Uncategorized

Abban Sojoji Page 53 Book 2 Complete Hausa Novel

 

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

     _💋BOSS BATURE💋_

*Zuwa ga masu karkasamun littafin duk wanda ya ƙara haɗamun document,ban yafe ba!babu yarda za’ae ni ina cikin rubuta littafi na biyu,wasu kuma sun haɗamun document na book 3 don iyayi da kuma ƙarfin hali,sai ja mun surutu sukeyi nacewa naja littafi har book 3 duk da idan naga dama har book 5 ma sai inyi bani naji zan iya ba😒😏🙄😒, wasu har gardama sukeyi mun nacewa book 3 suke so complt,bayan ni iya book 2 nake cikin rubutawa ma,*

Abban sojoji part 2 ❤

Bayan Haroon yayi parking ɗin motar,hayaam tayi mashi godiya tare da ɗaukar bag ɗinta,ta fito daga cikin motar sannan ta nufi cikin gidan,

  Shu’umin murmushin nan nashi ya saki yabi ta da kallo tare da cewa”Nifa bana abu don Allah,kowani tsautsayin ne da ƙaddara suka kawo ta cikin gidan nan!Allah yasa ta kwanan mana biyu….” ya jinjina kai tare da cewa “tsuntsu daga sama gasasshee!”ya ƙarashe maganar tashi tare da zura hannun shi cikin aljihun jeans ɗin dake a jikinshi,wayar shi ya ciro tare da duba screen ɗin, missed calls aka mashi da wata hidden number,

    shiru yayi yana tunanin taya zai bi kiran saboda kira ne mai mahimmanci a wurin shi gashi dole sai in shi mai 6oyayyiyar numbar ne ya kira ka,

  Yana cikin wannan tunanin sai ga kiran ya sake shigowa,cikin sauri yayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnan yana jiran jin me za’a sanar dashi

  Wata irin muryace ta irin hamshaqan matan nan waɗanda suka ji duniya ta soma magana”Haroon!kana shirin jamin bala’e ko?meyasa ka fiye shiririta ne?ko kamanta plan ɗin mu ne”?

   nan take haroon yashiga en ina murya na rawa yace”ban manta ba,inaso nabi komai a hankali……’bata bari ya ƙarasa maganar ba ta kwatsa mashi tsawa”Ya isa Haka! kasani wlh akanka bazan bari nayi gangancin rasa damar da nake da ita ba!haroon zaka iya rasa ranka muddin kace zaka kawomin wasa acikin lamarina!kai kasan wacece NI!bani da imani,”

  Wata irin zufa ce ta soma gangaro mashi daga cikin sumar kanshi,lokaci guda duk yabi ya rikice yashiga zazzare idanu,

   sautin dariyarta ce ta karaɗe kunnan shi,tsagaitawa tayi da yin dariyar sannan ta sassauto da muryarta wurin cewa”Am sorry fa,na tsorata ka ko?

Nannauyar ajiyar zuciya haroon ya saki tare da cewa”Yanzu me kike so ayi ne,just command me zanyi maki koma menene,”!

   “So nake ka kashe JUNAID!saboda shikaɗai ne hanyar da zanbi wurin ƙuntata masu,banaso junaid ya rayu,muddin yana araye toh farin cikin gidan zai cigaba da wanzuwa ne,ni kuma abunda bana so kenan!,”

     girgiza kai haroon yashiga yi tare da cewa”Kiyi haƙuri wannan ne karo na farko da kika ban umarni na musa maki tunda na fara maki aiki!junaid is innocent  I can’t kill him,zan iya kawar maki da duk wanda kikeso acikin gidan nan,Amma banda junaid!banda Abbana,Rafayet kuma yafi ƙarfina banda wata hanyar da zan iya cutar dashi,sai ma in jefa kaina cikin matsala!”

   fashewa da dariya tayi tamkar zata fasa screen ɗin wayar,bayan ta tsagaita da yin dariyar taci gaba da magana”kasan koni wacece,kasan kuma abunda zan iya!idan har bazaka iya kawar mun dasu ba,to ni zan iya kawar dasu ta cikin ruwan sanyi,Haroon u must do what i command you!if not i wll expose ur secrets,kai kasan me zai biyo baya,ko ka kashe junaid ko kuma ni in kashe maka rayuwa gaba ɗaya…!!!!

   Waro ido waje Haroon yayi yana sauraronta,

  Cigaba da magana tayi”Maganar videon su Twins daka ɗauka,nasan ka goge na wurinka,amma akwai wani a hannuna,zanyi amfani dashi wurin tarwatsa zuciyar mahaifin nan nasu,da kuma masoyina Rafayet!inason ganin tashin hankalin shi sosai….”

  A tsorace haroon yace”Kada ki kuskura ki saki bidiyon nan!in ba haka ba asirina zai tonu ne!kuma kina sane da cewa,muddin asirina ya tonu to ke ma kin gama yawo!!atare zamu fuskanci sakamakon mu,zasu kamo ki ne aduk inda kika 6uya!!”

    ya ƙarasa maganar yana faman sakin huci yayin da idanun shi sukayi jawur saboda tsananin 6acin rai,

   fashewa ta kuma yi da wata irin mahaukaciyar dariya kafin ta tsagaita da yin dariyar tace”Haroon!Iska bata ruƙuwa!domin ni tamkar iskar nake,kada kamanta ina amfani da baƙaƙen aljanu wurin gudanar da aiki na,kuma zanyi amfani dasu ne wurin ganin na tarwatsa dukkan zuri’ar Salahuddeen Hussein!wannan alwashi ne na ɗauka,rai uku masu mahimmanci suka kashe mun,ni kuma rayuka zan ɗauka!don bana yafiya arayuwata!”

  Shiru yayi bai ce komai ba kusan minti biyar, sam baison wani abu ya samu abbanshi shi kaɗae yafi ji sannan yace”Maganar yaran nan fa?su kuma ya zakiyi dasu?

   “Inaso saina fara sanya soyayyarsu acikin zukatan ƴan uwansu sosai,saboda inaso inyi amfani da wannan damar ne wurin ƙuntatawa dukkan wani jin daɗi na zuri’arsu,kamar yarda suka ƙuntata ma tawa zuri’ar,”

    Jinjina kai haroon yayi kafin ya kuma cewa”Yanzu menene plan ɗinki”?

   Wannan karan anatse ta soma magana”plan ɗina shine kawar da junaid,dalilin dayasa nakeson kawar da junaid shine!sihirina bazai ta6a tasiri akan Rafayet ba har sai an samu lagwanshi,kuma ba kowa bane lagwanshi ba fa ce Junaid,da zarar ya rasa junaid zaiyi sakaci da ibadarshi hakan zai bani damar yin aiki akanshi,kuma shi ya kasance Bugun zuciyar family ɗinsu inaso na ɗanɗana masu raɗaɗin rasa mutumin daka kwallafa rai akansa!sannan maganar bidiyon nan zan sake shi a social media kowa ya gani,daga zarar hakan ta faru nasan cewa Martabar family ɗinsu da kuma ƙimar da suke dashi a duniya gaba ɗaya zasu zube,kowa zai tsani zuriyarsu duk wata daraja da suke dashi a idon duniya zata tashi abanza ne!ni kuma hakan nakeso,kafin na saki bidiyon inaso kayi amfani da kuɗin da suka baka wurin barin ƙasar,ka koma malaysia da zama,na shirya maka komai najin daɗin rayuwa acan,giya da mata har saika gaji dasu,”

   shu’umin murmushin nan nashi ya saki aranshi yana ayyana irin rayuwar da zaiyi acan cikin daular da aka shirya mashi,nan take yaji cewa zai iya aikata komai takeso,

  Sam yama manta da waya yake yi saboda tsabar farincikin da ya ziyarce shi,mayar da bayanshi yayi a jikin seat na motar yana cigaba da sakin murmushi,

   “Kana jina kuwa,”muryarta ce ta ratsa kunnan shi,hakan yasa ya dawo daga dogon tunanin daya tafi,

   Sai da ya samu natsuwa sannan yace”Naji duk abunda kika ce,hakan yayi mun sosai,musamman da kika ambaci giya da mata,sai naji wani nishaɗi araina dama irin rayuwar da nakeson yi kenan,amma akwai wata shawara da nakeson baki,in ba damuwa,”

  Tace”ina sauraronka haroon,”

“Ga me da bidiyon tsaraicinsu twins,kada ki sake shi a social media pls,sun riga sun biyani kuɗi kamar yarda na buƙata,shiyasa nakeso ayi masu sassauci,mutun biyu kawai nakeson suga bidiyon nan Abban su da kuma wannan ifiritun sarkin jin kan nan,sannan maganar kashe junaid nasan ban isa na hanaki aikata abunda kika yi niyya ba,amma abunda nakeso ki bar komai a hannuna,ni ko ke babu wanda zai kawar dashi!kiyi amfani da sihirin ki kawai ta cikin ruwan sanyi yarda babu wanda zai zarge ni!!”

     Dariya sosai tayi da alama shawarar Haroon tayi mata,

   Sannan tace”daga yau komai zai fara”!!! 

murmushi haroon ya saki tare da cewa”Allah yaba mai rabo sa’a”

  daga haka su kayi sallama ya kashe kiran,kasa fitowa daga cikin motar yayi ba don komai ba sai don kasalar da yaji ta baibaye shi,fuskar junaid kawai yake gani acikin idanun shi,😢

   ******************

Lokacin da Hayaam ta shiga cikin gidan da sallama abakinta tashiga main palour ɗin,tsayawa tayi da tafiya ganin babu kowa acikin babban falon,takun tafiyar da taji ne yasa ta juyawa ta gefen hagunta tana kallon mai tafiyar,bakowa bace face Sehrish sai faman sauri take yi don ta shiga kitchen,har yanzu shigar ɗazu ce a jikinta,amma ta yafa mayafi ajikinta tayi rolling ɗinshi,

   ta wutsiyar idonta ta hangi mutum hakan yasa ta dakata da yin tafiyar ta ɗan juya don taga wanene,karaf idonta suka haɗu akan na Hayaam,cike da mamaki take kallonta,batasan ko wacece ita ba,amma ganin hasken fatarta yasa tayi tunanin ko ƴar uwarsu Junaid ce,

   tunkararta sehrish tayi fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙarasa inda hayaam take,tunkan sehrish ta ƙaraso zuciyar Hayaam ta shiga bugu,don ta gane cewa itace Ƴar aikin da Aunty laila take bata labarin cewa tana rayuwa acikin gidan,yarinyar da Abbansu ya mayar da ita ɗiyar shi,

   fuska ɗauke da murmushi sehrish tace”Sannu da zuwa,”

   hayaam tace”yawwa,ina mutanen gidan nan?naji shiru ko ba kowa ne”?

  sehrish tace”duk sun fita,amma junaid da Fawan suna acikin bedroom ɗinsu,sai Aunty azmee tana acan cikin kitchen,

   Jinjina kai Hayaam tayi har ta buɗe baki zata kuma cewa wani abu,sai ga Azmee ta fito daga cikin kitchen ɗin,ganin Hayaam yasa ta soma Sakin fara’a kamar gonar auduga,cikin sauri ta tunkaro wurinsu tana cewa”Wata sabon gani!Anya ba idona ne ke nuna min badaidai ba?

  dariya hayaam tayi tare da wuce sehrish ta tunkari wurin Azmeen suka rungume juna,

  ɗago da ita azmee tayi daga jikinta tana cewa”Oh ni Hayaam!ashe dama zan sake ganinki a duniyar nan?gaskiya kun yada zumunci!ina ji tun bikin Amani yaushe rabon ki da gidan nan!

   Sai faman washe baki Hayaam takeyi ba don komai ba sai don sanin cewa Azmee zata kar6eta hannu bibbiyu kuma zata goya mata bayan zama acikin gidan,

     “Kai Aunty azmee,nafa zo bayan bikin Amani kin dai manta ne,gaskiya nayi missing ɗinku sosai,shiyasa ma nace dole nazo naganku,”

  Magana takeyi amma hankalinta na akan Sehrish,dake tsaye tana sauraronsu,

   Azmee tace”mu ma munyi kewarki sosai,amma dai bada wuri zaki koma ba ko?don bazan bari ki tafi batare da kin zauna mana ba,”.  

   Anzo wajen da tafiso nan fa tashiga washe baki tana cewa”ae Aunty azmee har sai kun gaji dani,in dae ba ku kuka kore ni ba,amma ni ina nan ba inda zanje,”

  murmushi Azmee tayi tare da cewa”Ae bama wanda zai kore ki hayaam,”. 

  taƙarasa maganar tare da mayar da idonta kan sehrish tace”wannan Hayam kenan!ƙanwar matar yayansu ishaq,da kuma Amani wadda tazo ran nan harna gabatar maki da ita”?

  wani irin bugu taji zuciyarta tayi mata ba don komai ba,sai don tuna kalaman Amani da tayi in har wannan takasance ƙanwarta ce,lallaikam akwai matsala,

  da ƙyar sehrish ta ƙaƙalo murmushin yaƙe sannan tace”Allah sarki,ashe kanwarsu ce,naga suna yanayi da Aunty amanin,”

   ta6e baki hayaam tayi jin abunda sehrish tace,

   ruƙo hannunta Azmee tayi tare da cewa”Kada na cika ki da surutu,mu shiga ciki ki huta don nasan ba ƙaramar gajiya kika kwaso ba,”

  atare suka wuce ciki da Azmeee,zuru sehrish tayi ita dai tun da tayi arba da Hayaam taji sam bata kwanta mata arai ba,kama hanyar shiga kitchen ɗin tayi tana cikin tafiya taji muryar junaid ya ambaci sunanta,

   dakatawa tayi da tafiyar sannan ta ɗan juya tana kallon shi,fuskar nan tashi a yamutse alamar daga bacci ya tashi,sai faman sakar mata wannan kyakkyawan murmushin nashi yake,

   acikin ranta tace”Shagwa6a66e halan yunwa yake ji ne,”

   ƙarasa saukowa yayi daga saman stairs ɗin kai tsaye wurinta ya nufa, 

     Lokacin da ya ƙaraso inda take tsaye muryar shi cike da kasala yace”Reesh har yanzu Abbanmu bai dawo ba”?

ɗaga mashi kai tayi alamar eh,tamkar zaiyi kuka yace”dama nasani,tunda wannan abokin nashi yazo mai farin gemu,nasan cewa ba zai barshi ya shigo ciki ba,yana can yaja shi sun tafi yawo gidan abokanansu,”

  maganar shi ba ƙaramin dariya taba Sehrish ba,

   “Amma dae baka da mutunci junaid,abokin abban naku ne kake ce ma mai farin gemu”? 

   turo baki yayi cike da shagwa6a yace”eh mana,farin gemu gare shi,ae ba ƙarya nayi ba,

Ya ƙarasa maganar da cewa”nidai yanzu ki taimakamin bana jin daɗin bakina farfesu nakeson sha,”

   bin lips dinshi tayi da kallo yarda yake magana ashagwa6e,sunyi dark red dasu kamar wanda yashafa jan baki,

      Tunanowa tayi da maganar shi ta ɗazu da ya furta mata kalmar so,acikin ranta tace”yanzu ace dagaske junaid sona yake yi,tabbas zan iya haƙura da wanda nakeso don na aure shi,saboda ba ƙaramin tausayi yake bani ba,komai nashi kuma yana burgeni,sai dai bansan ya rayuwar auren mu zata kasance ba,yarda yake shagwa6a66en nan ba ƙaramar wahalar shi mace zata ci ba,wannan rainon shi ma zanyi kenan?kullum sai ya tashi tsakar dare da kukan rigima,don haka sai in tanadi feeder da zan rinƙa haɗa mashi madara yana sha…….’

KARANTA ZAFAFA 2023

*IDON NERA By Mamuh ghee*

Kasa ƙarasa zancen zucin nata tayi saboda dariyar data zo mata,tafin hannunta tasa tare da rufe bakinta,ta ƙumshe dariyar don karta fito da ita,junaid ya gani ranshi ba ƙaramin 6aci zaiyi ba,

  Harara ya watsa mata tare da cewa”meyasa kike kallona ne?kuma kinsa hannu kin rufe mouth ɗinki da alama baki da gaskiya sehrish,”

   kafin tace wani abu,sai ga haroon ya faɗo cikin main palour ɗin,jin takon tafiyar shine,yasa gaba daya suka juya suna kallon shi,adaidai lokacin shima ya ɗago da idanunshi kai tsaye suka sauka akansu,

Nan take sehrish taji gabanta ya faɗi rass,saboda ta tsani ganin shi acikin idanunta,

  da alama wurinsu yake tunkarowa,murmushi junaid ya shiga sakar mashi yana cewa”Ya haroon sannu da dawowa,”

    “Yawwa baby junaid,me kuke yi anan ne”?

.   yayi maganar yayin da yake ƙarasawa wurinsu,

   sunnar dakai sehrish tayi batare da ta ɗago sun haɗa ido dashi ba,

  Junaid yace”muna magana ne da sehrish,”

  ɗan ta6e bakin shi yayi kafin yace”okey,ka wuce ciki inason magana da ita,”

   batare da musu ba junaid ya wuce cikin palourn tare da samun wuri saman 3 seater ya zauna,

    ja da baya sehrish tayi aɗan tsorace tana jiran jin mai zai ce,

   “Kinyi kyau sosai,shigar jikin ki tayi mun,”ya fadi yana faman bin wandon jikinta da kallo,

   Shiru tayi mashi batace komai ba,jira kawai take yayi ƙoƙarin ƙure mata ta watsa a guje,

   “dama nasan ba zaki ce komai ba,hakan yayi mun sosai,bakomai ne yasa nace inason magana dake ba face don in baki wata shawara mai kyau,sai dai bansan ko zaki ɗauka ba 

  Sai lokacin ta ɗago da idanunta tare da kallon shi tace”wata irin shawara kenan?kada kayi tunanin cewa zan ɗauki shawarar ka,saboda kai ba abun yarda bane!nagama yarda da duk wani abu da zai fito daga wurinka,burinka kawai ka cutar dani!”

   hannunshi ya zura acikin aljihun shi tare da ƙara matsawa dab da ita yace”shawarar ba akanki bane!akan junaid ce!

   daram!!taji gabanta ya faɗi a ɗan rikice take kallon shi,

   “Nasan tunda na ambaci sunan junaid,yanzu zaki so ki saurari me zance,don na lura ba ƙaramin jinshi kike yi ba,” 

  Murya na rawa sehrish tace”me…me..kake son cewa ne agame da junaid?me junaid yayi ne?

    Maimakon ya bata amsar tambayarta sai cewa yayi”ran nan nayi maki ƙarya na cewa ni shaiɗanin aljani ne,wannan maganar ba gaskiya bace,abunda ya faru shine akan idona Omar yashigo cikin falon nan kai tsaye naga ya wuce upstairs sai raina ya bani cewa dole zai ji sautin kukan ki,kasancewar part ɗinshi dana sgr basu da tazara sosai a tsakaninsu,maganar cewa ni na shaƙe maki maƙoshinki  alokacin da kika zo ambaton sunana agaban Marshal Omar shima duk ƙaryace,bani nayi maki hakan ba,kawai nayi guessing ne kuma da alama na canka dai dai,nasan kin tsorata alokacin kuma kinyi tunanin cewa ni ba Mutum bane,don haka inaso kisa aranki cewa Ni haroon cikakken mutum ne kamar kowa,”yana ƙarasa maganar tashi yasa ƙafa zai wuce part ɗinsu,

..cikin sauri sehrish tace”ka manta baka ban shawarar da kace zaka bani ba,”

   dakatawa yayi da tafiyar batare da ya juyo ba yace”ku dage da addu’a,” yana fadin hakan yasa kai ya wuce ciki,

   Tsayawa tayi cike da zullumin maganar haroon nacewa su dage da addu’a,tana cikin wannan yanayin muryar Azmee ta katse ta da cewa”Sehrish!tsayuwar me kikeyi anan ne?nayi tunanin zan zo na same ki a cikin kitchen,’

  cikin sauri sehrish ta nufe ta,tana cewa”yanzu nake ƙoƙarin shiga kitchen ɗin,wani abune ya ɗauke mun hankalina,”

   Atare suka shiga kitchen ɗin,batare da 6ata lokaci ba suka soma aikace aikacen girke girken nasu kamar yarda suka saba,

  

    Tun bayan da azmee takai hayaam ɗaya daga cikin bedroom ɗin da suka saba ajiye baƙi insun zo,zame hijab ɗin jikinta tayi,wata ƴar short gown ce ajikinta daidai guiwarta,kai tsaye toilet ta faɗa,bayan wasu ƴan mintina sai gata ta fito waist ɗinta ɗaure da towel,sai lokacin ta tuna cewa ashe tabar trolley ɗin kayanta acikin boot ɗin motar Sofwan,yanzu dole ta neme shi ko don ya kawo mata abunta,

   ƙarasawa tayi tare da hayewa saman gadon ta zauna,sannan takai hannu tare da ɗauko purse ɗinta da ta ajiye asaman gadon tun shigowarta tare da Hand bag ɗinta,

    wayarta ta ciro anan taga missed calls na Aunty babba har kusan uku,

  Murmushi ta saki tare da bin kiran nata,wayar na fara ringing Aunty babba ta ɗaga,. 

   kara wayar a kunnanta tayi tare da cewa”Auntyna takaina!yanzun nan naga missed calls ɗinki,banji ma da fitowa daga toilet ba,

  on the other hand aunty babba tace”kin isa gidan ne!”?

  Hayaam tace”eh,yanzu hakama gani asaman gadona inaso nayi bacci don na rage gajiyar dake ajikina,amma fa aunty nasha wahala kafin nasamu shiga cikin gidan nan!”

   Aunty babba tace”wahala?kamarya kenan?

    Nan hayaam ta kwashe duk abunda ya faru a wurin shigowarsu cikin gidan ta sanar mata,

   uban tsoki aunty babba ta saki tare da cewa”Ke kika ban haushe wlh!taya zaki tsaya yi masu kwatance cewa ke ƙanwa tace?to menene alaƙar dake tsakani na dasu ne da har zasu shaidaki!tun a lokacin yakamata ki kirani awaya sai inyi ma wani magana daga cikin gidan akan yayi masu magana su barki ki shiga,amma don kince hayaam ƙanwar matar yayansu,to koni nan da kike gani Sgr baisan sunana ba,bare har yasan naki sunan hayaam,wannan mutumin ma bana tunanin yasan kamannin fuska ta nikaina,”

   yatsina fuska hayaam tayi tare da cewa”aunty inaso in kwanta bacci nake ji,”

.  Aunty babba tace”to shikenan!kardae ki manta da abunda yakai ki cikin gidan,so nake kafin sati mai zuwa naji ana zancen bikinki da Sgr,kafin shekara mai zuwa kuma inji kukan jariri,”

  Fashewa da dariya hayaam tayi jin abunda Aunty babba ke cewa,

   Sun jima suna waya kafin daga bisani sukayi sallama,wurgi da wayar tayi gefe guda sannan ta kwanta asaman lallausan bedmattress ɗin,nan take bacci yayi awon gaba da ita,

**********************

Abun da ya faru bayan barin Amal gidan,wuraren bayan sallar la’asar mammy da Abra suka shigo cikin gidan,jikinta na sanye da hijabi abra kuwa atampa ce ajikinta ta aza mayafin asaman kafaɗarta,sai faman fira suke yi atsakaninsu,

   “Mammy yanzu me zakiyi da kuɗin nan da sofwan ya baki?naga kamar suna da yawa,dama akwai ankon bikin wata ƙawata da nakeson yi,kinga sai ki aramun dubu takwas aciki inyi amfani dasu,”

.   tsuke fuska mammyn tayi tare da cewa”matsalarki kenan!daga kinga wani ya bani kuɗi sai ki bijiro da maganar anko,tun wuri ma ki fidda rai don ko sisi bazan baki acikinsu ba,malam zan kaima cikon kuɗin shi sannan sauran ni zanyi amfani dasu,ko ɗan farfesu naman nan an samu ayi,dama na kwana biyu ban sha ba,

  ta ƙarasa maganar a lokacin da suka ƙarasa tsakiyar filin gidan,.  

  Rai a6ace abra tace”mammy kalli kiga fa har yanzu yarinyar nan bata fito daga ɗakin ba,ko ubanwa takeso ya ɗaura mana girki?gidan ma ko share shi ba tayi ba!

   cike da masifa mammy ta shiga kwaɗa mata kira”Amal!!Amall!!don ubanki kina ina ne?bazaki fito kiyi mana aikin cikin gida ba!

  Jin shiru bata amsa masu ba,yasa mammy ce ma Abra”maza kije ki tashe ta,ta fito tayi mana aiki,ko tasha na jaki,”

  Kama hanyar ɗakin nasu abra tayi har ta kusa shiga ɗakin,ta tuna wata mugunta,cikin sauri ta juya tare da nufar fanfon cikin gidan,ƙaramin bokiti ta ɗauka na plastic ta ciko shi da ruwa sannan ta wuce dashi ɗakin a hannunta,

   Murmushi mammy tasaki tare da cewa”haka nakeso,ƴa’ƴana su dinga koyi dani,”ta faɗi hakan tare da sa ƙafa ta wuce cikin ɗakinta,

   ae tana shiga cikin ɗakin ta aza idonta akan gadonta inda tabar kuɗin da sofwan ya bata nan taga wayaam babu komai a wurin,hannu tasa tare da murza idanunta don ta tabbatar da abunda idanunta ke nuna mata,again ta kuma ganin wayaam babu komai asaman gadon,

  Cike da mamaki tace”wai ba nan na jiye kuɗin da sofwan ya bani ba?kodai na jefa su wani wuri ne bansani ba!

  ta faɗi hakan tare da sanya hannu ta zame zanin gadon tana kakka6e shi wai koda zata ga kuɗin a ƙasan shi,nan ma babu,

  Cikin sauri ta zuƙunna tare da zoƙa kanta tana leƙen ƙasan gadon koda sun faɗo sun shige ƙarƙashin gadon,nan ma wayaam babu su,

   Hankali atashe ta miƙe tana tafa hannu ranta ajagule tace”To wai kodai kuɗin nan ƙafafu ke gare su ne?in ba haka ba taya akai suka bar saman gadon nan!nifa nan na ajiyesu ban canza masu wuri ba,”

  Lokaci guda tabi ta rikice ta rasa natsuwarta,saboda mace ce mai shegen son kuɗin tsiya,har faɗi take da naira biyar ɗinta ta faɗi kwara haƙorinta guda ya cire,

   Acan kuwa bayan Abra tashiga cikin ɗakin da Amal take,sam bata lura babu mutun asaman katifar ba,saboda yarda shape din bargon ya bada kamar akwai mutun acikin shi,

  Ciza le6anta tayi tare da cewa”ƴar jakar uba,yau zaki gane kuranki,wato banza tasamu tun jiya kike ja mana na rago asaman katifarmu duk kin 6ata mana katifarmu da yawun bacci,yanzu zanyi maganinki,ƙazama kawai

  ta ƙarasa maganar tare da ɗaga bokitin ta kwarara ruwan asaman bargon tana faman 6a66aka dariyar mugunta,abun mamaki shiru babu alamar Amal zata saki ihun jin saukar ruwa ajikinta,. 

   Hakan yasa dariyar abra ta soma komawa ciki,ganin yarda bargon ya lafe ajikin katifar,yasa ta gane cewa babu mutum asaman katifar,

  Hankali atashe ta saki bokitin ƙasa tana faman kwala ma Amal kira,

Shiru bata amsa ba,cikin sauri ta fito tana nemanta a tsakar gidan,babu inda bata duba ba daga kitchen har cikin toilet ɗinsu duk bata nan,

  da gudun gaske ta koma ɗakin mamynsu a firgice mammyn ta ɗago tana kallonta ganin yarda ta faɗo mata yasa tace”Abra lafiya meke faruwa ne”!

   Muryarta har wani shakewa takeyi wurin fadin”Mammy!babu Amal acikin gidan nan!Amal ta gudu!dama saida raina ya bani cewa zata iya guduwa,’

   jin hakan yasa mammy cewa”hakan na nufin itace ta kwashe kuɗin da Sofwan ya bani?

   “Mammy dagaske baki ga kuɗin ba!aiko indae hakane toh Amal itace ta kwashe kuɗin,innalallahi bansan ya akai wannan daƙiƙiyar yarinyar har tayi tunanin guduwa ba,ina mata kallon shashasha….’

    Katse ta mammy tayi da cewa”amma shegiyar yarinyar nan ta gama dani wlh!naci buri akan kuɗin nan,maimakon ta gudu tabarmin kuɗin shine ta haɗa dasu ta gudu,insha Allah a wulaƙance rayuwarta zata ƙare,Allah ma yasa kidnappers su ɗauketa su kwace kuɗin,sannan su lalata rayuwarta…..” 

   “Subhanallahi!!me nake ji haka!”

  Muryar Abbansu Abra ce ta karaɗe kunnansu,shigowarshi kenan cikin gidan ya same su suna ta tsinar Amal,

   wani koɗaɗɗen mutum ne,tamkar baya a cikin hayyacinshi haka zubin shi yake,tsohon yadi ne ajikinshi duk yayi uban squeezing,kamar kanshi farau talauci,

   ƙarasawa bakin kofar dakin yayi yana tambayar lafiya menene ya faru,

    Tsawa mammy ta daka mashi tamkar ba mijinta ba haka tashiga ɗura mashi zagi

   “Munafukin banza,munafukin wofi kazo kaji abunda muke tattaunawa ne!Anya bakaine kayi ma Amal hanyar guduwa daga cikin gidan nan ba!wlh ban yarda dakai ba!ka faɗamin gaskiya taya akai Amal tabar cikin gidan nan!?don nasan hakanan banza Amal baza tayi tunanin barin gidan nan ba!dole da taimakon wani,

   Tuni yasha jinin jikinshi,saboda mugun tsoranta yake ji,gaba daya ta gama asirce shi,shiyasa baida ikon yin komai sai da Umarnin ta,

   tsawa ta daka mashi tare da cewa”ba zaka faɗamun gaskiya ba!taya akai amal tabar gidan nan!

   Zuru yayi da ido sai faman kyafta ido yakeyi yana mazurai kamar mara gaskiya,

   tsoki abra taja tare da cewa”mammy dama kin daina wahalar da kanki,Abba bai ma da cikakken hankalin da zai iya taimakon Amal wurin barin gidan nan!6ata mana lokaci kawai zaiyi,ni ina ganin ki fito kawai muje mu nemo ta acikin gari,

   harara Mammy ta watsa mashi tare da fitowa daga ɗakin ita da Abra suka kama hanyar fita daga gidan,

  Bayan sun fuce daga cikin gidan,matsawa abi yayi tare da kai hannu ya ɗauki kujera ƴar tsugunno ya zauna asamanta,

   Muryar Amal ya tuna acikin kunnan shi,ashe sun haɗu da ita akan hanya sai faman sauri take yi tamkar zata tashi sama,kamar daga sama taji an ruƙo mata rigar jikinta a firgice ta juya tana kallon shi,ganin Abbansu ne yasa ta fashe da kuka don tasan cewa zai iya mayar da ita gida,cikin shessheƙar kuka tace”Abie nasan inda Aunty amani take,bazan cigaba da zama acikin gidan nan ba,kana gani zasu kashe ni,amma ba ka iya tsawatar masu akan su daina cutar dani,dan Allah Abie kabarni in tafi,kada ka sanar ma mammy cewa ka ganni akan hanya,ka nuna cewa bakasan komai ba,”

  tsananin tausayinta ne ya kama shi,nan take yaji cewa zai iya taimakonta gudun karta faɗa hannun mutanen banza,tun da ƙaramar yarinyace mai ƙananun shekaru tsaf za’a iya yi mata wayau,

   “Kiyi haƙuri Amal akan dukkan abunda ke faruwa,nima bada son raina bane,bani da yarda zanyi ne gaba daya mammy ta addabi rayuwata,ta hanani dukkan wani farin ciki na rayuwata,tun bayan da Allah yayi ma mahaifiyarku rasuwa ban ƙarasamun kwanciyar hankali ba,komai na duniyar nan ya fita raina Amal,mammy ta jima tana cutar da rayuwata da kuma rayuwarki,yanzu ina da kwarin guiwar iya taimaka maki!dama abunda yasa tuntuni banyi hakan ba saboda bani da ikon yin magana dake acikin gidan,inaji ina gani an rabani da ƴata kuma ana cutar da ita akan idona,babu komai akwai ranar sakayya,”

  Yana kai karshen maganar tashi ya ruƙo hannun Amal tare da janta suka tafi,da kanshi yakaita tasha sannan ya damƙa ma drivern amanarta,kasancewar drivern ɗaya daga cikin abokanshi ne ana mutunci sosai,agaban motar drivern yayi mata wuri ta zauna kusa dashi,

  Sai lokacin drivern yake tambayarshi inda zasu sauke ta a abujan,shi kanshi abie baisan inda amani ke zaune ba acan,

   Cikin sauri Amal tace”ina da numbar wayar Aunty amanin,idan mun isa sai ya kira mun ita awaya,nasan zata zo,”

   Murmushi abie yasaki yana tsaye daga waje yashiga tofa mata addu’o’i tare da yi masu fatan sauka lafiya,

   tuni Amal taji hawaye sun wanke mata fuskarta,ji take kamar ta fito daga cikin motar tabi mahaifinta,haƙiƙa ta tausaya mashi sosai,haka ta dinga jin raɗaɗi azuciyarta har motar tasu ta kusa barin tashar,ya jiyo muryar Amal tana kwala mashi kira,

  “Abie!!Abie!!”

da saurin gaske ya ƙarasa inda motar take,kowa na cikin motar tsayawa yayi yana sauraron muryar yarinyar,

   murmushi ta sakar mashi,tare da zura hannu cikin aljihun rigar Abra dake ajikinta,zaro kuɗin nan tayi kusan dubu arba’en,sannan ta zura hannunta ta saman glass ɗin murfin motar ta miƙa mashi su,

   ganin ya tsaya yana kallon kuɗin yasa tayi saurin cewa”Abie dan Allah kada ka tambaye ni ina nasamu kuɗin,in dai ka yarda dani to ka kar6a kawai nasan kana buƙatarsu,”

    Murmushi yayi tare da sanya hannu ya kar6i kuɗin,sannan a hankali glass ɗin ya soma dagawa sama,

   Tana jiyo muryarshi yana cewa”ki kula mun da kanki,sannan in Allah ya haɗaki da ƴar uwarki Amani,ki gaishe mun da ita,kice Abbanta yana gaishe da ita sosai,

    har motar tabar tashar Amal bata daina leƙenshi ba ta glass ɗin motar,haka zalika shima yana atsaye yana kallon motar tasu,har sai da ta 6ace ma ganin shi,sannan ya haƙura ya juya tare da kama hanya ya soma tafiya yayin da idanunshi ke akan hannunshi yana kallon kuɗin da Amal ta bashi,

  Ba ƙaramin daɗin kuɗin nan ya ji ba,yaushe rabon daya ruƙe naira dubu tashi ta kanshi harya manta,ba damar ya samu kuɗi yashiga gidan shi,da zarar mammy ta gani zata amshe kuɗin,ko sisi bata son taga ya ruƙe a hannun shi,tafi son taganshi a matsiyacin shi yana yawo,wannan ba damuwarta bace,

   Sanin cewa zata iya ganin kuɗin a hannunshi ta kwace mashi su hakan yasa baiyi gangancin zuwa gidan dasu ba,kai tsaye ya wuce wurin wani abokin shi mai siyar da nama abakin hanya,wuri yasamu ya zauna bayan sun gaisa ya bashi ajiyar kuɗin duka,sannan yace ya zuba mashi naman na dubu uku yaci,bai bar wurin ba sai da yaci ya ƙoshi sannan sukayi sallama da mai naman ya wuce gaba,

   Murmushi abie ya saki bayan ya kammala tunanin nashi yace”Allah sarki Amal!kin taimaki mahaifinki,ba don ta bani kuɗin nan ba,da yau haka zan kwana da yunwa,”

  

   Mammy da abrah tamkar zasu yi hauka wurin neman Amal,gida gida haka suka dinga bi suna nemanta,saƙo da lungu ba inda basu duba ba,har bayan sallar magrib suna waje wurin nemanta,a ƙarshe dasuka gaji agalabaice suka koma gidan suna faman haki kamar waɗanda suka sha gudu,tun acikin zauren gidan mammy ta yanke jiki ta faɗi a sume,saboda tsabar baƙin cikin Amal data gudar mata da kuɗinta,

. hankali atashe abra tashiga zabga ihu tana kuka tana ambaton sunan mammy,

  Da alama dae mammy sai anyi jinya,

****************************

Around 11pm,

fitowa tayi daga cikin toilet jikinta na sanye da sleeping dress riga da wando,white colour,da alama tayi shirin kwanciya,tun acikin toilet take jin wayarta na ringing,hakan ne ma yasa tayi hanzarin fitowa,ƙarasawa tayi cikin sauri tare da kai hannu ta ɗauki wayar dake ajiye asaman mirror,duba sunan mai kiran tayi,ganin baƙuwar number yasa taƙi ɗaga kiran,sai tayi rejecting ɗin kiran,kafin ta ajiye wayar sai ga wani kiran ya ƙara shigowa na baƙuwar numbar,

Cike da mamaki tace”Wai wanene ke kirana a irin wannan lokacin,kuma da bakuwar number,salon ajamun bala’e,bari dae in ɗaga inji,picking call ɗin tayi tare da karawa a kunnanta,muryar namiji ce taji ya zabga mata sallama,aikuwa cikin sauri ta katse kiran tana faman dafe saitin zuciyarta,ta tsorata da jin muryar me kiran nata,koma wanene ba ƙaramin mutum bane,

  tsayawa tayi tana tunanin wa tasani da wannan muryar,bata ta6a jin mai irinta ba,

   tana cikin wannan yanayin sai ga message ya shigo cikin wayarta,cikin sauri takai hannu tare da janyo saƙon daya shigo daga saman screen din wayar tashiga karantawa kamar haka

   _baiwar Allah,ina ta kiran wayarki kin ƙi ɗagawa,dama ƙanwarki Amal ce ta ban numbarki don na kira na sanar dake cewa kizo ki ɗauke ta,ni ne drivern daya kawota abuja,idan ba damuwa ki kira kuyi magana da ita,don kiji muryarta_

  Wani irin bugu zuciyarta tayi,cikin tsananin mamaki tashiga maimaita sunan Amal,muryarta na kerma tashiga cewa’Amal!wata Amal yake nufi!ko dai Amal ƙanwata!!!

   Cikin sauri ta danna ma numbar kira,yatsun hannunta har kerma sukeyi don aƙagare take da taji bayanin mutumin daya turo mata saƙon………..

 Pls read this👇👇👇

*Assalamu Alaikum,barkanmu da juma’a fatan kowa na lpy,yauwa inaso indan yi wani karin haskene,aduk lokacin da bansamu yin update ba har ranar ta wuce ina kokarin ganin nayi long page don yayi covering da wanda bansamu yi ba,nasan wasu sun fahimci hakan,yayin da wasu kuma basu fahimci hakan ba sai suyi ta maganar page kaza yakamata inyi tunda banyi na rana kaza ba,duk page da nake saki yafi ƙarfin page guda a ƙa’idar page,ina haɗe 2 pages ne sometimes ma yana haura 2 pages, Shiyasa in na sanya short page wasu ke complain saboda sun saba ganin long page,sannan ban kin yin typing sai don uzurin da ba yadda zanyi,da fatan zaku fahimce ni,sannan akwai masu maganata abayan idona nacewa wai ina jan littafi? Allah sarki rashin sani yafi dare duhu,bani da wani burin daya wuce inga na kammala littafin nan ayanzu saboda abubuwa da sukayi mun yawa,bani ke jan littafin nan ba!bada son raina ba kuma hakana ke faruwa ba!yanayi ne dake nake ciki,yakamata mutane su dinga yi mun uziri bai kamata arinƙa yi mun irin waɗannan maganganun ba,duk wanda kuma yake yi Alhakina na akanshi, wai wasu ma har cewa suke yi don naga littafinna yasamu kar6uwa mutane naso. shiyasa nake jan labarin,wlh dana ji wannan maganar kamar na fasa ihu don takaici, hmmmm babu komai akwai Allah,to my real fans nagode kwarae da hadin kai da kaunar littafi na da kuke,godiya mara adadi kuci gaba da yi mun uziru kuma acigaba da yi mun addu’a,shine kawai insha Allah komai mai wuce wane,Littafin nan inaji araina cewa kammaluwarsu tazo zanyi ƙoƙarin tabbatar da hakan!insha Allah*❤

*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃

*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI.  MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*

*LOCATION KANO*

08062073990

Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka 

Wadrobe balls 

Madarar kulleccham 

Vaseline kulleccham 

Kajiji

Halut

Couscous 

Khumrah 

Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka 

Wadrobe balls 

Madarar kulleccham 

Vaseline kulleccham 

Kajiji

Halut

Couscous 

Khumrah 

Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

It’s not just good …it’s finger linking good faster than fast food, better fine dining.

Snack

Awarah 

Farah

Zobo

Samosa

Cup cake etc 

Contact me 09063302182or 09012179727.

Back to top button