Sirrin Rike Miji

Yadda Ake Turaren Wuta Dan Mai duguri

Daga Amina Yusuf Gwamna

Turaren wuta ana yin sa ne da itace, domin turara ɗaki, da dukkanin jiki da na tsugunno, da kuma na sutura. Ana zuba shi cikin gaushi (garwashi) ne a kasko. Nan da nan kuwa ka ji ƙamshi ya gauraye ko’ina a cikin gida. Daga cikin Itatuwa da ake turare da su kuwa Sun haɗa da:

  • Icen Sandal
  • Ice, Hawi
  • Icen Gab-Gab
  • Icen Durot

Da dai Sauransu.

 

Karanta>>> Ga Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah

 

Ana yin turare na soyawa kuma ana yin na jiƙawa. Ya danganta da buƙatar mutum.

 

Larabawa da kuma mutanen Maiduguri ne suka fi shahara wajen amfani da turaren wuta. Mazansu na taimakawa sosai, su siya wa matansu turare akai-akai. A wajensu tamkar dole ne amfani da turare . Mace ba ta da daraja sai da kasancewa cikin ƙamshi a kodayaushe.

 

Karanta>>> Yadda Zaki Kara Girman Kugu Cikin Sauki

 

KAYAN TURAREN WUTA

  • Icen Hawi
  • Matan Arewa
  • Farce
  • Misik
  • Alhaji Abdullahi
  • Salamalekum
  • Sasorabia
  • 20 fragrances
  • Madara turare (8)

Karanta>>> Amfanin Hulba Guda 21 Ga Lafiyar Jiki Musamman Yan Mata Da Matan Aure.

 

YADDA AKE HAƊAWA

Za a sa icen Hawi a turmi a daddaka shi sama-sama. A sa icen gab-gab shima haka. Sai a juye su cikin mazubi. A dauko ruwan turare Matan Arewa a zuba a kan itatuwa. A juye Soyayyen farce. A zuba Misik. Sai a ɗauko turaruka: Alhaji Abdullahi, da salamalekum, da Sasorabia, da 20 fragrances. Kowanne a buɗe a juye. Sai kuma a dauko madarar turare masu matukar ƙamshi a zuba su. A juya da kyau ko’ina ya samu ya haɗe . A samu mazubi a juye a ciki. Kuma a rufe shi sosai.

 

Karanta>>> Tusar Gaba Da Abinda Ke Kawota Yana Da Kyau Ku Karanta Wannan Bayanin

 

Littattafai da aka duba:

Taron karawa juna ilmi.

Hikimomin Kulawa da Mai gida.

Mu Koyi Sana’a.

7th Nuwanba, 2015,

Gidan Mumbayya, kano.

Back to top button