Uncategorized

Abban Sojoji Page 1 Hausa Novel

“`The father Of Soldiers“`

        

Story 

     &  

       Written 

                   By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)

Dedicated to my beloved sisters. 😍   

Special thanks to Fadeela Lamido & Sadeeq Abubakar. Wannan littafin sadaukarwa ne a gare ku, jinjina ta musamman.

Page  1,2,3&4

Hannu tasa ta toshe kunnenta saboda ta gaji da jin masifar da Buzun maigadin yake ta surfa mata, “Ke wannan idan mayya ce kika kama mutun wallahi sai an yi da kyar za a samu magani.”

“Na she miki hajiya ba ta nan kullum sai kin zo, ba ki da zuciya ne kare ya lashe ko? Yarinya karama da ke sai taurin kan tsiya, da wasu kwala-kwalan idonki kamar na kwarton mazuru, kina kallon mutane da su ba kunya ko? Kai ga d’an iska!”  

Dagowa ta yi a hankali tana kallon sa jin cin mutuncin da yake yi mata , idonta ne suka ciko taf da kwalla, kananun labbanta suka soma kyarma, tuni yanayin fuskarta ya canza.

Duk a tunaninsa yarinyar za ta mayar masa da martani saboda ya san yaran zamanin nan ba ka taba su su yi maka shiru, zuba mata ido ya yi kuri yana kallon ta. Gani ya yi tana ja da baya a tunaninsa tafiya za ta yi tabar wurin amma sai ta samu wuri a jikin bangon gidan ta tsugunna tare da kifa kanta a saman guiwowinta sannan ta soma rera kuka mai tsuma zuciya.

Tsayawa ya yi yana kallon ta, da alamun nadama a tattare da shi, har cikin zuciyarsa yake jin bai kyauta mata ba, yana Musulmi da shi ya gaza fahimtar yar karamar yarinyar da ke zarya kullum a bakin gate din gidan, bai taba tambayar kansa dalilin da yasa yarinyar take zuwa wurin ba. Ba irin korar karen da bai yi mata ba amma hakan bai sa gobe taki dawowa ba.

Jiki a sanyaye ya matsa inda take ya tsugunna a gabanta ya ce, “Kai kukan ya isa haka! Dago ka gaya mini mene ke damun ka me yasa kake zuwa kullum kana neman hajiya?”

Dagowa ta yi fuskar nan ta yi jaga-jaga da hawaye ga majina cikin shesshekar kuka ta ce, “Ina zuwa neman hajiya ne saboda na ji an ce tana taimakon ‘yammata ta sama masu aikatau ana biyan su kudi.” 

Jim ya yi yana kallon ta kafin ya ce, “Kai ko mai yasa kake neman aiki karamin yaro da kai gidanku ba manya ne?”

Girgiza kai ta yi, “A’a babu kowa, ba mu da kowa, ni da ‘yan uwana ne kuma ba su da lafiya an kwantar da su a asibiti, kuna likita ya ce aiki za a yi musu, ba ni da kudin aikin saboda suna dayawa, shi ne nake so na samu aikin da zan yi ina samun kudin da zan tara a ayi musu aiki kada su mutu su bar ni ni kadai!” Karasa maganar ta yi tare da mayar da kanta kasa tana kuka.

Yanzu ya gane dalilin da yasa yarinyar ta nace sai taga hajiyar, a cikin zuciyarsa ya ce, “Baiwar Allah tana shikin damuwa karama da ita. Oh amma yana da tunani mai kyau!”

Riko hannunta ya yi tare da cewa, “Share hawayen ya isa haka, zan taimaka maka ka ga Hajiya, taso mu je ka zauna saman benchi ka ji.” 

Mike wa ta yi ta bisa, a tare suka zauna saman bencin, jim suka yi na d’an wani lokaci kafin ya ce, “Ka yi shiru kaji ka daina kuka Allah shi ne gatan bawanSa ko mutun bai da kowa indai ya yi imani da Allah shi ne zai zama gatansa, ka shi gaba da addu’a ‘yan uwanka za su samu sauki har ku yi wasa da su.”  

Murmushi ta yi saboda ta ji dadin maganarsa, hannu ya kai ya dauko ruwan bunun da yake dafawa a saman ‘yar butarsa, dama akwai karamin kofi guda biyu da yake amfani da su wurin zuba shayin.

Lekensa ta dinga yi tana kallon ‘yar butar karfen da yake dafa shayin da ita, ta burge ta musamman abin da ke cikinta. Kofin ya dauko ya tsiyaya mata  a ciki, mika mata ya yi. Hannu biyu ta sa ta karba don rabon ta da ta ci wani abu a cikin ta tun jiya. Sannan shi ma ya zuba wa kansa a d’ayan kofin yana kurba yana ba ta labarin gizo da koki.

Sam ba ta gane me yake cewa, d’an ruwan bunun da ya ba ta ya dauke mata hankali saboda dadinsa musamman daya sanya sugar a ciki, a hankali take kurbarsa, kusan so uku tana shanyewa yana kara mata, a karshe ya ce “Aradun Allah shegen ci ne da kai ga shi harka shanye mini ruwan bununa, idan hajiya ta samo maka aiki ka fara yi sai ka biya kudin shayina.” 

Murmushi ta saki tana sauraron shi tana mamakin yadda yake suffanta ta da namiji, ga shi shi dai ba makaho ba sarai ya gan ta da kayan mata a jikinta, 

har marece ya yi hajiya ba ta dawo ba, da lokacin sallar Azahar ya yi da kansa ya bude musu kofar dake a jikin gate din suka shiga. Ruwa ya debo musu a buta, suka yi alwala tare sannan ya shimfida musu tabarma, shi ya ja su sallar yana gaba tana daga bayansa. 

Bayan sun gama , suka ci gaba da zama a saman sallayar yana jan cazbi a hannunsa ita kuma ta shiga tunanin duniya, a haka har La’asar ta yi suka sake kabbara sallar, tun kafin su sallame yake jin karar motar hajiya alamar ta iso.

 

Dadi har cikin ranta yau dai Allah ya yi za ta gana da hajiyar nan, yana sallame sallar da sauri ya tashi ya bude mata kofa, ta shigo da dankareriyar motarta, wucewa ta yi da motar zuwa wajen ajiya. Zuge kofar ya yi sannan ya bi motar hajiyar a baya yana mata kirari kamar yadda ya saba. 

Farinciki ya sa ta kasa rufe bakinta sai faman murmushi take yi, ba ta tashi daga samman sallayar ba, zama ta yi tana jiran maigadin ya yi wa hajiyar maganarta. Bude mata motar ya yi ta fito, ma sha Allah irin matan nan ne masu jiki ‘yar dumurmur da ita, ta ji hutu fara ce tas amma da alama tana karawa da man bleaching, jikinta na sanye da tsadadden leshi shudi wanda aka yiwa ado da stones, ba karamin kyau ya yi mata ba. Ta kashe daurin kallabinta, hannunta na sanye da diamond rings, haka sarkar wuyanta ta diamond ce, kwalliya ce sama-sama a fuskarta tana da dara-daran idanu ga hanci dogo, tubarkalla, sai jan-baki da ta shafa ja ne. 

Cikin girmamawa ya ce, “Barka da isowa hajjaju makkatu!” 

Ya mutsa fuska ta yi da alamun gajiya a tare da ita ta ce, “Yawwa Aku sarkin dumi akwai wanda ya zo ba na nan?” Ta yi maganar ne a yayin da take bude kofar motar ta baya, saboda ba ita kadai ta zo ba akwai ‘yammatan da ta zo da su daga kyauye. 

Maigadin ya amsa mata da cewa “E mutane sun zo sosai amma duk ban rike shunansu ba na dai ce musu ba ki nan kin yi tafiya, sai dai akwai yaro d’aya da ya zo neman ki kullum shai ya zo yau dai na ce mashi ya jira ki dawo.” 

D’aga idonta ta yi tana hangen ‘yar yarinyar da ke sanye da hijab saman sallaya, mayar da idonta ta yi kan ‘yammatan da ke zaune cikin motar, ganin ta bude musu motar amma sun ki fitowa, tsaki ta ja tare da cewa, “Kwana za ku yi ne a cikin motar?”

Washe baki su ka yi wata mai surutu a cikinsu ta ce, “Hajiya wallahi dadi motar nan ga wani sanyi da ke ratsa zuciyata kamar kada na fito.” 

Girgiza kai hajiyar ta yi tare da sakin guntun murmushi ta ce, “Ai irin wannan sanyin da kuke sha na A.C ne kuma in mun shiga ciki ma akwai A.C ko ina.”

Cike da jin dadi suka fito daga motar su biyar ne, kai ka ce wadanda aka kwato ne daga bakin kura kayansu sun yi uban squeezing, ga shi riga daban zane daban dankwali daban, takalman kafafuwansu wari da wari ne, ga wata irin kwalliya da suka dambara a fuskarsu, janbaki ya sauka daga saman labbansu har kumatunsu, kamar wasu mayu. Ga black point din da suka diddiga a hancinsu har izuwa goshinsu, sai faman soshe-soshen kai suke.

A haka take dauko su daga kauyen kayau ta gyara su ta sama masu gidanje aiki, a nan take samun kasonta ita ma.

Kallon buzun ta yi ta ce “Ka shigo mini da yarinyar.”

Sannan ta kalli ‘yammatan ta ce “Mu shiga ciki amma kusa ni duk wacce ta yi mini hauka kauyensu zan mayar da ita ta je can ta ci gaba da tallar fura a bakin kasuwa.” 

Cikin falo ta shiga da su a daidai lokacin ita ma yarinyar ta biyo su, nan fa suka fara kalle-kalle ganin yadda wurin ya hadu, har kokawa suke yi wurin yunkurin hawa saman lumbutsa-lumtsan kujerun da ke a ciki, dakatar da su ta yi ta hanyar yi musu tsawa, “Kul! Kada wacce ta hau mini saman kujeruna, ga carpet nan shimfide ku zauna, haba ku rinka abu irin na mata mana.”

Nutsuwa suka yi kowacce ta samu wuri ta zauna, ita da ma ba iri su ba ce da wayewarta wuri ta samu ta zauna ita kadai, yayin da su kuma suka cunkushe wuri daya kamar kifin gwangwani. Shiga ciki hajiyar ta yi tana kwalama mai aikin ta kira, “Larai, larai! Ina kika shiga haka gida sai ka ce ba kowa?” Karasowa ta yi tana hamma alamun daga barci ta tashi.

“Sannu da dawowa hajiya, wallahi barci ne ya yi awon gaba da ni da ma na sha maganin mura saboda ta takura mini.”  

Tabe baki ta yi ta ce, “Ni fa ban yarda da ke kullum shan maganin mura anya ba shaye-shaye kika fara ba?” Cikin zolaya ta yi maganar tana kallon ta, 

Dariya Larai ta yi ta ce, “Haba hajiya Allah ya tsare ni dayin shaye-shaye tsofai-tsofai da ni.” 

Murmushi hajajju ta yi “Ya yi kyau! Yanzu dai akwai abinci gidan na zo da yara ne daga kauye.”

Girgiza kai larai ta yi, “A’a hajiya sam ban yi tunanin yau za ki dawo ba ai, da na girka muku abinci.”   

A jiyar zuciya ta saki kafin ta ce, “Koma mene dai laifina ne da ban sanar da ke cewa yau zan dawo ba. Yanzu dai na san muna da bread, ko shayi ne ki hada musu da indomie.” 

Amsawa ta yi da, “To hajiya!” sannan ta juya ta nufi hanyar kicin din.

 

Hajiya ta nufi dakinta saboda tana bukatar ta d’an watsa ruwa ta canza kayan jikinta.

Rokon Allah yarinyar take yi a cikin zuciyarta, Allah Ya sa ta samu wannan aikin ko ta samu ta taimaki ‘yan uwanta wadanda suke cikin wani mawuciyan hali, muryar d’aya daga cikin ‘yammatan nan ta jiyo tana mata magana, “Ke kin iya kunna kallo ki kunna mana mu kalla.” 

Girgiza kai tayi alamar a’a, ba wai don ba ta iya ba sai don tsoron kada hajajju ta yi mata fada har ma ta kore ta ta hana ta samun aikin. Tana jin su suna cewa, “Karyar banza babu wani ta iya kawai ba ta kunna mana ne ‘yar bakin ciki.” 

Dagowa ta yi ta kalle su harara ta watsa musu ta ce, “E na iya ba zan kunna ba ne ba ku da hannuwa ne ku?” Tsit suka yi ganin yadda ta daure musu fuska sun yi tunanin ‘yar shiru-shiru ce, ashe ita ma ta iya fada. Fitowa hajjaju ta yi jikinta sanye da kayan barci, riga da wando ruwan madara, ta daure gashin kanta da ribbom, hannunta rike da waya kirar Infinix Hot 10, suna ganin ta suka gyara zamansu cikin natsuwa.

Wuri ta samu ta zauna a saman 3 seater, yadda za ta ji dadin yi musu magana, yarinyar na jingine jikin 2 seater wadda ke bangaren dama su kuma suna duban ta ta sashen hagu. 

A nutse ta soma magana, “Ku na riga da na yi muku bayanin komai ko?” Da’ga kai suka yi alamar e. 

Ta ci gaba da cewa, “Yanzu abin da ya rage mini shi ne na koyo muku yadda za ku gudanar da aikin naku don ba zai yi yu ku je gidan mutane a matsayin ‘yan aiki ba, a haka kaca-kaca da ku ba tsafta ba. Dole ne kusan yadda za ku tsaftace kanku, da tsaftar muhalli da kuma yadda za ku tsaftace abincin da za ku girka. Kuna bukatar sanin abubuwa sosai daga wajena, kuma insha Allah zan nusar da ku.” 

Ta mayar da idonta kan yarinyar ta ce “Yammata kin yi shiru ga shi ni ban san ki ba amma yanzu ina son na san me yasa kike nema na ne?”

Bude baki ta yi za ta fara magana amma ganin yadda ‘yammatan kauyen nan suka zuba mata ido kamar zomaye, hakan ya sa ta kakare ta kama in ina.

Muryar hajjaju ce ta sa su janye idonsu akanta, “Ku fa matsalarku ke nan sai shegen kallo salon gulma ko?” Sunkuyar da kansu kasa suka yi amma kunnuwansu na bude don su ji me za ta ce?

Cikin sanyin murya ta soma magana, “Da ma na ji an ce kina taimakawa ki sama wa yara aikatau shi ne na zo ni ma ki taimaka ki samo mini don Allah!”   

Dafe kai hajju ta yi da hannunta na hagu ta ce “Kash! Da na san wannan ya kawo ki da tun dazu na ce ki koma gida saboda yanzu babu wadanda suka yi mini magana akan na samo musu ‘yar aiki, wad’annan ‘yammatan da kika gani su ne kawai suka rage na mika su ga wadanda na yiwa alkawarin zan sama musu ‘yan aiki amma yanzu babu wani da ya yi mini magana. Ki yi hakuri ‘yata!” 

Tamkar an d’aga guduma an buga mata a kai haka ta ji, jikinta ya yi mugun sanyi tuni kwalla ta ciko mata a idonta, saboda ba karamin wahala tasha ba, kusan kullum tana fama zaryar zuwa gidan matar neman aiki, tunanowa da ta yi da halin da ‘yan uwanta ke ciki ne ya sa ta ji ba za ta iya hakura ba komai zai faru sai dai ya faru, amma ba inda za ta je sai ta samu aikin da za ta samu kudi, saboda ta san ba wanda zai taimake ta ya ba ta kudi haka nan don Allah face ya nemi wani abin daga gare ta. 

Tamkar za ta fashe da kuka ta ce, “Don Allah ki taimaki wallahi ko wane irin aiki ne zan iya yin sa. Ki taimaka mini ‘yan uwata na kwance asibiti  ba ta da lafiya kuma aiki za a yi mata, kudin da doctor ya fada ba mu da su kuma ba mu da wanda zai taimaka mana ni ce kawai nake fafutuka akan yadda zan samu na biya.”

 

Ganin yadda yarinyar ta bi tana rokon ta cikin lallami ya sa ta ji tausayin ta ya shiga ranta, “Ya isa haka, share hawayenki. Nawa likitan ya ce kudin aikin nata?”

“Dubu dari takwas ne.” Ta ba ta amsa tana kokarin goge hawayenta. Jinjina kai hajjaju ta yi jin kudin, “Da a ce ina da su da na taimaka da wani abu  amma halin da muke ciki yanzu komai tsada hakan yasa kudi ba sa jimawa a wurina. Amma yanzu abin da nake so na sani ina ne gidanku saboda dare ya yi sosai, na mayar dake gid, idan kuma za ki tsaya nan is shike nan in yaso gobe sai ki koma ko?”

Cikin sauri ta ce “Zan tsaya a nan, ba kowa gidan suna asibiti kuma na yi sallama dabsu babzan sake komawa ba har saibna fara biyan kudin aikin, babzan iya jure ganin su cikin mawuyacin hali ba!” 

Hajajju ta ce “To shike nan amma gobe zan bincika kuma za mu je asibitin tare saboda ba na daukar yaro ba tare da iyayensa ko wani nasa ya sani ba!” 

Yarinyar ta amsa da, “To!”

Larai ce ta shigo dauke da faranti, ta jera sinkin bread guda 3, sai jug mai dauke da tea da kananan kofuna, a jiye masu tayi sannan ta koma ta dauke sauran abin da ta hada musu a kicin.

Tun da y’ammatan nan suka ga bread suka gaza samun natsuw, sai kokarin zura hannu suke su dauka, ganin haka yasa ta taso da kanta ta rarraba musu ta bawa kowa nasa, dawowa larai tayi dauke da  karamin tray wanda ta baza musu taliyan a ciki ta ajiye masu,  zama sukayi suna ta aikin ci, ita dai a hankali take ci tana kallonsu hannu baka hannu kurya suke cunkusa wa a bakin, bakomai yazo mata a ranta ba face y’an uwanta, in ta tuna irin wannan yanayin sai taji komai ya fita ranta.

Bayan sun kammala ci , hajjaju ta kai isu zuwa bedroom din da ta ware domin irinsu in ta dauko su anan suke kwana sannan ta yi masu sallama ta fice, tana fita y’an matan kauyen nan suka haye saman bed din dake ciki kuma shi kadai ne, bin su da kallo tayi ganin yadda suka wawware kafafunsu saboda kar tasamu wuri tace zata hau.

Murmushi tasaki, “Allah sarki rayuwa ni ina ne bazan iya kwana ba, bed is ur problem, Sisters dina sune damuwata,

Cire  hijab din dake jikinta tayi, wardrobe din dake manne a bango, ta bude babu wasu kayan kirki a ciki, zannuwan atamfa ne kawai, saka hijab din tayi ciki ta rufe,  

toilet din dake ciki ta shiga, komai na ciki a tsaftace yake, fari kal! Gaban mirror ta karasa tana kallon fine face dinta, fanfo ta kunna ta tarba hannuwanta tana wanke fuskanta, bayan ta gama tasa hannu ta cire head din dake kanta, ta yi holding dinsa a hannunta tana kallon doguwar kitson kalabar da akayi mata guda biyu ta zubo tun daga head dinta har zuwa west dinta, tana da Yalwatacciyar sumar kai dark brown colour very smooth ga kwantaccen saken gefen fuska.

Fitowa ta yi daga toilet din, samunsu tayi sai minshari suke ja tamkar raguna, wardrobe din ta sake bude wa daya daga cikin zannuwan da ta gani ciki ta dauko, ta shimfida a kasa, ta kwanta

Washe gari tunda sassafe suka fita, hajajju ce ke driving yayin da yarinyar take a gefenta , sai kalle kallen hanya take ta glass din motor, hajajju ta ce “Har yanzu baki fadamun sunanki ba ! da age dinki yakamata nasani ko”? tayi maganar ne a lokacin da take kokarin juya sitiyarin motar wurin canza hanya tabi titin da zai kai ka har izuwa asibitin.

Murmushi yarinyar tasaki tare da cewa “Sunana SEHRISH amma Oumman mu tana ce mun RISHI , shekarata 17 cif ,” jinjina kai hajajju tayi tace “Wow nice name and it really deserves , ” cike da jin dadi Sehrish tace “thanks”  har suka isa asibitin basu kara magana , 

Sehrish tayi ma hajjaju jagora har izuwa ICU intensive care unit , inda aka kwantar da sisters din nata, lokacin da suka shiga ciki, da gugu wata kyakkyawar yar matashiya ta taso ta rungume sehrish, tsananin mamaki yasa hajajju sakin baki, sai ta dinga ganin tamkar mafarki take yi, tun da Allah ya halicce ta bata taba ganin yara masu shegen kama irin wadannan ba basu da wani banbanci ko miskala zarratin komai nasu iri daya sak , lokaci guda ta rikice takasa gane wacece ma suka zo da ita, wacece sehrish din don ta saje da dayar, hajjaju bata gama mamaki ba sai da taga dayar wadda take kwance saman gadon marasa lafiya ansa mata Oxygen dakyar take jan numfashi gwanin ban tausayi , nan takara rikicewa saboda itama wacce take kwancen Sak kamaninsu ba banbanci hakan na nufi su y’an uku ne kenan.

Kankame ta tayi tana kuka , itama sehrish din kukan takeyi hannunta tasa tana d’an bubbuga bayanta tace “Jahad ki daina kuka hankalina yana kara tashi komai zai tafi dai dai insha Allah, janye jikinta tayi daga nata tace “ina kuka ne ba don kai na ba sai don Husanna dr yace in ba mu fara biyan kudi an mata aiki ba , mutuwa zatayi kuma ynx haka kudin gado ya kare sallamar mu zasuyi ko kudin magani babu ,”  hankalin Sehrish ba karamin tashi yayi ba,

Hajajju dake tsaye tana kallonsu, jikinta yayi mugun sanyi saboda tsananin tausayi, ita kanta wadda sehrish takira da Jahad akwai wound a goshinta, anyi mata dressing da bandage duk jini a jikin sa , hannunta ma akwai kanula alamun anyi mata karin wani abu jini ko ruwa , a kagare hajajju take da taji labarin wadannan y’an ukun lallai bakaramar wahalar rayuwa suka sha ba.

Muryar Sehrish ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga “Jahad ga hajajju ku gaisa kuma kiyi mata godiya sbd  itace zata sama mun aikin da zan fara yi nasamu kudi nabiya ayi maku aiki,” matsawa tayi gaban hajjaju tana share hawayenta cikin girmamawa tace” ina kwana hajiya ,” murmushi hajajju tasaki tare da dafa kadarta tace “lafiya lou ya jikin naku “? Jahad tace “Alhamdllh ni da sauki husanna ce abun sai kara gaba yake yi don dr yace koda an mata aikin ba lallai ta dawo yadda ake so ba….” 

Kuka ne yaci karfinta har takasa karasa maganar , rungumo ta hajjaju tayi a jikinta tana lallashinta ” am sorry my daughter stop crying insha Allah everything will be ok , cikin kuka ta amsa da “zandaina mungde ssai ,” karasawa Sehrish tayi wurin husanna dake kwance rai hannun Allah , gefen gadon ta zauna tana kallonta idonta cike tab da kwalla tace “Allah ya baki lafiya yar uwata ina jin duk wani irin radadi da kike ji a zuciyarki wanda yayi sanadiyar shigarmu cikin wannan halin bazai taba gamawa da duniya lafiya ba Allah ya isa tsakanin mu dashi mugu azzalumi macuci …” a karshe ta fashe da kuka ta kwantar da kanta a saman jikinta , har cikin ranta take kukan.

Tsohuwar dake kula dasu ce ta shigo cikin sauri hannunta rike da magunguna da takarbo masu , a nan tasamu hajjaju tsaye ita da jahad tana lallashin ta , jin alamar shigowarta yasa suka jiyo suna kallon , cikin sakin fuska tace “Sannun da zuwa hajjaju ke ce da kanki ,” murmushi hajjaju tasaki dama sun son juna da alama , ” kwarai kuwa nice gwaggo dama ke ce ke rike da yarannan amma ni ban taba ganinsu ba gsky ,” murmushi gwaggo tayi tace “bakya leko mune shiyasa amma sun jima wuri na ni nake kula dasu ,”  jinjina kai hajjaju tayi tace “hakane amma gwaggo jikokinki ne su”? Goggo ta girgiza kai tare da cewa “a’a Allah ne ya hadani dasu nima labari ne mai tsawo , amma ynx bani da kwanciyar hankalin da zan zauna na baki shi , ki bari saina samu natsu,” tana gama fadan hakan ta mika ma Jahad magungunan “karbi nan naki ne dakyar nasamu kudi na siyo su,” godiya tayi mata ta karba , a tare suka taka izuwa inda sehrish ke kwance jikin Husanna , cike da nuna tsantsar tausayi hajjaju tace “Allah ya bata lafiya Allah sarki mutum baya sanin halin da duniya take ciki wani sa’in sai ziyarci asibiti nan zai ga marasa lafiya iri iri gwanin bantausayi hakika na tausayawa wannan yarinyar tana cikin hali Allah ya kawo musu sauki da duk marasa lafiyan dake fama da ciwo ,” amsawa sukayi da amin , har time din sehrish bata dago da kanta ba , ita kadai tasan yadda take ji aranta.

Hajjaju ta mayar da idonta kan Gwaggo tace “idan ba damuwa muje ki raka ni wurin likitan zanyi magana dashi ,” 

fita sukayi a tare , wuri Jahad tasamu ta zauna a chair din dake facing din gadon mara lafiyar, kallonsu takeyi su biyun tana kara jin kaunar y’an uwan nata , taji dadin zuwan rishi har cikin ranta , jajircewarta akan ganin sun samu rayuwar mai kyau yana kara mata ninkin son yar uwarta ta, tazama tamkar uwa agare su , alhalin ita age dinsu daya duk da tare suka zo duniya amma sun tsere wa rishi da mintina a wurin haihuwa ,  tunani iri iri ke zo mata a ranta runtse idonta tayi hawaye na kwaranyo wa daga idonta 

Gabad’ayansu sun shiga cikin yanayi , duk sunyi zurfin tunani , numfashinta suka soma ji da karfi da karfi wani irin sauti mai matukar razanarwa , a firgice sehrish ta dago da kanta cikin rudu ta furta “Subhanallah! jahad husanna ta cire oxygen da aka samata,” a rude jahad ta matso kusa da su hannu tasa ta tana kokarin mayar mata roban oxygen din , buge mata hannu tayi tana wani irin gurnani ga zufa sai ke to mata take yi ga wani irin tari da take yi cikin kuka take ambaton “Seh..seh..sehrish ,” 

Dakyar sound din ke fita , hakan ya tambatar masu da cewa so take tayi ma Sehrish magana amma takasa , matsawa sehrish tayi kusa da ita tare da sa hannu tana shafa mata gefen fuskarta cikin kuka tace “pls husanna kiyi hkr kinji Allah zai baki lafiya , nasan mai kike ji a zuciyarki, zanyi kokari koda zan rasa raina ne wurin ganin kin samu lfy , wlh sai inda karfina ya kare , ina sonki sosai my sister,” gaba dayansu kuka sukeyi , mayar mata da roban oxygen din Husanna tayi , bin ta su kayi da kallo ganin tana kokari kakaro murmushi a fuskarta , wani sabon kukan suka sake fashe wa dashi.

“Yar’uwata kada ki tafi kibarni ni nafiso na mutu a gabanku dan Allah kada ki tafi ,” lokacin da sehrish ta tuna da wannan kalami na Husanna sai jikinta ya kara mutuwa lukus , kamar ba kasusuwa a jikinta, zamewa tayi ta zauna kasan tiles din tare da jingina kanta gefen gadon , wasu abubuwa ta dinga tunawa arayuwarsu wanda in har taci gaba da tuna su to tabbas zuciyata zata buga ne!  komai ya dawo masu sabo fal , komawa Jahad tayi ta zauna tana shesshekar kuka hada majina a hancinta ,  

Hannun husanna taji cikin nata , dayake ta aza hannun nata a saman bed din, ta rike shi gam cikin nata , dagowa sehrish tayi da fuskanta wadda tayi jawur , ga idonta sun kada , fuskarta tayi kwaba kwaba cikin kasalalliyar murya tace “Husanna ki daina zubar da hwayenki nasani abun da ciwo , zafinsa yakai kunar wuta amma ki daure pls , ba irin whalar da bansha ba wurin ganin nasamu kudi an miki aikin nan ke da jahad especially ke , kai karshe ma an kokarin bada kaina nayi amma dana tuna abunda mama ta fada saina gaza , duk da haka ban hkr ba na soma kokarin samun wanda zai siye ni yabani kudi kawai na kawo muku ni natafi amma saina tuna cewa in na tafi wazai kula daku ? duk da nasan akwai Allah shine gatan kowane bawansa …’ muryarta ce tashaqe ta gaza idasa maganartata saboda kululun bakin ciki daya tokare mata makoshinta .

Jahad da ke sauraron maganar yar uwarta su sai taji wani sabon kukan ya balle mata,  domin duk wannan gwagwarmayar da Sehrish tayi sam basu sani ba a boye tayi kayanta.

Sun sha kuka kamar ba gobe nima na tayasu kukan duk da bansan takaimaiman tarihin rayuwarsu ba da kuma dalilin kukan nasu.

A haka goggo da hajjaju suka same su gwanin ban tausayi , wayar hajjaju dake cikin yar purse dinta sai ringing take yi don haka tace ma serish ta taso su tafi , cikin kuka ta tashi a hankali take tafiya tana waiwayansu , goggo tace ” kada ki damu rishi hajjaju ta biya mana kudin gadon kuma tace zata samu koda bashi ne a fara biyan kudin aikin inyaso daga baya kin fara aikin kin samu sai ki biya,” 

Ba karamin dadi sehrish taji ba , haka jahad ma godiya suka shiga yi mata , a karshe tayi masu sallama suka tafi , 

Har a cikin motan kuka takeyi dakyar hajjaju ta lallashe ta tayi shiru….

Time din da suka dawo , larai  na kitchen ita da y’an matan kauyen nan tana koya masu wasu abubuwan daya kamata su sani.

A falon suka zauna gaba daya jikinsu a sanyaye, sehrish na zaune kasan carpet jingine da 2 seater , tana sauraron abunda hajjaju zata ce , 

magana ta soma mata “Sehrish ni yanzu bansan ya zanyi dake ba, game da aikin nan m, gashi ni already ina da y’ar aiki kuma gsky ko da ace ban da ita, ba zan iya daukarki sbd kina bukatar kudi masu yawa ni kuma iya salary din da nake biyan larai 10k ne.”

*Comment And Share*

Back to top button