Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 17 Book 2 Complete Novel

 

Yauma Jalila seda sukayi fada da wani lecturer dinsu, saboda dalibai biyu sunyi laifi ya kori daya yabar daya, dayake wadda yabari din sameera wata muguwar fitsararriya ce, ba dalibai ba har malamai tsoronta sukeji, babban abunda yake bakantawa Jalila be wuce, yadda wasu daga cikin yaran talakawan nan kemata shishshigi ba don samun gurin zama, itakuma taita hantararsu tana musu tsawa, tana zaginsu ko haushi basaji kusan duk ajin suna shakkarta, kaf ajin nan aminiyarta dayace wadda batayiwa wannan rashin mutuncin wato saleema, tun zuwan Jalila ta lura da halin kowa, ita saleema itama babanta yana da rufin asiri yanada kudi amma ba kaman Samira ba, sedai yadda Jalila ta kula saleema ba karamar yar iska bace ba kowa ke gane hakan ba saboda ta iya takunta. 

Yanzuma samira ce takewa, wata yar gefen seat dinta magana zahra, zahra ta bada attention dinta sosai akan lectures dinta, koda lecturer ya juyo, samira ya gani tana magana amma ya kori zahra sannan yace bata da attendance dinsa na wannan semester gaba daya, ya kyale samira be koreta ba, har ya juya ze cigaba da lectures Jalila tace

“Excuse me sir” ya waigo yana kallon Jalila, yace mata “Ya dai?” “Sir meyasa ka kori zahra, ba ita tayi magana ba, bakaga ba ita take magana ba, kamata yayi ka koresu su biyun, koka kyalesu duka, amma bekamata a kori wata abar wata ba, amma am sorry idan na fadi ba daidai ba” juyowa yan ajin sukayi suna kallon ta, zuwa yanzu sunfara gane halin Jalila, ba karamar kwalluwar mara mutunci bace, yayinda take birge wasu, saboda iyayinta, da fadar gaskiya, malamin yai saroro yana kallonta ya hade rai yace

“waye lecturer tsakanin nidake?” kanta tsaye tace “Sir wannan ai amsace a bayyane kaine lecturer, nikuma daliba” 

“dan me zan yanke hukunci kiyi challenging dina? Ke wacece? Ido kika fini banga abunda yake faruwa bane, ke har kin isa inyi magana ki kalubalanceni a gaban students dina, are u out of your sense” nan fa ya dau zafi ze farayiwa Jalila masifa ta inda ya shiga bata nan yake fita ba, yace ta tashi ta barmasa ajinsa, yauma babu batun ta bada hakuri ta dau jakarta zata kara gaba, shikuma yacigaba da zage2 hardace mata mara tarbiyya aikuwa a take tace “Excuse me sir, daga fadan gaskiya zaka fara min fada hada cemin mara tarbiyya, am just your student not your daughter, am sorry for what i did, kayi hakuri in har na bata maka rai, amma karka manta fadar Manzon Allah ne salallahu alaihi wassalam, duk wanda yaga ana aikata abunda be dace ba, ya kawar da hannunsa, in ba ze iyaba yayi da harshensa, in baze iyaba yaki abun da zuciyarsa wanda shine mafi raunin imani, sir be kamata aji tsoronka aki fada maka gaskiya ba, tunda Allah ne kadai abun tsoro, dan kana shugaba ko malaminmu baze hana a fada maka gaskiya ba, duk wanda ya shigo aji ba dan me kudi dana talaka, kayi treating dinsu equally, yazakaji in zahra yarka ce aka hukunta ta akan laifin wani, kasani wannan hukuncin dakayi mata ranar alkiyama sekun tsaya a gaban Allah, wannan abunda kayi mata ya isa ya toshe maka hanyar arziki a rayuwarka, kudena raina daukar hakkin dalibanku ku dinga ganin ba wani abubane ba dan Allah yabaku dama, bekamata kace gaba daya batada attendence din wannan semester dinba, but with do respect sir this is against our Islamic teachings, da na kowame” daga nan ta juya taana wannan takunnata na kasaita tafita waje, koda Jalila ta fito ta tarar da zahra tasamu guri ta zauna tana kuka, kusada ita Jalila taje ta durkusa ta dafata, “Kidena kuka kinji, Insha Allah komai zezama dai2, kidena zama inda wannan yarinyar take kinga ta cazami ki an koreki” zahra ta kalli Jalila dan ko sannu bata taba hadata da Jalila ba a hankali zahra tace “kema ya koreki ne” “Eh korata yayi” nan Jalila tagaya mata abunda yafaru, zahra tace meyasa kikayi masa magana, rannan ma an koreki daga aji, karki jawa kanki matsala “Jalila ta danyi murmushi tace” babu wata matsala, indai ka dogara da Allah ta ya isar maka, be kamata ya kyaleta keya hukuntaki ba akan laifinta, waima tukuna me kikayi mata naga alamun ta takuramiki”

tsit ajin yayi, aka rasa me cewa wani abu, shiru lecturer yayi na wani dan lokaci, sannan ya kalli wani dalibi yace yaje waje ya kirasu Jalila, aikam ya kirasu sukazo, yace sunemi guri su zauna, sukakoma gurin zamansu, bekuma cewa komai ba yacigaba da gabatar da lectures dinsa, koda yafita haka wasu suka cigaba da surutai akan Jalila, samira ce da yan group dinta tace “ina son sanin waye uban yarinyar nan da take wannan gadarar, harni zata kalla tace a hukunta, tasan waye uabana a kasar nan” saleema tace “kedai bari, amma dagani ba yar talaka bace yanayinta kawai zaki kalla kisan hakan, kuma motar da akekawosu ma babba ce, da alama itama babanta wanine, babyn tama hutawa” tsaki samira tayi “duk kudinta tayi na ubanane, saleema inaso ayiwa yarinyar nan warning, sannan kota halin yaya ina bukatar zahra” sameera tai murmushi “yadda kika dama haka za a sha yar masu kasa, sanan kizuba ido kiga wannan yarinyar carry overs din dazata kwasa a school din nan” suka kwashe sa dariya, Jalila ta kalli zahra, “Zahrah baki gayamin ba, meye hadinki da samira ta takura miki haka, kekuma kinkasa daukar mataki” ajiyar zuciya zahra tayi tace “Jalila ina cikin matsala, ni kinga babana bakowa bane ba a garin nan, ni yar talakawa ce, kinga samira da salima yaran masu kudine sannan kuma… Setayi shiru” inajinki cigaba mana wata ajiya zuciya Zahrah takumayi “Jalila samira da saleema, ba kawayene kawai ba yan iska ne, tun suna yara suke tare, daga maza har mata ba wanda basa nema, wannan yan group din nata dayawansu yaran talakawa ne, amma tasasu a wannan harkar tana basu kudi masu yawa, dayawa lectures sun santa, ba wanda ya isa tasa kara ya tsallake, saboda babanta dan siyasa ne suna da kudi, koda anyi niyyar yimata wani abu a makaranta se tayi amfani da alfarmar mahaifinta, in bata gadamaba setasa a kori mutum, da kike ganin ta haka hatta a hukumomin tsaro taana da mutane, kuma harkar da takeyi har wajen kasar nan, mu amalarta hada manyan masu kudi, itada saleema suke wannan abubuwan, shine tace wai tana sona” zahra ta karashe maganar da hawaye, kallonta Jalila tayi labarin ya daki zuciyarta, amma ta dake tace “to kekuma kikace mata me?” “shine nace mata a’a shine taketa bibiyata take takuramin, tace setasa an koreni a makarantar nan, nikuma inajin tsoro saboda, inason inyi karatu” ta karasa maganar tana zubar da hawaye, Jalila tayi tsaki “kekuma saboda wannan shashancin naki dole ta takuramiki, kin nuna kina tsoron ta, tashi muje muyi salla, semuga ya za ayi” suka tashi suka nufi masallaci, a hanya suka ci karo dasu Samira amma, ba wanda ya kula wani, Samira ta kalli saleema tace “sweet heart, bi yaran can, bana son ta shiga tsakanina da zahra, dan haka ki kiramin ita kice ina kiranta” “bakida wata damuwa, bari inje” kafin saleema taje su Jalila har sun kai masallaci, tana zuwa masallacin taga Jalila ta cire hijjabinta tana alwala, tsayawa saleema tayi tana kallon Jalila, yanzu takekuma ganin kyawun Jalila, parkistan ne a jikinta wando da riga, se dogon gashinta irin na fulani, tana tsugune tana alwala, tubarakallahu komai yaji a jikin Jalila,  koda Jalila ta idar tai ido hudu da sameera, tsaki tayi tasaka hijjabinta, suka shige masallaci, haka samira tacigaba da jiranta seda ta idar, saleema ta karaso gaban Jalila ta zauna ta kalleta taimata wani murmushi irin na rikakkun yan isaka tace “baiwar Allah dukda kasancewar, ajinmu daya amma bansan sunanki ba, aikoni akayi gurin ki, samira ce takeson ganinki” shiru Jalila taimata ta dauki jakarta tana saka wayarta, ta kalli kalli zahra tace “zahra taso muje department dinsu Nana, muje capteria muci abinci, saleema tace tab lallai wannan yar rainin hankali ce, saleema tace” baiwar Allah, magana nake fa, samira tace tana son ganinki ” Jalila ta kalli samira tace ” bani da lokacin kowace kucaka a school din nan amma zuciyata zata iya canza ra’ayi “

Daga nan taja hannun zahra suka fita daga masallacin, koda sukaje gurin cin abinci zahra tana ta bawa Jalila labarin halin su saleema. Koda suka gama cin Abinci suka koma aji, lecturer be shigo ba, samira ce ta shigo da mukarrabanta, se wani shan kamshi take, tazo seat din Jalila ta zauna a kusa da ita, ta kalleta tace “dukda bansan wace ce keba, hakan baze hana kisan wacece niba, kuma yar wace niba, kisani ba amin shishshigi, baki isa inyi wani abu kice zakisa a hukunta niba, tunda na shigo makarantar nan, naga yadda kanki yake rawa, to kitsaya a iya matsayinki, nan fada tace duk wanda yake ajin nan a karkashina yake, dan haka kitsaya a matsayinki” samira ta mike zata tafi Jalila batace komai ba, sema murmushi da tayi “yaro be san wuta ba seya taka, baki sanni ba ne, amma muje zuwa” 

Ana haka lecturer ya shigo wanda yasa kowa nutsuwa, tunda lectures suke shigowa sau dubu inzakayiwa Jalila tambaya shiru zatayi tace bata saniba, hakan yasa aka fara gulmar ko dakikiyace se tsabar fitsara da izza a cikinta, dasuka fito daga lectures, tay8 sallama da zahra tai tafiyarta gida saboda Manu direba bezoba, Nana kuma basu gama lectures ba, Jalila ta tafi gida tanata tunanin labarin da zahra tagaya mata akan su saleema, lallai dole wasu iyayen su hana yara mata neman ilimi, katura yarinya makaranta amma ta lalace saboda abun duniya. 

Haka Jalila taje gida a gajiye, tanata tunani daban2 kanta har yafara ciwo, gida ta shiga, tana tura kofar palour taci karo da yaya mairo da Naja da Maama a palour suna hira, seda jikin Jalila yayi sanyi ganinsu a gidan nan, dan ta san bacin rai zata sha yau, sallama tayi ta shiga, ba wanda ya amsamata se Maama itama a ciki ta amsa, Jalila ta ce “ina wuninku” yaya mairo tai saurin cewa “ke dan Allah ki wuce ni banason kinibibin gaisuwarki, wuce kibani guri” Naja tai saurin cewa “tsabar kinibibine wai ita dole ace ta Allah” Jalila batace komai ba ta wuce dakinsu, tana shiga nan ma ta tarar da sa’ada kwance akan gadonsu tana danna waya gefe ga kwanon abincin dataci da jarkokin lemo da ruwa akan gadon duk ta bata gadon, ta zubar da abinci akai, kallo daya Jalila taiwa sa’ada, ta dauke kanta kaman bata ganta ba, ta ajiye jakarta da hijjabinta, ta dau towel ta shiga wanka, tagama ta fito ta zauna a gaban dressing mirror tana shafa mai, sa’ada ta dago kai ta kalli Jalila ta tabe baki “tabdijan anzo an samu guri, se murjewa ake ana yadda aka gadama, Allah ya rufa asiri ba a girma a cikin arna ba da yanzu ko ana gona hakan doya da goyon shege kokuma anayiwa   coci hidima” 

Ware gashinta tayi tana tajewa, ba tareda da tayiwa sa’ada magana ba, Naja ce itama ta shigo, ta haye kan gadon gefen sa’ada tana tauna cingam, ta kalli Jalila tace “Allah sarki, mukam mungode Allah da yayimu a musulmai, ba arna ba” haka suka ding a yiwa Jalila rashin mutunci suce wannan suce wancan, amma taki kulasu, ta dauki doguwar riga tasaka, halima ta shigo dakin da sauri ta Rungume Jalila, Jalila ta kalleta “leemart saukar yaushe?” halima tace “dazun nan na dawo akace kina makaranta, Aikena akayine se yanzu na dawo” “Allah sarki ya kika baro mutan garinnaku” “kowa lpy kalau Alhamdilillah, nayi kewarki sayyada Jalila” murmushi Jalila tayi “nima nayi missing dinki da hirarki me ban dariya” Naja tace “Ke halima meye haka kike wani rungumeta, kokema kin hada iri da arnan ne, ko kyamarta ba kyaji” saroro halima tayi tana kallon Naja, Jalila tace “leemart dan Allah hadomin madara da sugar a cup ki hadomin da spoon ina son zansha goldenmorn” halima ta gyada kai ta fita, sa’ada tace “tabdijan wayaga basa banba ansamu guri se abunda akeso a keci sekace a gidan ubanki, lallai Allah ya temakeki wai, da yanzu ana can anacin teba a kauyen su tsohuwa, ko ana gona ana bauta” Jalila kam gaban mirror takoma ta shafa turarurrukanta, ta dau mayafin rigarta ta daura akanta, halima ta kawo mata madara, ta karba tayi godiya, seda tagama shirinta tsaf, sa’ada da naja suna gayamata bakaken maganganu, a hankali Jalila tazo gaban su ta tsaya sannan tace

“nan gidan ubanane, inada ikon yin abunda nakeso inci abunda nagadama inyi yadda nakeso, kufa meye matsayinku a gidan, se abunda yakawo ake diba a baku, kokuma ayi amfani da abunda aka farauto a bariki” da sauri Sa ada ta kalli Jalila, Jalila tacigaba da cewa “kukiyayi cimin zarafi kyaleku kawai nakeyi, ranar dana tashi nuna muku ainihin kalata, zakuji babu dadi, a kiyaye” tanagama fadin haka ta tashi ta fito takoma harabar gidan tai zamanta, a inuwar data saba zama, amma me tunani ya addabi zuciyarta, ga tunanin yadda zata sami tarihin waye Jalal, taya ya zata samu mafita akan

al amuransa, ga tunanin labarin da zahra tabata akansu saleema, jikinta yana bata wani abu akan su, amma takasa gane menene? Kai ita wace kaddarar ta kawota kano, tana zamanta cikin kwanciyar hankali da umminta, kaddara ta kawota kano tunani kaman ze haukata ta, ga jarabar dangin mamansu Jawwad dabasa kaunar ganina”Allah sarki Ummi na, Allah ya bayyanamin ke” a hankali ya rike hannunta

“Yar babyna, tunanin me kikeyi hakane, da alama kin gaji sosai kuma akwai damuwa a tareda ke, kinkasa cin abincin naki, kuma ga hawaye a kwance a idonki, abunda nafi tsana ganin hawaye a idonki, gayamin tunanin me kikeyi? ” Jawwad ne a durkushe a gaban Jalila ya hada hannunta da kofin ya rike a nasa, a hankali kwallar dake idonta ta gangaro, Jalila ta dake tareda kakaro murmushi taimasa ” Yaya kadawo ashe? ” ” naki wayon gayamin meyake damunki? 

“bakomai fa nagajine kawai” “amma kika kasa cin abinci” ya karbi cup din hannunta ya debo goldenmorn din ya nufi bakinta dashi “bude bakinki” dauke kanta tayi, ta rike hannunsa “A’a yaya Jawwad, karkashiga matsala, kasan su Yaya mairo suna gidan nan, kar ayimaka fada” 

Kallonta yayi “Baby, ni ban damu da hakan ba, bana fargabar kome ze faru indai akanki ne, nasan maybe zuwansune ma yasa sukayi miki wani abu daya bata miki rai” 

“A a basuyi min komai ba” “Baby hakan be kamata ya dinga damunki ba, kome za ayimin zan iya jureshi indai akankine, komai tsanani ina tareda ke Jalila, bazan iya rabuwa dake ba, nasan Abba ze bamu goyon baya, ina sonki Jalila ” dan tsura masa ido Jalila tayi a ranta tace “Allah sarki yayana, goyon bayan uwa shine, nasan indai dasu yaya mairo to bazasu barmu tareba” murmushi tayi masa “yaya ka tashi ka zauna akan kujera mana” “A a sekin gayamin kema kina sona tukuna” rufe idonta tayi tana dariya 

Jalal ne ya turo gate ya shigo ya tunkaro inda su jalila suke.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Ransa a hade ya tunkarosu, yana zuwa ya kalli Jalal yai murmushi, seda hakoransa suka bayyana, Jalal be fiye fara’a ba seda dalili dan kullum fuskarsa a hade, hakan ya tabbatatwa da Jalila, Jalal yana cikin farinciki 

“Kasan wani abu Jawwad?” Jawwad yace “A a seka fada mutumina” Jalal se ya juya harshe yaiwa Jawwad magana da wani yare wanda Jalila bata iya fuskanta, dan zare ido Jawwad yayi tareda yin murmushi “dagaske kake?” 

“kwarai dagaske nake, daddy ze dawo gobe Insha Allah, amma kasan meyafi sani farinciki”? “A’a seka fada” 

“daddy ya tabbatar min da cewa ‘yan maiduguri zasu kawo mana ziyara, zasuzo kano Jawwad, kaga hakan na nuna komai ya wuce” yakarasa maganar da kwalla a idonsa mikewa tsaye Jawwad yayi, “Dagaske zasuzo Jalal” “hakane daddy ne ya gayamin, zasu kawomana ziyar” “Alhamdilillah Jalal nafika murnar hakan, naji dadi, Allah ya kaimu suzo, hakan na nuna komai ya wuce a gurin su” 

“Hakane gobe insha Allah zamuje dakko daddy karfe hudu ze dawo” “to Allah ya kaimu” ita dai Jalila ba tace komaiba sema wata cakwakiyar tunanin dasuka kuma sata, dama Jalal yanada yan uwa a maiduguri amma basa zuwa, ita bata taba ganin baki sunzo gidansu bama, se abokan kasuwancin Mummy dakuma wasu tsirari daga danginta, dan ko a gurin birthday din Jalal wadanda tagani, sunfi kama da Mummy, Jawwad ya kalleta yace “sarkin tunani, mekuma kike tunawa? Zamu wuce nida Jalal zamu fita” 

“Hmm sekun dawo” Jawwad yai murmushi suka fita shida Jalal. 

Yaya mairo ce take korawa Maama jawabi

“Zainab yakamata mu karfafa zumuncinmu ta hanyar hada auratayya a tsakanin yaranmu, kinga yaron gurina Nura tun Nana tana yarinya yakesonta, yakamata kubashi Nana, sannan Jawwad mu hadashi aure da Naja, kinga haulat kuma dan gidan baba habu Dini shize aureta, tunda Nana kanwar Nura ce kinga duk se a hada su koya kikagani?” seda Maama tai Jimmm, dan gara batun hada auren Jawwad da Naja akan auren Nana da Nura, dan tasan Nana bazata yadda ba, balle Abba tasan baze mata auren dole ba, dan sam Nana ta tsani Nura basa jituwa balle data girma gashi duk wanda yasan Nura yasan ba mutumin kirki bane, dan zuwansa prison sau uku

“Yanaga kinyi shiru ne? Ko baki yadda bane?” tab tasan a yanzu idan ta nuna mata rashin amincewarta zasu samu sabanine dan haka tace

“gaskiya Yaya mairo, wannan tunanine me kyau Allah ya tabbatar mana da Alkhairi saura kuma amincewar yaran” 

“to meye inma basu yaddaba ai dole subi umarninmu” “A’a Yaya mairo in har basu amince ba Abbansu baze yadda ba, har gara Jawwad amma kinga Nana kinsanta da taurin kai” 

“Ki barni dasu kawai, kinga Jawwad in aka hada shi da Naja kinga zamu dauke hankalinsa daga kan wannan makirar yarinyar, bari Nanan ta dawo” Maama dai ta amsamata ne amma badan ta yaddda da abunba har cikin zuciyarta. 

Jalila tana nan inda su Jawwad suka barta halima tazo ta zauna sukai ta hira, har la’asar, Jalila na shirin komawa cikin gidane manu direba ya kawo Nana gida daga school, ta gaji sosai 

Ta kalli Jalila “sarkin gudun makaranta kin gudunne tun azahar” 

“wayagaya miki, mungama lectures ne da wuri kawai, sannu” 

“Yawwa, au halima kindawo ashe” “eh na dawo” “yayi kyau” 

Suka dunguma zuwa cikin gida, suna zuwa suka tarar su Mama duk suna palour, Jalila tai wucewarta dakinsu, tanaji Yaya mairo tanawa Maama mita

“Zainab ashe har yanzu baki janye yaranki daga jikin wannan kinibabbiyar yarinyar ba ko, saboda munafunci data dawo seta koma waje ta zauna, amma Nana tana dawowa kinga tabiyota ta dawo” 

Sa’ada tace “hmm kema dai kyafada, muna funci a gurin kabilu bama dai ita tana wa mutane gadara sekace a gidan ubanta” dogon tsaki Nana tayi, ta wuce dakinsu

Binta sukayi da kallo, Naja tace “Tabdijan zama da madaukin kanwa, Ace kina magana Nana tayi miki tsaki, lallai abun ya girmama” 

Nana tana shiga daki ta tarar da dakinsu kaca2, kan gadonsu hada kwanukan abinci “Jalila meye haka? Yanaga dakinmu a haka, sekace makwanci mahaukata, dakin dayake tas amma hada kwano akan gado” 

“Ke karki saukemin gajiyar makarantarki, ni kin taba ganin ina cin abinci akan gado, kuma in tashi in bar kwano, nima haka na dawo naga dakin, bakinku ne sukayi masa haka” 

“Kutmelesi, waisu Naja aikuwa sena musu rashin mutunci sun dauka kowa kazamine irinsu, suna abu kaman sakarkaru” fuuu Nana tai waje tana zuwa palour tafar zazzaga masifa “Ke sa’ada akanme zaku shigar mana daki kuci abinci akan gado, wannan wane irin shirme ne? Muda a haka muka bar dakin zakuyi marmarin shigane,” Maama ta daka mata tsawa “Nana meye haka? Sa ada ba gaba take da keba? Kuma ya akayi kikasan sune sukayi hakan? ” cikin shagwaba kaman zatayi kuka tace

“Maama dan tana gaba dani sesuyi  mana haka a daki, kuma koba a gayamin ba ai nasan Jalila tafini gyara dakin nan tunda bata son kazanta bata tabcin abinci a guri ta barshi ba, amma daga zuwansu zasu bata mana daki, wallahi karku kara shigar mana daki, tunda baku da hankali, kazamai kawai” bude baki sukayi da mamaki Naja zatayi magana Yaya mairo ta hanata tace “rabu dasu yi hakuri bazasu karaba, sannan inason in kin samu lokaci kije gida kisameni ina son ganinki” seda Nana ta yamutsa fuska, sekuma tayi shiru  takoma daki tana kunkuni tana mita, seda tafara gyara gurin sannan ta shiga wanka, dan Jalila tace wallahi kartin banza bazasu bata daki ta gyara ba. Koda Nana ta wuce daki Yaya Mairo tace “kingani ko zainab yaranki na neman sufi karfinki ace har kina fada tana mayarwa saboda waccan yar karuwar, kinsansu arna ba ruwansu yayansune suke juyasu shiyasa take so ta mayar miki dasu irinta ki tashi tsayefa wallahi aikine babba agabanki” 

Koda su Yaya mairo suka tashi tafiya seda aka bude store aka jido musu kayan abinci, banda wanda Abba yakesawa a diba a basu, banda kudi da take bawa yaya mairo, se anbi kayan abincinsa na gida bada saninsa ba anbasu banda sitira da sauran kayan more rayuwa, dayake Yaya mairo akwai mugun sonn abun duniya, duk an kwashi kaya an kai boot Manu direba ze maidasu gida. Nana ta fito daga wanka zata shafa turare, amma ta lura babu wasu abubuwan akan mirror dinnasu, tsaki tayi “Allah ya kyauta wannan masifar, Jalila kallifa hada kayan mu suka sata, wallahi senaje se sun bamu” da sauri Jalila ta dakatar da ita “bari Nana ai yan uwankune inkikayi haka kaman kin tozartasune, ai arzikine sekinada abun sata za a sata, bakomai semu sayi wasu” haka Jalila ta lallabata ta hakura badan tasoba. Jin alamun fitarsu daga palourn yasa Jalila ta fito palour, hakan yai dai2 da dawowar 

sa ada zata dauki wasu kaya data bari a palour wanda na Nana ne da Jalila ta dauka bada izininsuba, hada kayan man shafe2 da turaruka da Nana take mita, Jalila ta kalleta tai murmushi “Allah sarki bariki batayi rana ba, ace duk iskancin da ake a bariki ba a tara abunda za a rike tsofaffi ba se an hada da maula a dangi, bayan haka kuma se an hada dana sata to Allah ya kyauta” a fusace ta kalli Jalila ta nunata da yatsa “Karki kara dangantani da bariki” “Ke sauke yatsanki karki kuma nunani  karki rainamin hankali mana nasan komai kallonku kawai nake daga ke har mahaifiyarku, kuma wallahi kigayamata ta kiyayeni inasane da abunda takemin da cin mutuncin uwata datakeyi, idan na tashi yimata rashin mutunci se tagane bata da wayo, har yanzu ban taba gwada muku wace Jalila ba, ta kiyayi haduwata da ita” Jalila tai gaba tabar sa ada da bude bakin mamaki. Bayan tafiyar su Naja da daddare Nana se mita take “nikome yaya mairo zata gayamin wani wai senaje gidanta, Allah yasa wani abun Arzikin nanba rainamin hankali zatayiba, nibana son zuwa gidanta saboda wannan Jarabar tata”

“To ai hakuri zakiyi, maybe abunda take son gayamikin yanada mahimmanci ne” 

“Anya Jalila bana tunanin hakan amma bansaniba” 

“Yawwa Nana dan Allah in tambayeki mana?” 

“to Allah yasa nasani” “dama Jalal suna da wani yarene naji sunayi shida Yaya Jawwad” murmushi Nana tayi tace “Eh sunadashi, ta bangaren daddynsa, kakanin Jalal kanuri ne” Jalila ta gyada kai tace “Amma ya akayi Yaya Jawwad ya iya” 

“Lallai Jalila har yanzu kina daukar amintarsu da wasa, tare suke kwana su tashifa, yanzune suka dena kwana guri daya, saboda Yaya Jalal yana fita yawonsa, da har maiduguri suke zuwa suyi kwanaki” jinjina kai Jalila tayi tace “lallai kam dole ya iya yaren” daga nan suka bar wannan zancen, Jalila ta kwanta bacci Nana kuma tafara waya da saurayinta. 

    Yau lecturer su Jalila ya kudiri aniyar yimusu test, unexpected saboda ya hukunta Jalila sir Hafiz kenan, matashin mutum me matukar izza da jin kansa, bashi da mutnci kokadan, kayadda dalibai a course dinsa shiyafi komai sauki a gurinsa, ga kwauron maki shiyafara korar Jalila daga class, sau biyu yana korarta daga class, na farko yana lectures tana tunani na biyu kuma kullum ya shigo class yamata tambaya bata sani ba, gashi ya lura seta gadama take attending class ya fuskanci dakikiya ce amma tana da izza da jin kanta dan haka, bayan anfito daga lectures karfe biyu, unexpected ya kira captain dinsu yace, ze musu test bayan sallar azahar, students din sun shiga damuwa saboda basu shirya ba, kowa yakama littafin sa, zahra ma ba abarta abayaba ta dage tanata dudduba littafinta, yayinda hajiya Jalila bayan ta idar da salla, ta janyo abincinta tanaci tana chatting da yaya Jawwad yana dariya , zahra ta kalleta “Jalila ke bazakiyi karatun ba? Test fa zeyi kuma ance yanada kwauran maki” “don’t mind me, yi karatunki kawai, ni yunwa ce ta dameni” “to amma ai gara….” “shhh ya shiru kicigaba da karatunki kar haddarki ta zube” zahra ba karamin mamaki Jalila take bataba, ga dukkan alamu dai ba wani ja take ba saboda ba ataba tambaya ta bada amsaba amma za ayi test ko a jikinta, se tsabar iya tsiwa fal cikinta, 

Karfe biyu da rabi suka shiga test din nan, wadda duration din test din 30minutes ne kawai, ga tsaro a hall din dan duk ya rarrabasu, bame iya ko kyakykyawan motsi, sannan Jalila ita kadai aka ajiye agaba bakowa a kusa da ita bayanta ko gefenta, gashi ya dakko wasu malaman department din su tayashi invigilation, Jalila ta lura yasamata ido sosai, ya dinga safa da marwa yana kallonta, kowa ya dukufa amma ita tana zaune tana kalle kallenta karewa ma ta tafi tunanin abunda yake gabanta na rayuwar Jalal, sir hafiz yazo kanta ya duba paper dinta ammma empty, ya kalleta yai kasa da muryarsa ya dan sunkuyo da fuskarsa yace “dakikiya kawai ba abunda kika rubuta, dama ba kyaja se tsabar iya shege ko? Rashin mutunci kawai shine a kwakwalwarki, bakomai se shirme, sokuwa kawai barikiji in gayamiki wannan shine last chance dinki idankika fadi test din nan kin fadi exams dina” wani irin kasaitaccen murmushi Jalila tayi masa alamar sam bataji zafin maganganunsa ba ta dauke kanta, seda yayi gaba ta bude paper dinta ta amsa tambayoyin, nanma itace karshen bayarwa, yauma batajira manu ba ta tafi gida. 

Tana tsaye tana jiran mota, amma bata samuba dan haka ta yanke shawarar fara trecking, tana cikin tafiya taga wata katuwar mota range rover baka wuluk se sheki take, ga wasu mota biyu gaba da bayan motar, range rover tazo ta tsaya agabanta, kokari take ta wuce motar, amma se kokarin rufemata hanya me motar yake, “wai wani tsabar wulakanci ne haka? Bana son wulakanci fa. Wasu yan sanda ne biyu, suka fito daga motar ” Yan mata kinsan waye a cikin motar nan kuwa, ki iya bakinki fa, kinsan matsayinsa kuwa? yanzu dai yace yana son magana dake kishiga motar semu ajiyeki” cewar daya daga cikin yansandan, wani mugun kallon banza Jalila tayiwa yan sandan, “ai mutum ne a motar ba aljan bako, to duk matsayinsa ace masa bazanzoba, malam bani hanya zan wuce” kuma shan gabanta sukayi “Ke waime kike takama dashi haka kike mana wulakanci kinsan suwaye mu, kinsan dawa muke tare?” “matsalarkuce koku suwaye kodawa kuke tare ba damuwata bace, kuban hanya kawai in wuce tunkafin in taramana jama’a” motar aka bude, wani hamshakin mutum ne yafito daganinsa yaci ya koshi, sanye yake da kakin yan sanda, nan suka dinga sara masa, babban mutum ne ba yaro bane, dan ze haifi Jalila, gabanta yazo ya tsaya “Am sorry mun tsareki a hanya, kizo mu saukeki a gida kinga da rana sosai” Jalila da rashin kunya taso tayi masa amma ganin babban mutum yasa tafasa “A a bakomai nagode, inada kudin mota, amma kace subani hanya in tafi” “zasu baki hanyane, amma kitemakeni da lambarki inaso zamuyi magana” dan zare ido Jalila tayi “laifin menayi maka?” 

‘laifine babba kam tsakaninki da hukuma , amma tsakaninki da hukumar zuciyata”a ranta tace “ji tsohon kawai, tab wallahi wrong number zanbashi” 

“yakikayi shiru, kitemakamin mana” 

“kawo abu inrubuta maka” ya mikomata galleliyar wayarsa, dazata samasa wrong number kawai wata zuciyar tahanata “ze iya zama garkuwa gareki daga sharrin su Jeje” ajiyar zuciya tayi tasaka masa lambarta

“Nagode sosai beauty, muryarki kawai ta isa sani bacci cikin nishadi, bankiba muyita tsayuwa anan kinamin magana, gayamin sunanki” 

“Kaga ni nagaji, tafiya zanyi rana ta dameni” “hmm se anjamin aji kenan, to shikenan tunda bazaki bari inkaiki gidaba i will call you Insha Allah” bata kuma cewa komai ba ta wuce. 

Tana zuwa gida tai wanka tai salla taci Abinci, Mummy takira Maama awaya tace dan Allah ta turamata Jalila ko Nana,su karbi sakon Ilham tana bacci, Dayake Nana bata dawo ba seta tura Jalila, wani tea flask ne me kyau a kwali Mummy tabawa Jalila tace ta kaiwa Maama, wata coustomer zata siya, ta karba ta fito, Jalila na fitowa harabar gidan motarsu Jawwad ta shigo sun dakko Daddy daga airport, tsayawa Jalila tayi daddy ya fito daga motar dauke da brief case dinsa, kana kallonsa kaga mahaifin Jalal, amma yafi Jalal kyau, sedai wannan dogon hancin Jalal ya dakkoshi, shaye2 ne yabata Jalal amma yana da kyau irinnasa, har kasa Jalila ta zube tana gaisheshi, da fara’a ya amsamata

“Takwarar Jalal, ashe kina kanon har yanzu ya kike ya karatu” cikin tsantsan ladabi Jalila tace “Karatu Alhamdilillah daddy” “Masha Allah, Allah ya temaka yayiwa rayuwarku albarka” “Ameen daddy” Jawwad ya dakko trolley da traveling bag na daddy sukayi gaba yayinda Jalal ya tsaya rufe mota, ta taka ta karasa gurin Jalal yana juyowa yaci karo da ita hade fuska yayi kaaman yaga kashi, dan da yaganta yake tuno cin mutuncin datayi masa, seyaji kaman yaimata shakar da seta kusa zuwa lahira 

“Kalleka a haka sewani zumudi kake wai kai kafi son mahaifinka, sekace gaske, abunda inka ga dama shima daga masa murya kake, kokagaya masa maganar daka gadama, kana nuna kana sonsa amma baka hakan a aikace, ka girmamashi, tausasa lafazi a gareshi, in gari ya waye kaje ka gaisheshi, in yana maka fada ka nutsu ka danne zuciyarka, kayi hakuri dashi a duk lokacin daya bukaci taimakonka ko alfarmarka zama taredashi da gudun bacin ransa wanda hakan zesa yaji dadi yayi alfahari dayana da ďa me kaunarsa, duk fa bazaka iya wannan ba, ta yaya zaka nunawa duniya cewa kana son mahaifinka, hmmm bazaka iyaba banda zafin zuciya da raina iyaye baka iya komai ba kodayake ba abun mamaki bane no need to expect anything good from you, giya ba karya bace, a canza hali abokin Yaya. 

Ta danyi murmushi tai gaba, tana addu’ar Allah yasa abunda tafada yai tasiri a zuciyar Jalal, Jalal karasa rufe motar yai ya nufi cikin gida jikinsa a sanyaye, Jalila tazame masa karfen kafa ta uzzuramasa dayawa, gashi har yanzu yakasa samun mafita akanta. Cikin gida yanufa jikinsa a sanyaye yana zuwa ya tarar dasu a palour a zazzaune, daddy ya kalli Jalal yace “Ya dai naganka a haka? Meya faru” dan girgigiza kai yayi “bakomai daddy” haka dai akayi hira sama2 aka watse domin bawa daddy damar ya huta. 

      Hannah ta na kwance juyi kawai takeyi, zuciyarta fal tunani da damuwa, dagaske son Jalal ne yake damunta, gashi har yanzu takasa samawa kanta wata mafita sam Babu alamar Jalal ze amince ya aureta, a da aikin datakewa Jeje na son Jalal ya amince da ita, sudinga shedanci hakan ya gagara, amma ita yanzu babban burinta ya aureta in har ya aureta tagama karuwanci har abada, to amma tayaya? Yazata samo kan Jalal ya yadda da ita ya karbeta ya aureta, abaya tasan ta taka rawa gurin kara ingiza shi akan shaye2 amma yanzu tayi nadama, son gaskiya takewa Jalal yanzu ita meye abunyi meyakamata tayi, shiru tayi daga can kuma tayi wani guntun murmushi. 

Koda dare yayi, Jalal rasa abunda yake masa daďi yayi, tunani ya dameshi, ransa yagama baci Jalila ta dameshi, to amma dagaske take baya son daddy? Shidai yasan yana son daddynsa to amma fa wataran shima yanamasa masifa kaman yanda yakewa Mummy, to hakan yana nufin hakan danakeyi daddy bayajin dadinsa? , to meyasa nake hakane? Gaskiya ina son daddy na, dan bani da takamarsa, jiyayi kirjinsa yafarayi masa nauyi dan haka yatashi yakunna sigari, yana gamawa ya dora da giyarsa seda yafita hayyacinsa sannan ya kwanta bacci

Abun takaicin, ya kwanta da bacin ran Jalila, zuciyarsa har wani tafasa take dan bacin rai, amma abun takaicin yauma kwana yayi yana mafarkin Jalila, cike da shaukin soyayya da kauna, a yanayi irin na ma’aurata, mafarkinsa na karshene me ban tsoro, ya firgita kwarai ganinshi yayi wasu mutane sun daureshi akan dutse, maza da mata suna saransa da wasu dogayen wukake, Jalila ta bullo daga wani guri ta taho da sauri ta rungumeshi, tana tare masa saran, yayinda sukuma mutanen suka dinga saranta jikinta yana zubar da jini, ta rungumeshi gam itakuma jini na zuba a jikinta a hankali take kiran sunansa a cikin kunnensa ABDUL JALAL. Juyi ya dingayi yana kokarin ya tashi, A firgice ya tashi daga baccin dayakeyi, yana haki, a hankali ya daga kai ya kalli agogo karfe takwas da rabi na safe, tashi yayi zaune yai shiruu yana nazarin mafarkin dayayi na karshe, jujjuya abun ya dingayi a ransa yana tuno yadda take furta sunansa, tunani yake meye alakarsa da wannan mutanen haka suke saransa, dan gutun tsaki yayi, “komeyema na bata lokacina akan wannan shirmen mafarkin” mikewa yayi ya sakko daga kan gadon ya tafi toilet don yayi brush yai alwala kawai ya tuna se yayi wanka, sannan zeyi salla wani dogon tsaki yayi “Jarababbiyar yarinya ta addabawa rayuwata, tazomin a farke ta dameni, dan jaraba har cikin baccina ma seta biyoni, ji yanzu ga rana tayi amma senayi wanka zan salla komeye hakan oho” haka yaita mita yai wanka yafito yai sallar asuba. 

Bayan ya idar da sallar ya tafi cikin gida, kai tsaye part din daddy ya nufa, ya tarar daddy ya tashi har yana breakfast Shida Mummy suna hira, sallama Jalal yayi, daddy yadago yana kallonsa yafara murmushi, Jalal yaje kusa dashi ya zauna, cikin girmamawa yace ” good morning daddy” ba Mummy ba har Daddy seda ya kalli Jalal, rabon da ya gaida daddy haka da safe cikin girmamawa tun kafin ya lalace dan sedai daddy ya gaida Jalal amma badai ya gaisheshi ba, dama Mummy ba a maganarta itadama baya ta tata, amma abun mamaki yau hada sallama, daddy ya fadada murmushinsa yana shafa kan Jalal yace “Morning yarona katashi lafiya?” “Lafiya kalau daddy, ya gajiyar ka?” “Ba gajiya Jalal, kayi breakfast ne? Ko Jawwad din kake jira?” “No daddy Jawwad nasan ya tafi makaranta” “taho muci nawa to” girgigiza kai Jalal yayi, “kaci Abincin ka daddy, ni zanci nawa daga baya, dama zuwa nayi in gaisheka, sannan in kalleka inajin dadi, kasan na dade ban ganka ba nayi kewarka daddy” 

Mummy tace “Hmm wannan soyayya haka, lallai Jalal” daddy yai murmushi yace “to ya ranki, nima kllonka yana sani farinciki yarona, idan na kalleka ina jin daďi, wannan gudan jini nane, babbar kyauta daga Allah, ina alfahari da godewa Allah dayabani kai” dan shiru Jalal yayi cike da damuwa yace “daddy yanzu har farinciki kake da kasancewata danka, kalleni fa daddy kalli rayuwar danake yi, mutane dayawa na kyamar halayena, yayinda wasu suke gudun a dangantani dasu a matsayin danginsu saboda munin halayyata, mutane kalilan ke kaunata suke son farincikina daddy kai da Jawwad bansan wani irin so kukeminba, kai mahaifina ne amma Jawwad da rana ďaya be taba kyamata ba” 

“Jalal ko a yaya kake kai Allah yabani, kaine nawa ko halinka yafi haka muni inamaka fatan shiriya, amma ni a haka nake sonka, sannan lamarinka da Jawwad soyayyace daga Allah wanda samunta a wannan zamanin abune me wahala, shiyasa nake maka fatan samun mace tagari, Jalal ba abunda yafi zama da wanda yake kaunarka daďi”

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

“hakane daddy, Jawwad na musamman ne, naso a ce ciki daya muka fito dashi, amma daddy dagaske bana sauke nauyin dayake kaina a matsayin danka ko? Yadda nake treating dinka bahaka ya dace ďa nagari yayiwa mahaifinsa bako? Kayi hakuri daddy zan dena Insha Allah” 

“waya gaya maka haka kai yaron kirkine, kana kokarin farantamin karka damu lokacine wataran se Labari, Allah ya shirya min kai” “Ameen daddy”

“Jalal ta mahifinka kawai kake, a tunaninka shikadai yake da hakki akanka, ni ko oho ko, da inyi farinciki dakar inyi baka damu bako?” hade rai Jalal yayi, yaiwa Mummy wani kallo me cike da ma’anoni, ya tashi ya fita ya bar dakin gaba daya, daddy ya dan dubeta ” Hadiza sam bahaka yakamata ki dinga treating Jalal ba, ko kina manta kece me laifi a gurinsa, yakamata kiyi tunanin hakan. “haba daddy Jalal, shikenan shi abu baze wuceba a gurinsa, kullum da laifina zetamin hukunci” “hadiza ke kike ganin laifinki karamine, banga laifin Jalal ba lokacin danake jan hankalinki, baki saurareniba se yanzu data kwabe miki, seki nemi daidaito da ďanki”. 

   Jalila tana tafe akan varander na class dinsu ta ga captain dinsu da takaddu a hannunsa, yanata sauri da alama class zeje, wanda tayi Imanin takaddun hannunsa tests dinsu ne, sauri takara ta hada da dan gudu ta tana kiran sa, tsayawa yayi ya waigo, mamakine ya kamashi yaukumashi wannan yar kwalisar takewa magana ya tsaya suka gaisa da ita “Captain wannan tests dinmune ko?” “Eh sune, me yafaru” “yawwa dan Allah alfarma nake nema, sonake kabani tawa anan” “amma meyasa?” “bakomai kawai inason kabani tawa anan ne, banaso sekaje aji” yadda ta kafeshi da ido yaga tayi masa kwarjini matuka dan haka yace  “to shikenan ya sunan naki, se in duba miki” “A a bani in duba tawa da kaina, karka damu ba ta wanda zan duba tawa kawai zan dauka” ba musu ya mika mata takaddun an faďi test din nan sosai, kuma gashi over 40 ce duk an faďi tunda test din be fadi zeyita ba, Jalila tana ganin tata ta zare, tana kokarin mika masa takaddun taga wani suna Samira Kabir Idris, Tunawa tayi Kabir Idris shine sunan dake dauke ajikin katin da baban faruk yabata a banki, mika masa takaddun tayi tace” Thank you very much “

” You are welcome ” tunani ta dingayi waye me irin wannan sunan a ajinsu, maybe ma kawai sunane yazo ďaya, da sauri ta tafi class taje gurinta ta zauna, Captain yana raba takaddu tanajin ya ambaci sunan Samira Kabir Idris, ta juya dan ganin kowace, wadda tai tsammanice Samira kawar saleema, se yanzu taga tsananin kamaninta da Alhaji Kabiru, kenan ‘yarsa ce, ajiyar zuciya Jalila tayi, barewa bata gudu danta yayi rarrafe, ba a banza ba Allah yabashi irin wannan yar, Alhamdilillah bincikena zezo da sauki, sena gane alakarsa da Jeje, tana cikin tunanine taji captain yana cewa 

“Yan class kunga munyi test, ga a yadda tazo dan haka se mudage a exams, sannan muyita addu’a dan banga wanda ya ci talatin bama, amma yace yanason ganin Jalila Aliyu Imam, in taji tasan kanta taje yana neman ta, danni ban santaba” zahra ta kalli Jalila,” bake ake nema ba? “

“nice”

“Naga ba abaki naki test dinba, ni dai kinga wai 19 na samu” “kigode Allah ai kinyi kokari, yawwa zahra dan Allah samira sunawane yan gidansu” “Su biyune kawai yayanta faruk, sekuma ita sukenan” “Kuma a gidansu ansan me takeyi? ” 

“Gaskiya bansaniba babansu dai yana da zafi, wataran yana kawota makaranta, mamansuce dai ance ba ruwanta da tsanani akan tarbiyya” 

“Mene sana’ar babansu?” “Kai Jalila sekace wata lawyer wannan tambayoyi haka” “yi hakuri akwai abunda nakeson ganewa ne” “gaskiya ban saniba, amma naji kaman ance dan kasuwa ne” “shikenan nagode sosai”. 

Bayan antashi daga school Jalila tai tafiyarta gida bataje kiran sir hafiz ba, tanata tunanin yazata bullowa lamarin Alhaji Kabiru, dan tana zargin mutumin nan sam bata yadda dashiba, wayarta ta dakko ta duba what’s app dinta, taga lambarsa tayi appearing a contact dinta na wats app, dan bayan dawowarta gida ranar tasaka lambarsa a wayarta hotonsa ne akan dp dinsa tayi sa’a yana online, dan haka tayi masa sallama, seconds kadan ya amsamata, suka gaisa yace mata be gane me maganaba, rasa me zatace tayi, kawai ta kashe datarta ta ajiye wayar tai shiru tana tunanin anya haka yakamata tayi, ko kawance zata kulla da samira, amma in tayi haka itama za adingayimata kallon ‘yar iska, lambar hanan ta kira amma taki shiga dan haka ta hakura. 

  Hanan kam tana kwance, tana trying lambar Jawwad amma a kashe, ta ajiye wayar ta dafe kanta, turo kofar dakinta, dan dago kai tayi da mamakinta setaga Siyama, zumbur Hanan ta mike tana murmushi “oyoyo Siyama matar Yaya yauke kika kawomin ziyara” murmushi Siyama tayi “yau nina kawomiki tunda kin mance dani nace bari inyi surprising dinki” “amma naji dadi” Siyama ta zauna, Hanan taje ta kawomata ruwa da lemo da snacks suka zauna sunata hira, Hanan ta kalleta “ta Yaya Abdallah gaskiya Siyama, kin rike wuyan yayana over, komai ke ni ya manta dani gayamin meye sirrine” “haba Hanan waceni rike wuyan Yaya, shiya rike nawa wuyan, wallahi Hanan Abdallah ya iya soyayya shiyake tabarani, bana tunanin akwai namijin daya kai yaya Abdallah iya soyayya da kula da mace” dariya sukayi gaba daya “Siyama ya bakyacin snacks dinne?” “A a ni snacks be dameniba dama chocolate ne” “Ahh sekace queen J, kinsan inkinaso ki birgeta kibata chocolate, gaskiya ina missing Jalila ina kaunarta har cikin raina, amma alakarmu na shirin samun matsala wanda hakan bazemin daďi ba, amma nakasa samun mafita, dama kobakizoba ina son zuwa siyama” hanan ta karasa maganar cikin damuwa, 

“Amma Hanan bangane mekike nufiba, kamarya alakarku na shirin samun matsala kamar yaya?” 

“Siyama Jawwad nakeso, da farko na dau abun wasa, inayine domin Jalila ta maida hankali akan Jalal, saboda sunfi dacewa amma yanzu nagane wallahi son gaskiya nake masa kota ina yaya Jawwad ya hadu” zare ido Siyama tayi “Hanan kin san irin soyayyar datakewa Jawwad kuwa?” “Siyama soyayyar dake tsakanin Jawwad da Jalila na yan uwantaka ne, amma da Jalal ta dace shike bukatar taimakonta, ina kaunar Jalila amma bazan iya rabuwa da Jawwad ba” Hanan ta riko hannun Siyama, idonta taf hawaye tace “Siyama babu wasa a zancena, wallahi dagaske nake inason Aliyu Jawwad, so na gaskiya, sannan ina kaunar Jalila ina jinta kaman wani tsagi na rayuwata, amma bazan iya rabuwa da Jawwad ba” Ajiyar zuciya Siyama tayi, ta gogewa Hanan hawaye “For now kiyi hakuri ki dan bani lokaci, zanyi tunanin mene mafita, amma kidena kuka” gyada kai Hanan tayi kaman karamar yarinya, daga nan suka shiga wata hirar

   Seda aka kwana biyu, Jalila bataje kiran sir hafiz ba, captain ne yazo yana kuma shela a aji, danshi besan wace me sunan ba, tashi tayi ta fita tatafi offers dinsa, tana zuwa ta shiga da sallama ta tarar da shi da wasu lecturers a office din ammasu dattawane ba kamanshi matashiba, amsamata sallamar sukayi, kaman yadda yake ďabi’ar Jalila har kasa ta zube cikin girmamawa ta gaishesu, suka amsamata cikin mutunci, shi sir hafiz mamaki ma ta bashi, ya kalleta a fusace “uban mekikazo yimin office, kin fadiko? Ba abunda zanyi miki aidama seda nagaya miki fita kibani guri, dakikiya kawai kisawa ranki kin gama faduwa exams dina” batace komai ba ta juya tai tafiyarta

Malaman nan suka dinga jinjina tarbiyyarta, saboda a wannan zamanin a yan matan jami a asamu me durkusawa har kasa ta gaida malamai abunda wuyar samu “hmm bakusan halinta bane, tsabar iya makircine dakikiyace gata fitsararriya, nayi test ta faďi shine takamo hanya tazo”. 

Bayan kwana ďaya sir hafiz yakuma sawa a kira Jalila Aliyu Imam, tareda kashedin in batazoba zesakamata zero a test dinsa, kuma zuwa office dinsa Jalila  tayi, yau wasu yan matane a ciki se iyayi suke suna yauki, gani tayi bashida niyyar saurarta dan haka tazo gaban tebur dinsa tace “Sir tunda baka da lokacina karka kara turawa kace inzo, zuwana nawa office din nan kaki saurarata, bayan kaikace inzo” daga kai yayi ya kalleta, yayinda yan matan suka bita da kallo “ni nace kizo? Kizo in miki me” “bakai kace inzoba karka kara tura captain yana shelar wacece Jalila Aliyu Imam dan bazan kuma zuwa ba, kaitasamin zeron inka ga dama kasamin abscent se wani wulakanci kakemin menayi maka hakane? , in akwai abunda be kai zeroba kasamin” da sauri ya kalleta “What kece Jalilan?” zumbura baki tayi “Eh nice” “karya kikeyi” ba tace komai ba ID card dinta ta dakko ta diremasa a gabansa, dauka yayi ya karanta ya kalleta tabbas itace

“Ya akayi kikacinye test dina gaba daya alhalin wani abunma banmuku ba, kaf ajinku ba wanda yaci ko 30,ko satar amsa kikayi? Kallon yan matan dake office din tayi tai ta kalleshi tace

” Sir Hafiz , Never Judge book according to it’s cover, bana satar amsa kuma bantabayiba, kana muzantani agaban yan aji kana cemin dakikiya, abun ba anan takeba, kayi alkalanci, idan baka yadda da wannan test dinba ka canzamin wata, amma karkayi tunanin zaka tambayeni a gaban yan aji in baka amsa” shiru ya danyi, ya kalleta yafarayi mata tambayoyi, a nutse take bashi amsa, gashi ta iya turanci matuka, ga mamakinsa har abunda be koya musuba inya tambayeta seta bashi idea dinta, ajiyar zuciya yayi “shikenan zaki iya tafiya zan nemeki” Jalila ta juya ta fita. Sir Hafiz ya dade yana mamakin kwakwalwarta, gata gentle, amma meyasa tsarin rayuwar ta daban da saura ko maganarta ma daki daki kuma a tsare, kuma ba ruwanta maganar kozatiwa wanda ta fadawa dadi ko a a seta fada kuma ko  a gaban waye. haka yaita mamakinta. 

  Yau weekends dan haka tun sassafe Jalila taketa gyaran wardrobe dinta, tagama tsaf seta ga qura’nin da daddyn Jalal ya taba bata, ta jujjuya qura’nin yana nan kar dashi a cover dinsa “Yakamata in dinga tilawa da qura’nin nan, Allah ya bawa daddyn Jalal ladan” tagama gyaran drower dinta, ta tafi kitchen, wainar masa suka tsiriyi itada halima, a matsayin abincin rana, seda suka gama Jalila taje tai wanka ta dawo ďaki ta zauna tana kwalliya wayarta tafara ringing, tana dubawa taga bakuwar lamba ce, bata san wayeba dan haka ta saka wayar a silent. 

Tunda daddy yazo garin nan Ilham take kasa kunne taji, anyi batun aurensu da Jalal amma shiru yau kwanan daddy uku da dawowa amma bataji Mummy tace komai ba, dan haka ta yanke shawarar zuwa tasamu Mummy, dakin Mummy taje bata nan, dan haka ta tafi kitchen, aikuwa Mummy na can tana hadawa daddy fruit salad

“Mummy sannu da aiki” 

“Yawwa daughter, kin tashi daga baccin ne?” “ina wani Bacci Mummy alhalin duk ina cikin zullumi da damuwa” “akan mefa?” “Mummy maganata da Jalal mana, har yanzu naga Daddy ya dawo amma bakice komai ba fa” 

“Ilham kenan akwai gajen hakuri, ina nan zan gayamasa insha Allah kafin yakoma za asa ranar aurenku” Murmushi Ilham tayi “Allah yasa Mummy, dan na kagu inganni na mallaki yayana” “hmm daughter ba kunya ko” Ilham ta dan rufe ido tana dariya. 

Jalila tagama kwalliyarta tasaka turare, ta mike taje ta dauki Abincin Jawwad ta nufi part dinsa dashi, tana zuwa ta tarar bakowa a palour, ta ajiye abincin tasamu guri a palourn ta zauna, tana jiransa koyana wanka ne, ta dora kafa ďaya kan ďaya tana danna wayarta, hankalinta yana kan wayar sosai, tana game tanayi tana murmushi, warin sigari taji ya daki hancinta, da sauri ta ďaga kanta, tai tozali da Jalal ne ya fito daga bedroom din Jawwad, kallo ďaya tayi masa ta ďauke kanta taji tsigar jikinta ta tashi, dagashi se gajeren wando, kana ganinsa kasan yana cin karfe, a murďe jikinsa yake, ga ko ina na jikinsa lullube yake da gashi, fatarsa se sheki take, babu alamun wahala a tareda shi, ya nufo inda Jalila gadan2  zazzare ido Jalila tayi, kirjinta ya shiga dukan uku2 tanaso tayi magana amma takasa. 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button