Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 14 Book 1 Complete Hausa Novel

Murmushi Jawwad yayi, “kasan ban zaci zaka zoba, na dauka dagaske bazaka zoba” 

“nima na fada ne ai dan in tsokaneka, kuma kaji haushi” 

“aikam dai naji haushin da farko amma yanzu na huce, ya me jiki?” 

Jalal ya kalli Jalila, sannan ya kalli Jawwad “Nima bansaniba, yanzu aka fito da ita” 

Jawwad yace “nayi mamaki da haryanzu bata farkaba,” 

“hakane, amma zata tashi very soon, karkayi kuka, baban soyayya” 

Murmushi Jawwad yayi tareda girgiza kai, “Jalal kafiye neman magana, nine baban soyayya ko?” 

“eh mana nagani ne zakayi kuka” 

Sukayi Murmushi gaba daya

   Maama ta sha jinin jikinta yadda Abba ya rufe ido yake ta fada, yana da matukar hakuri, rabon da taga yana fada kaman haka harta manta, duk abunda zatayi masa yana dauke kai, amma yanzu ta inda ya shiga bata nan yake fita ba, 

Duk yadda taso ya tsaya ya saurareta yaki, balle ta bashi hakuri, seda yayi mata wankin babban bargo sannan ya fice ya barmata palourn, 

Yana fitowa palour yakira Nana, yace tazo suje asibiti, ko shi seya kwana da Jalila, tunda yayi waya da Jawwad yace masa anfito da ita kuma ana sa ran zata iya tashi a kowane lokaci, Nana ta fito suka tafi a Asibiti. Sukaje suka tarar da su Jalal, suka gaisa da Abba, Abba yaje kan Jalila ya tsaya yana mata addu a, ta rame kwarai, kuma har yanzu bata farkaba, 

Abba yace “Jawwad ku koma gida, mu semu kwana anan, nida Nana” 

Jalal yace ” A a Abba, Jawwad da Nana dai su zauna kai ka koma gida, be kamata ace kai zakayi jinya ba bayan gasu” 

Jawwad yace “hakane Abba kabar Nana anan ka koma gida kawai” haka suka lallaba Abba ya koma gida, bayan tafiyar Abba Jalal ma ya mike yace ze tafi, 

Jawwad ya rakoshi waje, Jalal ya kalleshi sannan yace

“Jawwad meyasa mamanku bazatazo ta zauna da ita ba, be kamata ace Abba yazoba, har yana batun ze kwana a gurinta ba” 

Jawwad yai ajiyar zuciya “Jalal kaima ka fada, Maama bata da wani dalili na kyamar baby, tunda ta kwanta batazo ko Asibitin nan bafa ina tsoron inyi magana ne” 

“shikenan seda safenku, nina tafi” 

“to Jalal nagode, Allah ya saukeka lafiya” 

Jalal ya jinjina kai daga nan ya nufi motarsa, Jalal yana barin asibiti ya nufi club, dayaje be samu su Jeje ba dan haka shika dai ya sha giyarsa, seda dare ya raba sosai , sannan ya tafi gida, 

Maama ta kira wayar yaya mairo ta sanar da ita abunda yafaru tsakaninta da Abba, da fadan da yaitayi, tsaki yaya mairo tayi

“to ba seyayitayi ba dalla ki rabu dashi, mezakije kimata, baiwarta ce ke, ai Allah be doramiki wahalar ta ba, in yagama fushin ma ze sakko” 

“A a yaya mairo kinga kuwa yadda yaimin yau, yana ikrarin ze iya rabuwa da kowa akanta, haka kurum aurena ya mutu, gaskiya dai banda wannan shawarar, idan yasakeni ina na kama, baniba harku se mun shiga matsala” 

Download>>> Alkawarin Zuciya Complete Document

“Kuma fa hakane, amma kurarine baze iya sakinkiba, to ki dai kula karki saki jiki sosai, suma su Jawwad din kisa ido akansu, dan bana son su fiye shige mata, in kin samu lokaci ki leka ki ganta ko yan mintuna ne, shima dan ki rufe bakinsa, amma baze iya sakinki ba” 

Motsin dawowar Abba, Mama taji, dan haka tayiwa yaya mairo sallama ta tafi gurinsa, ta shiga dakinsa tana zaune Abba yaje yai wanka, yai salla yazo ya nemi guri ze kwanta, 

” Abban Jawwad gurinka nazo”

Banza yayi mata ya nemi guri, ya kwanta, 

“Dan Allah Abban Jawwad kayi hakuri” 

“kinga tashi kibani guri bani da lokacin jin maganganunki, indai zaki guji Jalila nikika guda tunda jinin dan uwana ce, ki kyaleni” 

“Dan Allah…. 

” Zainab fita kibani guri, koni in fita in baki guri”

Haka Maama ta fita ta bar dakin, lallai yayi fushi, abune mawuyaci kaga fushinsa, bashi da hayaniya sam amma wannan karon ransa ya gama baci. 

   Dare yayi Nana ta samu guri ta kwanta, Jawwad kuma ya zauna akan kujerar dakin a haka bacci ya daukesu, cikin dare Jalila tafara motsawa tana atishawa, da sauri Jawwad ya tashi yana kiran sunan ta, tana gama atishawar tacigaba da baccinta, ba tareda ta tashiba, tunda ga wannan farkawar da tayi, Jawwad be kuma komawa bacci ba har gari ya waye, 

Da safe Abba ya shirya ba tareda ya kula Maama ba, a palour ya tarar da halima da hijjabinta, ta gaishe da Abba ya amsa, tace

“dan Allah sonake in bika inga jikin Jalila, tunda aka kaita Asibiti ban dubata ba” 

Ta karashe maganar kaman zatayi kuka, Abba yace ta taho su tafi, da sauri Halima taje kitchen ta dakko, kayan tea data dafa ta bi Abba, Abba a ransa yace “Baby ko bayan raina, nasan bazata rasa mutanen kirki dazasu kula da itaba, kodan saboda kyawawan halayenta, Halima me aiki duk ta damu, hada dawainiya haka, amma matarsa dayake tareda ita yake kyautata mata da danginta amma takasa yimasa alfarma akan yar dan uwansa saboda wani dalilinta mara tushe”

Haka Halima ta  shiga bayan motar suka tafi Asibiti, koda suka isa Asibitin, Halima taga Jalila da yadda ta rame seta fashe da kuka, Abba yace tayi shiru ta dinga yimata addu a, bayan Abba ya duba Jalila ya tafi gurin aikinsa, 

Hawaye halima ta cigaba da sharewa, 

Jawwad yace “Halima kidena kuka cikin dare tayi atishawa akwai yuwuwar, ta farka a kowane lokaci, daga yanzu, kidena kuka, kimata addu a” gyada kai Halima tayi sannan 

Jawwad yace tunda ga Halima tazo, bari ya kai Nana gida tayi wanka taci Abinci, Nana ta tashi suka  tafi, aka bar Halima a gurin Jalila, 

halima ta mike ta koma kujerar gaban gadon Jalila, ta kifa kanta a gefen Jalila tana share hawaye, 

“Allah yabaki lafiya, Jalila, Allah ya dubi maraicinki, ya baki lafiya” 

Doctor salis da kansa ya shigo yayiwa Jalila allurai, ya samata wani ruwan, yauma tsayawa yayi yana karewa Jalila kallo, Halima ta dan kalleshi, 

“Likita wai yaushe zata farkane? kwananta biyu a haka fa” doctor salis ya kalli Halima, “karki damu muna sa ran zata tashi ba dadewa,” 

Halima tace “Allah yasa” 

Daga haka doctor ya fita, 

Yayi awa daya da tafiyar su Jawwad, Halima taji an turo kofar dakin, dan dago kai tayi ta waiwayo, da mamakinta taga Jalal ne, seda gabanta ya dan fadi, dan batayi zaton ganinsa ba, ran nan nasa a hade ba fara a, babu alamarta, mikewa halima tayi daga kan kujerar da take, ta koma gefe

Ta dan risina sannan tace “Ina kwana”  be amsaba yace mata 

“Ina Jawwad?” 

“dazu suka koma gida, amma zasu dawo” 

Gyada kai yayi ya jawo wata kujerar ya zauna ya harde kafa, yana karkadawa sekace wani basarake, ya zaro sigarinsa ya kunna, Halima ji tayi duk ta tsargu, ga mara lafiya a kwance amma taba yake sha, ji tayi duk ta takura, dan haka ta mike ta fita ta bar dakin, 

Yana nan zaune yana shan tabarsa, yaga kafar Jalila tana motsawa, a hankali ta fara motsawa, tana kokarin bude idonta, a hankali ta cigaba da motsawa, ta bude idonta, dishi2 take gani kafin daga baya kuma ta bude idonta fes akan Jalal zaune kan kujera da taba a hannunsa, kallon dakin dake ciki tayi, tana kokarin gane mafarki takeyi kokuma a gaske ne, yunkurawa tayi zata tashi zaune amma taji cikinta ya kulle, ta kasa tashi, Jalal yana kallon ta amma be cemata uffan ba, 

Yunkurawa tayi zata kuma tashi zaune, ga drip da yake shiga jikinta, tana nema tasa ya goce, Jalal ya kalleta, 

“Malama kikoma ki kwanta, idan ruwan ya goce kuma fa, wayace ki tashi zaune daga farkawarki,” ya fada a dan tsawace se yanzu Jalila ta tabbatar da ba mafarki take ba, tashi yayi yaje ya zare ruwan da ke shiga jikinta, 

Yai waje, office din doctor salis yaje ya gaya masa Jalila ta tashi, da sauri salis ya Mike yana fadi” Alhamdilillah, gani nan zuwa ” Jalal yakoma ya tarar Jalila ta lumshe ido, tanajin motsin Jalal ta dan bude ido tana kallonsa, ko ta kanta be kuma biba yasamu guri ya zauna, doctor salis ya shigo, yai sallama, ya kalli Jalila, ya kira sunanta a hankali ta bude ido ta kalleshi, 

” sannu ya jikin naki” gyada masa kai kawai tayi, doctor salis yace

“Yanzu me yake miki ciwo” cikin muryar marasa lafiya, tareda shagwaba tace “Ni sonake in tashi in zauna, cikina kuma ciwo yakemin, nagaji da kwanciya amma nakasa tashi” ba karamin jin dadin muryarta doctor salis yaiba

“Ok zaki iya tashi zaunen”? 

“A a nakasa tashin” 

“Ok let me help you, sit up” ya kai hannu yana kokarin tabata, da sauri tace “A a nika kyaleni zan tashi da kaina” 

“Bazaki iya tashiba, ki bari in temakamiki” 

Yamutsa fuska tayi, “Nace maka ka kyaleni” 

Jalal dake gefe yace “to ka kyaleta mana dolene, tunda tace bata so, base tayi ta kwanciyar ba,” 

Kallon Jalal tayi ta dauke kai, salis yana jin tsoron Jalal, saboda yanada matukar kwarjini, dan haka yabar maganar temakamata ta tashi zaune, yace, “in Jawwad yazo, akwai magani daze siyo abata, amma a tabbatar taci abinci, dan zata bukaci abinci, asamu abu me dan ruwa2 abata ta sha,” 

Jalal bece komai ba, doctor yai waje, Jalila trying ta kumayi ta tashi amma gefen cikinta a kulle, taji kamar an soka mata wani abu a cikinta zuwa zuciyarta, a hankali ta danyi kara, ta koma ta kwanta, kukanta ne ya karu yanzu hada sauti, da sheshsheka, takeyi, Jalal ya kalleta yai tsaki

“Malama kimin shiru kincikamin kunne,” 

Banza tayi masa ta cigaba da kukanta

“Ni wallahi nagaji da wannan kwanciyar bayana ciwo yakemin” 

Shiru Jalal yai mata, yacigaba da danna wayarsa, ita mamaki ma takeyi, me take a asibiti ita da Jalal ina yan gidansu, tanaga dai mafarki takeyi, kukanta tacigaba hawayene na bin gefen idonta,

tashi Jalal  yayi ze fita, har yaje bakin kofa, ya dawo ya kalli Jalila yasa hannu ya dago Jalila daga kwanciyar da take, ya jinginar da ita, ji tayi gefen cikinta ya kara kullewa, saboda ba a hankali ya dagata ba

Ihu tayi ta rike hannunsa da karfi tana fadin

“Wayyo Allah cikina, ni cewa nayi ka dagani, saboda mugunta, bakasan me nakejiba, zaka dagoni a haka wayace ka tabani” ta fada tana hawaye, dan tsuramata ido yayi, ita dai bazata canzaba da kyar take magana, kai dakaji muryarta kasan tanajin jiki, amma bazatayi shiruba 

“yimin shiru ko in maidake inda kika taso” dauke kanta tayi, kamshin turaren Jalal da warin sigarin dayakene Yasa Jalila taji tana yinkurin amai, dama gashi kwanakin nan cikinta ba komai, shi ya haddasa mata kullewar cikin, 

Daga haka Jalal yai waje ya barta, Halima tana reception taga wucewar Jalal dan haka ta mike ta nufi dakin da Jalila take, tana zuwa ta tarar da Jalila a zaune, zare ido Halima tayi, ganin Jalila a zaune “Jalila kin tashi sannu” 

Karanta Littafin>>> YEL Hausa Novel Document

Murmushi Jalila tayi, kafin tayi magana, Jawwad yai sallama, shima da mamaki yaga Jalila a zaune, da sauri ya karasa gaban gadon “Baby kin tashi sannu, ya jikin” 

“Da sauki yaya Jawwad, ina kuka tafi kuka barni, anan ni kadai, waima me nakeyi anan” 

“Bakida lafiya ne muka kawoki nan, yanzu me ke damunki” 

“Cikina ne yakemin ciwo, da kirjina,” 

“Ok Sannu bari inkira salis” 

Halima tace “likitan yazo dazu yace abata abume ruwa2 ya mata allurai” 

“Ok temakamata tayi brush, ina zuwa” 

Jawwad na fita Jalila tace “Halima wai meyasameni ne, aka kawoni Asibiti” 

“Bakida lafiyane kawai” 

Halima ta dakko toothpaste da brush amma Jalila takasa sakkowa daga kan gadon, dan data motsa ko ina ciwo yake mata, bama ya cikinta, 

Haka ta hakura, ta zauna akan gadon tayi brush tai alwala, ta kalli Halima

“Halima yaushe aka kawoni nakasa tuna komai, bansan sallan me zanyiba yanzu” 

Dan shiru Halima tayi, dan bata san mezatace mata ba, 

Jawwad ya shigo da leda a hannunsa, “sannu halima tayi brush dinne?” 

“Eh tayi,” 

Tea yasa halima ta hada, yazo gaban gadon Jalila ya zauna, yace “Baby karbi kisha se kisha magani” 

Ta kalleshi “Yaya Jawwad salla zanyi, amma meyasameni aka kawoni asibiti” 

“kinga kiyi hakuri, fara sha tukuna zamuyi magana” 

Karba tayi ta dan sha kadan, yana shiga cikinta, taji ya murda ajiyewa tayi, idonta ya ciko da hawaye, zeyi magana wayarsa tafara ringing, 

Yana dakko wayar yaga Abdallah ne yake kiransa

Dagawa yai yasaka a kunnensa tareda yin sallama, suka gaisa da Abdallah, 

“Aliyu meyasamu wayan Jalilane? Hanan ta kirata tagaji bata shiga” 

“Eyya batada lafiyane, kwananta biyu tana asibiti” 

“Subhanallah me yasameta haka?” seda Jawwad ya kalli Jalila sannan yace

“ba ta jin dadine, amma taji sauki Alhamdilillah” 

“Allah sarki, amata sannu dan Allah, zan gaya ma Hanan din insha Allah” 

“to shikenan a gaida mutanen gidan” 

Jawwad ya maida hankalinsa kan Jalila, hawaye ya gani shabe2 a fuskarta

“meya farune, Dan Allah baby kisha kinji” 

“Yaya Jawwad ni na koshi, cikina ciwo yakemin” 

Ana haka Jalal ya dawo, “Jawwad kana nan”. “eh Jalal nakoma gida na maida Nana ne, sannu da zuwa dan uwa” 

“Yawwa yanemi guri ya zauna” 

Jawwad ya maida hankalinsa kan Jalila, suka cigaba da fafatawa da Jalila taki cin Abincin, Jawwad se wani lallabata yake tana wani shagwaba, taki cin Abincin balle ta sha maganin, Jalal ransa yabaci ya dan kalli Jawwad

“Namanta ban gaya maka ba, dazu kafin inshigo doctor Salis yace kaje, yana son ganinka”

“Ok bari ta ci Abincin se inje” 

“No kaje kaji kowani abunne mana” 

Jawwad ya mike ” to Bari inje,” ya juya ya kalli Jalila”baby dan Allah kisha tea din nan kinji, yanzu zan dawo” Jawwad ya juya ya fita, yana fita ya rage daga Jalila, Halima se Jalal, 

Jalal ya kalli halima yace “hada wani tea din a katon cup” ba musu Halima ta hada, yasa hannu ya dauka ya mike ya nufo gadon Jalila, yana zuwa ya dire cup din a gefenta, ya hade rai

“dauki ki shanye” 

Zunbura baki tayi “nina koshi, tayaya zan iya shan wannan uban shayin” tsawa ya dakamata “Ki dauka nace, se wani shirme kikeyi shikuma yana biye miki, inkin ki sha, wa kikayiwa inba kankiba, ki dauka ki shanye nace, kokuma wallahi in danneki se kinsha katon cup din nan biyu, danni ba Jawwad bane” 

Kallon cup din tayi, ta kalleshi yanayin fuskarsa ya tabbatar mata he mean what he said, fuskarsa babu alamar annuri, Halima kam tana gefe tana kallon ikon Allah, hannunta na rawa ta dau cup din, tana fara sha seda taji kaman ana kuma nannade mata hanji, yamutsa fuska tayi, tana dan sha a hankali, shikuma ya kakkafeta da jajayen idanunsa duk ya takurata, dire kofin tayi “ni gaskiya na koshi” 

Bece mata komai ba, ya cigaba da kallonta, itama kallonsa tayi, “to waini bana koshi ba” wani mugun kallo yacigaba dayi mata, ba shiri takuma daukan kofin tana sha tana haawaye ga wani amai dayake tasomata, 

“Wallahi kikayimin amai sekinsha cup uku” 

Da kyar da nishi Jalila ta shanye tea din nan tana zare ido tana kuka, seda ta shanye shi tas, sannan ya koma inda ya tashi ya zauna, 

Jawwad ya dawo da magani a hannunsa, ya duba cup din tea yaga ba komai a ciki yace “Yawwa baby ashe kinsha saura magani kuma” shima maganin da kyar tasha, taji dadin jikinta sosai, har tasamu tafara rama sallolin da suke kanta

Jawwad ya kira Abba yagaya masa Jalila ta tashi, Abba yayi murna yace Insha Allah yana dawowa zezo ya dubata, 

anci sa a Maama tazo ta dubata, bisa shawarar yaya mairo, amma ta tsorata dataga Jalila dan ba karamar rama tayi ba,

Jalila tace “Maama ina Nana” 

“anan ta kwana, shiyasa yanzu nahanata zuwa, gara ta zauna ta huta” daga nan Jalila bata kuma cewa uffan ba, Mama batafi minti goma da zuwaba ta tafi abunta,

Bayan tafiyar Mama, Jalila ta kalli Halima tace “Halima wai kwana na nawa a asibitin nan ne? Ni dai nasan lafiya ta kalau” 

“Kwananki biyu cif” 

“Kwana biyu kuma”? 

Jalila tayi shiru tana tunani kaman an tsinkuleta ta fashe da kuka ta kalli Jawwd

 “Yaya Jawwad ina Ummi ba a ganta ba ko? Wai dama duk abun nan ba mafarki nakeba, Jawwad ina Ummi, ta mutu ko?” 

Jawwad yace “A a Baby Ummi bata mutu ba har yanzu ana nemanta” 

“Yaya Jawwad kacemin ta mutu kawai, shikenan nikam ita kadai taragemin dama, nasan ta mutu, haba Ummi, meyasa kika tafi kika barni, dan Allah Ummi ki dawo” 

“Ke dalla kiyi mana shiru, daga farkawarki kina ma mutane kururuwa a asibiti, wayace miki mutuwa tayi,? Zaki dinga yimana ihu, kowa ba gatansa Allah ba” 

“Ba ruwanka dani nayi kukan, ko dan kai bakasan darajar uwaba kake gani kowama haka ne agurinsa, dole inyi kuka, bansan halin da uwata ke cikiba, dakasan soyayyar da da uwa dabakamin tsawa ba, ita kadaice dani, ba uwa ba uba ba dangin uwa, ” tana maganar tana hawaye numfashinta na fita da sauri

Jalal zuba mata ido yayi, wani abu na sukarsa a zuciyarsa, tabbas besan soyayyar tsakanin da da uwaba, 

” Jalila meye haka, sa ankine shi, kike gaya masa haka”

Jawwad ya dakawa Jalila tsawa abunda be tabayiba.

Mamakine yakama Jalila jin yadda Jawwad ya mata tsawa, abunda betaba yi mataba,

“Jalila meyasa kike haka, na sha gayamiki Jalal ma kamanni yake agurinki yayanki ne shima”

Dauke kanta Jalila tayi, ta cigaba da zubar da hawaye, Jalal juyawa yayi ya fita yabar dakin, Jawwad ya bi bayansa

“Jalal dan Allah kayi hakuri, rashin fahimta ne tsakaninka da Jalila amma bazata karaba, yanzuma tana cikin damuwane shiyasa”

Murmushi Jalal yayi “Never mind dan uwana, nima ba fushi nayi ba, Allah yakara sauki” daga haka ya nufi motarsa ya shige, sam Jawwad beji dadin abunda Jalilan tayiba bata kyauta ba, be kamata ace tagayawa Jalal wannan maganar ba dukda basa jituwa, yasan ba danshiba babu wanda ya isa yagaya masa wannan maganar ya kyale, 

Ya juya ya koma cikin Asibiti, yaje ya tarar da Still Jalila tana kuka, tana surutai akan Ummi, Halima nata bata hakuri, bebi takanta ba, ya kwashi wayoyinsa ya kwasa ya fice daga dakin. 

Ana idar da sallar magariba Abba yazo, yaji dadin ganin Jalila, ta farfado ta fara samun sauki, sedai tarame sosai, ta danyi duhu, shima Abban haka ta dinga masa kuka, tana surutai, ita ummi, 

Abba ya shiga yi mata nasiha me ratsa jiki

“Jalila ki karbi kaddararki a duk yadda tazo miki, nima inata kokarin inga munsamu inda take amma abun ya gagara, inkika mika al amuranki ga Allah komai zezo da sauki, jikina yana bani har yanzu tana raye, kuma zata dawo, karki cutar da kanki da wannan kukan da kikeyi, “

Abba ya kalleta sannan ya kira sunanta” Jalila”

“Na am Abba” 

Download>>> Cousin Ne Complete Romantic Novel Document

Ya cigaba da cewa “nidin nan ma misaline a gurinki, ba uwa ba uba, ba danuwana, gashi bamu da wasu dangi nakusa kona nesa, nasan bazaki rasa sanin tarihinmu ba nida mahifinki a gurin umminkiba, mu biyune kawai a gurin iyayenmu, kuma suma ba yan garin nan bane, gudun hijira sukayo, a yanzu haka bani da kowa, daga Allah seku ya’yana, ku nake kallo inji dadi, lokacin da nake kan ganiyar bukatar kulawar dangina, Allah ya karbesu gaba daya, amma hakan be hanani rayuwa ba, dukda har yanzu inata fafutuka ko Allah zesa insamu wani daga cikin danginmu, 

Dan haka ki kwantar da hankalinki, kinada Allah kuma ni mahaifine a gurinki, duk rintsi duk wuya, babu abunda zesa in juya miki baya, ko Ummi na nan kobata nan, ina kaunarki yata ce ke jinin dan uwana, kicigaba da addu’a ki kwantar da hankalinki, kinji yarinyar kirki, zuciyata na shiga kunci idan naga hawayen marainiyar nan kuma amanar Aliyu, bana son zubar hawayenki, kiyi hakuri duk lokacin da kike kuka ji nake kaman naci amanane, “

Sosai nasihar Abba ta ratsa zuciyar Jalila, wanda yasa jikinta yin sanyi matuka ga kuma tausayinsa daya kamata

“insha Allah, Abba zan cigaba da addu’a in tana raye Allah yasa tana hannu nagari, inta rasu kuma Allah ya………. Kawai seta fashe da kuka

Sosai tausayinta ya kama Abba, Halima dake gefe ma kuka take, Jawwad ma ji yayi kaman ya tayata

Abba yace” tana rayema Insha Allah, kuma zamu gano inda take “

Gyada masa kai tayi, Jawwad yace

“Abba Maama tazo dazu ta dubata” 

“yayi kyau” shine kawai abunda Abba ya fada, ya tashi ya tafi, bayan tafiyar Abba, Jawwad ma barin dakin yayi, yaje office din doctor Salis, bayan sun gaisa, Jawwad yake tambayarsa yaushe ze sallami Jalila 

“se ta dan kara hutawa, nan da ko kwana biyune, tana bukatar kulawa, saboda abunda ze iya biyo baya, amma nan da kwana biyu ze sallameta Insha Allah” daga haka sukayi sallama ya fito, Jawwad koda ya fito bekoma gurin Jalila ba ya tafi gida, seda akayi sallar isha’i sannan ya dauki Nana ya kaita Asibiti, daya kaita ma a gate ya tsaya ta sauka ya juya, Nana tayi murna ganin Jikin Jalila da sauki, hira Nana take tayi mata amma tayi shiru, zuciyarta duk babu dadi, dakewa kawai takeyi, 

“Nana ina yaya Jawwad”? 

“Ai yana ajiyeni ya juya, inaga ko wani gurin zashi” Jalila ta dan jinjina kai, 

    

Jalal kwance a dakinsa ya kurawa ceiling ido, dagani yayi zurfi sosai cikin tunani, dan lumshe ido yayi, tareda yin Ajiyar zuciya, kirjinsa yamasa nauyi matuka, ya mike zaune ya dafe kansa da hannunsa biyu, sallama tayi a palournsa, yai shiru be amsa ba, ta karaso da tray a hannunta ta nemi guri ta zauna a kusa da shi, hannunta biyu ta saka ta cire masa tagumin

“Yaya Jalal meyake damunka tagumi fa babu kyau” dan kurawa Ilham ido yayi ya dauke kansa

“Yaya kayimin magana mana, naganka wani iri” 

“Me kikazo yimin nan?” 

“Fruit na kawo maka, kuma naga kwana biyu baka zama a gida, kwana uku banganka ba, duk na damu, ko cikin gida baka lekamu” 

“Inkingama ki tashi kibani guri” 

“Haba yaya Jalal, in damu da kai har inzo inda kake amma ka koreni, please yaya Jalal kabani dama mana a rayuwa, wallahi I love you Yayana, please marry me, in ba kaiba rayuwata tana cikin hatsari ina bukatar kulawarka, bazan iya auren wani ba kaiba” 

“Idan kika bari na kuma yi miki maganar ki barmun dakina, sena miki abunda baki taba zatoba, sha3 mahaukaciya kawai” daga haka ya tashi yabar palourn ya shige bedroom dinsa, 

Mutuwar zaune tayi, gaba daya notin kanta ya kwance tarasa mezatayi, ita namiji yake wulakantawa haka, dole tanemi mafita, Jalal yafara kaita bango matuka, tana cikin nazarinne wayar Jalal daya bari a hannun kujera tafara ringing, amma setaga lambace ba suna, hannu ta kai ta daga wayar tasaka a kunnenta, da dagawarta taji muryar mace tafara magana

“Haba my Jalal, kwana na uku ban ganka ba, ban saka a idona ba duk na damu, gashi baka daga wayata ina ka shigane, I want surprise you” 

Ran Ilham ne ya baci, dan haka cikin masifa tace “Ke dalla Malama dakata mahaukaciya, dabbar inace ke, to Wallahi bari kiji in gaya miki, ko ke kika kaso maita duniya bakisa ki auri Jalal ba, Jalal nawane ni kadai, inbiki kiyayeni ba wallahi se kinyi danasanin zuwanki duniya, gara tun wuri kisan inda dare yai miki, Jalal bashi da wata mata in ba niba, munafukar banza data wofi, maci amana”

Hannah tace 

“Ke saurara Me kike da suna, karki kuskura kice zaki zageni, bani da lokacin ki, haduwarmu ta farko kin gayamin magana son ranki, na kyaleki, bani da lokacinki, kuma idan ina raye Wallahi karya kike kema ki auri Jalal muzuba nidake, dan halak ka fasa, sokuwa kawai” 

Jin hargowar Ilham ne yasa JALAL fitowa daga bedroom dinsa, yana zuwa ya tarar da Ilham rike da wayarsa tanata bala’i da surutai, karasawa inda take yayi, yasa hannu ya karbe wayarsa, ya juya ya nufi dakinsa, mikewa Ilham tayi tabi bayan Jalal tana masifa, a kunnensa ya kara wayar

“Ya akayi?” 

“haba Jalal, meyasa kanwarka mahaukaciya ce, toka gayamata idan a wancan lokacin mun hadu ta zageni na kyaleta ta kiyayeni(a zatonta Jalila ce Ilham) , kasan halina zan mata rashin mutunci, kuma ka gaggauta gaya mata, nida ita shege kafasa” 

“meyasa ke baki gaya mata ba”? 

“Hakama zaka ce? Shikenan Jalal, ina ta wahala akanka, amma wata tana cimin mutunci ko, shikenan zatasan wata zaga wallahi, kasani duk me shirin kawomin matsala tsakanina da kai, sena gwada masa ni a mata ta dabance” 

“Look Hannah bana son shirme kaina kemin ciwo, kuje kuyi tayi, tunda daga ke har ita baku da hankali, banzaye kawai” 

Hannah kuma Ilham ta faada a hankali ba Jalila ba, wace kuma hannah, inma rainamin hankali suke, zasuga tsiya, yana gama wayar ya ajiyeta, wannan jarababbun sun kara hargitsa masa lissafi ransa a matukar bace yake, ya balle rigarsa ya aje kan gado ya juyo, yaga still Ilham tana tsaye, tana huci

“Meye haka ina cire kaya kinzo kin sani gaba, malama ki wuce ki bani guri, bana son shirme ds hauka”

“Wallahi Yaya Jalal, bazaka tabbatar da nayi hauka ba se ranar dana fara yimaka haukan, ni kake cewa mahaukaciya ko?……. 

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Tinkarota yayi gadan2 ta juya da gudu ta fice, dan data bari ya karaso ta san sauran, amma shi a gurinsa yayine dan ya tsorata ta, saboda tun ranar da Jalila tace masa ragon namiji shike dukan mata, be kara dukan Ilham ba, sedai yayi mata tsawa, shiyasa tasamu damar kara yi masa shishshigi, tana juyawa ta tafi, ya dawo ya zauna yai shiru, sun kara dagula masa lissafi, ga maganganun Jalila sun tsaya masa a rai, daga baya yaga bashi da mafita, ya tashi ya dakko mutuniyar tasa, yaiwa kansa caji ya kwanta anan, yafara bacci. 

Jalila ta fuskanci Jawwad fushi yake, a lokacin itama taga rashin dacewar abunda tayi amma ba yadda zatayi, itama bata san tayiba, tana cikin dimuwane, shikuma yasata gaba da jaraba, tana wannan tunanin bacci yai awon gaba da ita

Yana kwance akan cinyarta, tana shafa sumarsa, tafara magana cikin sigar rarrashi, da daddadar muryarta me cike da iyayi da shagwaba

“AbdulJalal dina, kadena shan giya kaji, banason abunda kakeyi, bana son ganinka a irin wannan yanayin raina bayamin dadi, sonake kazama mutumin kirki kaman kowa, mutane sudena kyamarka,” 

Murmushi yayi, 

“To Babyna, nima bana son abunda nakeyi, zuciyata bataso bansan meyasa nakasa denawa ba, amma ki dinga yimin addu’a zan dena, amma nima kidena yimin wulakanci a gaban mutane banaso” 

“Kullum ina yimaka, addu a, idan naga kana rashin kyautawa, gaba daya rainane yake baci, shiyasa nakema ka haka, amma nima na dena, amma promise me kaima zaka dena” 

Murmushi ya kumayi “Allah yayi miki albarka My queen u mean a lot to me, Insha Allah ze wuce kaman banyiba, yayinda mutane ke guduna da kyamar halayena, lokacin kuke kaunata ke da yayanki, can’t forget your sacrifice “same to me, u mean a lot to me, ABDUL JALAL, fuskarta ta sunkuyo zata sumbaci goshinsa, “

“Jalal ka tashi rana tayi haske fa, nasan ko salla bakayiba, se wani Murmushi kake a cikin bacci, wai me kake ganine a baccin”? 

Se yanzu Jalal ya gane mafarki yakeyi, Kallon Jawwad, Jalal yayi yayi tsaki

Jawwad yace “Ya dai?” 

Ajiyar zuciya Jalal yayi “Bakomai” 

“Bakomai kake ta murmushi a bacci haka, gayamin mafarkin me kake?” 

“Kaga ni ka rabu dani” 

“Anyway kaje kayi salla, takwas da rabi fa” Jalal bekuma cewa komai ba ya mike yaje yai wanka, yai alwala yai salla

Ilham ta boye damuwarta tayi breakfast, bayan tagama breakfast ta mike ta nufi gidansu Nana, bakowa a palourn gidan, dan haka ta wuce dakinsu Nana, taje ta tarar da Nana tana wanka, amma bataga Jalila ba, neman guri tayi ta zauna, ta jira Nana ta fito, Nana ta kalleta

“Lafiya kuwa da safiyan nan? Naga kwana biyu ma bana ganinki, ko kun jone da Yaya Jalal ne no more matsala, shiyasa kika yadani” 

“Nana ba wannan ba ina yar uwarki?” 

“aini dama a kule nake dake Ilham, kwanan Jalila uku a Asibiti se jiya ta farfado, amma kokice tana ina, ta sha jiki kaman zata mutu” Ilham a ranta tace ” A a tana asibiti to wace ce mukayi waya jiya,? cikin ko in kula Ilham tace

“Niban saniba, bansan bata da lafiya ba, Allah ya sawwake” 

“Ah haba zakicemin baki saniba, bayan yaya Jalal ya jejje Asibiti dubata”

Ji Ilham tayi kaman Nana ta soka mata kibiya, “yaje dubata fa kikace” 

“wallahi kuwa, kullum se yaje, nima yabani mamaki, amma kinsan kobeje dan kowaba yaje dan Yaya Jawwad” 

Jinjina kai Ilham tayi, ta Mike “na tafi se anjima” 

“daga zuwanki zaki tafi” 

“eh naga kaman fita zakiyi” 

“A a ba inda zani Asibiti ne se anjima zani” 

Bata kuma bi takan, Nana ba, Daga haka tai waje, zuciyarta fal takaici, wai kullum se yaje asibiti tunda aka kwantar da ita, “ko uban me yake zuwa yi, ta tabbatar ko uwarsa a aka kwantar baze je dubata kullum ba, tokuma wace ta kirashi, jiya? Karfa inje ina can ina hauka, aikin gama ya gama ina gefe, kai da sake wallahi, dole in tada balli” daga nan tai gida kaman mahukaciya. 

Bayan su Jalal sun gama breakfast, Jawwad ya tafi asibiti be takurawa Jalal seyaje ba dan ko shine baze komaba sabida abunda baby tayi masa. 

Doctor salis ya shigo yai mata allura ta cannula, bayan yagama ne ya kalleta

“Baby ya jikin” banza tayi masa

“ya kikayi shiru?” 

“nace maka ba sunana Baby ba” 

“Amma yayanki yake gaya miki” 

“to ba Yayana kace ba, ko kai yaya nane? ” 

“am sorry, Jalila ya jiki” 

“da sauki Alhamdilillah” 

“Masha Allah, Allah yakara miki lafiya, jinake ciwon nan kaman ya dawo jikina, duk na damu wallahi” 

Dan ya mutsa fuska tayi

“dan Allah ni ka sallameni yau” 

“Amma meyasa?” 

“To zaman me nake bayan na warke, ni kawai ka sallameni nagaji da zaman asibitin nan, gara in  koma gida” 

“Dan Allah kiyi hakuri nasan in kika tafi ba lallai inkuma ganinki ba” 

“wani mugun kallo Jalila tayi masa, to in zauna in maka mene? Ni gaskiya nagaji gida nakeson komawa, kobaka sallameniba sena tafi, ko in Abba yazo in gaya masa mekace” 

“A a yi hakuri, zan sallameki yau Insha Allah tunda kin warware” 

“da dai yafi maka” 

Download>>> Kadangaruwa Complete Document

A ransa yace lallai haka wannan yarinyar take da tsiwa, lallai Jalal yayi gaskiya, amma shidai a hakan yana sonta don komai nata yana birgeshi, ana haka Jawwad yazo suka gaisa da doctor salis, ya gayawa Jawwad yau ze sallami Jalila, tace ita tagaji da zaman Asibitin, Jawwad yai murna sosai yace “indai ba wani matsala ai gara a sallamemu,” 

Bayan fitar doctor Salis, Jawwad ya nemi guri zauna, ko kula Jalila beyiba, 

“Yaya Jawwad, ina kwana?” 

“lafiya kalau” shine abunda Jawwad yace, 

Daga nan bekuma cewa komai ba, wayarsa ce ta fara ringing ya dakko ya daga

“Salamu alaikum” 

“Wa alaikum salam, My Jawwad barka da safiya,” 

Muryar ya dauka, ya gane me maganar, dan haka yayi murmushi

“Hanan kin tashi lafiya” seda Jalila ta waigo ta kalleshi

“Lafiya kalau, yame Jiki, Abdallah yacemin batada lafiya, da sauki jikin nata? Ko kuwa? ” 

“Kwantar da hankalinki, Hanan taji sauki, muna sa ran Insha Allah yau za a sallameta” 

“Me yasameta ne”? 

“Ta samu stroke ne, amma yanzu ta farfado tana lafiya” 

“Allah sarki na kira wayarta ne bata shiga, itakam baby me yayi zafi haka, har tasamu stroke? in kana kusa da ita bani muyi magana” 

Wayar a hansfree take Jalila tana jin komai

Ya kalli Jalila sannan yace

“Bacci take in ta tashi zan gaya mata” 

“to shikenan” 

“kayi saving lambata, mu dingayin waya” 

“to shikenan, karki damu” sukayi sallama da Hanan

Ya mike ze fita Jalila ta kira sunansa, tsayawa yai ya waigo yana kallonta

Idonta taf hawaye “Yaya Jawwad fushi kake dani ko? Dan Allah kayi hakuri, bazan, kuma ba” takarasa maganan hawaye na gangarowa daga idonta, ita dai zubda hawaye baya mata wahala 

Dawowa yai yazo gefen gadon ya zauna

“Baby sam banji dadin abunda kikayiwa Jalal ba, haba baby, gaba yake dake fa, indai zakiyi masa haka nima zaki iya yimin kenan” 

Girgiza kai tayi “A a Yaya dan Allah kayi hakuri, nima ba a son raina na fada ba, raina ne a bace, shikuma yafaramin masifa, amma kayi hakuri” 

“Bani zaki bawa hakuri ba, inkina so in hakura, Jalal zaki bawa hakuri” 

Da sauri ta dago ta kalli Jawwad.

Jawwad ya dan daga mata gira

“Yes se kin bashi hakuri, sannan nima zan hakura”, lallaima wai sena bashi hakuri, ajiyar zuciya tayi

“to yaya Jawwad, zan bashi hakuri Insha Allah”

“Yawwa baby, Allah yaba ki lafiya” 

Jikinta a sanyaye, tace “Ameen” 

Kamar yadda doctor yai mata alkawari, da yamma aka rubuta musu sallama, jikinta yayai kyau sedai rama, duk yadda doctor Salis yaso Jalila ta dan sakarmasa fuska ya samu kafa kansa taki, dan ita wannan shishshigin daya kemata haushi yake bata, shiyasa kome yace setayi masa shiru, ta hade rai, haka ya gaji ya hakura, suka shirya suka hada kayansu, Jawwad ya daukesu se gida, Abba yayi murna matuka da ganin an sallamo Jalila, Nana ma se murna take, Jalila ta dawo, saboda Jalila ba karamin alkhairi bace a gidan

Har yanzu Abba yana fushi da Maama akan Jalila, tayi mamakin tsawon lokacin daya dauka haka, yana fushi akan wannan yarinyar, yanzu takuma tabbatar da idan har batayi taka tsan2 ba aurenta ze iya mutuwa saboda ita, se yanzu taga gaskiyar maganar yaya mairo, su Nana ma ba bi takanta sukeba, duk saboda Jalila, lallai tayi kuskuren yadda da Jalila ta zauna mata a gida, gashi tafara hada mata husuma a gida, dole tasan abunyi. 

  Kwana biyu da sallaman Jalila daga asibiti ta kara murmurewa, ta shiga sabgoginta, amma takan kebe ita kadai tayi kuka me isarta, gudun tayarwa da mutan gidan hankali, sannan tanata addu’a In Ummi na raye Allah ya bayyanata, tana cikin matukar damuwa amma, tayi iya kokarinta domin dannewa, kar a gane duk abunda take karfin haline kawai, Jalila ta lura Abba baya kula Maama, da tasaba kullum ta rakoshi in befita da wuriba, sucu Abinci ai wasa ai dariya, amma yanzu taga ko magana tayi se yayi mata banza, Jalila setaga hakan ba dadi, gidan ma ba dadi da suke zaune a haka, itako Nana ko a jikinta sabgoginta take. 

  Yau Maama ta fita bata gida da yamma, har magariba bata dawo ba, dan haka bayan an idar da sallar maghariba, Jawwad yasamu damar kiran Nana a waya yace ta tura masa Jalila, 

Ba musu Jalila ta tashi ta dau dan sirin gyale tasaka akanta, ta fita, part dinsa, da sallama ta shiga, taje ta tarar da shi yana aiki akan system dinshi, tana zuwa ya kashe system din, ya dago ya amsa sallamarta, karasawa tayi taje ta zauna a kasan carfet

“Yaya gani, Nana tace kana kirana” 

“Eh Jalila, ya jikin naki” 

“da sauki Alhamdilillah yaya” 

“masha Allah haka akeso, dama kiranki nayi inji ya maganarmu ta rannan, kin bashi hakurin kuwa”? 

Dan hade rai Jalila tayi

“To yaya ni ina zan ganshi, niban bashiba” ta fada tana dan zumbura baki

“To taso muje” 

“Yaya ina zamu?” 

“Zo muje seki gani” yafada yana tashi tsaye

Ba musu itama ta mike tabi bayansa, waje ya fita tana biye dashi, gidansu Jalal ya nufa, suna zuwa yai musu jagora zuwa part din Jalal, Jalila tayi mamaki duk yadda take ganin kyan dakin Jawwad amma na Jalal ya fishi dayake Jalila bata taba zuwa part dinba, babban part ne, dan seka zata amaryace a ciki, an zuba dukiya a ciki sosai, Suna shiga ta karewa dakin kallo, palournsa katone sosai da dakuna biyu a ciki, akwai kitchen da toilet a palourn, ba laifi ko ina tsaf yake, ga katon tv plasma kusan rabin bango, palourn yasha labulaye da kujeru,sekace dakin amarya, ga kamshin turare yana tashi, kai bakace dakin mashayi bane

Jalal yana kwance akan 3 seater daga shi se wando 3 quarter da vest, yana ta danna wayarsa, yanajin sallamar Jawwad ya amsa a hankali, inba ka kalli Jalal ba bazaka san ya amsa ba, idonsa a lumshe yace,

“Jawwad kai nake jira dama” 

“to gani ai, tashi kabani abunda zaka bani” 

Jawwad ya amsa suna karasa shiga cikin palourn, Jalal sam be san Jawwad shida Jalila bane, sedayaji Jawwad yace “Jalila, karaso ki zauna mana” Jalal ya bude idonsa ya waiga yaga Jalila ce dagaske, seda gabansa ya fadi, doguwar riga ce a jikinta na material, se karamin mayafi da ta dora akanta, rigar kaman a jikinta aka dinka ta, se yanzu ya kara ganin ta rame sosai se idanuwa, gashi ta danyi duhu amma tayi kyau sosai, dauke kansa yayi daga kanta, be kuma cewa komai ba, Jalila ta shigo cikin palourn ta samu guri ta zauna a kasa kan carfet, kusa da kafar Jawwad, se zumbura baki take, Jawwad yace “Jalal gurinka mukazo fa” 

“Ina jinka” 

“Ka tashi mana, kaji dame mukazo” 

Ba musu ya mike zaune, yana kallon Jawwad, “ina jinka” 

“Dama abunda ya farune a Asibiti tsakaninka da Jalila shine mukazo mu baka hakuri, dan Allah kayi hakuri nasan bata kyauta ba, amma gata nan munzo tabaka hakuri” 

Wallahi ba dan Yaya Jawwad ba babu abunda zesa Jalila tabawa wani Jalal hakuri kome zatayi masa na rashin kyautawa kuwa, 

Jawwad ya kalli Jalila “Jalila kibawa Yayanki hakuri” 

Sedata yatsuna fuska, dayake Jawwad baya ganinta, amma tana facing Jalal, 

“Dan Allah kayi hakuri, bazan kara ba” Jalal yace

“Hmmm Jawwad kenan, ni nacemaka nayi fushine?” 

“A a baka cemin ba, amma bamu kyauta bane, dole mu bada hakuri, da fatan an hakura” 

“Se anwa mutum laifine za a bashi hakuri, ai har a tambayi koya hakura” 

“Haba Jalal wannan ai gwalewa ne, tunda ta baka hakuri kayi hakuri mana” 

Wani mugun hara Jalila takewa Jalal ganin se wani raina musu hankali yakeyi, 

Wayar Jawwad ce tafara ringing, Hanan ce ta kirashi, bazeso yadaga agaban Jalila ba, dan yaga Hanan itama muguwar yar rigimace, yanzu setayi abunda Jalila zataji haushi, dan haka yace “please excuse me, Jalila jirani ina zuwa” ya tashi ya fita amsa waya, Jalal ya dora kafarsa daya kan daya, shima yaja tasa wayar, yana dannawa, Jalila se jan tsaki take, wayar Jalal ta fara vibration, ya saka a  kunnensa “Ya JJ ina jinka” Jalila ta dan kalleshi, Jeje in bata mantaba Jawwad ya gaya mata shine farkon lalacewar Jalal, 

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

“Birthday kuma Jeje, ni kuka shiryawa birthday, yaushe kenan”? Ya danyi shiru sekuma yace

“Ok Allah ya kaimu, zanyi shawara ingani, if i can attend” yakuma cewa

“Eh kwana biyunne akwai abunda nakeyine, shiyasa bakwa ganina, amma zanzo very soon” 

Jalila a zuciyarta tace

“gaskiya zanso inga wannan Jejen, inga ya yake, kuma meye manufarsa akan Jalal” Jalal ya gama wayar yayinda ta danyi nisa a cikin tunani, kamar an tsunkuleta ta daga kanta kawai sukayi ido hudu da Jalal yana kallonta, cikeda tsiwa, da gadara tace “Meye haka zaka wani tsuramin ido, lafiya?” Jalal yace 

“idan kika kuma, zuwa inda nake da wannan dan gyalen, zan nuna miki ba lafiya ba, kalli dan gyalen da kika saka” dan bude baki Jalila tayi da mamaki, 

“to ina ruwanka dani, dazaka dinga kallona, ni banason kallo, inma tsirara nake yawo meya shafeka” 

“meye abun kallo a jikinki, mummuna dake, kwaila” 

Jalika rasa meza tace tayi, dan batayi zaton jin wannan maganar daga bakinsa ba, shi kuma ya dauke kansa ya kunna sigari, 

Ya tashi ya dakko, giya a fridge ya dawo ya zauna, binsa Jalila tayi da ido, ya bude ya dakko wayne cup dinsa ze zuba, da sauri tace

“Giya ce fa? Kai yanzu baka kunyar ubangiji, baka kunyar kowa, zaka sha giya a cikinka, meye hakane?” 

Shiru yamata yafara zubawa a cup

“Wai dagaske shan zakayi,? Mikewa tayi cikin zafin nama, ta nufoshi a fusace daa nufin ta fizge, ko a jikinsa kuma be fasa abunda yai niyya ba

” in kika karaso inda nake zan baki mamaki, stay where u are, wallahi kikazo sekema kinsha, kuma ko a gaban Jawwad ne, se dai ya hadiyi zuciya” ba shiri Jalila taci birki, 

“Wallahi tir da halinka, me abun kunya, angirma amma ba hankali, Allah ya tsareni da shan giya, yamin tsari da hali irin naka, gaba daya ka gama bata rayuwarka, baka da wani amfani daza kayiwa kanka ko kayiwa wani, a dai canza hali” 

Banza yamata, yaci gaba da abunda yake, yayinda ta cigaba dagaya masa magan ganu son ranta, ganin bashi da niyyar denawa yasata nufi hanyar fita aiko tai karo da Jawwad

” Am sorry na barki kina jira ko, yi hakuri dan jirani kadan ss mu tafi? “

Ranta a bace tace” ni tafiya zanyi gaskiya “

” Me yasa? Ko fadan kuka sakeyi? “

“ni bazan cigaba da zama ana sabon Allah a gabana ba, ko kunya bayaji ya dakko giya yana sha, ni tafiya zanyi,” daga hakka fuuuuu tai waje, Jawwad ya kalli inda Jalal yake, tabbas giyar yake sha, jikin Jawwad a sanyaye ya taka ya karasa gurin Jalal, sannan yace” Jalal yakamata kadinga boyewa in zaka sha giyar nan, bayyanar da lefunka ze cigaba da zubar maka da mutunci a idon mutane, bekamata ka sha giya a gaban Jalila ba, Jalal u have to do something good for your life rayuwa bazata tafi a haka ba”

A hankali JALAL ya aje cup din hannunsa ya dan kalli Jawwad 

“Jawwad in har banji kunyar ubangiji ba na sha giya, meye kuma abun boyewa wani abun halitta, da bashi da wuta bashi da aljanna, Jawwad i don’t know what to do, nasani abunda Jalila take fada gaskiyane bani da wani amfani dazanwa kaina ko nayiwa wani, ban san meyakamata inyi ba, ban san meyake damuna ba, fita kabani guri Jawwad, ka tashi kabarni, leave me alone i want have some rest “

    Ilham tana kitchen tana hada tea zata sha, dayake window kitchen a bude yake, kuma kana ganin harabar gidan ta nan, kawai taga Jalila ta fito daga part din Jalal, ta tsaya ta dan gyara mayafinta sannan ta nufi gate, mutsukke idonta takumayi don tabbatar da gaskiyar abinda ta gani, anya kuwa itace, da sauri ta juya ta bar kitchen din

  Jalal yafara fita hayyacinsa, idonsa yafara wannan abun, ga jijiyoyin kansa sun tashi, ya fadi kasa,Jawwad ya zo gabansa ya dutkusa ya dan dafashi “Allah yaye maka wannan matsalar” daga haka Jawwad ya Mike ya fito, dan haka shine samun nutsuwar Jalal, jawwad ya girgiza kai tareda yiwa Jalal fatan samun sassauci a rayuwarsa, 

Fitar Jawwad keda wuya, Ilham ta fito daga cikin gida, ta nufi part din Jalal, sam bata hadu da Jawwad ba, tana zuwa kamshin turaren Jalila ya daki hancinta, tana kokarin tabbatarwa ne taga handkchief a tsakar palourn, da sauri takarasa ta dauka, ta kai hancinta ta shinshina, tabbas na Jalila ne, ga Jalal taganshi zube a kasa yana bacci, dora hannu tai aka ta fasa ihu, sekuma tayi saurin toshe bakinta, 

“Na shiga uku Allah yasa ba abunda nake tunani bane, Jalal in kamin haka bakamin adalci ba, kaci amanata, kuma wallahi na tabbatar da abunda nake zargi sena kasheka na kasheta wallahi,” shikam yafadi a gurin yana baccinsa

Surutu ta cigaba dayi, tana zambarwa a gurin, Jalal besan tanayi ba, tagaji tayi waje ta nufi cikin gida, dakinta ta shige ta kulle kofa, ta dinga zarya, wayarta ta dauka, ta kira malamin su, akayi sa a bugu biyu ya daga

“Malam akwai matsala fa” 

“Mastalar mene haka?” 

“sonake ka bincikamin, kagani aikin nan kuwa ba a samu wata matsala ba?” 

“Matsala kuma kaman yaya, wani abu yafarune”? 

“ni dai kawai ka bincikamin dan Allah,” 

“To shikenan amma kibari seda safe, zan kiraki” 

Sukayi sallama da malam, amma fafur batun bacci ya kauracewa idon Ilham se surutai da zage2, kaman ta zare, kai kace mahaukaciya ce, yadda taga rana haka taga dare. 

Da safe Jalila dan cin Abinci tayi kadan bata wani ci dayawa ba takoma daki, dan tunda aka sallamota daga asibiti a daki take wuni, seda wani dalili take fitowa, Nana ta tafi gidan kawarta yau, ga Halima taje ganin gida, dama Maama ba shiga sabgarta take ba, tunani duk ya addabi Jalila, ga batada nutsuwa saboda rashin Ummi, ga kuma tunani daya addabeta akan rayuwar Jalal, hankalinta ya karkata kan son zuwa birthday Jalal, domin ganin waye Wannan Jejen, 

Tunani duk ya dameta, dan haka ta tashi ta fito harabar gidan, tasamu guri ta zauna, tai shiru tana kallon flowers, 

  Da safe Ilham ta kuma kiran Malam a waya don tambayarsa ko ya bincikamata, yace

“Na duba, nayi bincike amma ba abunda ya sauya, aikinmu yana nan a tareda shi, aikin da akayivakansa har yanzu yana tareda shi” 

Ajiyar zuciya Ilhan tayi, “har naji dadi, nagode sosai malam har naji hankalina ya kwanta” 

“Ai bakiga ta kwanciyar hankali ba indai baki kauda wannan yarinyar ba, yakamata fa kisan halin da kike ciki don tabbatar da cikar burunku keda mahaifiyarki, asiri kawai baze tasiri akanta ba dole ki tashi kisan meya kamata kiyi, ina ganin itace zata kawo wa aikin nan matsala, ni nariga nagaya miki yanzu, shawara da dabara yarage naki”

“To shikenan nagode sosai, nikuma zan san abunda zanyi,” sukayi sallama ta dakko handkerchief din Jalila ta fito se gidansu Nana, tayi sa a Jalila tana harabar gidan a zaune, gurin Jalila ta nufa, tana zuwa ta kalleta

“Gurin ki nazo zamuyi magana” 

Banza Jalila tayi mata, “magana fa nake miki” 

“in har zakizo inda nake bakimin sallama ba, banida lokacin saurararki” Ilham tasan inbatayi yadda Jalila take so ba, bazata kulata ba dan haka tai mata sallama

Jalila ta amsa sannan tace “ina jinki” 

Ta kalli Jalila ta nuna mata handkerchief din tace mata “wannan kaman naki ko?” 

Jalila ta kalli hannunta tace “ba kama bace nawane” 

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

“A ina kika barshi?” 

“A inda kika tsince shi” Jalila tabata amsa cike da rainin hankali 

“zuwa nayi muyi magana ta fahimta, bata fada ba” 

“Inma ta fadan kikazo a shirye nake” 

“Jalila meya kai handkerchief dinki dakin Jalal, meye hadinki dashi?, Jalila ina miki kashedi na karshe tun kafin insa ki zubarda hawayenki, inma akwai wani abu a ranki akan Jalal gara ki cire, kishiga hankalinki dan wallahi zan iya illata kowaye akansa, duk wanda yai niyyar hana min cikar burina senasashi zubda hawaye, Jalila wannan ne kashedina dake na karshe, kifita a harkar Jalal, tun kafin ta kwabe miki”

Jalila tai mata kallon tsaf sannan tace

“A matsayinki nawa kike min wannan kashedin haka? Matsayin uwata ko ubana ko wadda ta isa dani? Hmmm gaskiyar dan uwanki dayake cewa bakida hankali, ni kinga wani abu me kama da soyayya tsakanin da wannaan bugaggen dabe maida sabon Allah komai ba,? Ilham ko mazan duniya sun kare ba abunda zanyi dashi, banga abun so a gurinsa ba, Allah ya tsareni son Jalal, bashida kamala da cikar dazesa inso mutum kamarshi, baya jerin irin mazan dasuke birge Jalila, dukda bansan naki kudurin akansa ba, nima ina da nawa kudirin akansa, babu soyayya, ko auren Jalal a kudurina, kuma ki dena wannan tunanin, amma kisani idan har kudurinki yaci karo da nawa akan Jalal to tabbas kisawa zuciyarki sena tarwatsa naki!!! Ban taba sa abu agabana nakasa ba Ilham, ina iya tarwatsa ko shirin uban waye domin biyan bukata ta, wallahi Ilham kinyi kadan kisani kuka, idan harkika sani kuka, nikuma namiki alkawarin zan illataki a inda babu wanda ze gani balle ya miki magani, Ilham zuciyarki zanwa Illa ta har gaba da abada, ganin Jalila kike bakisan wace itaba, tunda kika zabi zaman takun saka dani am ready for you “daga haka Jalila ta fizge handkerchief dinta tai cikin gida, yayinda Ilham ta sandare a gurin.

Jalila na zuwa dakinsu ta kife akan gadonsu,

“Nikam Jalila nashiga uku, wace kaddara ce ta kawoni kano har nasan Jalal ne, wanda har rayuwarsa take neman hanamin tawa nutsuwar, Ummi dan Allah in kina raye duk inda kike ki dawo, nagaji da zaman nan ina cikin damuwa, Allah ka temakeni, kabani ikon jarraboyina na rayuwa”

Ta karasa maganar tan zubda hawaye, tayi me isarta sannan ta mike ta duba wayarta ta kira Hanan, seda ta kusa katsewa sannan Hanan ta daga, tana dagawa tace

“Tace afuwan ranki ya dade, ina wankane, ya jiki Jalila? 

” Da sauki Hanan, ya Baba na dasu Abdallah “

” Baba baya gari yana bauchi, Yaya Abdallah ma haka dagani se mummy, ya jikin kinji sauki”

“jiki Alhamdilillah na warke ganima a gida” 

“masha Allah, nakira Jawwad nace ya hadani dake amma se yacemin ba kya kusa, siyama ma takiraki bata shiga ki kirata dan Allah” 

“zankirata Insha Allah” 

Hanan ta ce

“nikan Jalila meyasameki haka har ya kai ga kisamu stroke ko wani abu na damunki ne?” 

Se Jalila taji kaman Hanan ta sosamata inda yake mata kaikayine, batasan lokacin da hawaye yafara fita daga idonta ba

“Hanan ni meye ma baya damuna, ko kinsan cewa a halin yanzu sati biyu kenan, bansan inda ummi takeba ko a raye ko a mace ban saniba” 

“Kamar yaya baki saniba, naje gidan fa ranar dazata taho kano, tacemin zatazo kuyi sallama zata wuce garinsu, kuma kice bakisan inda take ba” 

“Hanan tunda Ummi ta tafi, mukayi waya da ita, wayanta be kara shiga ba anyi trying har angaji, karshe aka kira Abba aka gayamasa, wai wani me mota ya bigeta, kuma ya dauketa ya tafi da ita, bawanda yasan ina ya kaita, kotana raye kota mutu bamu saniba” 

“Innalillahi wa inna ilaihi raji un, Jalila meyasa baki gayamin ba tunda wuri, kuma angayawa”yan sanda”? 

“Hanan Abba yana iya kokarinsa amma har yanzu ba labarin Ummi ni harna hakura na fawwalawa Allah komai” 

“kiyi hakuri Jalila, nasan abun da wuya a gurinki, amma mucigaba da addu a, insha Allah za a ganta, in daddy ya dawo zan sanar masa koda wani abu da za a iyayi akan matsalar, kiyi hakuri, Jalila insha Allah ummi tana raye za a ganta”. Hanan ta ke rarrashin Jalila yayinda itama take zubarda hawaye, har cikin zuciyarta takejin matsanancin tausayin Jalila, 

“Addu a ina nan inayi hanan, sedai kuma ina bukatar taku adduar” 

“Insha Allah zan tayaki addu a, kinji kidena damuwa sosai, kar wani ciwon yakamaki” 

“Karki damu kanwata na fawwalawa Allah komai, shi ze bani mafita” 

“Masha Allah haka akeso queen muzama masu karbar kaddararmu a duk yadda tazo mana,” domin kokarin kauda damuwar Jalila, se tace mata “nace ya gidannaku, ya mutuminki?” 

“waye kuma mutumina?” 

“kinfini saninsa Jalal mana” 

“Yana gidansu” 

“kai queen har yanzu kina masa rashin mutunci ko?” 

“ko jiya ma seda mukayi, yau kuma wannan mahaukaciyar kanwar tasa tazo zatamin hauka, wai ita alallai son Jalal nake, wai in ban fita harkar saba seta sani kuka kiji fa,” 

Dariya Hanan tayi, sannan tace

“queen J nasanki da kafiya, dan Allah karki bari Ilham tayi nasara, kizama silar shiryuwar Jalal, u can do it, kibata mamaki, kamar yadda kika bani” 

“ke nina fara gajiya, gashi jarababbe, ga taurin kai gashi mugu, itakuma gani take sonsa nake ko uwar me zanyi da wannan makakken, dan wahala daga ita harshi” 

“A a dai, banda cika baki, daga baya kizo kina zare ido akansa” 

“Kut me kike nufi, mezanyi da wannan Allah ya rufamin asiri” 

“Oho dai inda rabon an jone ne…. Jalila bata bari takarasa ba ta kashe wayar tareda fadi” ji muguwa zatamin mugun baki, ta Allah ba taki ba”

Daga haka Jalila ta Mike ta fito palour don samun dan abunda zata ci, Maama tana palour a zaune tana kallon Aljazeera, 

Jalila tace “Maama sannu da gida” 

Kallon Jalila tayi ta dauke kai ba tareda ta amsa mataba, har Jalila zata wuce kitchen, Abba ya shigo, ya dawo da wuri yau, da alamu ko mantuwa yayi, Jalila tace

“Abba sannu da zuwa” 

“yawwa Jalila ya jiki ya gidan,” 

“lpy qalau Abba” 

Maama tacewa Abba “Sannu da zuwa” 

Banza yayi mata da nufin shigewa dakinsa, Jalila tai farat tace “Abba, Maama na maka sannu da zuwa fa, bakace komai ba” 

Abba ya wayance da “Yawwa maman Yara, yi hakuri banji bane” ya wayance kar Jalila ta gane, sannan yace “Jalila dan kiramin Jawwad, kice ina son ganinsa, a dakina” 

“To Abba bari inje” 

Jalila ta tafi part din Jawwad, Jalila na fita Abba ya shige part dinsa ya bar Maama a palourn, binsa tayi itama, tana kuka, Abba ya kalleta

“meye haka zaki biyoni kina kuka, se yaranki sunce wani abun nayi miki” 

“Meyema bakayimin ba ina tabinka ina baka hakuri amma kaki kulani, sati kusan biyu kana gaba dani, kaki saurarata haba Abban Jawwad, dan Allah kayi hakuri, kadena fushin nan haka” 

Kukan dayaga tanayi seta bashi tausayi, 

“Zainab, komenayi miki ke kika jawa kanki, nima ba a son raina naimiki hakaba sedan in nunamiki kuskurenki, akan abunda kikayimin,” 

Download>>> Silar Fyaɗe Complete Novel Document

“kayi hakuri hakan baze kuma faruwa ba Insha Allah” 

“Zainab kenan indai halinki ne ba wanda ban saniba, bana tunanun wannan maganar har cikin zuciyarki” 

  Jalila tana zuwa part din Jawwad ta tarar suna fada da Jalal, 

“JALAL dan me zasu shirya maka wani birthday, dacan ma aibasu suke hada maka ba, bayan kasan mutanan nan bana kirki bane, su kaika wani guri su hada maka birthday kuma ace shabiyun dare haba Jalal kayi tunani mana,” 

“Jawwad ya kakeso inyine? Sokake ince musu bana so ko inki zuwa, ko wa akayiwa haka baze ji dadi ba, mene a ciki abu na lokaci daya ayi a watse, basu taba hadamin ba, wannan karon sunmin se ince banaso, kana ganin idannayi hakan na kyauta, shikenan bance kaje dole ba fa, dama zuwa wannan gurin da daddare ai da irina ya dace ba da kai ba” 

daga haka Jalal ya juyo fuuu ze fita, da sauri Jalila ta bashi hanya kar ya bigeta, bayan ya fita ta shiga palourn, Jawwad yanemi guri ya zauna yayi shiru

“yaya Jawwad ya dai? 

” Bari Jalila, Jalal ne yake neman ya cazamin kwakwalwa, kullum fatana in janyeshi daga jikin wannan miyagun abokannasa shikuma yana kara shige musu, “

” Meya farune? “

” Wai an hada masa birthday, se sha biyun dare zasu fara har gari ya waye, kuma a baya tare muke hadewa muyi dashi kuma  a gida amma wannan karon wai su suka shirya masa, nasan kwana zasuyi shan giya, nace kar yaje kuma yana neman yayi fushi, seyaje yai tayi ai, am tired da halin Jalal”

Sosai taji tausayin yayan nata, taga kokarinsa ma tsawon wannan lokacin yana tareda Jalal, duk da miyagun halayensa, ga shi da wuyar sha’ani amma haka Jawwad yake tare dashi, kuma tasan wannan fushin na dan lokacine, dole se daya ya nemi daya, ta numfasa tace

“Yaya Jawwad ai be kamata kayi fushi ba fa, tunani yakamata kayi, tsawon shekaru suna tareda shi basu taba cewa zasu shiryamasa birthday ba se wannan karon, kuma ma wai se tsakiyar dare zasu fara, baka tunanin wani abun suka shirya akansa? Bakayi tunanin suna da manufar yin hakan ba? Kn kayi fushi kace yaje yaitayi, kaga sunyi galaba zasu kara janyeshi, shikenan yazama  nasu gabadaya”

Shiru Jawwad yai yana kallon Jalila 

Taci gaba da cewa “Kayi tunani yaya na, dan uwanka ne fa, u have to think” 

Ajiyar zuciya yayi “Hakane baby kema kinyi magana, amma yanzu me yakamata inyi” 

Jalila aranta tace yawwa, nima ga dama ta samu, 

A fili tace, “Yaya dole ka shiga cikin lamarin nan, kawai ka yadda da maganar birthday din nan, ka lallabashi kasashi a maida partyn kaman daga karfe ta kwas zuwa goma, sannan dolenka ka halarci gurin domin sakamasa ido, in takama har abokanan ku da yanuwa ku gayyata, hakan ze hana faruwar wasu abubuwan, karfe goma nayi, ka janyeshi daga gurin, yanzu kayi hakuri ka sakko, har ya gaya maka shirye2 da sukeyi, kaima seka san shirin dazakayi, amma inka barshi ya tafi shi kadai jikina na bani akwai dalilin dayasa suka shirya hakan, sun san babu wani dan uwansa daze yadda ya bishi guri irin wannan karfe shabiyun dare”

Murmushi Jawwad yayi, tareda yiwa Jalila salute 

“Gaskiya baby kina da tunani me zurfi, hankalina be kai kan hakan ba ni, gaskiya nagode, zan jarraba insha Allah” 

Murmushi Jalila tayi

“nifa aikoni akayi, Abba yace kazo yanzu” 

“To shikenan ina zuwa” 

  A ranar bayan Jawwad yaje kiran Abba, ya je yanemi Jalal suka shirya, yace masa ya yadda, zeje birthday dinsa amma gaskiya zasu gayyaci mutane, dan haka sedai a canza lokacin daga shabiyun dare zuwa karfe takwas, Jalal yace ya yadda. 

   “Jeje wannan ce dama ta karshe dazan baka, a wannan karon banason asamu kuskure, dukda tsawon shekarun nan kayi aiki tareda ni, kamin duk abunda nake bukata to wannan karon, sonake komai ya kare, sonake a wannan lokacin komai yazo karshe, karka bari wannan shirin ya rushe, “

” Oga kb baka da matsala, munyi iya kokarinmu gurin ganin hanyoyin dazamubi domin gabatar da aikin cikin shiri, burinka ze cika, a wannan ranar zamuyi yadda zamuyi muga mun karasa wargaza rayuwarsa, “

Wanda aka kira da oga KB ya gyara tsayuwa yai ajiyar zuciya

” shikenan ina jira zan saka ido inga kokarin ka, a wannan karon, aje acigaba da shiri,”

” Shikenan oga, wannan karon komai zezo karshe”

Daga haka sukayi sallama,

Hannah na gaban dressing mirror tana kwalliya, Jeje ya kirata, seda ya kira sau uku tana kallon wayar sannan ta dauka

“Hannah ina kika shiga ne inata kiran wayarki, ya za ayi mu hadu ne?” 

“mu hadu kuma, akwai matsala ne?” 

“eh haduwar tamu tanada mahimmanci sosai, akan shirunmune, yanzu haka daga gurin oga KB nake, akwai bukatar mu hadu” 

“To zanzo, muhadu inda muka saba” 

“To shikenan sekinzo” 

         

Ilham se safa da marwa take, a cikin dakinta, ta rasa inda maganganun Jalila suka dosa, tace ita ba son Jalal take ba, amma itama tanada kuduri akansa, kuma inyaci karo da nawa, to tabbas zata rusa nawa, koda tazo nan a tunaninta seda ta zare ido, ta rusa nawa burin saboda nata muradin, to ko ta san menene shirina ne, to amma tayaya zata sani bayan ko Nana bata saniba, 

Dakko wayarta tayi, zata kira yaseera, sekuma ta fasa, dole in dau mataki, bazanyi wahalar banza tsawon shekaru ina kallo wata sakarya ta rusamin shirina ba, gara tun yanzu in rusata ita danata shirin, ta mike da sauri ta nufi dakin mummy, tana zuwa ta tura kofar dakin, ta sameta tana waya, taje kusa da ita ta zauna, tana jiranta tagama, 

Seda mummy tagama waya, sannan ta kalli Ilham tace

“Ilham ya akayine, naganki wani iri haka kaman mara lafiya” 

Fashewa tayi da kuka, ta fada kan cinyar mummy 

“Mummy wallahi nakusa mutuwa, in har yaya Jalal be aureni ba, zan iya mutuwa, Mummy ina sonshi, dan Allah asaka ranar aurenmu,” 

“Yi shiru kiyi hakuri, kinji nima naga kamatar yin hakan, kila in kika aureshi ma ya shiryu sanadin haka, yanzu kidena kuka, bari daddynku ya dawo, muga me yakamata ayi, amma karki kuma zance zaki mutu saboda shi, aini na miki alkawari, indai ina raye Jalal shine mijinki, indai nina haifeshi baze taba auren wata mace inba keba, kidena kukan nan haka ya isa”

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Ilham tayi, tareda yin murmushi a boye, a fili kuma tace

“dan Allah mummy asaka da wuri, ina tsoron ya auri wata baniba,” 

“ki kwantar da hankalinki, shi kinga alamar ma zeyi soyayya da wata, ko kina tunanin akwai wadda zata aureshi a haka, aini kingama min komai da kikeson Jalal a haka, dan haka bari daddyn sa ya dawo, zamuga yaushe yakamata asaka” 

Ilham ta riko hannun mummy, 

“Nagode sosai, mummy” 

“bakomai, kidena kuka” 

   Hannah zaune akan fararen kujerun dake  gurin, fuskarta dauke da wani arnen glass dayake barazanar cinye fiye da rabin fuskarta, ga barima da tasaka a akan dogon hancinta, se tauna chew gum take, tana fuskantar Jeje, 

“Hanna daga gurin oga KB nake, kuma yace lallai wannan itace damarmu ta karshe akan Jalal, yazama dole muyi yadda zamuyi mukammala aikin nan,” hannah ta dan nisa ta cire glass din fuskarta, sannan tace

“Idan ban mantaba shekaru uku zuwa hudu muna aikin nan, duj wani salon makirci, da kisisina ba wanda banyi ba, tunda nafara bariki, bantaba ganin dan bala’i ba kamar Jalal, ban taba haduwa da mutum me azabar taurin kai ba kamar Jalal, babbar nasarar dana samu a rayuwa akansa shine, a labarin daka bani, bayan sauyawar Jalal, ina cikin jerin matan daya sake dasu, har yake shiga harkata, amma naiyi iya kokarina alakarmu ta wuce haka amma yaki yadda, ni yanzu bani da wata dabara, 

Nagama nawa, bansan meye shirinka ba”

“Hakane Hannah, nasan kinyi mana aiki, kinyi iya yinki kinmana kokari, abaya a koda yaushe ina galaba akan sa amma yan shekarun nan, nafara ganin sauyi a tareda shi, koda nagama aikina akan Jalal, sena tabattar da nayiwa Jawwad babbar illa shima, saboda tsawon wannan shekarun shiya hana cikar burin mu, Jalal yanajin maganar Jawwad fiye data uwar data haifeshi, wadda ita ta haddasa komai, “

” Baka ganin ina aka cutar da Jawwad ba a masa adalci ba, shi meye nasa aciki “

” yana da laifi Hanna kuma dole ya karbi hukunci, yanzu ki tsaya ki saurareni”

“ina jinka” 

“a gurin birthday din damuka shirya masa komai ze kare,” hannah ta kalleshi sannan tace

“bangane mekake nufi ba” 

“zaki gane ne Hannah, nagama shirya komai, kinsan meze faru?” 

“No seka fada” 

“kamar yadda muka shirya, shabiyun dare zamu fara gabatar da taron, a cikin cake din dazamu bawa Jalal ke zakiyi wannan aikin, zaki saka kwaya, a dai2 inda za a bashi, saboda sonake ya bugu ya fita hankalinsa yadda baze iya komai ba, za sakama a lemon da zs sha, da zarar ya fita hayyacinsa zamu dauke shi, mu kaishi wani gurin, kekuma zaki gabatar da aikinki”

Dan tsaki Hannah tayi

“Ni gaskiya ba a haka naso aikin yazo ba” 

“to ya za ayi se hakuri, tunda shi dan taurin kaine, zamu nuna masa munfishi iya bariki” 

Wayarsa ce tafara ringing, jeje ya kalli Hannah “Dan halak shike kirana” 

Tai murmushi tace

“Pick it” 

Dagawa yayi yasa a hands free 

“Allah ya temaki, mazaje, namijin duniya sha gwagwarmaya, namjin damusa bakason raini”  Jalal yace

“Kai Jeje ya isa haka, magana nakeson yi maka akan maganar partyn nan” 

“ok inajinka” 

“Munyi magana da Jawwad, dan haka dole a maida shi eight Jawwad yace baya son ya kai karfe shabiyu in bahakaba baze attending ba, dan haka ina so amaida shi eight pm, saboda inason Jawwad ya kasance a gurin” 

What!!!!!!! Jeje yafada da karfi yana mikewa tsaye

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Share please 

Back to top button