Uncategorized

Abban Sojoji Chapter 46 Book 2 Complete Novel

 

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

_💋Boss Bature💋_

*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃

*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI.  MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*

*LOCATION KANO*

08062073990

11:30 na dare

Fitowarta kenan daga toilet jikinta ɗaure da towel,ba ƙaramin canzawa tayi ba gaba daya ta sauya saboda hutun da take samu ga kuma kwanciyar hankali,tun daga kan natural skin colour dinta zaka gane hakan,yanzu bata wasa da tsaftace jikinta kullum cikin ƙamshi take,

  Ƙarasawa tayi gaban mirror tana cigaba da tsane jikinta da towel ɗin hannunta,bayan ta kammala tayi hanging dinsa daga gefen mirror din,sannan ta kai hannunta jikin drawer chest na mirror,janyowa tayi tare da zura hannunta ta ɗauko hand dryer,jona ta tayi ajikin socket nan take ta soma buso da iska, cikin sauri ta kanga ta saitin kanta taci gaba da busar da gashinta,cikin nishaɗi take yi saboda ta mayar da abun tamkar na wasan yara, natsuwa tayi tana tunano abunda suka tattauna da Azmee acikin kitchen bayan ta sanar da ita maganar da sukayi da abbansu nacewa tafara kamun ƙafa tun daga yanzu,

  dariya sosai azmee tayi tare da cewa”Abba da zolaya wato in marks dinki yazo da F shine zai aura maki haroon gsky kwara ki dage,”

  Murmushi sehrish tayi tare da cewa”Amma aunty azmee ya akeyin kamun ƙafa inaso na iya”?

   ɗan gyaran murya azmee tayi kafin tace”Kyautatawa mana,kinsan ita zuciya nason mai kyautata mata,kamar abbansu atlease yakamata ace duk safiyar Allah kina zuwa har bedroom ɗinshi kina miƙa gaisuwa hakan zai ƙara maki daraja a idanunshi kuma zai tabbatar da cewa kina da tarbiyyya sosai,sannan 6angaren girki yakamata ace ma yanzu kinfi ni iya girki,tuntuni dama inaso nayi maki magana akan koyon girki,saboda maza nason macen da ta iya girki,kin ga mazan gidan nan basa wasa da abinci akwai son cin mai daɗi,shiyasa nake da kusanci dasu sosai saboda yarda nake masu girki,don haka kema daga yanzu ki fara trying bafa dole sai irin nawa ba a’a salo na daban yakamata ki koya,bari na baki satar amsa kamar abincin gargajiya haka namu na hausawa saboda a gidan nan sunfi sabawa da abincin turawa,yakamata ki fara jaraba yi masu shi,ki koyi sarrafa abinci kala kala hada abunsha da kuma irin kayan makwalashe haka da sauransu,sannan 6angaren tsafta domin kuwa itace gaba da komai,idan ma kina da tsafta to ki ƙara akan wadda kike da ita,saboda mazan gidan nan basa son ƙazanta ko miskala zarratin,tun daga kan tsaftar jiki yakamata ki fara kulawa,wurin yin shaving na armpit dana under,da kuma kula da teeth dinki wurin yin brush akai akai banda barin datti ajiki,da kuma kula da gashin kanki wurin gyare shi,hatta nails ɗinki ki runƙa kula wurin yankesu banda tara akaifa,ina fada maki wannan ne domin amfanin kanki,don ita mace da tsafta akasanta da son ado,inaso kema ki kasance haka………

  Sosai azmee ta koyar da ita abubuwa da dama na rayuwa waɗanda zasu amfane ta,kuma tun daga lokacin duk in suka shiga kitchen suna aiki tana ƙara ilmantar da ita,hakan yasa sehrish ta soma canzawa sosai, yanzu kullum cikin gyara kanta takeyi,sannan bata wasa wurin koyon girki dalilin hakan yasa tashiga whatsapp grp na koyon girki,kullum tana cikin ɗaukar videos ɗin girki tana kallo donta koya,a hankali a hankali yanzu harta fara jin zata iya jaraba yi masu abinci acikin gidan 😇

 murmushi ta saki bayan ta kammala tunanin a fili tace”bansan da wasu kalmomi zan iya godema aunty azmeena ba,saboda tagama yi min komai a rayuwa ina jinta tamkar mahaifiyata ne,Ya Allah ka barni da aunty azmee na,”❤

   jin alamar shigowar motocinsu yasa ta yin saurin cire hand dryer ɗin daga socket ta mayar da ita inda ta ɗaukota, sannan ta taka izuwa wurin wardrobe ta buɗe tana neman kayan da zata sanya,wurin jerin kayan baccinta ta duba,wasu riga da wando ta dauko ƴan qasar indonesia masu matuƙar kyan gaske ga laushi jikinsu,launinsu maroon colour ne masu ɗigon baƙi baƙi ajikinsu, cikin sauri ta zurasu ajikinta sannan ta ɗauki mayafi tayi rolling dinsa akanta, sai da ta tabbatar da cewa sun shigo ciki kusan 15 mins ta ƙara sannan ta buɗe ƙopa tare da fitowa daga ɗakin nata,ƙafarta na sanye da flat shoes,miƙo hanya tayi tana tafiya a hankali ta biyo ta main palour din babu kowa har sun wuce ciki,kitchen ta wuce don ta haɗa mashi tea tare da kayan marmarin dayake buƙata kamar kullum,

Tare da Marshal Omar suka bar gidan,amma SGR ne kawai ya dawo saboda Omar ya wuce wurin su Hossana,tun akan hanya suka rabu dashi,

a galabaice ya shiga part dinsa saboda rashin jin daɗin jikinshi dayake yi,tun safe bai da lafiya amma saboda juriya irin tashi da ƙarfin hali ba wanda ya lura da hakan,wani irin sever headache tare da zazza6i mai zafine ya rufe shi,

Jikin shi na sanye da Army trouser tare da shirt light green colour,kai tsaye yana shiga bedroom dinsa ya faɗa saman bed dinsa batare da ya rage kayan jikinshi ba,saboda rashin ƙarfin jikin shi da yake ji,abun yazo mashi wani iri saboda kafin yayi ciwo da wuya mutun ne mai cikakkiyar lafiya,sam bai sanarwa kowa ba saboda baya son tayar masu da hankali kuma baison aga raunin shi,

Sehrish

Fitowa tayi daga kitchen ɗin hannunta ruƙe da tray mai ɗauke da ƙayataccen plate na fruits sai cup mai ɗauke da Hot tea sai faman tiririn Zafi yake yi,a natse take tafiya kai tsaye ta nufi stairs ɗin tana cikin tafiya kamar daga sama taji muryar haroon yana cewa”Wurin Namiji za’a ne”? A wani irin firgice ta juya tana neman ta inda zata ganshi,

  Yana zaune saman 3 seater shi kaɗai abunshi jikin shi na sanye da night dress riga dai dai guiwa,ya aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya yana faman sakar mata murmushi,

    Ba ƙaramin tsoro ya bata ba saboda bata tsammace shi a wannan lokacin ba,cikin sauri ta wuce upstairs gabanta na faɗuwa aranta tana cewa”Anya haroon Ba Aljani bane?in ba haka ba yaushe har ya shigo babban falon nan amma banga gifcin shi ba,” tana tafiya tana sambatu aranta har ta ƙarasa part dinsa, sai da ta tsaya tare da dai daita natsuwarta sannan tashiga ciki, wayaam babu kowa a falon hakan na nufin yana a cikin bedroom dinsa,

Takawa tayi a hankali har zuwa ƙopar bedroom din nashi sannan tayi sallama,kusan sau uku ba’a amsa mata ba sai a na huɗun ne taji muryarshi ƙasa ƙasa ya amsa mata “come in,”

  a hankali tasa ƙafarta tashiga ciki,lokacin da ta ɗago da idanunta nan take taji faɗuwar gaba rasss!yanayin da taganshi yayi uban goho saman gadon yana fitar da numfashi daƙer daƙer ba ƙaramin tayar mata da hankali yayi ba,tuni jikinta yayi mugun sanyi,ƙarasawa tayi ciki tare da ajiye mashi tray din saman table tace”Sannu da dawowa ga tea nan na kawo maka,ko akwai wani abu da kake buƙata”? shiru bai bata amsa ba sai numfashi kawai da yake fitarwa mai hucin zafi,bin shi tayi da kallo sumar kanshi ta rufe dukkan fuskarshi side by side,tana so ta tambaye shi ko lpy amma tana jin tsoro,

  Kusan 15 mins tana a tsaye bai ce komai ba ƙoƙari yake ya tashi amma sam jikinshi ya hana shi,sai da yayi dagaske sannan ya samu ya miƙe tare da matsowa ya sauko da legs dinsa ƙasa idanunshi a rufe rufff,fuskarshi ba ƙaramin canzawa tayi ba,jikin shi sai kerma yake yi tamkar wanda yashiga snow hatta pink lips dinsa sun gaza tsayuwa,tsananin tausayin shi ne ya kama sehrish saboda ta tabbatar da cewa bai da ƙoshin lpy sbd alamomin da tagani atattare dashi,tuni taji hawaye na ƙoƙarin zubowa daga idonta,

  muryarshi ce ta tsinkayeta da cewa”ki duba a cikin side drawer ɗina thete’s a jotter wit pen pls bring it 4 me,” cikin sauri sehrish ta matsa tare da kai hannu jikin side drawer ɗin,ta janyo gida na farko ajikinta, anan ta samu Jotter ɗin tare da biro,ɗaukowa tayi tare da miƙa mashi,

  daƙer ya cire hannunshi ya kar6a har lokacin eyes ɗinshi na’a rufe,aza jotter ɗin yayi daga gefen table ɗin gabanshi,buɗe papers din ciki yayi kafin ya aza biro din ya soma rubutu bayan ya kammala yayi tearing wurin da yayi rubutun ya ɗauko takardar ya miƙa ma Sehrish,cikin sauri tasa hannu ta kar6a tare da aza idonta kan rubutun wani irin handwritting gare shi domin koda ta kalla ko *A* bata iya ganewa ajiki ba hakan yasa ta kalle shi tare da cewa”Bangane menene ka rubuta ba,”ta faɗi a ɗan tsorace

“Go nd bring it 4 me,” shine kawai abunda ya iya furta mata,

Cikin sauri sehrish ta kama hanyar fita daga bedroom ɗin nashi tana waiwayonshi,

  Saukowa down stairs tayi tana faman cizon yatsa saboda tarasa gane menene ya rubuta mata,tamkar zatayi kuka,tana cikin wannan halin muryar haroon ta katse ta da cewa”Can I help u”? ɗagowa tayi aɗan razane tana kallon shi,fuskarnan tashi nadauke da murmushi yasa hannu ya kar6i takardar yana duba rubutun jiki,daga bisa ni yace”Ki jira ni anan yanzu zan dawo,” yana fadin hakan yajuya da sauri ya shige part ɗinsu na nan downstairs,

   ajiyar zuciya ta saki aranta tana Allah Allah saboda tsoron kada haroon ya tafka mata kuskure don tasan halin shi,bai da tabbas gajiya da tsayuwa tayi,don haka ta samu wuri saman last step na benen ta zauna tana jiran dawowarshi,. 

Ba da jimawa ba sai gashi ya fito daga part din nasu, sai faman sauri yake yi irin da himmar nan hannun shi na ruƙe da syringe da kwalbar injection,tunkan ya ƙaraso sehrish ta miƙe tare da sa hannu ta kar6a tana yi mashi godiya,,

 

  da buɗar bakinsa sai cewa yayi”Ba sai kin gode mun ba,Aikin lada ne fa nidae burina ki kai mashi allurar ya hanzarta yi yanzu,in ma godiyar ce gobe da safe kinzo ki same ni kiyi mun ita,” yana magana yana sakin wannan shu’umin murmushin nasa,

jiki asanyaye tasa hannu ta kar6a tana kallon fuskarshi shima kuma ita yake kallo da wannan murmushin nashi, cikin sauri ta juya tare da hayewa upstairs cikin sauri take tattaka matattakalar benen har ta wuce part dinsa

Ruƙe qugu haroon yayi tare da sakin wani irin bazawarin murmushi yace”Lokacin Bacci yayi bari naje na kwanta gobe da safe akwai labari zazzafa,ƴar shila zata zo miƙo mun godiya da kanta,” ya fadi tare da sakin dariya ya wuce sashen shi 

  Lokacin da sehrish ta koma ɗakin nashi yarda tabarshi haka ta same shi zaune idonshi a rufe, cikin sauri ta ƙarasa tare da miƙa mashi allurar da sirinjin tace”Ga allurar,” hannu Sgr yasa ya kar6a daƙer ya iya buɗe idonshi sam baya iya gane wace kalar allura ce yarinyar ta kawo mashi saboda idanunshi biji biji suke gani hakan bai bashi damar karanta abunda aka rubuta ajikin ƙaramar kwalbar allurar ba, 

   fasa bakin kwalbar yayi tare da curo sirinjin ya fiddo da kan allurar ya tsoma acikin kwalbar ya zuƙo ruwan allurar iya yadda yasan ya dace yayiwa kanshi, 

.Tuni jikin sehrish ya soma rawa saboda tsoron allura gareta,cikin sauri ta kama hanyar fita daga dakin saboda ta bashi damar yin allurar,

  Muryarshi ce ta tsinkayeta da cewa”kada ki tafi,” ya furta yana faman sakin huci daga bakin shi da hancinsa,

A bakin ƙopar ta tsaya idonta a rufe jikinta na kerma,muryarshi ta kuma ji yace”ki zo,” cikin sauri ta koma ajiyar zuciya tasaki ganin harya kammala yin allurar, miƙa mata kwalbar allurar yayi tare da syringe din duka yace”kisa a dustbin,” amsa mashi tayi tare da kar6a ta wuce wurin bedroom dustbin dinshi ta saka tarkacen allurar, sannan ta dawo ta tsaya tana jiran jin ko zai buƙaci wani abu tunda ya nuna baison ta tafi,

  Lokacin da allurar ta gama gauraye ko’ina na jikinshi da wani irin ƙarfi ya ware idanunshi azare,har sai da sehrish taɗan ja da baya saboda firgitar da tayi,bin yatsun hannunshi tayi da kallo ganin yarda yake wawwaresu suna miƙewa tsaye,tamkar dae yadda mutun ke komawa Zombie acikin film,gabanta ne yashiga faɗuwa saboda tsoran da taji murya na rawa tace”Zan iya tafiya”?

  ɗagowa yayi da wannan sexy blue eyes din nashi da launinsu ya ƙara Cizawa gwanin ban tsoro kai kana ganinsu kasancewa akwai matsala,ido cikin ido yake kallonta batare da ya kawar da idonshi ba hakan yasa zuciyarta ƙara karaya ga wani irin fargaba daya zo mata,ganin irin kallon da yake yi mata ne yasa nan take tadinga jin bugun zuciya,ja da baya ta soma yi jikinta na kerma har lokacin bai janye idonshi daga kanta ba bin ta kawai yayi da kallo,sai da taga taɗanyi mashi nisa sannan ta nufi hanyar fita daga bedroom din nashi da saurin gaske sai dai ina, kafin ta Ankara tuni SGR yayi wani irin kwakkwaran motsi tare da miƙewa tamkar wani Zaki ya bi bayanta azafafe yakai ma Waist ɗinta wani irin ruƙo ya ɗaga ta sama gaba ɗaya ta saki wata irin razananniyar ƙara mai rikitarwa bata gama rufe bakinta ba yayi wani irin wurgi da ita kai tsaye ta faɗa tsakiyar gadon shi yaraaaff tuni mayafin da tayi rolling dashi ya jima da barin jikinta !!!! Ba ƙaramin buguwa sehrish tayi ba daƙer ta iya tayar da kanta daga jikin bedmattress ɗin ta ɗago hankali a matuƙar tashe take kallon shi ganin yasanya hannayenshi tare da ruƙo shirt ɗin dake ajikinshi ya cire ta gaba ɗaya tare da yin wurgi da ita ƙasa,

   gabanta ne yasake yin wani irin mugun bugu tuni hawaye sun soma wanke mata fuskarta cikin tsananin tashin hankali take girgiza mashi kai tana cewa”innalalahi wa’inna ilaihirraji’un nashiga uku !!!!”

   Sam babu alamar sassauci a tattare dashi kai kana ganin yanayin action dinsa zakasan cewa ba a hayacinshi yake ba, Hatta ƙarfin jikinshi bana shi bane a matsayin shi na wanda bai da Cikakiyar lafiya, Ganin ya zame belt ɗin wandon jikinshi gaba daya yayi throwing dinsa, tare da sa hannu yana ƙoƙarin zame wandon dake jikinshi, hakan ya ƙara tsoratar da sehrish yunƙuri tayi da ƙarfi zata diro daga saman gadon ta gudu,aikuwa batayi wani aune ba taji saukarshi saman gadon gaba ɗaya ya afka mata tare da yi mata Rumfa da faffaɗan ƙirjinshi tsulundum taji ta ajikinshi,🙆🏽‍♀

  nan fa ido ya raina fata,dukkan ilahirin jikinta rawa yake yi gaba ɗaya tagama rikicewa muryarta har wani shaƙewa take yi wurin cewa”Dan Allah kayi haƙuri kabarni na tafi,ni nasan cewa ba halinka ba….ba yin kanka bane…….’ kasa ƙarasa maganar tayi saboda idonshi dake kallon cikin kwayar idon nata,SGR fa a halin yanzu zamu iya cewa baya ji baya gani,

   Wani irin huci yake yi yana groaning just like a hungry lion,runtse idonta tayi saboda bazata juri kallon cikin nashi ba yayin da idonta ke cigaba da zubar da hawaye………..🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♂️😳

Zuwa ga masu share na littafina lokacin da mutun zai sayi littafin nan ba muyi yarjejeniya nacewa zai turama wasu ba, amma sai gashi grp ba iyaka ana tura littafin koma waye yaje don kanshi kuma yasani akwai haƙƙina akanshi👍ya Allah kashiga tsakanina da koma waye, 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

*************

It’s not just good …it’s finger linking good faster than fast food, better fine dining.

Snack

Awarah 

Farah

Zobo

Samosa 

Cup cake etc 

Contact me 09063302182or 09012179727.

Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka 

Wadrobe balls 

Madarar kulleccham 

Vaseline kulleccham 

Kajiji

Halut

Couscous 

Khumrah 

Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku😍

Back to top button