Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 15 Book 1 End

Jalal yace “Lafiya naji kana wani what, ko baka gane menace bane?” 

“Amma meyasa zakayi manaa haka Jalal, mun riga mungama shirya komai, sannan kace wai se a maida shi eight, haba Jalal dan Allah, dolene se Jawwad yaje gurin, mene a ciki dan munyi iyamu da abokanmu yanzu…. 

” Kaga Jeje ba dole ai bani na rokeku ba dama tun farko dan haka, inbazaku canza lokacin ba bazan zo ba” yana zuwa nan ya kashe wayarsa, jeje ya daki tabur ya zuba ashar, 

“kingani ko Hannah wallahi dole a hukunta Jawwad, a koda yaushe shi ke bata mana shiri,” 

Hannah tace

“Kaga kaifa fushi banaka bane a yanzu, ka yadda kawai, in ba hakaba wannan damar ta wuce aiki ze kuma komawa baya, gara ka kirashi kace ka yadda” , jinjina kai Jeje yayi

“Shikenan amma Jawwad seyaga abunda zanmasa” 

Haka jeje ya kira Jalal, yace masa sun yadda, 

Washe gari babu zato babu tsammani, Daddyn Hanan sukazo shida Abdallah, suka duba Jalila, taji dadi sosai da zuwansu, dukda ba wani dadewa sukayiba, dayake hanan  gaya masa abunda yasamu Jalila, daga bauchi suka dawo suka biyo suka tsaya a kano domin dubata, Daddyn Hanan yace Insha Allah shima ta bangarensa zesa aimasa bincike game da batan Ummin, sannan yaita rarrashin Jalila tareda yimata nasiha, 

Daddyn Hanan yacewa Abba 

“gaskiya wataran zanzo kabani Jalila, mutafi da ita bauchi, gurin kakarsu Hanan, itama taga wannaan kamannin nasu, daga bata labarin Jalila se magiya take dan Allah akaita ta ganta, dayake ta tsufa bata iya fita aida da ita zamu taho” 

Abba yace

“Allah sarki insha Allah randa kuka shirya kuzo ku kaimata ita” 

“To shikenan, nagode kwarai da karamcinka Alhaji usman” 

Sukayi musu sallama suka nufi kaduna

Kwanan su Abdallah biyu da zuwa, su Jalila suna cikin farin ciki, sun samu admission a BUK daga ita har  Nana, ranar litinin zasu fara zuwa makaranta, Abba yayi musu nasiha sosai game da rayuwar dazasuyi a cikin Jami a, ita Nana 

mass communication zatayi, itakuma Jalila catering craft zatayi, da farko Jawwad yaita mata mita akan mezatayi da wani catering duk kwakwalwarta, itakuma tace shi takeso, dan tana son harkar girke2 da sanao’in hannu. 

Download>>> Yar Harka Complete Document

Anata shirye2 birthday Jalal, Yanzuma Jalal ne da Jawwad a harabar gidan akan fararen kujeru, suke zancen yaya birthday din ze kasance, Jalila ta fito zata fita, 

“Yaya barka da yamma” 

“Yawwa baby ina zuwa haka?” 

“Maama zan karbowa kaya, a jambulo” 

“Bari mu tafi tare, semu ajiyeki dama fita zamuyi” 

“To yaya, bari inje waje in jiraku” 

Jawwad ya kalli Jalal, “Dakko motar, bari inje insaka kaya” 

Jalal ya fito da motar waje, Jalila bata shiga motar  ba tana tsaye a waje har Jawwad ya fito, suna shirin tafiya sega wani abokinsu Jawwad yazo wucewa, tsayawa yayi suna gaisawa, dayake  tsohon abokinsune kuma sun dade basu hadu ba, 

Jawwad yace “kai faruk ba a ganinka ko a gari, ina ka shige haka ne?” 

Wanda aka kira da faruk yai dariya “ina nan Jawwad, makaranta ce munata fama, kasan yanzu ina ABU zaria bana zama sosai a kano, yanzuma wani filin baba mukazo gani unguwar taku, Jalal nema bana ganinsa sam” Jalal ya kalli Faruk ya danyi murmushi, sannan yace

“Nima ina nan haduwa ce dai tai wuya, ya karatun? ” 

“Alhamdilillah Jalal, y garin, ya karatu ko har yanzu baka koma makarantar ba” Jalila dai na tsaye jikin mota tana jinsu, Jalal yace

“Gari gamu a cikinsa, makaranta kuma bana zuwa har yanzu” 

Jawwad yace, “Faruk, yana Jalal yana shirin komawa makaranta kwanan nan insha Allah” 

“To Allah yasa” 

Jawwad yace “au Jalal nayi mantuwa, bari inje in dakko wayata, ka karbi lambar faruk mudinga gaisawa” 

Jalal yace “Ok seka fito” 

Jawwad ya shiga gida, faruk ya kalli Jalal, yace “Jalal wannan kuma wacece?” jalal ya dan kalli Jalila sannan yace

“gata nan tambayeta mana” 

“Hmm Jalal halinka yana nan dai” faruk ya kalli faruk “y’an mata yakike? “

“Lafiya kalau” faruk yakuma cewa “Jalal ban san wannan ba, kanwarka ce kota Jawwad, kokuma…. Jalal ya katseshi ta hanyar cewa

” kai faruk, kaima surutun nan naka yana nan da shegen son mata” dariya sosai faruk yayi, ana haka sega wata mota tazo wucewa, amma akayi parking mutumin ciki ya fito, babban mutum ne, ya tunkaro su a fusace da farko faruk be ganshiba seda gabaya, dan bude baki yayi ya zaro ido, mutumin yana zuwa ya kalli Jalal sannan ya kalli faruk, 

“Kai faruku, ban hanaka kula wannan dan iskan yaron ba, danayi sa a na rabaka dashi, shine yauma kakuma lallabowa, gurinsa ko, sekaima ka lalace kamar sa, kai ko kyamarsa ma bakayi, dubeshi kana kallonsa kaga mutumin banza wuce kabar nan gurin ko in kifa maka mari, “

Faruk ya fara in ina” A a Bab… Baba, dan Allah kayi hakuri, gaisawa kawai muke 

“Zaka wuce ko sena marekan, nahanaka hulda da yaron nan, inkuma kaima kafara shaye2 ne kaima se inji, ba Shiri faruk yai gaba, yana waiwayensu

Jalal dai bece komaiba ya sunkuyar da kai yai shiru, Haka nan se Jalila taji ba dadi, mussaman da Jalal ya sunkuyar da kansa bece komai ba, 

Mutumin ya juyo ya kalli Jalal, ya nunashi da yatsa

“kaikuma bakai ba dana, idan nakuma ganinka dashi wallahi hukuma ce zata rabamu da kai, dana ba lalatacce bane ba kamar kai, ni dana kamiline, baze yiwu ka koyamasa shaye2 da rashin tarbiyya ba,” Jawwad ne ya kawo kai ya fito ya tarar da cin zarafin da akewa Jalal, tsayawa yai cak yana kallon ikon Allah, mutumin ya cigaba da bala’i

” ni banyi sake ďana ya lalace ba dan haka bazan bari ka lalata min shiba, niba nusarin ubane ba kamar ubanka, daya bari ka lalace kalleka, kowa ya ganka yaga dan iska mara tarbiyya sha3″ harzuka Jalal yayi, ya kura ma baban faruk ido, amma abun mamaki still Jalal yaki cewa mutumin nan uffan

“Shima baban nasa bashi ya saiwa kansa ba, kuma ba laifi yayiwa Allah ba ya jarrabeshi da fitinanne yaro ba, haba baba, a haka gaka dattijo amma aji wannaan maganganun suna fita daga bakinka, to in Allah ya doramaka ya zakayi? Akan wani dalilin zaka dinga zaginsa dan kawai ya gaisa da danka, shi Jalal din shi yaiwa kansa, ka gayamin wanda akayi shawara dashi kafin a halicceshi, ko kaddara abunda ze faru a rayuwarsa”

Gaba daya ido suka zuba mata baki bude, suna kallonta, tsagwaron bacin raine kwance a idonta, bil hakki take fadan maganganun da take, kana kallonta kasan har zuciyarta ranta ya baci, Jawwad ne yai yunkurin cewa

“Jalila meye haka, ba kya ganin babban mutum ne? Baba kayi hakuri insha Allah Jalal baze kuma… 

” Wai yaya Jawwad laifin me akayi masa kake bashi hakuri, ABDUL JALAL ne ya taka kafa yaje inda dansa yake kokuma shi yakawo kansa, baba irin wannan abubuwan da akewa mutane irinsu Jalal shike kara lalatasu, yazama bame jansu a jiki, kowa se kyama da tsangwama, danka da kake fada akansa ma mutum ne, kuma baka isa ka hana Allah ikonsa akan shiba, in Allah ya jarrabeshi shima, yazakayi a ganina in bakayimasa addu a ba bekamata ka zage shi haka ba, da kake cemasa mara tarbiyya kazagi mahifinsa da ya dau mataki akanka fa, kasan a hakan nan se ya zageka tsaf bazaka iya masa komai ba, kuma kaga hakan baze maka dadi ba”

Jawwad yace na shiga uku, halin Jalila yana nan ashe, bata canza ba, shiru2 da take na kewar Ummi ne ashe, yayinda Jalal yai shiru yana satar kallonta, Jawwad yace

“Ke kiyimin shiru, meyasa kike haka, sa ankine” 

Baban Faruk yace, “Kyaleta i like her confidence, kin birgeni sosai yarinya at least, kin tunamin abunda na manta, nagode sosai” ya kalli Jalal yace

“Am sorry my son, nasan na bata maka rai, kayi hakuri” yajuya ya wuce ya hau motarsa ya tafi

Jalal be taba tunanin tsiwar Jalila ta kai haka ba, babban abunda yabashi mamaki yadda ta zakakalkale haka, bayan itama rashin mutunci takemasa, juyawa tayi ta bude bayan mota ta shige abunta kamar batayi komaiba, Jawwad yacewa Jalal “taho mu tafi” ba musu Jalal ya bishi, amma Jawwad ya zauna a mazaunin direba, Jalal yana kusa dashi, Jawwad dan waigo ya kalli Jalila sannan yace

“Baby ya haka, abunda kikayi kin kyauta kenan? Babban mutum ne fa, haba baby dama baki canza ba?” 

“ka taba ganin an haifi mutum da hali ace ya canza, in tsoho beji kunyar hawa jaki ba jaki baze ji kunyar kada tsohoba, a matsayinsa na babba abunda yayi ya dace kenan, kozakayiwa mutum rashin mutunci karka hada da mahifinsa, shima daganinsa kaga criminal idonsa kawai zaka kalla kasan ba mutumin kirki bane”

Shi Jawwad Jalila ta dena bashi mamaki tsoro take bashi

“Ke Jalila ya akayi kikasan criminal ne, karki kuma, baban wanine koba komai ya haifeki” 

“Yaya nifa ba karya nayiba bakaji yadda yake magana ba ne? Shima wannan nusarin Jalal din yanaji ana zaginsa yai shiru, inkaga yana masifa to akan Matane, yadinga wani muzurai, matsalar mutum ya dinga abunda bashi da kyau kenan wanda ya isa da wanda be isaba sunemi suci mutuncinka”

Bude baki Jawwad yayi ya waigo yana kallonta, dama haka take, tunda ake fadar iya tsiwa na Jalila be taba tunanin ta kai nan ba, rasa bakin magana yayi, shikuwa Jalal ko motsawa beyiba daga inda yake balle ya nuna yasan dashi take, sema tunani da yayi zurfi a ciki, amma yana jin duk abunda take fada, haka motar tai tsit har sukaje jnda zasu sauketa, tace

“Yaya Jawwad ka jirani man in shiga in karbo, semu tafi bannaa son tafiya ni ka dai, kasan ban san kan garin  nan ba” 

“gashi kuma ba gida muka nufa ba, zamuje siyayya ne” cikin shagwaba tace ” eh naji, ko ina zakuje dai, dan Allah kujirani” 

“To yi sauri karkimin kuka” tayi murmushi ta bude motar ta fita”

Jawwad ya dan kalli Jalal sannan yace

“Jalal, Jalila ba karamin mamaki ta baniba, ban taba zaton zata iya haka ba, babban mutum kaman wannan sam bata da tsoro, amma kaima bazan gaji da baka hakuri akan abubuwan datake yimaka ba, kuruciya na damunta, har yanzu yarinya ce” 

“Wane kalan kaya kakeso musaka ranan, so nake muyi shiga iri daya” 

“A a ya ina maka magana kaikuma kana min wani zancen daban” 

“Kasan akwai kaya da daddy ya turo dasu zamuje mu duba, in bamu samu wanda mukeso ba semu siyo wasu, i wish daddy yana Nigeria zanyi birthday” Jawwad ya fuskanci Jalal rainin hankali yakeji, wato baya son wancan zancen da sukeyi, dan haka ya rabu dashi. 

  Bayan barin Alhaji kabiru gurin nan, ya dinga tunanin wace wannan yarinyar haka, wace ce ita, mene alakarta da Jalal haka, wayarsa ya dakko ya kira lambar Jeje, bugu biyu Jeje ya dauka, 

“Allah ya temaki, oga KB” 

“Jeje tambayarka zanyi” 

“to Oga Allah yasa nasani” 

“akwai wata yarinya danagani a gurin Jalal, ko kasan wacece dinsa” 

“ya take oga?” 

Ya fasalta masa siffar Jalila, jeje yace gaskiya be santa ba amm ze bincika masa. 

Jalila ta fito, tazo ta bude motar ta shiga, Jawwad yace “har kinfito” 

“Eh Yaya banason bata muku lokacine” 

Jawwad ya kunna mota, suka hau titi, suna hirarsu da Jalal, aka jima se cewa tayi

“waimu ba za a gayyacemu bane?” 

Jawwad yace “mu mun isa dole a gayyace ku mana” 

“hadasu Nana, da Ilham” 

“Eh mana hadasu” shidai Jalal bece uffan ba, baze so zuwan Jalila gurin nan ba dan yasan tabbas setayi surutu intaga abunda be mata ba, kuma yasan dole ayi shaye2 a gurin, meyasa Jawwad ya amsa mata suje gurin nan, a titi suka sauketa, sukuma sukayi gaba, ta dade tanajira sannan ta samu napep ta karasa gida, a palour ta tarar da Maama da Abba ta kaiwa Maama kayan, Abba yana mata sannu da zuwa, Maama ta bubbude kayan ýan kunnaye da sarka masu matukar kyau, 

Jalila tace “Maama bari in daukesu a waya a tura social media, za a samu costumers tunda new design ne” dayake a gaban Abba ne se Maama ta sakar mata fuska, 

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

“eh hakan yayi kyau, in anjima dan Allah ki mikawa mummy, dama saboda ita nasa aka karbosu tacemin ana so” 

“to shikenan bari inyi salla” harta mike zata tafi, Abba ya kirata ta dawo

Yace “daukar muku, keda Nana kowa biyu, se a gayamin kudin” 

“to Abba mungode Allah yasaka da Alkhairi, Allah yasa afi haka” 

“Ameen ya Allah, Allah yayi Albarka” Jalila ta tashi ta tafi dakinsu, yauma Nana bat nan, Jalila tayi salla taci Abinci, ta kwanta tana hutawa, ta dau wayarta tana ta tura kayan nan social media a haka har bacci ya dauketa

  Jawwad sun sha yawo, shida Jalal se kusan la’asar sannan suka dawo sun gaji matuka, sallar la’asar sukayi, sannan Jawwad ya kira Jalila a waya yace dan Allah akai musu Abinci, ji tai kamar tace A a saboda batason yawan zuwa inda yake tunda mahaifiyarsa bata so, amma Nana bata nan Halima ma haka, badan haka ba da bazataje ba, 

“to Yaya gani nan zuwa, bari in kawo” 

“to shikenan muna jira” 

Jawwad ya kalli JALAL, bari in shiga in dan watsa ruwa kafin ta kawo abincin” Jalal yace

“to kifi, sarkin ruwa seka fito” befi 3min da tafiyar Jawwad wanka ba Jalila ta shigo da kayan Abinci, tai sallama amma Jalal ya mata banza dama bata sa ran ze amsa ba, ta ajiye Abincin, harta juya zata fita taji muryarsa

“Ke zo nan” kutmelesi wai ke, juyowa tayi da niyyar yi masa rashin mutunci, kawai taga yamata wani mugun kwarjini, gashi ya kafeta da ido, 

“gani mene?” tazo kansa ta tsaya tana zumbura baki, hannayenta ya janyo da karfi seda ta durkusa akan gwiwoyinta, seda ta danyi kara ta dago ta kalleshi tareda fizge hannunta, saboda taji zafi

“Idan na kuma kiranki, kikatsaya min aka, kamar itace sena miki abunda zaki karye, mara kunya kawai” kallon up and down ta masa ta dauke kanta 

“Ubanwa kike cewa nusari dazu, wait tukuna ma, uban wayasa kiyiwa mutumin nan rashin kunya, ke yayiwa koni, meye alakarki dani da zakiyi wa babban mutum kamar wannan rashin kunya, inkinyi dan ki birgeni ne, to baki birgeba dan JALAL bayasin shishshigi” 

Murmushi Jalila tayi wanda yai matukar yi mata kyau, “wayace maka saboda kai nayi, aini birgeni yayi da yayi maka haka, kasan wanda yasan darajar dambu shike zuba masa mai, duk inda naji ana cin mutuncin iyaye koba nawa bane raina baci yakeyi, saboda karya zarce da zagin daddy shiyasa nai magana domin dakatar dashi, ba wai dan kai ba, kwakwalwarka ta dinga lissafa maka dai2 mana” kuramata ido yayi baya ko kiftawa, sekuma yayi dariya

“Karya kikeyi, idonki ya nuna abunda kike fada  a yanzu karyace kawai,

Sekuma ya hade rai

” Zan miki wani kashedi, idan kika kuskura kikazo gurin birthday na duk abunda yasameki kekika jiyowa kanki, danban gayyaceki ba, tashi kbmibani guri, mummuna uwar magana kawai” mikewa tayi ta danyi gaba sannan ta waigo ta kalleshi

“wallahi senaje, ai ba dan kai zaniba, saboda yaya Jawwad zani, tunda shi yace inje, dayake abun na rashin gaskiyane shine wai ba a gayyaceniba, to wallahi senaje, inyaso in naje a dakeni, ragon maza kawai nusari. 

Tana gama fadin haka ta juya tai tafiyarta, dan girgiza kai Jalal yayi, ya cigaba da danna wayarsa, Jalila na komawa taga Maama tafito daga kitchen “Ke daga ina kike?” “Yaya Jawwad ne ya kirani yace in kaimasa Abinci” tsaki Maama tayi sannan tace “inkinyi sallar magariba, ki mikawa Mummy kayan nan” “to zan kaimata Insha Allah” Maama ta wuce, Jalila kuma ta shige dakinsu tana zuwa ta tarar Nana ta dawo, “Nana Ashe kin dawo, sarkin kawaye” “bawani sarkin kawaye, zumunci dai” 

“hhh to naji, ya kika baro su” “suna lafiya amma naso tare mukaje, ke kullum kina gida” “ai bayan tafiyarki nima na dan fita Maama ta aikeni” “inyee kinfara gane gari” “sosai makuwa” sukayi dariya sannan Jalila tace “Nana wai ranar Saturday za ayi birthday din Jalal” “Are you serious, ya akayi kika sani?” 

“Yaya Jawwad ne yagayamin” 

“Amma ya haka duk shekara tare sukeyi fa” “nima bansaniba, guri zasu kama amma muma zamuje” 

“dan Allah ai basu gayyacemu ba” 

“Injiwa Yaya yace zamuje muma” 

“kai amma naji dadi Jalila dama an kwana biyu banfita wani outing ba” 

“Haka kika iya sarkin yawo” 

Download>>> Bakar Inuwa Complete Document

   Bayan Jawwad sun gama cin Abinci suka fito suna hira, a harabar gidansu Jalal suka koma suna basket ball, se magariba suka bar gurin, bayan sallar magariba Jawwad yacewa Jalal, yazo suje gurin Mummy “muje muyi mata me?” “yakamata dai muje kwana biyu ban ganta ba bamu gaisa ba” “kaje kai kadai mana, ba dolene se naje ba” “Jalal ba shawararka nake nema ba, ka tashi mu tafi” Ganinda Jalal yai Jawwad ya hade rai sosai, shiyasa shi mikewa, “tashi muje” Jawwad ya tashi suka tafi cikin gidansu Jalal, Jalal ne a gaba Jawwad yana binsa, Ilham ce kadai a palourn kwance akan three seater tana daddanna wayarta, mikewa zaune tayi tareda fadin “sannunku da zuwa” Jawwad ne ya amsamata, “yawwa Ilham, ina Mummy ne?” “tana dakinta, inaga salla takeyi bari inje in kirata” ta mike ta nufi part din Mummy, Jalal dai se cika yake yana batsewa sekace wanda akayiwa wani laifi, ba a dadeba sega mummy ta fito, Ilham na bayanta, ta karaso ta nemi guri ta zauna a palourn, dan risinawa Jawwad yayi “Mummy ina wuni” “lafiya kalau Jawwad kwana biyu ya gida, yasu Maaman” 

“tana lafiya” “Kwana biyu bamu hadu da ita ba, ina jira zata aikomin da kaya” “eh dazu naga an karbo, amma zata aikomiki ne” “Yayi kyau” shidai Jalal bece uffan ba, sema mike kafarsa da yayi ya kashingida, Jawwad yace “Mummy ranar Saturday yakama birthday din Jalal fa” “ina sane Jawwad, wannan karon ba tare zakuyi ba” “eh mummy, nashi zamu farayi tukuna, nace bari agaya miki” “Assalamu Alaikum” gaba daya suka amsa sallamar tareda waigawa, ko be juyoba yasan muryar Jalila ce, karasowa tayi cikin yanga, ta kalli Jawwad tai masa murmushi sannan ta durkusa kasa tace “Mummy ina wuni” “lafiya kalau ‘yan mata kwana biyu, kin buya bana ganinki” murmushi Jalila ta kumayi “ina nan Mummy bana fitane kawai” “amma baki da lafiya ne, naga kin rame haka?” Jawwad yace Mummy ta danyi rashin lafiya kam””Allah sarki ba labari, Allah ya sawwake” suka amsa da Ameen banda Jalal da Ilham dan tunda ta shigo Ilham ke mata kallon banza

Mummy tace “Jalila yi hakuri bari in dan saki aiki, jeki dakina akwai drowern mirror dina akwai, key ki dauka ki bude wardrobe dina, zaki ga akwai wani kit kibude ki dakko kudin ciki

Ilham seda ta kalli Mummy dan sam Mummy bata sata harkar kudinta, amma yau ta tura Jalila har bedroom dinta ta dakko kudi, seda Jalila tayi Jim kaman bazata ba sannan ta mike, ta nufi dakin Mummy, 

“Yawwa Jawwad ina jinka, yi hakuri na tsaya surutu” “bakomai Mummy dama cewa nayi, ko zaki halacci gurin birthday din nasa” Jalal ne ya dago da sauri yana wa Jawwad wani mugun kallo, shikuma ya dauke kai kaman besan me yake ba, murmushi Mummy tayi “waceni Jawwad, Allah ya temaka, ya raya Jalal sannan ya shiryamin shi” 

Koda Jalila tashiga taga part din Mummy ma ya tsaru, katon palour ne, me dauke da kayan alatu, se tangamemen kofar bedroom dinta, ya tsaru matuka, kaikace a kasar wajene, Jalila ta nutsu ta dau abunda aka sata ta fito. 

Jawwad ya gyara zama sannan  yace “Mummy in bazakije ba ga Ilham, ko yan uwa ai yakamata sumana kara suyi attending” Jalal ji yake kaman ya make Jawwad, shi bayason gayyar surutu, amma Jawwad se gayyato masa tarkace yake Ilham tace “Jawwad aini ko ba ku gayyaceni ba zuwana gurin birthday din yayana dolene, dan haka zanje nida kawayena” wani uban tsaki Jalal yayi, duk suka juyo suka kalleshi, Mummy tace “kagani ko Jawwad, nikam Allah yakawo silar shiryuwar Jalal, yanzu a haka kake tunanin inyi attending gurin birthday dinsa, ya dizgani a gaban abokansa, Sam baya ganina da mutunci” 

Ai kuwa Jalal a fusace yace “kagani, nidama bance tazo gurin birthday na ba, seda nace bazanzo ba amma ka janyoni kaga har zata faramin korafi sek……. Sekuma sukaji yayi shiru, ya koma ya kashingida, fitowar Jalila taji Jalal yana wannan masifar suka hada ido, ta girgiza masa kai, alamar ya dena, shine abunda yasashi yin shiru, yakoma ya kashingida, duk abun nan ba wanda ya lura dame ya faru se Ilham, wadda taji kaman an dakko dutse an sakamata a zuciyarta. 

Jalila ta karaso ta durkusa tabawa mummy kudin, Mummy tace “tafi dasu, kibawa Maama kice kudin wancan kayanne, ban mata transfer bane saboda wayata, ta dan samu matsala” “to zan gaya mata Insha Allah, seda safenku” Jawwad yace “bazaki jirani ba” “a a yaya, seka taho” 

Ilham ce tafara mikewa ta tafi dakinta, sannan Jalal, shima tashi yayi ya bar dakin, dan Jawwad yagama bata masa rai, Jawwad kuma ya tsaya, yaita rarrashin Mummy kan halayen Jalal, sannan yai mata sallama ya tafi. 

Koda Ilham ta koma dakinta ji tayi kaman ta dora hannu akanta ta fasa ihu, wannan wace irin masifa ce, tunda take a gidan nan, mummy bata shigar da ita cikin sha anin kudinta, amma yau da kanta ta tura Jalila kan kudinta, kuma karewar abun takaici wai hartayiwa Jalal signa ta hanashi abu, kuma ya hanu, lallai akwai sauran aiki, meyasa wannan yarinyar ta shigo rayuwarmu tayi kane2 haka, me yakamata inyine, kozan yi yawo tsirara se burin mahaifiyata ya cika, amma ta yaya? Wata zuciyar ta tambayeta, shiru tayi zuwa can kuma tayi wani irin shu’umin murmushi, tareda jinjina kai, “muje zuwa, Jalila kin tara kin samu, senayi sanadiyar da mujiya seta fiki farinjini a cikin al umma” 

     A satin ranar Monday su Jalila suka fara zuwa makaranta, Abba ya daukar musu driver saboda Kar a dorawa Jawwad nauyi dayawa shima ga nasa karatun, Jalila taji dadin fara zuwa makaranta, in ka ganta kai kace irin salihar nan ce, dan ko magana batayi sosai, wanda yana cikin halin Jalila in taje guri seta karanci kowa tsaf sannan zaka san wacece, ko magana bata fiyeyi ba, sannan bata yadda tayi kawa ba har yanzu, a satin nan tunda tafara zuwa hijjabi take sakawa har kasa, se farin glass, yauma uban dogon hijjabinta dark blue har kasa ne a jikinta, se jakarta data rataya, sunfito daga lectures tana jikin wata bishiya inda suke haduwa da Nana, taji  wasu suna zundenta wai ga ustazan jami a, gigin secondary ne ta shigo a ustaziyya kafin afita kuma anyi clean, irinsune mugayen tantiran makaranta in suka waye, itakam ko ta kansu batabiba, dan ko kallo basu isheta ba, a ranta tace “kucigaba karku fasa, ku bari in zama yar gari, zaku gane baku da wayo dan ba ruwana da wata jami a, mutun yayimin senayi masa, but now kuci karenku babu babbaka” tana tsaye nan Nana ta karaso, suka nufi motarsu, a hankali Jalila take gane halin yan ajinnasu, da yaran masu kudi, dana talakawa masu dorawa kansu karya, yan rainin hankalin lecturers, da masu iyayi, kowa tana ankare da halinsa, tana ganesu, amma still ba ruwanta da kowa, wasu suyi gulmarta a gabanta wasu a bayan idonta, seta nuna musu ita magana ma abun wahala ce a gurinta, 

Nana kam hartayi kawaye daga zuwanta, yayinda dabi un Jalila suka tafi da imanin kawayen Nana, ta iya gayu maganarta kawai abun burgewa ce balle tafiyarta da sauran

mu amalarta, sedai suna mata kallon me girman kai, saboda gani suke kaman wulakanci take musu, inba Nana ba bata kulasu, dan ta yanayin shiga da mu amala tana iya gane, mutanen banza dana kirki, Jalila kenan me abubuwan ban mamaki

Ilham ta gayyaci kawayenta gurin birthday din Yayanta kuma masoyinta wato Jalal, se wani rawar kai take tana shirye2, ta gayyaci su yaseera da sauran kawayenta, se shiri takeyi, taje sabon gari ta sha kitso, tayi booking din make up, hatta shigar da zatayi sabon kaya ta siya. 

Jalila ma nata shirin takeyi, saboda mugayen mafarkan da take da Jalal, dan haka da shirinta, zataje gurin birthday din nan, tanason tayi taka tsan2 sosai a gurin nan dan ita sam bata yadda da wannan birthday dinba, tana so taga suwaye abokan Jalal ne, mussaman Jeje, dakuma wasu abubuwa da take shirin yi a gurin, tanason tabattar wa Ilham Jalal baya gabanta, Bangaren Jeje ma shidasu hannah da abokan shaye2 sun shirya tsaf domin gudanar da mummunan kudirinsu akan ABDUL JALAL. 

Ranar juma a da daddare, wanda yakama jajibir din birthday din Jalal, Jalila ta tafi Dakin Jawwad domin tana son magana dashi, tai sa a kuwa shikadai ta tarar a palourn, taje tasamu guri ta zauna, Jawwad ya kalleta”Babyn Yaya Jawwad, ya akayine?” 

“gurin Yaya nazo” “to Yar gidan Yaya, ina jinki” 

“Yaya Jawwad , gaskiya abokinka tunda mutane masu hankali zasuje gurin nan, dan Allah ka kaishi a rage mai gashin kansa, sannan kar kabari yasaka sarkan nan dayake sakawa sekace wani kare, ga wan….. Kai tsaye ba sallama sukaga Jalal ya shigo, hade rai Jalila tayi” a dai dinga yin sallama” banza Jalal yai mata, ya kalli Jawwad “kai gurinka nazo” Jawwad yace”ai gani, Allah yasa lafiya” wayar Jawwad tafara ringing “excuse me bari in amsa waya” yadaga wayar yasaka a kunnensa tareda yin sallama “Assalam Alaikum” 

Download>>> Yaro Ne Complete Document

Muryar Hanan Jalila taji “wa alaikum salam barka da yamma Taurarona fatan kana lafiya?” 

“lafiya kalau Hanan, ya gida, yasu Abdallah da daddy?” “suna lafiya, nice dai bani da lafiya” “yasalam meyasameki” “kewarka mana, itace take damuna, yanzu yaya queen take, naga kwana biyu haushina takeji” “tana lafiya, yanz… Juyawa yayi da nufin yabawa Jalila wayar, yaga Jalila ta cika ta batse, ta hade rai sosai, fasa bata wayar yayi, yace

” Queen dinki tana lafiya” “Masha Allah ina sirikata Nana, kodayake ita muna waya, dan Allah Yaya Jawwad yaushe zakuzo Kaduna ne, inaso inkuma ganinka, kullum senayi mafarkinka fa” Jalal dake gefe ya kalli fuskar Jalila kawai ya kwashe da dariya ganin yadda ta hade rai, Jalal ya tashi ya fita daga palourn, yana kuma yin dariya, ba karamin kyau Jalal yakeba idan yana dariya, Jawwad seda ya sha jinin jikinsa yakuma kallon Jalila, muryar Hanan ya kuma ji “my Haidar bakace komai ba, dan Allah yaushe zakuzo?” mikewa Jalila tayi ta fice daga palourn dan bazata iya cigaba da jin wannan hirar ba, ashe Hanan dagaske take son Jawwad tajeyi, kishi ya lullube Jalila ta fito ko ganin gabanta batayi, tazo fita taga Jalal a tsaye, a kofar fita, shiru tayi ba ta cemasa komaiba ya kalleta, yadda ta hade rai, tuntsurewa yakumayi da dariya, “kinji abunda Ilham takeji ko? Kinji yadda takeji idan taga kinamin shishshigi ko?, are u jealous of your brother” wani mugun harar tayi masa “ni matsa in wuce” Jalal yace”in naki fa? Ji yadda kike wani hade rai” sekuma ya hade rai kaman bashi yake dariyar nan ba yace “to bari in gayamiki, dakaina zan dauki Jawwad in kaiwa Hanan, ubanme Jawwad zeyi dake gaki mummuna gaki kwaila, se tsabar iyashege da rashin kunya da kikasa a gaba, ni zan tsayawa Hanan seta auri Jawwad, in yaso kije kinemi me tsautsayin daze aureki, wanda ze iya tolerating wannan nonsense din naki, sokuwa kawai, wuce ki ban guri” murguda masa baki tayi, tazo zata wuce ya kuma rufe hanyar, ya kalleta 

“Kashedina dake na karshe, gobe in Allah ya kaimu kika sake na ganki gurin birthday na, duk abunda ya sameki kekika jawa kanki, idankuma kinkiji kinje gurin, idan kika sake kikayi wannan karambani a gurin, shima kome ya biyo baya ke kika sani,”

Cikin bacin rai tace” waini kadai ka tsana zakace bazanje ba, wallahi senaje, sedai in baza ayi ba, kuma wallahi niba mummuna bace ba, Mummuna tana gidanku wato Ilham” kallonta ya kumayi tsaf, sama da kasa, be kuma cemata komai ba,  yabata hanya ta wuce, tana tafe tana mita, harta je dakinsu, Nana ta kalleta “lafiya dai, naganki kina fushi hada mita” “Ke rabu dani ba komai” 

Sallar isha i tayi ko Abincin dare bataciba, tanemi guri ta kwanta, banda kishi da bacin rai ba abunda yake damunta, “haba Hanan yazaki min haka, meyasa kikeson Jawwad din, kema ina sonki, zan iya sadaukar miki da komai nawa da kikeso, saboda kaunar da nakemiki, amma banda yaya Jawwad dina” haka taita juye2 da kyar bacci ya dauketa

Jalal yana tsaye se fara a yakeyi, ga wani katon cake 🎂 agaban sa, ga mutane nata hada2 Hannah ta yanka cake ta dakko tasaka masa a baki, cake din na shiga bakinsa yazama baki, jini yafara zuba daga bakinsa ya fadi a gurin, da gudu Jalila ta karasa ta kifar da tebur din da cake din kafin ta juyo ba kowa a gurin daga ita se Jalal, ta tafi tana lekawa taga koda wanda ze temaka mata ya dauki jalal a kaishi Asibiti tana dawowa taga, Ilham ta shake Jalal tana kokarin kasheshi

   “Subhanallah!!!” ta furta da karfi

  _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)

Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa’azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

Download>>> Tubali Book 1 Complete Document

A firgice ta mike zaune tana waige2, Nana ta tashi zaune itama, “lafiya Jalila, meyasaki ihu haka” Jalila ta hada zufa, se haki take hannu tasa ta dafe kanta “bakomai Nana, yi hakuri na tasheki, kwanta abunki, na dan tsorata ne kawai” “to shikenan, ki kwanta kema, darene sosai yanzu” “to zan kwanta” Nana ta cigaba da baccinta, yayinda bacci ya kauracewa idon Jalila, se tunani da yacika mata zuciya, da taga baccin ya gagareta, ummi ce ta fado mata a rai, dan tasan da ummi na nan da yanzu tana sallar dare, tashi tayi itama taje ta dauro alwala ta tada salla, tayi addu a sosai wanda galibin addu’ar ta ta, tana fatan Allah ya bayyana mata Ummi, dakuma fatan Allah ya shiryi Jalal, ya bata nasara akan makiyansa, a haka tasamu bacci yakuna daukanta.

   Yau Saturday yakama ranar birthday din ABDUL JALAL, shirye shiryensu suke yayinda Jalila banda aikin tunani ba abunda takeyi, Jawwad ma a wani bangaren ya damu ganin yadda Jalila kishinta ya fito karara a fuskarta, duk ya damu gashi ya kira layinta amma a kashe, gashi yana tsoron ummi dayaje da kansa gurinta. 

Ilham se shiri take kaman wadda zata biki tun safe take hada2, tana waya da kawayenta akan yadda abun ze kasance, 

Abun duniya duk ya ishi Jalila dan haka ta dau mayafinta ta fita, se azahar ta dawo, ba wanda tagayawa ina taje, tana dawowa ta hadu da Jawwad a harabar gidan, yaji dadin ganinta sedai besan mezece mata ba yana ganin har yanzu tana fushi dashi, 

“Baby daga ina haka da ranan nan?” fuskarta a sake tace masa

“Yaya na dan fitane, ai ban dade da fita ba” 

“to shikenan kidena yawo a rana, kar kanki yayi ciwo, bazan so hakan ba” murmushi Jalila tayi

“to Yaya, amma kaima ai naga a ranar zaka fita, kaima bazanso kanka yayi ciwo ba ai” 

“Baby dolene yasa zan fita ai” 

“Amma ranar da zafi fa” ta fada a shagwabe, dariya yamata “zaki fara rigima ko” tuno wayar da sukayi da hanan jiya tayi, nan da nan taji ba dadi, ranta ya baci dan haka ta wuce cikin gida ta barshi a gurin. 

Jeje yanata jadaddawa Hannah, karta bari a samu matsala akan aikin dazasu gabatar yau akan Jalal babbar dama ce suka samu, karta bari ta kubu cemusu. 

Allah ya temaki Jawwad ya lallaba Jalal ya kaishi aka rage masa sumar kansa, anyi masa gyaran fuska yayi kyau sosai, amma shi Jalal se mita yake wai Jawwad yasa an masa aski an maida shi mummuna, bayan sun dawo daga gurin askin ne suka hadu da Nana da Jalila a hanya sunje sunyo siyayya suka dakkosu, Jawwad yace “in anjima tare zamu tafine kokuma yaya?” 

Jalila tai farat tace “A a tafiyarku daban tamu daban” 

Jawwad yace “meyasa?” 

“bakomai amma bazamu tafi daku ba, ka dau abokinka ku tafi, dan bana son mita da korafi” “Wane me mitar da kuma me korafin” “nidai ban kama suna ba” dariya Nana tayi

“hmm Allah ya shirya Baby Jalila” 

“Ameen” duk abubuwan nan da takeyi karfin haline, dan ji take duk jikinta yayi sanyi, 

Bayan sallar magariba, Ilham ta shirya tsaf, ta dawo daga gurin make up, tayi kyau ba laifi abunka da farar mace ga kwala2 idanuwa inji Hanan, dogon wando tasaka baki, da 

t shirt blue wadda tazo har cinyarta, kanta ya sha kitson attach, ta dakko dan karamin bakin mayafi tasaka akanta, wrist watch dinta ma baki ne ga wani takalmi me uban tsini shima baki, se dan karamin jakarta data rataya, tayi kyau matuka, ta fito palour ta tarar da mummy, mummy tana ganinta tai murmushi

“Masha Allah, uwargidan Jalal kinyi kyau fa” murmushi Ilham tayi “Mummy har kinsa naji dadi wallahi” 

“se tafiya” “eh mummy tafiya zanyi” “to a dawo lafiya, kikula da kanki” “to mummy, ki bani key din” mummy ta mikomata key din mota tace gashi nan “ayi tuki a hankali” Ilham ta karbi key ta fita

Nana ma tayi kyau ba karamin haduwa tayi ba, dan ita high west tasaka baki da jan body hook se ta kawo mayafi tayi rolling din kanta dashi, 

Download>>> Captain Ahmad Junaid Complete Document

Har Nana ta gama shiri Jalila bata da niyyar ta shi ta shirya tayi wankanta tsaf amma ta nemi guri ta zauna, seda Nana ta fara mita sannan ta tashi, Nana tasata a gaba tayi mata light make up, kamar wadda kwai ya fashewa a ciki Jalila ta tashi ta dakko wata doguwar riga purple wadda ta sha adon duwatsu, ta taje gashinta tasaka masa ribbon, kasancewar kanta ba dan kwali, gashin gaban kanta me laushi irin na fulani ya kwanta kai dagani kasan kan akwai gashi, ta dauki mayafin rigar ta dora akanta, Nana tai murmushi “fa tubarakallahu ahsanil khalikin, wallahi Jalila kinyi kyau sekace y’ar sudan, dressing din ya miki kyau” “ke rufamin asiri, wani irin larabawa ana zaman lafiya, da an cuci larabawa” “amma kinsan fulani koba mu kai larabawa ba da kyanmu” “ji wani cika baki ina kyan anan” dariya Nana tayi “ni karasa shiryawa mutafi” Jalila ta dau Jakarta purple, se takalmi me tudu. Tayi kyau kaikace wata yar hamshakin attajiri ce. Suka jero suka fito

Maama ta kallesu, sedai hassada amma ita kanta tasan Jalila ba laifi tayi gadon dangin mahaifinta sosai a kyau, kamanta daya da babanta, mahaifiyarta ma ba baya ba wajen kyau, Nana ma ba laifi tana ds kyau amma sam bata kai Jalila ba

“har kunfito?” “eh Maama zamu tafi” Nana ta bata amsa “to Allah ya kiyaye, kar kuyi dare ku dawo da wuri” Jalila tace Insha Allah ” suna fitowa harabar gidan Driver su yake jira, suka bude mota suka shiga, suna tafe Nana tana ta musu hotuna, ana zuwa wani guri Jalila tace a tsaya zata karbi sako, ta fita ta karbo sakon tabude boot ta saka, sannan ta dawo mota tace a tafi, Nana tace” mekika karbone? “

” abune “” abu wane iri”

“kinji mace kin aikenine?” “a a ban aikeki ba jarababbiya” “eh naji jarababbiya” haka suka tafi suna fada

Suna zuwa gurin Nana ta bude mota ta fita yayinda Jalila ta kame a cikin mota taki fita

“fito mana” “yi gaba zan taho” Nana ta wuce cikin gurin. 

Abunda ya daurewa Jeje kai be wuce ganin yan uwan Jalal dake ta zuwa ba, dukda matasane amma abun ya bashi mamaki, dole sukara shiri su saka ido sosai, saboda kar a samu matsala. koda Nana ta tafi Jalila tacewa driver 

“manu dan Allah karkayi nisa akwai ajiyata a cikin motar nan anjima kadan zanzo in dauka” 

“karkiji komai Uwadakina, ina nan ina jiranku harku gama” 

Jalila ta bude motar ta fito seda ta karewa harabar gurin kallo, taga yanayin mutanen dasuke shiga suna fita, mutanen kirki dana banza, wasu daga cikin wanda tagani suna kama da mummy dan haka ta tabattar yan uwan su Jalal ne, dama Jalal sunada yan uwa haka, amma basa zuwa gidansu Jalal, gakuma yan iskan abokansa nan wanda da gani base an gayamaka ba kasan yan giya ne, kowa se hada2 yake, a hankali ta bude jakarta ta dakko katon glass baki tasa a idonta, tafara wannan tafiyarta ta me daukan hankali, hall din ya hadu yana da girma, kaikace biki ake ba birthday ba, an kawata gurin matuka guri ta samu a gefe ita ka dai ta zauna a wata kujera tana kallon kowa one by one, ta hangi table din da Ilham take ita da kawayenta su yaseera da wasu yan uwansu, se hotuna suke suna dariya, Hannah ta hango tasha kananan kaya tana up and down cikin maza ko kunya bataji, murmushi Jalila tayi a ranta tace “yakamata hanna su san juna itada Ilham” tanata kalle kallenta wani matashi yazo ya zauna a kujerar kusada Jalila, “sannu yan mata” banza tayi masa tama kara dauke kanta

“haba yazaki dauke kai haka, nazone in tayaki hira kawai kafin a fara, naga ke kadaice” juyowa tayi “to cemaka nayi na damu senayi hira da wanine” gani tayi yana dan kaama da Jalal, hakan yasa ta gane dan uwansane

“to in bakyason hirar ni inaso, muryarki da dadi gaskiya, gashi kinyimin kyau sosai” shiru takuma yi masa

Hannah ce tazo wucewa taji anata Ilham, da sauri ta dan tsaya ta juyo, amma setaga ba wadda take tunani bace, “may be sunan ne dai yazo daya” 

Jalila gani tai wannan gayen ya cika mata kunne da surutu, dan haka ta mike ta bashi guri ta tafi gurin Nana, ta ajiyewa Nana jakarta “Nana ina zuwa dan Allah” daga haka ta tafi dan nesa dasu Ilham, Hannah ce takuma dawowa taji Ilham tana “kai wai ina yaya Jalal ya tsaya haka, by now yaci ace anfara fa, Yaya Jalal kenan, zuma seda wuta” Hannah tsayawa tayi cak ta dan dawo da baya tace

“dan Allah kece Ilham, kanwar Jalal fa” Ilham ta mata kallon up and down “yeah nice, kanwarsa kuma matar daze aura” Hannah tace “anya kuwa, last time kaman ba dake muka haduba” 

“ke wai meye haka zakizo kinamin tambayoyi hakane, ke wace niban taba ganinki ba se yau, meye hakane” 

Download>>> Maraicin Nawaff Complete Document

“Hannah manyan mata, kuma me da’awar soyayya  a gurin ABDUL JALAL, gaskiyarki wannan itace Ilham ba niba” Jalila tasa hannu ta cire glass din fuskar ta, 

“yes itace Ilham nikuma Jalila” gaba daya suka tsaya suna kallon Jalila, suka ma rasa abun cewa

“dama ya dace kusan juna, Ilham ga Hannah, Hannah ga Ilham yanzu kusan juna, so u should count me out of your troubles, Ilham, Hanna, niba budurwar Jalal bace, bani da lokacin da zan bata akan soyayya da wani Jalal, dan haka idan kuna abunku to ku cire Jalila a ciki” tana gama fadin haka tai tafiyarta ta kyalesu, kallon kallo aka shigayi tsakanin Hannah da Ilham, wani shu’umin murmushi Hannah tayi, Ilham tace “ashe kece Hannah, ni na dauka zanga wata hamshakiyar mace meji da kanta, ashe ma karyar bariki ce kawai” Hannah ma tayi wata shu umar dariya sannan tace “ashe kece opponent dina ba waccan ba, thank God kece, bazam sha wahala ba, da waccan me siffar aljanunce da sena damu, dan ba karamin daukar hankali zatayi ba, amama me ban daukeki cikakkiyar mace ba ma balle in damu kaina, dan dake da namiji ba ku da banbanci” taana gama fadar haka  ta wuce tabar Ilham, 

Jalila kam tafita harabar gurin, tana waige2, tana tsaye taji ance Jeje da sauri ta waiga, tana ganinsa taga yaci sunan nasa jeje kai kace wani kasurgumin arne ne, gajeren wandone a jikinsa, da riga amless duk damtsensa a waje sekace dan dambe, gashi ya tara suma duk yamata kala, haka wani dan gemunsa shima ya samasa wannan kalar, ga katon sarka a wuyansa, lebensa baki kirin kaman gawayi, idonsa jawur, jeje ne ya tsaya suna gaisawa da wasu abokansu, muryarsa ba dadin ji, muryarsa a bude take, kai da kaji kasan kasurgumin dan shaye2 ne, ajiyar zuciya Jalila tayi tace “No wonder, wannan ko kisan kai akace yayi bazatayi musu ba” tana shirin komawa cikin hall din taga Hannah ta fito ta tafi inda yake, suka tsaya suna maganganu, Jalila bata iya jiyo me suke cewa, sun jima suna magana sannan taga Hanna ta koma cikin hall din, Jalila ma komawa tayi cikin hall din, tana zuwa taga an shirya high table cakes sun kai biyar manya2 kuma kala2, ga wasu manyan kwalabe, gurin Nana ta koma ta zauna, Nana na tayi mata mita ta cika yawo, ita dai tai mata shiru. da Jalila ta bada fuska da samarin da zatayi a gurin dayawa daga na kirkin har na kwarai, kowa se kawomata farmaki yake, ita kuma ta tsare gida, ta hade rai ba raini, suna nan zaune aka sanar da karasowar Jalal, mutumin naku ya hadu, suka shigo shida Jawwad kaman twins, sedai Jalal yafi Jawwad murdewa sosai, kuma shi Jawwad kalar ustazaine, shikuma Jalal kaman wrestler, yau anci sa’a da fara’arsa ya shigo, Jeje ji yayi kaman yai tsuntsuwa yaje ya shake Jawwad, ganinsu tare, ba karamin bata masa rai yayiba, gaba daya hall din ya dauki tafi, ana shewa cikin takunsa na kasaita yaje har kan stage din ihu aka dingayi ana masa tafi, akaita daukarsa a hotuna, MC yace to kafin Jalal ya yanka cake za a dan shakata tukuna. Nan aka shiga cashewa maza da mata ana watsin kudi a gurin. 

Jalila dai na zaune tana kallon stage din amma tunaninta baya kan me akeyi kamar an mintsineta ta waiga, tana waigawa tayi tozali da Jeje ido hudu sukayi da ita, kwata2 bashi da kyan gani a idon Jalila, se yanzu ta lura da zanen tatoo a damtsensa na hagu da kuma gefen wuyansa, harda pink dasu blue a kalolin gashin kan Jeje, wai yanzu wannan ne abokin Jalal, gaban Jeje ne yayi mummunar faduwa da yaga Jalila, kallon kallo suka shigayi, ko kyafta ido ba yayi akanta, haka nan yaji be yadda da itaba musamman dayaga kallon da take masa, amma fa yarinyar ta hadu iya wuya, komai yaji a jikinta, idanun nan nata ma kawai sun isa daukar hankali, wayarsa ce tafara ringing ya kalli wayar ya kalli Jalila ya juya ya fita, yana fita Jalila ta rufamasa baya, harabar gurin ya fita Jalila tana binsa a baya, dan nesa kadan ta tsaya daga inda yake

“Hello oga KB, ina nan nasaka ido komai ze tafi yadda ya dace, nasaka ido akan komai, kuma Hannah ma tana lure da komai, yanzu dai fatanmu yafara cin cake din nan, zakaji Labari me dadi a daren nan” Jeje na gama wayar ya juyo yayi tozali da Jalila a tsaye kyam tana kallonsa, wani murmushi yayi na rikakkun yan iskan duniya 

“Hi beb what are you looking for?” shiru tayi ta cigaba da kallonsa 

“kinada damuwa ne, can i help you? ” 

“u have nothing to help me with” jin muryarta ba karamin burgeshi tayi ba “wow muryarki da dadin sauraro” 

“Kai dakata, am not here to listen to your useless and dramatic words, am here for a porpose, waye kai meye hadinka da ABDUL JALAL kakeson cutar da rayuwarsa” 

Kallon tsaf yayi mata, sannan yafara takowa a hankali gabanta yace “Kekuma wacece? Haba beauty why trying to involve your self in this case, gaki little baby with beautiful body, baki dace da shiga rigimar manya ba da babu ruwanki” 

“na fuskanci kai karamin dan iska ne kai kake mun kallon yarinya, bari kaji ingayamaka ni bana fadar abu idan zanyi sedai kaganshi a aikace, wallahi indai da raina sena ga bayanka daga kai har wanda ya tsaya maka” hade rai Jeje yayi “da farko na dauka abun naki wasane, meyasa kikeson shiga abunda babu ruwanki, a kaf dangin Jalal ban sanki ba, meye hadinki dashi da kikeson kare rayuwarsa, kekin isa ki rusa shirin da aka dade anayi kusan shekaru goma sha biyar ke awa, kodai kina sonshi ne? Baki dace dashiba da irina kika dace musaki a harka ba karamin wuta zakiyi ba a duniyarmu ta manyan yara, da ina ganin kaman da Ilham zan tafi, amma kinfita haduwa” 

“Ni a mutum, duniyar ku ta dabbobi dai, marasa amfani, and i will show you what am capable of doing, wallahi sena rusa shirunku ko shekara dubu kukayi kunayi, Allah ya tsayamin muzuba mugani, sha3 dan asara, Allah yayi min tsari da kai, banza whalalle mara imani, ni ba son Jalal nakeba ina tausayin rayuwarsa ne da iyayensa, zanbaka mamaki, ka tsaya kagani a yau base gobe ba zan fara nuna maka, waceni useless and hopeless creature” ta juya tai tafiyarta.

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Kasa motsawa Jeje yayi daga inda yake, ji yayi kaman an daddaure shi, yama rasa me zeyi, babu alamun wasa a cikin maganganun yarinyar she has a full confidence, yana hango tsantsar bacin rai dakuma kwarin gwiwa a kwance a idonta, da sauri ya nufi cikin hall din, dan zeso yaga mezatayi

Jalila komawa hall din ta tarar Jalal na shirin yanka cake din, ga gifts da yan uwa suka dinga bashi da abokanansa, da sauri ta koma gefe ta kira Jawwad tai masa magana, sannan ta fita harabar gurin ta nufi motarsu ta bude boot din ta dakko kwali Hannah se rawar kai take ta kafa ta tsare ta janyo wani cake gaban Jalal tanaso lallai shi ze yanka yaci. Announcement sukaji MC yanayi 

“Babban yaya, kuma Man of the day, mun samu sanarwa yanzun nan, ance dan Allah ka dakata da yanka cake din nan your sisters want surprise you, zamu zuba ido muga wannan surprise din” 

mamaki ne yakama Jalal, sisters kuma wanne kenan. gaba daya hankaline ya koma kan kyakyawar budurwar da take tunkaro stage din, tana taku cike da iyayi da izza kai kace yar wani basarake ce, tana tafe Nana na binta a baya hotuna wasu suka fara yi musu, Jalila ko a jikinta ta karaso kan stage din, Jawwad ya tareta da murmushi, ya kamo hannunta yasata a tsakiyarsu, Nana kuma ta tsaya a gefen Jawwad, ture cake din gaban Jalal tayi ta aje kwalin gabanta, ta fito da wani katon cake, wanda ya sha ado da launin ja da fari, tana gama bude cake din mutanen gurin sukace “Wow” shikam Jalal mamaki ya hanashi magana kallonta kawai yake, 

Hannah tace “A a am sorry sister, gaskiya ba za ayi haka ba, wannan cake din naki ajeshi zakiyi, se yafara cin na friends dinsa, yakamata amana kara mussaman ma ni, ko Jalal” Hannah ta karasa maganar tana kallon idon JALAL cike da salon yaudara da jan hankali, Jalila tai murmushi cikin muryarta me cike da shagwaba tace

“gaskiya Yaya Jalal cake dinmu zakaci, kannenka kafin kaci na soyayya” ihu aka dauka ana ta daukansu hoto dan wasu sun zata budurwarsa ce, kodayake abun da mamaki dan sanin halin Jalal na jin kai baze barshi yai budurwa ba, shi mamakine yakama shi 

Saboda tsabar gulma yaushe Jalila tafara cemasa wani yaya, shida a bun kirki ma baya hadasu, shine hada wani kawo cake tace ya yanka, ko duk salone na ta bakantawa Ilham, Jawwad aka kira, ya sauka ya tafi amsa waya, Jalal ya kalli Jalila ga Hannah, sannan ya daga kai sukayi ido hudu da Ilham da ta kafe shi da ido, taketa hura hanci, ture cake din Jalila yayi, ya janyo wanda Hannah takeso ya ci, gurin yayi tsit ana kallonsu, ya kalli Jalila yaga yadda ta tsira masa ido, a hankali ya matso da fuskarsa daf da tata yace mata 

“ya dai, na canza mikine kikemin wannan kallon? ” banda Jalila, na kusa dashi ma basa iya jin meyace, itama a hankalin tace masa “koka canza din kasan ba birgeni zakayi ba, sedai ka birge makakku irinka, dakuma waccan mummunar kanwar taka jarababbiya, shawara zan baka,  dan Allah karkaci cake din nan” “kema ba kyan ne dake ba ai, dan Ilham tafiki kyau meyasa ba kyaso inci cake din, kinfini son rayuwata ne?” ya karasa maganar da wani murmushi na rainin hankali, itakuma tana kallonaa

Hasken camera ne keta haskasu kota ina MC yace “Wannan soyayya haka, atemaka abar manashi ya yanka cake din nan, Jalal me masoya da yawa, jin abunda MC ke cewa yasa Jalila dan ja da baya kadan, gaba daya abun duniya ya addabi Jeje, dama Jalal yanada budurwa ya akayi hakane, amma be taba gaya masa ba, anya wannan shedaniyar yarinyar zata bari komai ya tafi dai2 ga yadda tasa se bata lokaci ake, yana cikin wannan tunanin yaga Jalal ya yanka cake din dasukeso yaci, tafi gurin ya dauka, ana rera masa HAPPY BIRTHDAY TO YOU 

Ya yanko cake din har ya kai bakinsa, se yafasa, ya ga gadda Jalila ta kafeshi da ido, ya waiga ya janyo hannun Hannah ya doshi bakinta da cake din, nan da nan ta firgice, amma dayake yar duniya ce seta maze ta rike hannunsa tana murmushi, 

Jawwad ne ya dawo kan stage din ya kalli Jalal sannan yace “ya dai an yanka cake bana nan, gaskiya se an sake yankawa, kuma nasu baby za a yanka” ya janye hannun Jalal, ya dakko cake din gurin Jalila, yakama hannun Jalal suka yanka cake, 

amma Hannah ta tsargu da irin kallon da Jalal yake mata, dan har tafara tunanin kodai Jalal ya gane me suke kullawa ne. 

Ilham kam data san abunda ze faru kenan a wannan gurin da batazoba, domin ranta yayi matuka a baci, an cimata zarafi, kalli abunda Jalila tayi mata, ga abunda sukayi itada Jalal, bayan ita tunda tazo gurin kota kanta bebi ba, gakuma Hannah, yadda ya wani riko hanna ze bata cake, tsabar sun raina mata hankali, bama Jalila tafi uban kowa raina mata hankali ga yadda suke nema su hade fuska kaman zasuyi kiss itada Jalal, abunda ita be taba yi mata ba kuma tana ikrarin ita ba son Jalal take ba, dan haka a fusace  ta mike ta bar gurin, ko takan kawayennata bata biba, taje ta hau motar data zo da ita ta fizgeta da gudu, tana tuki kaman mara hankali, idan ta tuno Jalila seta ji zuciyarta kaman tayi bindiga, bata san lokacin da ta fara zubad da hawaye ba, tafara tunanin takanwa zata fara Jalila ko Hannah 

Jalal ya yanka cake din gurin Jalila yaci yabawa Jawwad a baki, aka cigaba da cashewa, Jalila tanata lura da cake din nan karsu dauka su bashi. Nana ce ta janyo hannun Jalila zuwa kasan stage din can gefe, ta kalli Jalila tace 

“Jalila kinsan wani abu kuwa?” 

“A a se kin fada” 

“Ilham fa ranta ya baci, abunda kukayi keda Jalal, ta tafi gida a fusace” 

“niba wani abu a raina game da wani Jalal, da ta kwantar da hankalinta niba abunda zanyi wannan makakken, nayine kawai saboda Jawwad, kuma da wani dalili, kinga ina zuwa” ta wuce ta bar Nana a gurin, tana dubawa taga babu Jalal a gurin, hankalinta ne ya tashi, se abokansa dasuketa rawa a gurin, dubawa ta shigayi amma bata ganshi ba, da sauri ta fita harabar gurin tana lekawa, hangoshi tayi akan wata mota acikin duhu, suna bashi giya, yana sha yana dariya, gashi Hannah ta manne a jikinshi kaman zata shige jikinsa, da gani yafara fita hayyacinsa, gefe Hannah ta koma tana waya, daga baya kuma ta bar gurin da wayar a hannunta, dan haka Jalila ma da sauri ta dauki wayarta ta kira Jawwad 

“Yaya kai sauri, kafito ka dauke Jalal, kaman akwai wani abu da ake shirin yi masa kai sauri dan Allah” tana gama wayar ta nufi gurin motarsu ga tarar da direbansu manu yanata goge2 mota, da sauri tace

“Manu dan Allah temakamin zakayi, zomuje ka gani, ba musu yabita a baya, suka tsaya dan nesa da inda Jalal yake a cikin wannan duhuwar, ta kalli manu tace” zan dauke hankalin wancan, dan Allah ka dauke ABDUL JALAL, ka kaishi gida” 

“Amma me……. 

” Manu kawi ka tafi da shi dan Allah, zan dauke hankalin wancan matashn, daka daukeshi ka tafi dashi, inkunfita waje ka kirani a waya, tana gama fadin haka ta nufi inda Jalal yake, matashin dayake gefensa yanakuma dura masa giya taje ta kalleshi

“sannu dai yaya na” 

“Yawwa yan mata ya akayine?” 

“Temakamun nakeso kayi” 

“Akan me fa?” kaga kudin motana na yar, dan Allah kozaka rage min hanya kokasa wani a abokanka ya ragemin hanya”

“haba yan mata kamanki ace an rasa me kaiki gida hakan be dace ba, bakece budurwar Jalal ba” 

“A a niba budurwars bace brother na ne, dan Allah yi sauri dare yanayi” matashin ya kalli Jalal yace “Man kajirani anan karkaje ko ina, ina zuwa yanzun nan” ya kalli Jalila “bari in kira wani a waya, yazo ya kaiki” 

“A a kaga muje kawai ka biyamin kudin motar se in tafi” 

“A a be kamata ki hau napep ba muje” har sunfara tafiya ya tsaya ya juyo

“to ni mene tukuicina” 

“karka damu, se abunda kakeso shi za a baka” ya washe baki “to shikenan muje” shiya shiga gaba tana binsa a baya

Manu yana ganin sunyi gaba yai maza yaje ya rungomo Jalal, gaba daya jikinsa ya saki dan a mugun buge yake, tangadi kawai yakeyi, ga Jalal da nauyi amma haka manu direba ya daukeshi, dan babu abunda Jalila zata sashi yakasa yimata, saboda mutuncin datake masa, ya kinkimi Jalal yasashi a mota ya kunnata ya bar gurin. 

Jalila kam suna shiga hall din, taga matashin ya doshi wani gungun yan shaye2 ta shige cikin mutane, Jawwad ya kirata amma bata dauka ba, ta koma gefe ta kirashi

“Baby kina ina, naduba ban gankiba, kuma banga Jalal dinba” 

“Yaya Jawwad ka fito kaida Nana mu tafi mu hadu a can waje, kuyi sauri” ta kashe wayar ta fita, tasamu wani guri ta tsaya can nesa da hall din, tana nan tsaye ta hango wata arniyar bakar jeep ta shiga harabar gurin, ba a fito daga motar ba, kuma ba a bude ba taga Jeje, ya fito yazo gaban motar ya tsaya, aka sauke glass din motar, wanda ta ganine ya sata zare ido, baban faruk ne da yadinga cin mutuncin Jalal ranar, saboda ya gaisa da dansa meye hadinsa da Jeje? Bata gama tunanin ba taga motar tajuya ta mike titi, shikuma jeje yabar gurin, Jawwad yazo yai parking a gabanta ta shiga da sauri, tana cewa “yaya yi sauri mubar gurin nan” da sauri yaja motar suka bar gurin

Jawwad yace “Baby nifa ban ganeba wai meye haka kikeyi ne? Nifa dole in koma gurin nan saboda Jalal, Jalila tace

” Jalal yana gida ai, manu direba ya tafi kaishi gida”

“meyasame shi? Ya akai ni ban saniba, tukuna ma naji kince wai wani abu ze sameshi” 

“da wasa nake dama sonake kazo mutafi” dagajin abunda ta fada kasan karyane, amma yai shiru ya kyaleta. Suna zuwa gida Jawwad yai parking din motarsa, ya tafi gidansu Jalal. 

Su Jalila na shiga cikin gida suka tarar su Maama ma sun kwanta, Jalila batace ma Nana komai ba itama bata cemata ba, Jalila ta shiga tai wanka, tai kwanciyarta jinta take sakayau hankali kwance, amma idan ta tuno fuskar baban faruk data gani tareda Jeje, se abun ya bata mamaki matuka, 

Jawwad na zuwa ya tarar da Jalal a kwance kaman matacce, an kwantar dashi akan gadonsa, girgiza kai Jawwad yai ya fito ya koma gida, yana son yayiwa Jalila tambayoyi amma by now yasan ta kwanta bacci. 

      Tashin hankli, tas mutumin ya dauke Jeje da mari, “baka da hankali ne, har gurin nan naje ka tabattarmin da komai ze tafi dai2, mahaukacin inane kai, kaikamin alkawarin zaka tabattar da cikar burina amma meyasa haka, na kashe kudi akan wannan shirin, an tanadi komai, a daren yau naso akaishi gurin nan da kwayoyi suke, a ajiye mugayen makamai da yan mata, muyi ikrarin yana musu fyade, sannan mu shuno hukumaa suzo su kamashi, a wulakanta shi a gaban uwarsa ta zubda hawaye fiye da yadda tasani nasa tawa uwar, kuma saboda hauka kabari damar nan ta kauce mana, in baka saniba har cin hanci na bayar cewar in ankama Jalal asashi a cikin ya’n fashi yadda, ko ubansa zeyi amfani da dukiya gurin kubutar dashi, se sun wulakanta se fiye da rabin dukiyarsa ta girgiza, sannan saboda jakanci kabari ya gudu”

“Wallahi oga KB na tsara komai, yaran naka ne basuzo da wuriba, muka nemeshi muka rasa, kuma har gadinsa nasa ayi aka bashi giya da kwayoyi a ciki wata hatsabibiyar yarinya ce ta hana shi cin cake din nan, muka samasa kwaya, amma muka neme shi muka rasa” 

“hatsabibiyar yarinya ta hanashi cin cake” oga KB ya maimaita, “wacece ita yar uban waye ita da bakuyi maganinta ba” “Wallahi oga ban santa ba nima a gurin nafara ganinta” “tasan sirrinmune?” 

“a a ba wanda yasani ko Hannah da take mana aiki bata sani ba” 

” ina bukatar ganin hotonta sannan ka ganomin yar uban waye, tashi ka bani guri maza2 tashi ka tafi bana son sake ganinka a gabana, kuma kaima zakaga abunda zanmaka, zan nuna maka sakamakon gaza cikamin alkawarina, tashi kabani guri” 

Jiki a sanyaye Jeje ya tashi ya bar gurin, abun duniya ya isheshi, bacci sam ya gagari Jeje, se tunani yake, yarasa menen mafita. 

Maganganun da Jalila tayi dazune suka dawowa Jeje, anya ba ita ta dauke shiba, kodai tasan sirrinmune, hakane ma to amma waya gayamata? to amma taya karamar yarinya kamar wannan zata iya dauke Jalal, shikam tiger wani irin banza ne haka, har yabari Jalal ya gudu, to amma mutumin dayake a buge taya yaya ze iya guduwa, to waima wacece wannan yarinyar? Anya bada tiger aka hada bakiba Jalal ya gudu?. 

Hannah ma abun yabata mamaki ya akayi, Jalal da suka bugar da kwaya ya akayi ya iya barin gurin nan, waye da wannan aikin haka, kuma taga tafiyar Jawwad shida Nana, ba bu Jalal, to ya akayi lamarin nan yazo a haka, ya akayi Jalal yabar gurin partyn nan ba wanda ya ganshi.

Ilham ma bacci ya gagareta, kwana tayi kuka da tunani, da tufka da warwara akan me zatayiwa Jalila da Hannah ta huce, nan ta kudurce wani mugun abu a zuciyarta. 

Washe gari da safe, Jawwad yakoma gurin Jalal, amma Jalal ko tashi beba yana kwance yanata fama da bacci, ya gwada tashin Jalal amma still be tashi ba yanata fama da bacci, Jawwad ya tabbatar da Jalal ba karamin buguwa yayi ba. 

Jawwad ya koma gida yakira manu direba suka gaisa sannan yace masa “manu ya akayi ka kawo Jalal gida jiya ban saniba”? 

“nima Jalila ce ta sani na dakko shi an bashi giya ya sha, wani yana gadinsa, shine tace zata dauke hankalin me gadinnasa, nikuma in dauke shi, in kaishi gida” Jawwad yai ajiyar zuciya yace “to shikenan nagode” daga nan ya tafi

Jeje ya kudurce wa ransa cewar ko da yaya se ya gano, wace ce yarinyar nan kuma seya gano ya akayi Jalal yabar gurin nan ba tareda kowa yasani ba, tabbas idan hasashensa ya tabatta itace to tasaka kanta a cikin mummunan hatsari, dan seta karbi hukuncin Jalal. 

Seda la’asar sannan Jalal ya tashi daga  baccin da yakeyi, Jawwad yasa shi a gaba da kyar yai salloli, sannan ya tafi dashi  gidansu ya  bashi abinci yaci, Jalal yace “Jawwad ya akayi muka dawo jiya”? 

“Kai zan tambaya, me yasa kasha giya jiya?” 

“ai kadan na sha bansan zan bugu haka ba” 

“kai kasani, seda namaka kashedi amma saboda taurin kai seda kasha” 

Banza Jalal yai masa yacigaba da cin Abincin sa

 Jeje ne yake ta masifa “Hannah wane irin hauka ne wannan, mun shirya komai amma kin bari komai ya tafi a banza, saboda tsabar shirme irin naki wannan wane irin haukane, kinsa oga KB yacimin mutunci jiya hada marina, wane irin sakarcine haka, meyasa ba kya abu da tunani” cikin tsawa tace

“Kai dakata, ka iya bakinka wallahi, karka sake ka zageni ka tuna da wadda kake magana Hannah ce, baka isa ka zageni akan wani banzan oganka ba, ai nayi iya abunda nace zan iya ko, to dan haka nagama nawa daga jiya, nagama yimuku aiki, tunda damar ta subuce muku, yanzu kaina zanyiwa aiki, zannemi soyayyar Jalal ta gaskiya dan duk Dunia babu namjin da yayimin sama da shi, dan haka zan tuba auren Jalal zanyi, bayan na tabattar danayi maganin wannan banzar kanwartasa, sannan in Gano wacece wannan hatsabibiyar yarinyar, dan in har da ita nasan Jalal baze aureni ba” 

A fusace yace

“Hanna kidawo hayyacinki, tawaye zakiyimin, kinsan dagani harke ba tsira zamuyi daga sharrin oga KB ba muddin asirinmu ya tonu” 

“Kai ta shafa kuma wannan, dan daga kai har ogannanka ban daukeku tsiyar komai ba, bari inkuma tuna maka dawa kake magana, Hannah ce duk hatsabibancin da kukeji dashi na fiku wallahi” 

**********************  ⬇ **************************

**********    Ai Hausa Novels  ****************

*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

 

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 08138873799

Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

**********************  ⬇ **************************

***************   Ai Hausa Novels   ****************

**********************  ⬆ **************************

Tirkashi!!!! 

Share please 

More Comments More typing………………………… 

Laifin dadi karewa anan na kawo muku karshen littafin ABDUL JALAL (2020) kashi na daya, zan dan huta na takaitaccen lokaci domin cigaba da kawo muku wannan littafi, ina godiya da yadda kuka jure bibiyata sannu a hankali a wannan littafi n farko, yanzuma ku biyoni a hankali, domin warware muku kulle kulle, da tarin tambayoyin da suke cikin wannan littafi 

Yan group din ABDUL JALAL NOVEL FANS masoya wannan littafi wanda nasani da wanda bansaniba masu turomin sakkoni da addu’oi ina alfahari daku inakumabkaunarku nima, dukda kasancewar shi littafina na farko amma kuna bibiyata kuna bani kwarin gwiwa nagode kwarai masoya na da yan uwana ina matukar godiya 

Se mun hade a littafi na biyu, taku har kullum Aisha humaira (daddy’s girl) 

Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a tuntubeni a ta what’s app akan wannan lambar

07063065680. 

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️

Back to top button