Hausa novels

Wace Ce Ita (Who Was She) Chapter 77 Complete Novel

WACECE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

                  Unique Barakancy🌹

SEVENTY-SEVEN📍

 

EID MUBARAK TO THE ENTIRE MUSLIM UMMAH, MAY ALLAH SWT ACCEPT OUR ACT OF IBADAT AND MAY THE JOY OF EID LAST WITH US FOREVER❤️…..

Dishi dishi haka yake ganinsu chan ya kulle idonsa yace mata;
“Babu kowa”….
Kokarin tashi ta sakeyi still yaki sakinta, ganin haka tace;
“Sakeni in kirawosu”…
Sai da yaji haka sannan ya saketa, mikewa tayi a hankali ta sauka daga kan gadon, basu san ya akayi ba kawai sukaji ta saki wani mugun kara saura kadan ta zube abby ya tareta, da sauri suka rufu kanta harda deen daya dawo back to reality a lokacin, tini numfashinta ya dauke dukda bata kai kasa ba, gadon dake gefen na deen umm ta nunawa abby ya ajyeta, babu bata lokaci ya kwantar da ita akan gadon, gadon da take deen ya nufa umm ta ruko hannunsa, juyowa yayi yana kallonta kamar wacce be sani ba ta girgiza masa kai ta nuna masa gadon daya sauka akai nufinta ya koma ya kwanta, ba musu ya koma ya kwanta hankalinsa kwance yana ganin baby tee a kusa dukda kuwa ya damu yasan abinda ke damunta, kachokam ya maida hankalinsa kan baby tee ko kifta ido bayayi kasancewar har a lokacin baya ganesu sosai, yayi nisa a kallonta yaji shigar allura a hannunsa, dagowa yayi yaga wani wanda be sani bane ya masa, ko kafin yace wani abu wani nannauyen bacci ya daukesa……

Download>>> Doctor Eesah Complete Novel

Wasu likitoci guda biyu ne suka kara shigowa aka bawa su mami umarnin fita saboda suyi aikinsu, umm kadai ta rage a dakin, rufuwa sukayi akan baby tee dan su gano abinda ya janyo mata sudden attack haka, basu sha wahala ba suka gano emotional trauma ke damunta probably saboda ta kasa daukan mutuwar khaleel, shawara sukayi sosai akan yanda zasu taimaka mata tayi recovering da wuri sannan suka chanza mata daki, duba deen suka karayi dan su tabbatar da lafiyarsa mentally saboda irin maganganun da sukaga yanayi gashi kuma ya farfado gabadaya babu weakness irin na comatose, ajiyar zuciya me karfi umm ta sauke a hankali tace;
“Alhamdulillah”….
Murmushi Dr. Hakim wanda tun dazu shi suka fara shigowa da umm yayi yace;
“He’s a hero! Who gets back to consciousness with full strength like this?”……
Murmushi umm tayi tace;
“Indeed!”….
“And he really loves his wife, can’t believe he responded to her voice”…..
Murmushi kawai umm tayi aranta tace dan ma bakasan abinda ya sashi ciwon ba kenan……
Washegari da asuba deen ya farka, yana farkawa ita ta fadomasa a rai da halin daya barta jiya, kalle kalle ya farayi yana tinanin ze ganta a gefensa kamar jiya, sai yaga shi kadai ne a dakin, infact amenity ne ma dan iya gadonsa ne a dakin, tashi yayi ya zauna yana jinsa garau, a hankali ya fara tariyo abubuwan da suka wakana a yan kwanakin da suka wuce, beyi nisa a tinaninsa ba yaji an bude kofa anshigo, da sauri ya dago ya kafeta da ido har ta karaso inda yake, zama tayi a gefensa fuskarta cike da farin cikin ganin ya farka, cikin tsokana tace;
“Son ashe ka tashi, ko kuma haryanzu a lahiran kake ne?”……
Sosa kansa yayi yace;
“When did I said that umm?”….
“Har ka manta kenan? Well I’m glad you’re okay”….
Shiru yayi zuciyarsa cike da san tambayarta ina zahrah?….
“Albishirinka?”….

Download>>> The Governor Wife Book 1 Complete Novel 

Ta sake katse masa tinani….
“Goro”…..
Ya fada blankly dan baya tinanin akwai wani albishir da za’a masa da ze sasa farin ciki a yanzu…
“Inaa baka isa ba, wannan albishir din tukuici ake fara bayarwa”….
Dan murmusawa yayi yace;
“Toh me kikeso umm?”…..
“Something huge that is worth my albishir”…..
“Bani da komai anan umm amma ki fadamin duk abinda kikeso ina komawa gida sai na dauko na baki”…..
Dariya tayi tace;
“Well zan bika bashi kawai, yanzu dai kunnenka nawa”…..
“Biyu”…..
“Toh kara biyu kasha labari”…..
Ganin yanda take ja masa rai sai yaji duk ya kagu yaji abinda zatace…..
“Dan Allah ki fadamin umm”…..
“Yanzu kuwa, the surprise is….”….
Tattara duka nitsuwarsa yayi yana sauraran abinda zata fada…..
“You got hitched to baby tee!”….
Kallonta yayi cikin rashin fahimta yace;
“Bangane ba umm?”…..
“You heard me right!”…..
Zaro ido yayi cikin mamakin daya kasa sakinsa yace;
“Umm kina nufin an auramin zahrah?”….
“Of course”…..
Saukowa kasa yayi ya zauna a gabanta akan tiles still finding it difficult to believe yace;

Also Download Ɗaudar Gora Page 8 By Billyn Abdul

“Umm dagaske? How did it happen? You mean zahrah is now my wife? She’s all mine? Ta zama matata? Don’t wake me up if I’m dreaming please”….
Dafa kafadarshi tayi murmushi dauke akan kyakkyawar fuskarta, all she knows is that baby tee is so lucky to have someone that love her this much, someone that can sacrifice anything just to see her happy, zata iya cewa a duniya baby tee bazata taba samun masoyi kamar deen ba, kwata kwata deen babu ruwansa da harkar mata amma tinda baby tee ta shigo rayuwarsa babu rules din da beyi breaking ba akanta har wani sukasa yayi impersonating deen a prison, suka gano bashi bane amma dukda haka ya sake guduwa, ya bijirewa mahaifinsa akan zama a kusa dashi saboda ita, ya kuma watsar da aikinsa ya maida hankalinsa kachokam kan lamarinta kamar mara aikin yi, bazata manta yanda yasha ce musu ya cire hannu a lamarinta ba karshe suga ya sake kawota, duk zafin zuciyarsa baya iya zuciya da ita kamar wanda aka yiwa baki, lokacin dayace ze bata kidney dinsa suka tabbatar yana sonta saboda ba yanda za’ayi kayiwa total stranger wannan sacrifice din amma kememe yaki accepting sonta yake, sunso suyi pushing abun sai sukaga kwata kwata bata shi take ba be kuma kamata su shiga hakkinta ba especially da sukasan mafarin soyayyarta da khaleel, a haka har Allah yasa sukasan wacece ita, kuma bata sauya zani ba ko bayan sunsan wacece ita sai ma wani dama da deen ya kara samu na ganin kanwarsa ce, yanda yake kokarin ganin rayuwarta ta inganta kosu da suke iyayanta kafin suyi ya rigasu, basu kara sallama masa ba sai da ya bata healthy kidney dinsa ko tinanin lafiyarsa bayayi, dukansu sunyi Glomerular filtration rate test (it’s a test to check how well your kidneys are functioning) a result din kuma na umm was the perfect one for the transplant kuma harta fara taking medication in preparation for the transplant, kwatsam sukaji wai anyi transplant, a lokacin umm ji tayi da zata iya juya komai ya tafi yanda ta keso da ba za’ayi attempting daura auren baby tee da khaleel ba, sai gashi Allah yayi hukuncinsa bayan sun fidda rai gabadaya, indeed Allah is the planner of all plans….
“It all happen miraculously by Allah’s will, you’re not dreaming habibi”…..
Sai gani kawai tayi ya rungumeta sosai, maganganun fal bakinsa amma ya kasa furtasu, kawai ganin abun yake kamar a mafarki….. “Kai kai kai Saifuddeen how could you hug someone’s wife haka?”…..
A tare suka jiyo umm tace;
“What do you mean by someone’s wife?”….

Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam

Dariya abby yayi yace;
“I mean nothing boddi”….
Sai kuma ya maida hankalinsa kan deen daya dan matsa kusa da umm yace;
“Saifuddeen dan gata!”….
Kamar jira yake yace;
“I still couldn’t believe it abby, gani nake kamar mafarki nake”…
“Ba mafarki kake ba dan gatan bappa, angon aisha da fatima”….
Abby ya karashe cike da tsokana…
Da sauri deen da yaji abun wani bambarakwai yace;
“Wacece aisha kuma?”….
“Your supposed to be wife mana”…
Abby ya bashi amsa a nitse…
Bece komai ba ya janyo hand bag din umm dake gefenta, budewa yayi ya shiga lalube, besha wahala ba ya samu abinda yake nema dama yasan ba za’a rasa a ciki ba….
Da mamaki suke kallonsa lokacin daya gama rubuce rubucensa ya dago ya mikawa Abby paper kai tsaye yace;
“Ni bazan iya adalci a tsakaninsu ba, gashi na saketa ku bama bappa”…..
“Sannu ja’iri rasa kunyar beran masallaci, toh gashi nazo da kaina sai ka bani”….
Mazewa yayi ko a jikinsa ya mika masa takardar….
Girgiza kai bappa yayi ya karba ya karanta content din cike da al’ajabi, salati yayi bayan ya gama karantawa yace;
“Lallai mahaifin yarinyarnan yayi gaskiya, yanzu da an daura auren haka zaka kunyatamu ka mata saki uku daga daura aure? Sai ka mai da wukar dan uwanta aka aurawa ba kai ba”…
Shafa gemunsa daya taru sosai saboda zaman asibiti dayayi yayi yana sunkuyar da kai, sai kuma yaji kunyar hakan da yayi ashe ba’a daura ba….

Abinda ya faru shine bayan bappa ya bar gurin daurin auren mahaifin eesha ya tubure akan lallai ba za’a aurawa deen baby tee da eesha ba saboda abinda idonsa ya gane masa, kwarai sunyi iya bakin kokarinsu gurin fahimtar dashi babu wani matsala Insha Allah amma ya dage ba za’ayi hakan ba, basu da yanda suka iya tinda shi keda iko da bada auren yarsa, dole suna gani aka aura mata dan uwanta bayan an daura auren deen da baby tee….
Koda bappa yazo asibitin sunso suyi masa bayanin yanda abubuwa suka kasance sai basu samu damar hakan ba saboda matsattsalin da suka taso, sai bayan bappa ya riga ya sanar dasu umm sannan daga baya suka basa labarin actual abinda ya faru, bappa be ja zancen ba yace Allah yasa hakan shine mafi alkhairi sannan ya kira shi mahaifin eeshan suka sake magana…
Wannan abinda ya faru yayi matukar farantawa mutane dayawa rai irinsu mami, Anna da mutane dayawa a familyn, umm ma ba karamin kwanciya hankalinta yayi ba da jin wannan labarin saidai dukda haka bata dena tinanin yanda eesha zataji ba….

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

Rankwashin deen umm tayi tace;
“Gaskiya bakada tinani saif, waya fadamaka ana yanke hukunci haka kai tsaye ba tinani?”…..
Bata rai yayi yace;
“Umm kunsan fa bana sonta amma kuka dage sai na aureta, even if this didn’t happen ni bazan zauna da ita ba”.
“Hmmm allah ya kyauta”…
Cewar umm sannan taja bakinta tayi shiru…
Karasowa bappa yayi bayan ya gama karanta abinda ke cikin paper da deen ya kama kunnensa ya murda yace;
“Dan nema da Allah be baka zara’un ba sai naga yanda zakayi”…
“Ouch karka cire min kunne mana bappa, ko fa amaryata bangani ba”…
Deen ya fada kasa kasa yana kokarin janye kunnensa…
Sake rike kunnen bappa yayi yace;
“Naji abinda kace sarai ja’iri kawai, amaryarka kuma in baka bini a hankali ba zan raba auren….
“Kajimin tsohon nan da wani zance, ai ni yanzu ko wuka zaku sokamin bazan iya sakin zahrah ba”….
Wannan shine abinda ya fada a ransa, a zahiri kuma cewa yayi;
“Afuwan yallabai”….
Girgiza kai kawai bappa yayi ya juya ya fuskanci su Abby yace;
“Ina fatima da abubakar, a kirasu suzo akwai maganar da nakeso muyi anan”…….
Ko rufe baki beyi ba sukaji sallamarsu a tare, mami na gaba dad na biye da ita a baya, binsu da kallo umm da deen sukayi kowa da abinda yake ayyanawa a ransa musamman deen da sai wani smiling yake, suda kansu sai da sukaji wani iri especially ganin bappa a dakin, kasa hakuri deen yayi ya matso kusa da umm yayi kasa da murya yanda babu wanda zeji sai ita yace;
“Umm…”…
Hannu ta dora a bakinta ta dakatar da fadin;
“Shhhh bansan surutu, I also don’t know anything about it”….
Gyada kai yayi ya koma ya jingina da gadon….
Gyaran murya bappa yayi kamar bega abinda ya faru ba yace;
“Alhamdulillah tinda kowa ya hadu, dama maganganun da muka tattauna ne akai nakeso in maimaita masa a gabanku”…..
Dawo da kallonsa kan deen yayi ya cigaba da cewa;
“Saifuddeen zara’u na cikin mawuyacin hali na alhinin shi wannan marigayin, haryanzu bata cikin hayacinta dan da sambatu take farkawa, idan aka matsa kuma tayita kuka har sai anmata allura sannan ake samun kanta, saboda haka muka yanke shawara bazamu sanar mata da daurin aurenku ba sai nan da wani lokaci in komai ya daidaita, ina kara gargadinka Saifuddeen koda wasa banaso tasan da wannan zance, idan lokacin daya kamata ta sani yayi da kaina zan sanar da ita”……
Wani iri yaji aransa dukda yasan kishi da mamaci shirme ne amma harga Allah abun ya dakesa sannan hakan ya sakashi tinanin indai har haka take son khaleel anya zata so shi kuwa? Sannan zuwa yaushe za’a bata kafin a sanar ita? A yanda yasan matarsace yanzu ze iya jurewa kuwa? Sunkuyar da kai yayi a hankali yace;
“Insha Allah bappa zan kiyaye, nagode ”….
“Allah ya muku albarka gabadaya”….
Hada baki gurin fadan ameen sukayi sannan bappa ya fita daga dakin….
Bappa na fita sudais ya shigo bakinsa dauke da sallama, sai da ya gaishe dasu mami da umm ya karasa kusa da deen yana dariya kasa kasa….
Fita daga dakin suma sukayi suka barsa daga shi sai sudais, sudais na ganin fitarsu ya sheke da dariyar da yaketa rikewa….
Wani banzan kallo deen ya masa yace;
“Wai meye hakane kasani a gaba da dariya kamar kaga mahaukaci”…..
“Saurara mallam, karka wani tsare min gida bayan ka gama kuka akan yarinyar da kace ko aure bata isa ba”….
“What do you mean?!”….
“Kalli nan”….
Sudais ya fada yana jujjuya wani abu me kama da flash a hannunsa….
“Da kyar na samoshi but it’s worth it, it contains duka koke koken daka gamayi akan baby tee bayan uban cika bakin dakayi kuma wallahi sai ta gani infact har ya’yanku sai na ajyewa suga how their father got their mother”…..
Ya karashe da tuntsirewa da wata sabuwar dariyar….
A nitse deen yake kallonsa ga mamakin sudais yaji yace;
“Duk a cikin wannan shirmen naka abu daya ne ya dameni, shine kiran matata baby dakayi kuma daga yau nayi canceling wannan sunan dan bazeyiwu tarkacen family kuna cewa matata baby tee ba, sannan banyarda a kiramin sunan uwa kai tsaye ba saboda haka fatima is out of the choice, zahrah ma kuma ban amince ba dan bazeyiwu ince mata zahrah kuce mata ba, suma wayenchan tsofaffin da suke ce mata zara’u zanyi maganinsu, sai kuje ku samo wani sunan ku kirata dashi, lastly I want to see my wife so take me to her!”…..
Kama haba sudais yayi yace;
“Tabb wallahi harna fara tausayawa baiwar allahnan, tsakani da Allah an hadata da aiki kota ina and ka dauka wasa nake akan batun flash ko? Zakaga cika aiki idan na kunnashi a family meeting”…..
“Idan kaga dama kaje BBC ka kunna, I don’t even believe you have a video like you claim, look sudais ni yanzu abinda yake damuna yafi karfin wannan chitchat din naka”….
Zama a kusa dashi sudais yayi ya sassauta dariyar da yakeyi ganin kamar akwai abinda yake damun saif din dagaske yace;
“Me yake damunka?”….
Numfasawa yayi yace;
“Is it true that she’s still mourning her ex and..”….
“Haba saif haba saif mutuwa fa? Allah na tuba ko makiyinka ne yayi irin wannan mutuwar ai dole abin ya tabaka bare kuma wanda zata aura, gaskiya dole ka mata uzuri, baza dai kayi kishi da matacce ba ita kuma she can’t keep being that way dole wataran zatayi moving on, be patient please”…..
Gyada kai deen yayi yace;
“I understand you sudais, bawai kuma ban mata uzuri bane, I just want to see how I will help her move on, another thing that is bothering me is bappa yace ba za’a fada mata zancen aurenmu ba, I’m just scared taje tana misbehaving da aurena akanta”….
“Bansan me suka gani sukayi haka ba but trust me it’s the best solution, tana cikin jimami azo mata da wani zancen ai beyi ba kawai ka saka ido akanta shikenan”…
“Toh amma haka zanna kallonta knowing the that she’s my wife and I can’t touch her?”…
Ya sake jehowa sudais wata tambayar kamar shi ya yanke hukuncin kar a fadamata….
Dan jimm sudais yayi kafin yace;
“You can’t touch her as how?”….
Cikin subutar baki yace;
“Yes do you know how good it feels touching her? I’ve kissed her for like three times or more but I’m still craving for thousand more, a very deep one and you know how attractive she can be, so how do I control myself?”…..
Tinda ya fara magana sudais ya saki baki yana kallonsa, sai da ya dire sannan da dariyar mamaki yace;
“Ashe ka riga ka gama lallatse musu yarinya Allah ya rufa asiri aka auramaka, su umm na zaune da katon dan iska basu sani ba”….
Filon dake gefensa ya dauka ya cilla masa ya nuna kofa cikin borin kunya yace;
“Tashi ka fita dan ubanka!”…..
Mikewa sudais yayi sai da ya kai bakin kofa sannan ya sheke da dariya yace;
“Toh wallahi kasan yanda zakayi controlling kanka, idan ka nuna zalamarka kayi mata ciki a cikin gidannan sai kasan da wani ido zaka kallesu, one thing I know is that a ranar da akayi cikin umm zata gane ba kuma zanzo intayaka explanation ba, zanje in dawo”…..
Yana fadin haka ya bude kofa ya fice….
“Sudais! Sudais!”….
Deen ya kwalla masa kira….
Kin kulasa yayi sai da yaji yace;
“Dan Allah ka dawo”…
Dawowa yayi yace;
“Gani, ya akayi?”….
Ya dauka magana ze mishi akan maganganun da yayi kafin ya fita sai yaji yace;
“Please take me to her, please”….
“Allah me iko,wato akan mace ka iya roko saif, muje toh”….
Bece masa komai ba ya tashi ya bisa, basu tsaya a ko ina ba sai dakin da baby tee take, luckily for them kuma ba kowa a dakin…..
Daga baki baki sudais ya masa sallama, yasan halin saif shiyasa yakeso yayi takatsantsan da duk sani abu daya shafeta yanzu…
“Ni dai kaga tafiyata, idan kaga dama kuma hmmm bari dai nayi shiru”….
“Ka karashe mana inka isa, zanyi maganinka naga nema kake ka renani”…
“Afuwan babban yaya”….
Dariya sukasa a tare sannan sudais ya fita…..
A hankali ya karasa inda take zuciyarsa na dukan uku uku, ganin abun yake kamar a mafarki shiyasa yake tsoro kar ya farka, zama yayi a bakin gadon yana kallon kyakkyawar fuskarta data rame lokaci guda, a rufe idonta yake alamun me bacci, matso da fuskarsa daidai tata yayi fitinanne kamshinnan da takeyi ya dakesa, lumshe ido yayi, yayi kissing forehead dinta kasa kasa yayi whispering;
“Mine….. I can’t believe you’re finally mine baby girl!”…
Dagowa yayi ya cigaba da kallon fuskarta kamshin turarenta na dada hawa kansa yanasa masa kasala, dama yaki yarda ya kalli sauran parts na jikinta, sauko da idonsa kan lips dinta yayi trying all possible means not to get intimidated amma duk da haka sai da yaji yanaso yayi feeling warmth din lips dinta, kin bawa zuciyarsa damar shawara yayi ya dora lips dinsa akan nata comfortably, yafi minti uku a haka kafin ya fara waswasi, wata zuciyar nace masa ‘don’t’ dayar nace masa ‘do’, ya dauki tsahon minti biyu kafin dayar zuciyar ta rinjayesa ya fara kissing dinta gently duk batasan anayi ba, kamshin turarenta ne ya kara zautasa ya koma kissing dinta da sauri da sauri kamar ze cinye mata baki, he was fiercely eating her lips up while deepening his hands into her soft silky hair, hakan sai ya kara masa armashi da jindadin yanayin yaji kamar ba’a duniyar yake ba, wai a haka ma bata responding……
He was so consumed in doing abinda yakeyi yaji karar bude kofa….

Karanta>>> Wace Ce Ita (Who is she) Complete Novel

Back to top button