gado ta daga wayar cikin sanyin murya tai masa sallama, kafin ya amsa sallamar yace “ina kikashiga haka tsayin wannan lokacin?” 

“hayatee bani da lafiya ne fa” 

Cikin sauri yace “subhanallah jikinne har yanzu? Yanzu kina inane?” 

“ina gida naji sauki” 

“dagaske kinji sauki kokuma wasa kike?” 

“Am serious, yau naci Abinci sosai nayi wanka nayi kwalliya, i wish kaga kwalliya nan hayatee” murmushi yayi yace “dagaske?” “Eh mana nayi kyau sosai, sedai ciwon so duk ya ramar dani” 

“yaushe zan ganki?” 

“Duk sanda kakeso, a shiryenake” 

“kiyi fixing time, seki gayamin zanzo mugaisa” 

“masha Allah, hayateee harnaji na warke gaba daya” 

“to Allah yakara afuwa, bari zan shiga gida” cikin sauri cikin shagwaba khadija tace “haba hayatee ni wallahi bangaji dajin muryarka ba, kalli tsayin lokacin daka dauka bana jin muryarka fa” haka khadija ta dinga hilartasa suka shantake suna waya, tana masa hira me dadi har gurin goma da rabi na dare sannan sukayi sallama, Kabir yagaji da jira gashi lokacin sanyi amma khadija taki fitowa maganar duniya tayi banza taki bude kofa tacigaba da wayarta, daga baya tace ace masa yacigaba da jira inyaga ze iya tana da abunyi me mahimmanci datakeyi. 

Seda ta gama wayarta tace ace masa ya tafi bazatazoba. Saudat ta shigo dakinta tace “khadija wai dan Allah wani zazzafan kika samune haka kusan awa uku kina waya, naga duk saurayin dakikayi bakya yiwa Kabir wulakanci amma yau kin shuka masa dayawa fa” khadija tayi wani shu’umin murmushi tace “ai ke bar gara kawai, najefa fatsata a ruwa kuma da alamu nakamo kifi me nauyin gaske, ba kama kifinne matsalar ba, sedai zanyi gwagwarmaya kafin kifin yazama mallakina saboda akwai masu farautar wannna kifin dayawa abakin ruwan” ta kuma kallon Saudat tace “kodayake kince ranar biyan bukata rai ba abakin komai yakeba yar uwa, dan haka zan jure gwagwarmaya da kubale in mallaki kifin nan” 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Saudat tace “kinga ni kiyimin hausar dazan gane, se wani kwana2 kikemin, nibangane mekike nufi ba” 

“karki damu zaki gane very soon yar uwa” 

Bangaren habib kuwa, Salma ta damu matuka baya kaiwa tsawon wannan lokacin a waje, amma yau ya kai, tayi2 yagayamata dalili yace bakomai wani abune ya rikeshi haka ta hakura.

Wasa2 taga ya maida hakan dabi’arsa baya shigowa gida se bayan goma, dataga bashida niyyar denawa itama ta watsar dashi tacigaba da sha’aninta, seta ajiye masa abincin sa akan dining tayi kwanciyar ta, hakan yakara bashi damar sakewa suyi waya da khadija. 

Ranar juma’a da yamma suka shirya zasu hadu a wani gurin shakatawa, saboda khadija bataso yazo da rana gidansu Saudat ta ganshi, yarigata zuwa gurin yana zaune yanata duba agogo har yafara fidda ran kozatazo, yana kokarin kiran layinta ne, yaji kamshi me dadi yacika masa hanci, dukda yajuya baya, amma tana kallonsa tabaya tasan shine, a hankali ta tako tazo bayan kujerar dayake ta tsaya, ta durkuso da kanta a hankali tace “Hayateee barka da zuwa” ya dago kai ya kalleta daga sama har kasa, doguwar mace ce, sannan tana da dan kiba kadan, baza akirata da fara tas ba amma tanada hasken fata sosai, tabbas khadija tana da kyau dai dai2 gwargwado, murmushi yayi mata “sannu da zuwa masoyiyar boye” murmushi tayi ta zagaya ta zauna akan kujerar datake facing dinsa, suka gaisa sun sha hira sosai sannan ya dauketa ya kaita har bakin layinsu shikuma ya tafi. 

Khadija tayi nasara samun zuciyar habib tana nunamasa soyayya iyayinta, haka habib yasake da khadija suke soyayya ba tareda Salma tasani ba, yakanzo gurin khadija tadi, Saudat ta fusakanci yan kwanakin nan khadija tana cikin farinciki. Bayan sun gama cin Abinci khadija ta tafi daki ta shafe kusan awa uku tana waya, a iya sanin Saudat datayiwa khadija tasan bata son doguwar waya, amma ya akayi kwanan nan take waya haka, mikewa tayi tabi khadija daki, taje ta tarar da ita tanata zuba shagwaba a waya, tana ganin Saudat ta shigo dakin tai maza tayiwa habib sallama ta mike zaune 

“Saudat lafiya kuwa na ganki haka ba zato babu tsammani” 

“hmm dole kice haka mana almost 3hrs kina waya, ba’a kojin mekike fada, shikam wani me nasarar ne haka? Kodai kin hadu da dream hubbyn nakine” wani kasaitaccen murmushi khadija tayi “kwarai kuwa kedai kiyitamin Addu’a” 

“shine babu ko Labari balle a gabatarmin dashi” 

‘mekikeci na baka na zuba, shida zezama sirinkinku sekin gaji da ganinsa “Saudat tace” Allah sarki Kabir yanata tsuma ze aureki “

Tsaki khadija tayi

” ke dalla kidenamin zancen wannan wawan, nifa badan ina tausayinsa ba da tuni na dade masa wulakanci, kodayake wulakanci na nawa, bashida zuciya ne”

“Mhmmm nikam nace khadija waime ake ciki game danawa damuwar ne, wallahi khadija ko baccin kirki bana iyayi” Ajiyar zuciya khadija tayi tace

“gaskiya Saudat ina tausaya miki, abun nada matukar tausayi, nikaina na kagu inga kinshiga wannan daula amma semunbi komai a sannu, bakisan iya kokarin danakeyi miki ba, yanzu haka nabada cigiyar in yadawo a sanar dani, naje har layin gidansa dakaina, amma ance an hana shiga layin ba tareda wanda zakaje gurinsa yasaniba, amma inata miki kokari “

” to khadija Allah yasa adace”

“zama adace kakri damu Saudat”. 

Duk ranar da Habib zezo gurin khadija tadi sedai su hadu a gidan kanin mahaifiyarta acan suke zancen, soyayya ce me karfi tashiga tsakanunsu, duk kasar dayatafi A gaggauce yake ya dawo domin ya hadu da ita, baya jure dogon lokaci basu hadu ba. 

Habib da kansa yacewa khadija ze turo iyayensa ayi maganar aure, amma zeje maiduguri tukuna in yadawo seya turo, tayi murna ranar kamar ta zauce bata taba zaton a abubuwa zasu mata da sauki haka ba. 

Gefe guda habib yanata tunanin, yadsa ze sanarwa da Salma batun auren dayakeso yayi, dan yasanta da matukar kishi, dan haka ya yanke shawarar zefara zuwa maiduguri in magana tayi nisa yagayawa Salma. 

Koda Habib yajewa mahifiyarsa da zancem Aure bata bashi goyon bayaba hasalima faada takama yimasa “haba habib, yaushe kayi auren fari da har zakace zaka kara aure, yarinyar nan yar uwarkace fa, mahifinka da mahifiyarta uwa daya uba daya, hakan ze iya shafar zumuncinku, gaskiya ka hakura kozakayi aure ba yanzu ba” yakada yaraya amma mahaifiyarsa taki yarda, Habib tunda yake betaba yiwa mahaifiyarsa musuba se wannan karon, yaita mata magiya, karshe seda yaje yagayawa yayanta yazo yasa baki, badan tasoba haka ta amince, amma tace kafin aje neman auren se anyi bincike, akayi bincike amma bincike ya nuna khadija ba mutuniyar kirki bace, batada aibu, sedai rashin kunyarta da iya fitsara, yan uwan mahifin habib suka gayawa mahaifiyarsa nan ma ta dage tace baze yuwi ayi auren nan ba. 

Khadija yagayawa khadija halin da akeciki ta damu sosai nan ta shiga addu’a ba dare ba rana, ta sanarda mahifiyarta komai sukacigaba da addu’a habib yanakin baze iya rabuwa da itaba dan haka yacigaba da lallaba mahaifiyarsa. 

Habib ya canza gida, yakoma wani dankareren gida daya Gina a gadon kaya, gidane na alfarma matuka, anan ya tsara inya auri khadija ze hadasu da Salma. Bayan khadija ta tabattar da Habib ya tashi daga gidansa, taje ta samu dansandan dayake gadin rukunin quaters din dasu Habib suka tashi, tabashi kudi, ta shiryamasa abunda takeso yayi mata, sannan ta dauki Saudat sukaje tsohuwar unguwarsu Habib da nufin suje sugani yadda zasuyi kozasu samu Habib, suna zuwa dansanda dayake gadin rukunin quaters din yace musu “wakuke nemane?” khadija tace “gidan Habib kamal mukazo” 

Nan yagaya musu “Ai yabar quaters din nan, tunda yadawo daga Dubai bezoba” 

Da sauri Saudat tace “ina suka koma?” 

“kamarya ina sukakoma dokace, da sun yadda daku dakunsan inda suka koma dan haka kubar nan gurin” khadija tai kokarin yagaya musu amma yai musu korar kare tare da barazanar ze kullesu, khadija ta kashe masa ido alamar aikinsa yayi kyau. 

Habib yasha wahala sosai sannan mahaifiyarsa ta amince da maganar Aurensa da khadija, dangin mahifinsa ciki harda mahifin Salma, sukazo nema masa auren khadija gurin wan mahaifinta, sannan mahifin Salma yajawa mahifiyarta kunne kan be yadda wani yagayawa Salma Habib zekara Aure ba shida kansa ze gaya mata, dangin mahifin Habib suka kai kudin Auren Habib akasaka wata shida. 

Khadija jitake kaman ba itaba, habib yagaya mata ansaka wata shida ji take yamata nisa wata shidan nan, se murna take ta tafi dakinsu Saudat cikin zumudi tana kiran sunan Saudat, tana zuwa ta tarar da Saudat tana kuka, da sauri ta karasa inda take tadafata “Saudat meyasameki haka?” Saudat ta share hawayenta ta girgigiza kai tace “bakomai khadija” 

“A’a da komai gayamin menene?” Saudat ta dan gyara zama tace “khadija har yanzu burina becikaba, gashi ke zakiyi aurenki amma ni se gararamba nake, ba wani tsayayye wanda nake hangen yakasa samuwa, yanzu zakiyi aurenki ki barni” khadija ta riko hanun Saudat sannaan tace “Saudat dan adam be isa yasamu abunda ba rabonsa ba, indai habib rabonkime sekin aureshi, inba rabonkibane ba ba yadda zakiyi, shawarata agareki shine karki tsaya jiran Habib, ki bata lokacin ki, tun wuri kinemawa kanki mafita” 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

“khadija kina nufin in hakura gaskiya bazan iyaba kome zefaru, kedai kiyi aurenki ni zancigaba da fafatukata, sena auri Habib wallahi” murmushi khadija tayi “to shikenan Allah yabawa me rabo sa’a” daga nan ta tashi ta fice. 

Habib da kansa ya shirya ya dauki Salma suka je maiduguri, yakaita gidansu da nufin tayi musu yan kwanaki, mahaifin salma yasa aka kiramasa ita dakinsa, ya zaunar da ita yayi mata nasiha sosai sannan ya sanarmata Habib ze kara Aure, ji tayi kaman mahifinnata ya watsa mata wuta, take idonta yayi jawur ta kalleshi “Aabba kan nufin Habib dinane zeyimin kishiya, kuma kake gayamin innalillahi wa inna ilaihi raji un, dan Allah Abba kacemin da wasa kake, wallahi bazan iyazamabda wata a matsayin kishiyata ba” 

“Ke meye hakane? Akanki aka fara, to ki nutsu, akanme mijinki yanada halin daze auri mata hudu ya kuma iya rike su danme zakice baze aure ba, karki kuskura inji kin daga masa hankali shiyasa nace nizan gaya miki da kaina, dan haka kiyi hakuri, daba a aure dakema baze aureki ba, yakamata kija girmanki tunda kece uwargida, dan haka kiyi hakuri tashi kije Allah yayi miki Albarka ” da kyar ta mike tsaye tana tafe tana hada hanya ta tafi dakin mahaifiyarsu, tana zuwa ta zube a jikin mamansu takama kuka

” mama dama habib ze iya yimin kishiya, ko shekara biyu bamuyi da aure ba shine ze auri wata, mama anyimin adalci kenan” ajiyar zuciya mama tayi tana dan dukan bayan Salma alamun rarrashi 

“kiyi hakuri Salma kinji, kuma bazamu kira abunda habib yayi da rashin kyautatawa ba tunda shima danmune, ni macece salma masan meye kishi abune me ciwo amma kiyi hakuri zakiga ribar hakurin, kiyi masa fatan alkhairi sannan karki nuna masa kin damu” 

“A’a Mama bazan iyaba, wallahi zuciyata zata fashe, mama bakisan menakeji ba, bantaba mafarkin Habib zemun kishiya ba, in hakanema yabari sena kwana biyu a gidansa mana, amma yaushe mukayi auren zemun haka, toni na hakura da aurennasa yaje ya zauna da wadda yakeso” nan mama taita rarrashinta tana nunamata illar cewa zata kashe aurenta. Kwanan salma biyu a gida sannan habib yazo daukar ta, iyayen salma sam basu canza masa ba, sedai Salma fuskarta sam babu walwala zakayi zaton jinya takeyi, harsukazo kano batace masa uffan ba. 

Bayan sunkoma gidama ta tattara tayi watsi dashi, bata cin Abinci sosai kullum cikin kuka take abun yafara damun habib sosai dan haka yaje ya sameta a dakinta yanzuma idonta jawur da alama tasha kuka sosai. A hankali ya karasa ya zauna kusa da ita yayi kokarin janyo ta jikinsa amma ta kwace, ya kalleta “habibty dan Allah kiyi hakuri, bazanyi Auren nan dan in wulakanta kiba, matsayinki yana nan a zuciyata kaman yadda kika sani, dan Allah badanniba kidena azabtarmin da kanki, kidinga cin Abinci kin rame sosai kindena bani kulawar da duk kike bani, please my Salma calm down” kuka takuma saki me ban tausayi, ya rungumeta ya dinga mata nasiha yana rarrashinta a irin kishi na salma be taba tunanin ze iya rarrashinta ta hakura ba, kusan kullum se iyayenta sun kirata a waya anmata nasiha da addu’oi hakan yasa tasamu raguwar radadin da take ji a zuciyarta. 

Biki nata karatowa anata shirye2 amma har yanzu yan gidansu khadija basu taba ganin Habib ba, sunyi mitar sunyi harsun gaji amma taki yadda aganshi, yayyenta sunyi fada sosai dasukaji cewar ba Kabir ne yakawo kudin auren khadija ba, amma aka barshi yana wahala, amma mahaifiyarta ta goyamata baya, hatta yan anguwa bakowa yasan khadija zatayi aure ba saboda tace ba kowane garane zezo mata gurin biki ba, mussaman ma yan unguwarsu yan bakin ciki, Habib yana sakarwa khadija kudi yadda yakamata anata shirin biki. Babban abun mamakin yadda haryanzu kabir besan khadija zatayi Aure ba yana zuwa gurinta tadi, kuma yanabata abu takarba, yauma suna tsaye tagama hira da Kabir wani makocinsu yagansu, sungama tadi ya dakko uwar leda cike da kaya yabata, nan ya jinjina kai lallai wannan yarinyar tacika yar banza, aikuwa sena gayawa yaron nan, kokuma inje har gida ina sanarwa da uwarsa dan watakila idan nagaya masa wannan makirar yarinyar tace karya nake babarsa zanje ingayawa.

Washegari da yamma makwabcin su khadija yatafi gidansu Kabir, dayake abokin baban kabir ne kafin ya rasu, yaje gidansu kabir yai sallama mahaifiyar kabir tayi masa iso, bakowa a gidan se ita suka gaisa da mutumin, tunda mahaifinsu kabir ya rasu jefi jefi yakanzo su gaisa shima se a shafe shekara bezo ba, suna ciki gaisawa ne kannen kabir suka shigo suka gaisheshi ya amsa yana su karimane suka girma haka masha Allah, yana nan zaune yaga suna gaganiyar fita da murhu da ice waje, seda suka gama ya kalli mahaifiyar kabir yace “suwai ba waime yaran nan suke da murhu a waje” mahaifiyar kabir tace 

“kasan yanayin rayuwar ne se godiyar Allah, suna dam soye soyene a waje suna siyarwa, in sun siyar muke samun biyan bukatun yau da kullum da nauyin karatunsu, ga kuma batun aure na kokarin tasowa, ba mai yimana komai se Allah” 

“Amma ina kabir, naji ance yasamu aikin kamfani kwanakin baya, ga kuma nakan ganshi wataran a kasuwa yana neman kudi, ya akayi yake barinku har se kannensa sunfita waje suna siyarda abu” Ajiyar zuciya mahaifiyar kabir tayi 

“hmm lamarin kabir se addu’a inzaka yankani bansan inda yake kai kudi ba, kullum na tambayeshi se yace bashida kudi, semu shafe wata uku ko gawayin girki be saimin ba balle Insaran kayan Abinci, ficika kabir baya moramin a kudin dayake samu, haka kannensa zasu shafe tsawon likaci a gida ba makaranta saboda ba abiya kudin makaranta ba amma baze iya biyaba, tun ina magana harna hakura na zuba masa ido”

“Tirkashi anya kabir nason yagama da duniya lafiya kuwa?” 

“to yazanyi, na hakura na kyale shi yaje in abunda yakemin ya kyauta yaje shima ze gani” 

“to bari in gayamiki wani abu, kimanin shekaru shida kenan kabir yake zuwa gurin wata yarinya a kusa da gidana, ita yake kashewa kudadensa, yarana suna shiga gidan suna gayawa mahaifiyarsu irin hidimar dayake mata, yanzu haka yarinyar bikinta saura sati shida, shi kabir ne saniba kuma ko jiya akan idona yabata katuwar leda cike da kaya”

Zaro ido mahaifiyar kabir tayi “kana nufin dama dagaske ne kabir yana neman yarinya, a gayamin amma ban yadda ba” 

“Aiko yakamata ki yadda, dan yarinyar ba karamar hatsabibiyabacce ba, ya dade yanamata wahala duk abunda yasamu ita yake bawa, yanzu kuma zatayi aurenta ta barashi, gara tun wuri kisan halinda kike ciki, ni zan tafi Allah ya kyauta gaba” haka mutumin nan yatashi yabar maman kabir da bacin rai batasan lokacin data fashe da kuka ba “yanzu duk wahalar danayi daku amma sakamakona kenan agurinka kabir, ka fifita budirwa sama dani” haka ta cigaba da kuka, da magariba kannen Kabir suka dawo daga gurin sana’arsu amma suka tarar da mahaifiyarsu ranta a bace, na suka shiga jero mata tambayoyi, bata boye musu komai ba tagaya musu, karima tace “aini na dade da sanin zancen nan, banason ranki yabacine, amma yaya kabir har adashi yake yaje ya kaimata, komai yasamu ita yake kaiwa” 

“Amma karima shine baki taba gayamin ba” karima tace “to mama meye amfanin fadar, yanzu da kika sani meyakara inba bacin rai ba, ai ga sakayya nan, zatayi aure tabarshi kuma itama zata gani, dan Allah kidena kuka” haka suka cigaba da rarrashin mahaifiyarsu daren ranar mahaifiyar kabir kasa bacci tayi, mussaman inta tuna matsin rayuwar dasuke shiga amma Kabir baya musu komai yana can yanayiwa budurwa bauta. 

Yau khadija ta shirya ta tafi kasuwa bata nan, mahaifiyar kabir kasa jurewa tayi ta shirya ta tafi gidansu khadija, da taje khadija bata nan se mahaifiyar khadija ta tarar suka gaisa sannan maman Kabir tace “dama nice mahaifiyar Kabir” umman khadija tace “Allah sarki sannu dazuwa, kabir yaron kirki ya kuke ya yan uwansa” 

“muna lafiya kece mahaifiyar khadija?” 

“eh nice ya akayi ne?” 

“yanzu dama bazaku bashi auren yarinyar ba amma kuka dinga sawa yana kashemata kudi har tsawon shekara shida, ni ina can ina fama da maratun kannensa, kukuma ya tare a gurinku, ga wahala gashi yarinyar zatayi aurenta kunyi mana adalci kenan” takarasa maganara idon taf kwalla, umman khadija tace “to baiwar Allah ai se hakuri dama indai ka haifi namiji ai wata ka haifawa, kuma ita mace allura ce a cikin ruwa me rabo ka dauka, kuma kinsan halin yarn zamani ba’a iya musu dan haka se hakuri” 

“Yanzu hakan yayai daidai kenan”? 

“to inma beyi daidai ba aisedai kiyi hakuri” ana haka sega khadija ta dawo, batabi takan mamanta da bakuwar dasuke tareba ta shige daki abunta, mamanta ta kirata ta nunamata maman kabir tace “ke ga babar kabir nan tabiyo jin kadin ya akayi kinsan bazaki auri danta ba kika dinga ci masa kudi, itakuma baya kulada ita” kallon mahaifiyar kabir tayi tace “banda abunki aiba nina rikeshi nahanashi tafiya ba, kuma ni bance karya kulaldake ba, abunda nasani niba sa’ar aurensa bace dannafi karfin auren matsiyaci irin danki m, kidubeni da kyau  banyi kalarsa ba dan haka yaje yanemi daidai da shi baniba, sannam ze iya lissafa abunda ya kashe a biyashi konawane, zan auri miji daidaidani danki shine matsiyaci se abiyashi kudinsa sekuma me? “

Bude baki mahaifiyar kabir tayi cikin mamaki “Au hakama zakice” ta juya ta kalli mahaifiyar khadija “yanzu kun kyautamin, kina kallon yarki abunda kukayi adalci ne? Shikenan kuda Allah kuma wallahi ke sekinga sakayya a rayuwarki, se Allah yabaki dan dazemiki fiye da abunda kikasa dana yaimin, kirikiri insha wahala da yayana, tun suna kanana har suka girma, amma kika kanainayemin yaro, kin hanashi ya amfanamin komai, alhalin kinsan ba aurenshi zakiyi ba, wallahi na barki da Allah” kuka sosai mahaifiyar kabir takeyi, wanda hakan ya janyo hankalin mutan gidan suka fifito tsakar gida, ita kuwa khadija tace “ai kokinki ko kinso dole kibarni da Allah dama, kabir ne naci rabona dama rayuwa ta gaji haka, kinzo se hayagaga kike mana kin taramin mutane sekace namiki sata aikin banza kawai” khadija tai tafiyarta ta shige daki haka mahaifiyar kabir ta baro gidan gwiwa a sabule tanata kuka, tana zagin khadija. 

Koda mahaifiyar kabir takoma gida inta tuno abunda yafaru se tayi ta kuka, da magariba kabir ya shigo gidan, yazo ya gaisheta a fusace tace “ka tashi bana bukatar gaisuwarka kabir, kaje na yafewa diniya kai na sallamaka ga yarinyar daka fifita fiye da uwarka, kabir ashe tsawon shekaru shida kanayiwa yarinya bauta itada iyayenta, amma ni wani lokacin abunda zamuci da kannenka gagararmu yakeyi kana kallo ko a jikinka, kaje idan abunda kayimin ka kyauta kaje ga duniya nan”

“haba mama wacee irin maganace wanan wane munafikin ne yagaya miki haka?” 

“dalla rufemin baki nice munafukar, har gidansu yarinyar naje yau, suncimin mutunci ita da uwatta, kuma suka tabattar min da wani zata aura, kayi asara kabir, bazanma bakiba amma hakkina ya isheka wallahi” a sukwane kabir ya mike tsaye “bangane khadija zatayi aure ba wayagaya miki?” wani takaici ne ya tokare mata a kirji wato shi ta batun auren ne ya daga masa hankali, shiru tayi ta sunkuyar da kai tanata sharbar kuka, a sukwane ya fice yabar gidan. Be tsaya ko ina ba se gidansu khadija akayi masa sallama da ita, yau yaci sa’a ta fito, ko gaisawa basuyi ba a gigice yace “khadija wai dagaske aure zakiyi”? 

“injiwa? 

” mama tacemin tazo gidan nan, an tabattar mata aure zakiyi, khadija ki gayamin gaskiya “

” nifa bana son wannan abun ds kakeyi ka nutsu mana, nibawani aure da zanyi da auren zanyi da bakasani ba, ka dinga bincike ka tabattar da abu kafin kazo kanamin surutu”

“Alhamdilillah har naji dadi, khadija inna rasaki bansan ya zanyi ba” dariyar mugunta tayi masa tace “kaga zankoma gida ina aikine, adinga hakuri dan ba kullum ake kwana a gado ba, kaga dama A’ayi bikin kawata ne zanturomaka 100k a account dinka inaso asamomin sababbin dari biyar biyar”

“100k dijena ai sunyi yawa, yazaki lika har hundred thousand” 

“bacewa nayi kabani kyauta ba, zanturomaka ne kamin canjinsu kawai” 

“dija samun sabon kudi yana dan wahala, amma zan duba miki insha Allah zan kawomiki karki damu” 

“shikenan yayi kyau, ka gaida gida” daga nan ta shige cikin gida abunta. 

Lokacin biki nata kuma karatowa, Salma ta rame sosai, duk tayi duhu saboda damuwa, mahaifiyar Habib da kanta tazo kano, taitayiwa Salma nasiha tanabata hakuri, sannaan tajawa Habib kunne akan ya kulada Salma, Ta hadasu tayi musu fada sosai sannan takoma maiduguri. 

Saura sati biyu biki Habib tafiya takamashi, akai sa’a a ranar akakawo iv din biki, yaje dakin Salma ya sameta a kwance ya zauna a kusada ita yace “Habibty anjima zan tafi, ga katin biki an bugo ko da wanda zaki gayyata” 

“Allah ya sanya Alkhairi” shine abunda tace masa kawai 

“Habibty banajin dadin yadda kike shareni, nasan namiki laifi amma horon yayimin tsanani” 

“dan Allah habib ka kyaleni, ka tafi karka makara” 

“kina korata kenan?” 

“niban koreka ba amma ka kyaleni” 

“shikenan amma kimin Addu’a mana” 

“Adawo lafiya Allah ya kiyaye hanya” haka ya juya ya tafi jiki ba kwari, bayan fitarsa ta dakko wayarta tana kallon hotunan bikinta da Habib tana kuka, hotunan Sauda data ganine yasataga bata kyauta ba yaushe rabon dasuyi ko waya, dan haka tasaka tshohon layinta ta kira Saudat. Ba karamin mamaki Saudat tayi ba dataga kiran Salma dan haka cikin sauri ta daga wayar 

“salamu alaikum” Saudat tafada, 

“wa’alaikum salam, Saudat yakike ya gida” 

“lafiya kalau Salma, Salma naje gidanki ba adadi bana samunki, daga baya aka cemin kuntashi bansan inda kikakoma ba” 

“eyya kiyi hakuri Saudat, kinga mun dade bama Nigeria ne, kuma damuka dawo ba dadewa munkoma gadon kaya” 

“Allah sarki yanzu kina gari kenan, aiko insha Allah cikin satin nan zanzo dukda munata shirin biki” Salma tace 

“Masha Allah, bikin waza’ayi? Amma ba gayyata” 

“Khadija ce zatayi Aure saura 3 weeks” 

“Kai kice na bugo waya a dai dai, da yanzu se ayi babuni ai yakamata inzo bikin khadija, dukda nima Habib ne zeyi Aure kusan lokaci dayane ma dana khadija” seda gaban Saudat ya fadi

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

“A…. Au… Aure kuma, wai wani Habib din kike nufine?” 

“Hmm Saudat kenan, wane Habib kuwa, mijina mana, abun yabaki mamaki ko? Aure zeyi Saudat, amma Insha Allah zanzo bikin khadija ban manta dawainiyar da kukayi a bikina ba” cikin Saudat tace “to shikenan Salma se anjima, semun sake waya” ta kashw wayarta, mikewa tayi a sukwane ta tafi dakin khadija tana kwala mata kira

“lafiya kikemin wannan kiran, kaman wadda kikebi bashi meye haka?” 

Saudat ta karaso cikin dakin tana haki ta zauna sanna tace “Khadija na shiga uku” 

“Kamar ta kinshiga uku, meyasameki?” 

“Ni narasa ta ina zanfara, Salma sun dawo Nigeria yanzu haka mukayi waya da ita tagayamin unguwar dasuka koma, wai amma Habib Aure zeyi saura 3 weeks, Khadija Aure zeyi nikam na kade, wallahi ko wacece bata isaba wallahi ” 

“to shine kika daga hankalinki haka, kemafa mijin watane kike kokarin sekin Aura, har gara ke baki Aureshin ba, ita matarsa ma bata daga hankalinta ba seke, Saudat abun nan naki yafara yawa, you better find another solution, kidena bawa kanki wahala, inbahakaba ki mutu bakiyi Aure ba”

Mamakine yacika Saudat ta kalli khadija “Au hakama zakice, dole ki gayamin haka tunda ke zakiyi Aure, to bari kiji ingayamiki wallahi kowa ze aura inze auri mata hudu seyasaki daya ya aureni, duk bala’in daza’ayi sedai ayi wallahi, matsalata tawace zanyi kokarin shawo kan matsalata inci ka burina, zanje gidan Salma sedai ai duk wacce za’ayi “

Murmushi khadija tayi” To Allah yabawa me rabo sa’a, fada da aljani ba wasa ba, kije Allah yabawa me rabo sa’a” tsaki Saudat tayi ta fice daga dakin, sosai khadija take dariya tace “sha3 zakigane bakida wayo, keda Habib har abada” 

Duk yadda mutan gidan su khadija sukaso suga mijin dazata aura ki tayi , kome za’ayi sedai a gidan yan uwan babansu, amma taki yadda sam yazo gidan, invitation din daurin Aure ma hanawa tayi agani, saboda kar Saudat tagano, tayi mata hauka. 

Yau khadija ta yanke shawarar zata gayawa kabir Aure zatayi zata sallame shi, yadena zuwa gurinta yaje shuma Allah ya hadashi da rabonsa, da magariba kabir yakawowa khadija wannan kudin, lokacin saura kwana takwas biki, ta karbi kudin tayi masa godiya suka gama hira zetafi tace “dan jirani ina zuwa” ta shiga cikin gida ta dakko iv ta fito, yana nan tsaye inda ta barshi ta miko masa kati. Yasa hannu ya karba yace “wannan fa?” 

ba fargabar komai tace “duba kagani mana?” 

Kafin kabir yagama karanta katin, yaji kafarsa na rawa, fitsari yacika masa mara

“khadija wannan invitation din na waye?” 

“bangane ba bagashi a hannunka ba kana gani, sunan waye kuwa, katin Aurena ne, saura kwana takwas dama ita duniya haka ta gada, dan haka iname baka hakuri Kabir Allah yahada kowa da rabonsa, nasamu irin mijin danake mafarkin Aure dan haka 

Cikin tsawa Kabir yace “Dalla malama dakata, kina nufin zaki Auri wani baniba wallahi khadija karya kikeyi, shekara shida ina wahala dake, amma kice bazaki Aureniba wallahi karya kikeyi” 

“dalla dakata, kai namaka kalar auren matsiyaci kamarka, wanda se ya samo da kyar, nasamu hamshakin attajiri daidai dani kaima seka samo yar talakawa wadsa zata iya da talaucinka ku daidaita, inkana ganin bazaka hakura ba, ka lissafa nawa ka kashemin kobo bayan kobo za’a biyaka hada Riba “

” Wallahi baki isaba, kece babbar matsiyaciya kwadayayyiya, kije k Auri wani khadija, kin kyauta amma wallahi yadda nasa uwata kuka saboda ke, kema se kinyi wanda yafi na uwata, zan nuna miki ni dan halak ne, amma ki saurari matakin dazan dauka akanki, anta gayamin zakiyi Aure amma ban yadda ba yau kin gayamin da bakinki, wallahi sena wulakantaki a idon duniya, sena turamiki bakinciki mafi muni da zeyi ajalinki”

Kare masa kallo tayi tsaff sannan tace “kai kana ganin har akwai wani bakinciki, zanyi Aure a gidan Naira, zan rayu da wanda nakeso, jeka kayi abunda kaga zaka iya, khadija ce kafi kowa sanina sha3 kawai, idan nayi Aure bazaka kara ganina bama dan wahala” ta shige ta barshi a kofar gidan 

Zubewa kabir yayi a gurin, yanajin kaman zuciyarsa zatayi bindiga wai yaushi khadija tabawa katin Aurenta. 

Salma tana gabaan dressing mirror tana shafa mai, ta kalli envelope din invitations da Habib ya ajiye mata tsaki tayi ta ture envelope din invitations din suka zube kasa, a hankali ta kai hannu ta dakko na daurin Aure tana dubawa

Duf! Duf!! Duf!!! Taji kirjinta yana bugawa

Khadija Munir yakasai tunani take ina tasan wannan sunan, take sunan Saudat ya fado mata Saudat Munir Yakasai, taduba inda za’ayi daurin Aure unguwar su Saudat ne layinsa

Ji tayi kaman numfashinta ze dauke, wayarta ta laluba ta nemo lambar Saudat, jikinta na bari, Saudat ta daga sama2 Salma take jawo Numfashi tace 

“Saudat waye  ze Auri khadija?” 

Cikin rashin fahimta Saudat tace “lafiya kuwa Salma?” 

“ki gayamin wa khadija zata Aura?” 

Takuma tambayar cikin karaji

Saudat tace “nima bansaniba amma naji tace sunanshi Habib” 

“INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI UN!!!!!! ” 

Salma ta furta da karfi.

Da sauri Saudat tace “Salma lafiya kuwa? Wai meya faru ne?” 

Cikin kuka tace “dole kicemin meyafaru Saudat, kuncuceni ina zaman lafiya da mijina, amma ku yaudareni keda yar uwakki wallahi bazan yafe muku ba Saudat, kije da Allah nabarku da Allah daga ke har khadija” cikin rashin fahimta Saudat tace “bangane me kike nufiba Salma, dan Allah kimin bayani” 

“Au saboda baki da kunya har bayani kike nema inmiki, Azzalumai kawai, wallahi bazan yafe muku ba na yadda dake kun hada kai da yar uwakki kun cutar dani cuta mafi muni kuda Allah” ta kashe wayarta, ta dora hannu akai ta fashe da wani irin matsanancin kuka me tsuma zuciya 

“Na shiga uku ni Salma, menamuku kuka kwacemin miji, mijina mafi soyuwa a gareni shi zaku auremun Habibin nawa, shi zaku auremun na shiga uku ni Salma, meyasa nasanki Saudat” haka tacigaba da kuka tana surutai. 

A salube Saudat ta sauke wayar, takasa gane inda maganganun Salma suka dosa, meye alakarsu da Auren mijin Salma. Tana cikin wannan tunanine taji ana shelar ankai lefen khadija gidan kanin babansu, akwati ashirin da hudu, gida ya dau sowa da hayaniya

“Akwati ashirin da hudu”? , Saudat ta maimaita, “itakuwa khadija ina tasamo Attajirin mutum haka? Waye wannan ze Auri khadija haka, shiyasa take boye shi, to tabbas idan har bansamu Auren Habib ba, sena shiga na fita naraba khadija da Auren nan koda tayishi, dan bazeyuwu tayi Aure tasamu Attajiri haka, nikuma ina gararanba ba”

Tafito tsakar gida yan gida nata surutu, wasu na san barka wasu na kushewa, suna agarin kwashe2 kil dan yankan kaine, inbahakaba akwati ashirin da hudu sekace wata yar gwal, yayinda bakin mahaifiyar khadija yaki rufuwa dan murna. 

Khadija bata gida dan sedare ta dawo, yauma Saudat gurin khadija ta tafi

“Khadija nikam dan Allah ki gayamin waye mijin nan ko a hoto ki nunamin shi, akwati ashirin da hudu dozen biyu fa, sana’ar meyake haka” 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

“mekike ci na baka na zuba, har gidan nan zezo ranar daurin Aure kijira zaki ganshi ai, koma sana’ar meyake ni ina ruwana” 

“sewani Boyeshi kike kaman ciwo, zamu ganshi dai muga meye ake boye mana, nace wai yazakiyi da kabir ne”? 

Tsaki khadija tayi “Kabir din banza, nabashi katin daurin Aurena, yagama zage zagensa da kumfar baki, uwassa ma tayi tagama, nace yaje yai duk abunda yaga ze iya” 

“hmm khadija manya, amma Kabir be cancanci haka daga gareki ba, ya miki wahala be kamata ku rabu baran baran ba” 

“to ko zaku daidaitane keda shi?” 

“Allah ya kiyaye ke ki auri me kudi nikuma ki hadani da matsiyaci Allah ya kiyaye” 

“yo kuma ni sekiga laifina” 

“to abar wannan zancen dazu tela ya aiko miki da dinkinki” 

“Aiko ya kyauta, dama nagama biyansa kudinsa” 

“Khadija munyi waya fa da Salma dazu” wani mummunar faduwar gaba ta ziyarci khadija amma ta dake tace “Allah sarki” 

“Amma wasu magamganu ta dingayi da bangane musu ba” 

“kamar ya kenan” 

“ni kaina ban gane me take nufiba, Amma zankuma kiranta, yadda take maganar tana cikin damuwa” 

“Saudat duk wanda za’ayiwa kishiya ai dole yashiga damuwa, mussaman bw san da wacce kishiyar zata shigo ba, kibata shawara cewa ta mike tayi tsaye, dan duk wata mace a yanzu musamman wadda zata shiga gidan me mata toda shirinta take zuwa” 

“bata tsaya ta saurareniba balle in bata wata shawara, bari dai ayi bikinki agama, nikuma zan mike inyi fafatuka nima inshiga a ta uku” dariya sosai khadija ta dingayi mata “lallai Saudat yakamata kema seki dage Allah yabawa me rabo sa’a” 

Yau Habib yadawo daga tafiyar da yayi, dan satin biki yakama, dan gidansu khadija har sunfara wasu events din da mamakinsa koda yadawo Salma bata gida, yakira wayarta amma taki dagawa. Yasan bata da wasu kawaye ko gurin zuwa a kano dan haka a ranar ya shirya ya nufi maiduguri, aikuwa yanazuwa tana can gidansu gaba daya bata hayyacinta banda aikin kuka babu abunda takeyi, dayake shima gidansu ne be jira amma sa isoba ya shiga gidan ba kowa se ita kadai a palour a kwance akan doguwar kujera idonta duk ya kumbura saboda kuka

“Salma meyasa kika taho kekadai baki gayamin ba, inata kiran wayarki kinki ki dauka hankalina ya tashifa” 

Banza tayi masa ta dauke kanta, “haba Salam meyake faruwa ne?” 

“dan Allah ka rabu dani Habib karshen wulakanci kayimin shi, karasa wadda zaka Aura se yayar kawata duk matan dake garin nan, bakasan wacece khadija ba, amma ka rubuta ka ajiye sekayi danasanin wannan auren kuma bazan koma gidanka ba nagama Aurenka Habib, am really disappointed on you ” mikewa tayi zata bar palourn ya riko hannunta amma ta fizge ta wuce dakinta ta kulle kofa, jiki  a sanyaye yanemi guri ya zauna ya dafe kansa a gurin, Salma tanada mahimmanci a rayuwarsa baze taba bari kishinta ya rufemata ido ta rabu dashi ba, amma me take nufi daze auri yayar kawatta dama tasan khadija ne? Mikewa yayi ya nufi part din mahaifin Salma. 

Amma yana zuwa ya tarar yanada baki dan haka yajira ya gama sannan yashiga, mahaifin Salma na ganinshi yafara murmushi “Ango kasha kanshi, saukar yaushe haka ba Labari” dan sosa kai Habib yayi ya samu guri ya zauna yace “Abba dan Allah ka tayani bawa Salma hakuri, duk na rasa gane kanta, munyi sallama lafiya na tafi na dawo na tarar bata gida ta taho nan, nace tazo mukoma tace bazata koma gidana ba” Ajiyar zuciya mahaifin Salma yayi sannan yace “Mata se addu’a, ni na dauka kasani kai ka batta tazo ai, kuma mahaifiyarta batacemin yaji tayo ba, tashi muje yaudin nan zaku koma kano tare Insha Allah” 

Suka mike suka tafi dakin Salma, Abba yace ta bude masa shine, haka ta taso ta bude, 

Nan ya dirar mata da fada ta inda yashiga bata nan yake fita ba, yaimata kaca2

Cikin kuka tace “Abba kayi hakuri amma yayar kawatace fa, meyasa yaya Habib zemun haka” 

“ko kawartaki ce aiba haramun bane ba, kuma daba’a Aure daba a Aureki ba” daga nan ya yakoma yimata nasiha da rarrashi, ya hadasu gaba daya yai musu nasiha yai musu Addu’a, Abba be bari maman Salma ta dawo ba yace ta shirya tabi Habib sukoma Kano. 

Da magariba Saudat tanata safa da marwa a daki, tarasa meyake mata dadi, khadija zatayi Aure ta batta, gashi khadija tasamu me kudi itakuwa ko oho, ga Salma na wasu maganganu da bata gane kansu ba, “gaskiya yakamata inyi wani Abu, bari inji in Salma na gida gara tamin kwatancen gidanta inje inji komai, sannan inyi fafutukar haduwa da Habib” 

Wayarta ta dakko da sauri ta dannan lambar Salma, aiko a fusace Salma ta daga wayar “me kike nema a gurina kuma, kun kwacemin miji, hakan yayi sanadiyar samun sabani da iyayena, kun rabani da farinciki na, shine kika bugo kiji kona mutu ko? To ban mutu ba da raina” 

Cikeda mamaki Saudat tace “dan Allah Salma kiyi hakuri bangane mekike nufi ba” 

“dole kice baki ganeba, maciya Amana kin hada kai keda yayarki zata Auremin miji, Saudat kurasa wanda zaku cuta seni Habib dina yayarki zata Aura, nagode Saudat karki kara kirana a waya, kuma ko a lahira bana fatan Allah ya hadani da ireiren zuri’arku” Saudat bata karasa gane me Salma take nufi ba, dan kojinta bata gamayi ba, dan tuni ta saki wayar a kasa, kokari take ta tabattar da bacci take kokuma idonta biyu, kaman wadda aka tsinkula tayo waje da sauri daga dakin. 

Khadija tana kwance tana wayada Habib 

“Hayatee dan Allah kazo inganka mana, tunda satin biki yakama banaganka ba kuma kacenin kadawo daga tafiyar” 

“kiyi hakuri Dijart, wallahi Salmace duk ta birkicemin, kuma bata da lafiya dole ina tareda ita kiyi hakuri, Tana bukatar kulawa ta mussaman” 

“nibana bukatar kulawarka kenan? 

” bahakabane ba deejart, ita daza’ayiwa abokiyar zama tana bukatar rarrashi da kulawa, yawwa nace dama kinsan Salma ne? “

” Meyasa ka tambayeni”

Saudat ce ta fado dakin bako Sallama tayo kan Khadija, da sauri khadija ta tashi zaune ta kashe wayar 

“Khadija wane Habib din zaki Aura? 

Waye Habib din?” dama khadija tasan wannan ranar zatazo, dan haka ta mike da sauri ta rufe kofar dakin, saboda yan biki sunfara zuwa gidan da mutane, ta dawo ta kalli Saudat tace 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

“ina jinki, mekike cewa?” 

Cikin fada tace “tambayata ma kikeyi? Waye Habib din dazaki aura?” 

Cikin dakewa tace “Habib Kamal me Gwal, mijin Salma kawarki shi zan aura” A razane Saudat ta kalleta “ke yanzu khadija bakji kunyar gayamin haka ba, macuciya Azzaluma, na yadda dake kici amanata, mijin kawata, wanda nakeso nazo nagaya miki matsalata, kikace zaki temakamin ashe cuta ta zakiyi khadija, na yadda dake amma kimin haka” 

“ke dalla dakata, mekikace mijin kawarki, aigara ace nina aureshi akanki abun kunyar seyafi sauki, ni abun kunya gaba na bashi ba bayaba, kekikace ranar biyan bukata rai ba abakin komai yakeba, kema Auren cin amana kikaso kiyi ai, Saudat na dade ina mafarkin Auren miji irin Habib tun ranar da naganshi naji nakamu da sonsa amma abun mamaki, kika rigani gayamin kema kina sonshi, a lokacin nan dana gayamiki ina sonsa nima toda biyu babu za’ayi, shiyasa namiki shiru, na gargadeki da kinemi wani karki tsaya jiran Habib amma kimayi bris dani, kisani mutuwa ce kadai zata iya hana Auren nan, duk wani shige da fice dazakiyi a yanzu aikin gama ya gama baki isa kiyi komai ba, dan ba karamin shiri nayi ba”

Fashewa da kuka Saudat tayi tace “khadija da tun farko kin sanardani kina son Habib, dazan iya barmiki shi, da ban wahal da kaina haka ba, amma kika bari na dinga lalube kina rainamin hankali, tun tasowarmu kaf cikin yan uwana uwa daya uba daya dake na yadda, amma kinmin cutarwa mafi muni khadija!!!! Kinsa na zubda hawaye kin bakantamin rai kinmin tabo me muni da bazan manta ba, kin kwace abunda na kallafa raina aki, shikenan ki shirya ki rubuta ki Ajiye idan harni Saudat yar halak ce haihuwar uwa da uba, wallahi senamiki mummunan tabo kema ki Auri Habib ga daula nan kinsamu, amma ki saurar zakiga nima abunda zan iya” ta juya da sauri fuskarta duk hawaye zatayi waje khadija ta rikota, karo na farko dataji tausayin Saudat amma ta basar tace

“Saudat ki fawwalawa Allah lamarinki, kiyi wanka da fetur, sannan ki hau risho da wandon leda yafimiki sauki akan hana Auren nan, kisawa zuciyarki salama kibi a sannu kema sekiga kin samu ko wanda be karasa Habib bane, kinfi kowa sanin hatsarina karkije garin daukar fansa kikuma ruftawa wani tarkon wanda bazanso hakan ba, har yanzu ina kaunarki yar uwata, kar abunda nayu miki ya shafi zumunci da kaunar dake tsakaninmu”

Fizge hanunta tayi da karfi ta bude dakin ta fice, Ajiyar zuciya khadija tayi ta koma ta zauna tayi murmushi tace “Saudat kenan, na dade ina ankarar dake amma baki gane ba, naciki wasa se hakuri” 

Tundaga lokacin nan Saudat tafara rashin lafiya har akayi gama bikin khadija, tarasa nutsuwarta gaba daya, banda tunani babu abunda take, so take ta samu hanyar dazata turawa khadija bacin rai dan ta huce, tarasa mezatayi danta huce, kasa samun mafitane yasata takara shiga damuwa da halin rashin lafiya, yayinda khadija ko a jikinta hidimar bikinta kawai takeyi, anyi hidima sosai a bikin khadija anci an sha, anyi watsi da nera yadda yakamata. 

Kabir yashiga matsanciyar damuwa gameda Auren khadija, yayi kuka, yayi kukaba adadi, ga fushi da mahifiyarsa keyi dashi, ga basussukan mutane saboda yadda yakecin bashi yana kashewa khadija, gaba daya duniya tayimasa zafi, yarasa meyake masa dadi. 

Tunda Allah yasa khadija ta shiga gidan Habib komai yafara rushewa, gaba daya hankalin Habib yakoma kanta, Salma dama bata da surutu, khadija tafita baki, dan haka ta shiga hadasu fada, dama khadija bata kaunar dangin Habib tunda taji labarin basa son Aurenta, da Habib baya wata guda cikakke beje maiduguri ba amma tunda ya auri khadija seyayi watanni bejeba, Salma sedai ta zauna tasha kuka, ya shirya musu tafiyar wata daya Dubai shida Salma da khadija, Salma tace bazataba, ya dauki khadija suka tafi basu dawoba seda sukayi wata uku, gaba daya Salma ta zubawa sarautar Allah ido.

Idan yan uwan Habib sukazo gidan ta dinga rashin mutunci kenan tana habaici

Tunda taje dakin miji Saudat bata taba zuwa gidanta ba balle takirata a waya, hakazalika seda ta shekara guda cif sannan ta yadda tabi Habib maiduguri ta gaida mahaifiyarsa, tunda mahaifiyar Habib taga khadija taji sam bata kwanta mata ba dan sam babu alamar kunya ko kara a tareda ita, tunda ya aureta shekara guda sannan tazo ta gaishesu. Ta lura khadija a tsaye take ga Salma ta rame matuka tayi duhu, dan bata gayawa kowa meyake damunta, kota fada ba a goya mata baya sedai ace tayi hakuri kishine ke damunta.

Maman Habib ta kirashi dakinta, ta dinga masa fada, akan yadinga adalci tsakanin matansa, in bahakaba seyayu danasani, dan taga alamun wannan tsagerar daya aura kamar suna cutarda Salma, dan ita sam wannan yarinyar batayi mata ba, banda rashin mutunci shekara guda da aure sannan sukazo yakawota gida sugaisheta shi kansa ya canza gaba daya, 

Haka yaita bata hakuri, yace insha Allah ze gyara amna yana kokarin yimusu adalci. 

da kyar khadija ta hakura ta kwana biyu a garin tace ita ya maida ita gida ta fuskanci danginsa basa kaunarta. 

Watan khadija biyar a gidan ta fuskanci tanada ciki, koda tagayawa Habib yayi murna matuka, tunda ya auri Salma shekara biyu kan na uku amma bata taba ko batan wata ba, sunje Asibiti ance lafiyarta kalau, dan haka yayi murna da wannan cikin

“Habib kadena murna da wannan cikin zubar dashi zanyi wallahi!”

Cike da mamaki ya dubeta “kamarya ya? Ina neman abu in samu kice zaki zubar khadija why?”

“ban shirya haihuwa yanzu ba wallahi, da kuruciyata bazan tsufa ba wahalar yaya ta kasheni ba, tun kafin muyi Aure kasan burina inason yin karatu me zurfi a kasar waje, tayaya zanyi karatu da ciki, kwata2 yaushe nayi Auren zanyi ciki, wallahi sena zubar”

“khadija kiyimin rai dan girman Allah kiyi hakuri, kibari ki haifamin cikin nan seki tafi karatun”

“sekuma kayi, in kanason cikinka seka dauka ka maida shi jikinka ka haifa, amma indai a jikinane bazezo duniya ba gara ka hakura inkun matsu kaje kaimata cikin ta haifa maka”

Saroro yayi yana kallonta, ba kunya take gasa masa wannna maganganun.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

.

A ko yaushe ina alfahari daku masoya wannan Novel ina godiya da addu ‘oinku

Back to top button