Health

Amfanin Aduwa ga lafiyar mu.

Amfanin Aduwa ga lafiyar mu.

Idan ka karanta ka turawa sauran yan uwa domin su amfana.
Itacen Aduwa sanannen abu ne a kasar Hausawa musamman a karkara – Shi dai ‘ya’yan aduwa ana tsotsan sa ko kuma sha – Man shi da ‘ya’yan shi ana amfani dasu wajen magunguna da dama Itacen Aduwa itace ne dake fidda kwallaye masu matukar amfani a jikin mutum.

Aduwa ta yi matukar suna a kasar Hausawa musamman a karkara. Shi dai wannan ‘ya’yan aduwa tsotsansa akeyi ko kuma sha. Bayan sha da ake yi akan tatsi mai daga kwallan Aduwa.
Ana kiranta da ‘Desert Date’ da turanci. Bincike ya nuna cewa tsoson kwallon,man dake cikin ‘ya’yan, sannan kuma ita kan ta itacen na da muhimmanci.

Karanta>>> Amfanin Hulba A Jikin Yan Mata Dama Matan Aure.

Ga amfanin Aduwa a jikin mutum kamar haka:

1. Aduwa na kawar da cutar asma.

2. Mai fama da atini da zawo zai samu sauki idan ya tsotsi Aduwa

Karanta>>> Yadda Za’a Yi Amfani Da Kanunfari Wajen Magance Ciwon Sanyi

3. Aduwa na kawar da tsutsar ciki.

4. Yana maganin ciwon shawara.

Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata

5. Aduwa na maganin farfadiya.

6. Man kwallon Aduwa na rage kiba a jiki, idan ana girka abinci da shi.

Karanta>>> Amfanin Dabino Da Kuma Magungunan Da Yake Yi Guda 50

7. Yana warkar da ciwo a jiki musamman idan ciwon ya zama gyambo.

8. Man Aduwa na maganin sanyin kashi da kuraje.

Karanta>>> Maganin Toilet Infection Da Kuma Rashin Sha’awa Ga Mata

9. Yana kawar da kumburi.

10. Yana kawar da matsalar yin fitsari da jini.

Karanta>>> Amfanin  Zobo Ga Lafiyar Jiki Da Kuma Illolinsa

11. Man Aduwa na gyara fatar mutum da hana saurin tsufa.

12. Yana kuma kawar da ciwon bugawan.

Karanta>>> Ina Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah

Allah yasa mu dace.

Back to top button