Uncategorized

 

Wasu daga cikin matasa na kasar Nijar sun fusata inda suka bayyana cewar in har ba a dauki mataki akan mawaki Adam A Zango da Ado Gwanja ba to wallahi sai sun tada hargitsi domin kuwa inhar ba a dauki mataki daya kamata ba su zasu shiga har inda suke sun fito da su sun dauki mataki da ya dace da su.

Sanin kowa ne cewa duk wani mutum mai hankali da nutsuwa bazai yi abin da zai sa ya kashe mutum da gangan ba, ko kuma ya cutar da rayuwar wani ba, dole sai dai wannan abu ya zama cewar an yi shine ba bisa son rai ba, ma’ana Allah ne ya kawo shi.

Tabbas ahalin yanzu  ya kamata mahukunta na kasar Nijar da su dauki mataki akan mawaki Adam A Zango da Ado Gwanja tun kafin wadannan fusatattun matasa su dauki doka a hannun kamar yadda suka ambata, domin ba zai wa kowa dadi ba.

Da yawa daga cikin mutane ahalin yanzu sun soma tunanin cewar don anga Adam A Zango da Ado Gwanja sanannun mutane ne shi ya sa ake son a fitar da su, kuma ana tunanin idan aka yi masu wani abu na ba daidai ba to za’a iya fuskantar ɓacin rai, wannan ne yasa ake son bin lamarin a hankali har a ɓatar da batun. To wannan ne dalilin da ya sa wannan mutane suka fito wannan zanga zangar, sannan suka nuna wa duniya cewa inhar ba a dauki mataki ba to sufa za su dauka da kansu akan wadannan mutane guda biyu.

Mutanen Nijar da Nigeria dai sun kasance mutane ne dake matukar son junansu, wanda za ka ga inhar dan Nigeria ya ziyarci Nijar to zaka ga suna matukar mutunta shi, har ma su yi masa abin da bai yi tsammani ba saboda iya tarbar baƙin su, Amman kuma ahalin yanxu da wannan abin ya faru mutanen Nijar bazai masu dadi ba domin kuwa suna ganin cewar su idan nasu yaje wannan garin suna mutunta shi taya za ayi ace anxo garin su an masu ba daidai ba, amman baza a dau hukuncin daya dace ba akan wadannan mutane ba, kodan anga su wadannan mutane suna da wata daukaka ne shi ya sa ake nema a ki dauka matakin komai.

Za ku iya kallon cikakken bidiyo a manhajar youtube


Ga dukkan alamu in har ana son zaman lafiya a kasar Nijar to dole gwamnatin Nijar sai ta dauki mataki akan mawaƙa guda biyu wato mawaƙi Adam A Zango da kuma abokinsa Ado Gwanja.

Zamu so jin ra’ayin yinku a kasan wannan Labari.

Back to top button