Kimiya da Fasaha

Masu Amfani Da GB WhatsApp Suna Cikin Haɗari Inhar Kana Amfani Da GB WhatsApp Ya Kamata Ka Karanta Wannan Bayanin.

Masu Amfani da GB What’sApp saboda a dinga leken asiri ga shawarar da zan baku..🙄

 

Mutane da yawa suna amfani da GBWhatsapp ne, saboda yana wasu tsaruka da Whatsapp na asali ba shi da su, misali saving na hoto, bidiyo, ko kuma kwafin rubutu daga status na mutane kai tsaye, ko boye alamar karantawa ko karbar sako, ko don yana nuna alamar in mutum na online, ko don tura file mai nauyi, ko boye groups/chats, ko rubuta sunan group da harafai sama da 35, ko yin status da harrafai 250; a takaice dai GB WhatsApp yana da wasu features da Normal Whatssp namu na gargajiya ba shi da su..🙄

 

Amma, ka san duk wadannan tarko ne na masu datse (hackers)? Sun tsara shi ne ta yadda zai baka sha’awa sosai, fiye da manhajar ta asali (normal Whatsapp), tare da baka damar wasan boyo da ma’abota amfani da Whatsapp, (kana leken asiri) musamman ma yan uwa mata, ka tura mata sako, ta karanta, amma ba zaka ga alamar ta karanta ba, sannan ta duba status dinka ba tare da kaga alamar ta gani ba..

 

Maganar gaskiya babu boye-boye GBWhatsapp, “mod” ne; abinda ake nufi da “mod” shine ba asalin Whatsapp ba ne. Asali an kirkire shi da “code” irin na Normal Whatsapp na gaskiya, ba tare da samun lasisi daga kamfanin ba.

 

Ina mai baiwa masu amfani da GB WhatsApp shawara da su kauracewa manhajar saboda dalilai kamar haka:

 

1. Na farko, GBWhatsapp ba sahihi ba ne daga asalin kamfanin Whatsapp, ‘AlexMods’ ne suka yi shi, ba su da lasisi, kuma sun karya ka’idar kirkirar da bada lamunin amfani da sirrikan jama’a, shiyasa ba zaka sami manhajar a Google Playstore (apk) ko AppStore (iOS, na Apple) ba, ka ma taba ganin wani adireshi na yanar gizo na GBWhatsapp? Amsa babu, saboda ba su da gaskiya.

 

2. Na biyu, kai da kake amfani da GB WhatsApp ko ke da kike amfani dashi ki ko ka sani, duk wasu bayanai da suke cikin wayarku wannan manhaja na iya tattarewa, babu wani sirrin cikin wayarka da ba za su iya lekawa ba, siyarwa, ko suyi amfani dashi su dinga rokon mutanenka kudi a matsayin anyi maka hacking ko suci maka bashi a duk lokacin da suka dama.

Karanta>>> Sabbin Code Da Layin Mtn Suka Canza

3. Na uku, idan aka turo ma wani sako mai dauke da “Virus” GBWhatsapp ba shi da wasu matakan kare ka daga cutarwarsu. Shi ma kansa “spyware” ne mai hatsari..

 

4. Na hudu, duk abin da kakeyi a GBWhatsapp, tamkar tsirara kakeyi, yawanci wadanda ake musu kutse (hacking) ta Whatsapp, masu amfani da Whatsapp Mods ne, irin su GBWhatsapp, WhatsappPlus, Whatsapp Gold, Cleons, FMWhatsapp, OGWhatsapp, YO… da sauransu.

Haka kwanaki akayi ma wata yar’uwata hacking nata GB whatssp din aka dinga demanding kudade wurin yan’uwanta manyan kudade kuma suka dinga turawa, da ta kirani ta sanar dani da kyar da zufar goshi muka samu muka karbo shi.

 

5. Na biyar, GBWhatsapp baya backup (dawo da bayanai), kamar yadda na fada a farko, asali manhajar ta sabawa tsarin Google, kuma ana backup ne yawanci da Google account, shiyasa da zaran ya yi expire wani lokaci zaka rasa duk bayananka, har groups da kake ciki, sai ka nemi a maida ka.

 

6. Na shida, idan ka lura a duk lokacin da ka dauko shi daga yanar gizo, in dai wayarka tana “security patching” wato kula da tsaro, zata maka warning cewa wannan app din zai iya cutar da kai, ko bayananka; tsakaninka da Allah baka taba lura da hakan ba? In ka taba lura da haka, don me zaka sa kanka a halaka?

 

Kar ku yaudari kanku GBWhatsapp na mayaudara ne, in ba su cuceka yau ba, za su iya cutar da kai gobe. Kuma ma inaso kasani a kowanne lokaci Whatsapp na asali za su iya dakatar da mai amfani da ‘mods’ daga amfani da dandalin..

Allah yataimaka… 🙏

 

✍️Salisu Abdurrazak Saheel

Back to top button