Hausa novels

Wace Ce Ita (Who Was She) Chapter 75 Complete Novel

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

SEVENTY-FIVE📍

Da sallama bappa ya dauka hade da tsokanarta da;
“Amaryata amaryata”…..
Dariya tayi tace;
“Ina wuni grandpa”….
“Lafiya lau an zara’u, ya shirye shirye”….
“Alhamdulillah”…..
Murmushi bappa yayi yace;
“Daga ji bakinki akwai magana meya faru?”……
Kasa tayi da murya tace;
“Bappa a fasa auren”…..
“Wani auren?”….
Bappa ya tambaya a nitse…..
“Nafasa auren khaleel”……
“Ikon Allah sai wa toh zaki aura zara’u?”……
“Wani ne”….
Murmushin manya bappa yayi yace;
“Toh shikenan naji”…..
Da murna tace;
“Nagode sosai bappa”….
Sannan sukayi sallama ya kashe wayar…
Suna gama magana bappa yayi murmushi yana nazarin maganganunta, daga jin yanayin maganar kasan sharrin shedan ne dan ana yawan samun irin wannan sabanin dab da aure, in ba’a jajirce ba kuma sai azo ana dana sani, wannan magana ba sai yayita da kowa bama dan yasan tatsuniyace kawai, da kanta zata dawo kan hanya, biki nan da sati biyu in aka fasa me akayi kenan…

 

Download>>> Doctor Eesah Complete Novel

 

“Saif nida kai munsan babu yanda za’ayi someone at your age ya kamu da hawan jini batareda wani abu yayi triggering dinsa ba, ka gayamin gaskiya tinanin me kakeyi?”……
Cewar umm in a serious tone…..
Furzar da iska yayi yace;
“Umm bansan me nake tinani ba, haka kawai na kasa gane kaina”….
“Well kayita maimaita la’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin Insha Allah zakaji sauki a ranka sannan ka dena bawa zuciyarka space din yin tinani”…..
“Okay umm, thank you so much”….
“You’re welcome son and zaka dawo gurinmu saboda hankalinmu baze kwanta in kana nan kai kadai ba”….
“Toh umm”….
Ya amsa mata dukda ba haka yaso ba….
Umm har zata tashi sukaji sallamar baby tee, tsayuwa baby tee tayi a kansu tarasa abinda zatace saboda batayi expecting ganin umm anan ba, sai da umm taga shirun yayi yawa sannan tace;
“Kinzo kin tsaya mana aka, ko bakisan bashi da lafiya bane?”…..
“Nasani umm”…
“Toh baki iya ya jiki ba?”…..
Kallonsa tayi kamar ba dazu ta fita ba tace;
“Ya jiki?”….
Lumshe ido yayi yace;
“Naji sauki zahrah”….
“Allah ya kara lafiya”…
“Ameen”…..
Mikewa umm tayi tana kallonta tace;
“Muje ko, saif get ready sudais ze taimaka maka ka dawo chan din”…..
“Okay umm”…..
Daga nan ta kama hannun baby tee suka fita daga dakin, sai da suka fita daga part din deen taga kamar akwai abinda yake damunta, kamar jikinta a sanyaye yake, dafa kafadarta tayi tace;
“What’s wrong with you daughter?”…
Girgiza kai tayi tace;
“Nothing mom”….

Download>>> Zeenat Yar Jarida Complete Novel Document

“No karki boyemin komai please, baki da wacce ta fini a duniyarnan, just go ahead and tell your mama your problems”……
Shiru tayi na dan sakanni sannan tace;
“Umm inaso a fasa aurennan”…..
Umm ta dauka kunnenta ne beji da kyau ba ta sake fadin;
“Me kika ce?”….
“I don’t want to marry him again”….
Sai da umm tayi wani nazari kafin tace;
“Saboda me?”….
“Haka kawai”…
“No there must be a reason, ko ya miki wani abu ne?”….
“A’a”…
“Kunyi fada ne?”….
“A’a”….
“You had issues with any of his family?”…..
“No”…..
“Then why?”…..
“Nothing umm, kawai so nake a fasa”……
“Ki fadamim gaskiya in akwai abinda ya hadaku, If it’s valid I promise you zan tsaya miki a fasa aurennan koda kuwa kowa yanaso”….
“Wallahi be min komai ba umm, infact throughout yau bamuyi waya, lafiya lau muka rabu jiya kuma, I just lose interest in him suddenly”…..
Gyada kai umm tayi a nitse tace;
“If that’s the case then ina tabbatar miki da shedan ke nema yayi tasiri a zuciyarki, and it’s very normal idan biki yazo kusa, ko kinaso a fasa biki babu dalili ayita yawo damu ana zaginmu? Do you want to tarninsh our image mu zama kananun mutane masu magana biyu? Sannan ya kamata kina duba health condition dinsa”….
Jikinta ne yayi da maganganun umm, tabbas tayi saurin bin zuciyarta har ta kirawo bappa, and ya khaleel da yake da ciwon zuciya zeji idan yaji ta fasa aurensa? A sanyaye tace;
“Hakane umm, I’m sorry”….
“You don’t have to be dear, kawai kiyita addu’a a duk lokacin da kikaji irin haka kinji ko?”…..
“Insha Allah mom, amma fa na kirawo bappa na fadamasa”…..
Kada kai umm tayi tace;
“Subhanallah you were too quick in doing that, haka ake abu babu shawara? Don’t do that again please”…..
“Okay”…..
“Toh ki sake kiransa kice masa wasa kike”….
“Toh”…
“Yauwa, that’s my baby and next time kina shawara dani kafin kiyi komai kinji ko?”……
“Yes mom”…..

Download>>> The Governor Wife Book 1 Complete Novel 

Murmushi umm tayi daidai sun karaso part din mami, a dan kwanakin da suka wuce ta gane baby tee irin yarannan ne da sai ka bisu a hankali, fada da duka duk bashi bane ba, nasiha kadai inka mata ya isa kuma nan da nan take shiga taitayinta sannan kuma yaro in kana masa masifa da duka baya iya sharing damuwarsa da kai saidai yaje ya gayawa wasu chan daban da ba lallai su basa shawara me kyau ba, shiyasa yanada kyau mutum yaja dansa a jiki……
Bayan su umm sun koma mami taje ta dubasa itama, kamar yanda umm ta tsaresa da tambaya haka mami tayi amma kameme yace shi besan abinda yake damunsa ba kawai ciwo ne daga Allah, haka itama ta tashi ta tafi bayan ta barsu da sudais suna shirin tawowa part dinsu….
Mami na fita sudais ya tafi ya dauko papers din daya tura karkashin gado wanda deen ya zana baby tee a jiki, zubesu yayi akan gado yana kallonsu yace;
“Wannan kadai ya bani amsar tambayar da zan maka, saif believe it or not son yarinyar nan na neman maka illa, idan ma bazaka iya fada ba ni ka bani go ahead inje in fadamusu”……
Dauke papers din yayi ya tura karkashin pillow sannan ya juyo ya harari sudais yace;
“Ni na gayamaka ina sonta? Wai ina ruwanka ne? Kaje ka samu wani da maganarnan wallahi bani ba kai har abada and I’ll make sure I deny you”…..
“Toh inba sonta kakeyi ba saboda me zakana zanata? Sannan sambatun daka kirani kanayi duk akan waye inba ita ba? Ko an gayamaka banga yanda ka kafeta da ido bane dazu? Infact kasan nina jasu muka fita saboda mu baku space?”…..
“See duk wannan zancen da kakeyi bansan me kake cewa ba, idan kuma zaka cigaba dayi ka fitarmin daga daki”…
“Ai shikenan amma ina jiye maka danasani”……
“Mtseeeew”….
Yaja tsaki sannan ya mike ya shiga toilet ya bar sudais a tsaye…..
Kamar yanda umm tace tayi haka ta sake kiran bappa, yana dauka tace masa ita fa wasa takeyi kar a fasa aure, dariya yayi yace kaniyarki wato mu kika maida abin wasa, da na tara meeting haka zaki kunyatani kice baki san zance ba, dariya tayitayi shi kuma yana tsokanarta, karshe ya dan mata nasiha ya kuma maimaita mata abinda umm tace na shedan dake saka waswasi a zuciyar mutum sannan ya bata addu’oin da zata na yi, su kayi sallama cikin farin ciki…….

A week later……
A yau take ranar da za’a kawo lefen baby tee daga gidansu khaleel kamar yanda za’a kai na deen gidansu eesha shima, shirye shirye ake ba kama kafar yaro a gidan ko ina ya dau harami, har renovating both gidan umm da mami saida akayi ga uban decorations da ko ina yasha tun kafin bikin yazo, baki kuwa ta ko ina sun cika gidan ba masaka tsinke, har building din umm aka bude wasu suka zauna a hakama wasu a hotel kawai suka sauka, sosai gidan ya kachame da baki duk inda kabi sai kaga mutane, mutan maiduguri suma gayyarsu guda, har bappa yazo amma shi gidansa daban da suka sauka shida aminansa, anna kuma tana tare dasu anan gidan, baby tee har tagaji dan tinda yan maiduguri sukazo suke kara tsumata dukda uban gyaran datasha, turare ko ko zatayi wata batasa ba ba za’a g ane ba saboda yanda ta juku da turare dama ansan yan maiduguri ta wannan fannin, babu lungu da sako na jikinta da turare be kama ba, kayanta ma gabadaya sai da aka turarasu suka kuma koya mata yanda akeyi saboda ta cigaba da turara kayanta a gidanta, ba karamin kokari mami tayi da ita ba gurin koya mata ayyuka na yau da kullum kuma cikin ikon Allah ta dauka ba lefi, girki ma tana kokari saidai haryanzu hannunta be fada ba, amma tana kokari sosai…..

Karanta>>> Amfanin Zogale Guda 18 A Jikin Dan adam

Deen ze iya kiran wannan satin dayan worse days of his life, da farko ya sakankance da tace zata kira bappa, abinda ya kara masa gwarin gwiwa kuma shine dawowarta part dinsa amma umm bata basu damar yin magana ba, babban abinda ya mai dashi part dinsu kenan saboda yayi magana da ita yaji yanda sukayi da bappa, amma ya nemeta ya rasa kwata kwata ba’a bari tana fitowa, inma tana fitowa toh maybe tana daidaita time din da bayanan ne, kwanansa uku a part din be sata a ido ba, tin yana tausasa zuciyarsa har hakurinsa ya kare ya kasa jurewa lokacin kuma baki sun fara yawa a gidan, kawai ya tattara ya bar part din dukda su mami basu so ba amma ya kawo musu uzurin baki…..
Tinda ya koma part dinsa ya koma gidan jiya, abun sai yafi na da karfi dan yanzu har fashe fashe yakeyi idan ya huce ya tattara ya gyara gurin, hakan ba ze hana ya karayi ba, sosai yayiwa kusan komai na part dinsa lahani kar mutum yaso yagani, ya kuma ki gyara komai saboda su mami zasuga shigo da kaya shikuma bayasan a zargi wani abu, idan zasu shekara suna masa knocking baze bude ba, sai daga baya yaje ya samesu yace yana bacci time din da suka zo ne, sosai ya kara ramewa ta yanda kowa ya gansa sai ya tambaya ko bashida lafiya ne, baby tee ko so daya be kara ganinta ba shiyasa ya kara birkicewa, umm da kanta ta masa aski dan anyi dashi yaje yayi aski yaki, dole umm tasa a siyo mata clipper ta masa askin da kanta wai ya daina yawo kamar wani mahaukaci, abu daya yasani shine sauran numfashin daya rage masa a duniya yana irguwa ne daga ko wace rana zuwa ranar da za’a daura auren, tun eesha na chanza nambobi tana kiransa bayan yayi blocking dinta har karshe ta daina samunsa gabadaya saboda kashe wayar dayayi, umm babu yanda batayi dashi akan yazo yaga kayan lefensa ba amma yaki, sai dazu yakeji wai yau za’a kai……
Da azahar familyn daddy suka kawo lefen baby tee cikin shiga ta alfarma, akwati set biyar suka kawo masu shegen kyau da tsada, sunji kaya na gani da fada dan babu karamin abu a kayan, ga gold Jewries har set uku da mukullin mota biyu, babu wanda ya kalli kayan nan be yaba ba saidai hassada dan ko wata yar shugaban kasa sai haka, tukuici me tsoka su mami suka bayar sannan aka tilasta musu tafiya da duk wani kayan ciye ciye da akayi a gidan, haka aka rabu cikin mutunci da mutunta juna suna murna khaleel ya dauko yar gidan mutunci……
Bayan sallar la’asar bappa yazo yaga lefe ya saka albarka shima, part din da yake zama a gidan ya tafi bayan ya kira deen a waya yace yazo ya samesa, yaci sa’a wayar a kunne….
Da sallama ciki ciki saif ya shigo parlorn da bappa yake, kuresa da ido bappa yayi yana mamakin yanda ya fita hayyacinsa a haka ma ya dan rufe fuskarsa da wular rigar sanyi dayasa…
“Meya sameka haka saifu? Wannan ramar duk ta mecece? Kana kallon kanka a madubi kuwa?….
Sunkuyar da kai yayi yace;
“Babu komai bappa, kawai banajin dadi ne amma naji sauki yanzu”…..
“Toh sannu, Allah ya kara lafiya, ya kamata dai ka bincika lafiyarka da kyau”….
“Toh bappa”…
“Dama kiranka nayi inji me kake shiryawa game da bikinnan, yanzu ake shirin kai lefenka gidansu yarinyar”….
Bappa yayi maganar yana nuna masa cikin parlourn inda aka jere akwatuna reras gwanin ban sha’awa…
Gyada kai yayi batareda ya kalli gurin ba dan kwata kwata bayasan gani….
“Bakace komai ba, babu wani shiri da kakeyi kamar events da sauransu?”…
Bappa ya sake maimaitawa…….
“Bappa ai babu event din da za’ayi duka, baze yiwu a za’a tara maza da mata ana abinda be dace ba, kawai mata suyi walimarsu daban maza ma haka, ba sai an wani hada taro a event center ba”….
Sai a lokacin ya dago ya bawa bappa cikakkiyar amsa saboda an sosa masa inda ke masa kaikayi, ya riga yayiwa kansa alkawari kome zasuyi bazai bari ayi wani taro da za’a hada mata da maza a guri ba, not even after seeing yanda aka zagayeta a bikin chan ana shirme da sunan liki……
“Wannan gaskiya ne saifu, duk wannan bidi’ar be dace ba albarkar auren kawai muke nema, ayi walima kawai yanda ka fada”……
Wani sanyi yaji aransa har saida ya sauke ajiyar zuciya, a cikin sati dayan nan yau shine ranar dayaji abu ya dan sashi farin ciki……..
Dan tattaunawa suka sakeyi sannan bappa ya basa damar tafiya, yana komawa part dinsa yaci karo da sudais zaune akan couch da karamin trolley dinsa a gefe, be kulasa ba ya shigewarsa bedroom dinsa, yasan dawowa gidan yayi kamar yanda yace masa zeyi one week da biki, ya kuma ja masa warning yace bayaso amma beji ba, shi ko sauran guys din family ya nuna musu kar wanda yazo inda yake baya gayyatar kowa, amma sudais beji ba…..

Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam

Ranar daurin aure…..
Tun asuba sudais yake yiwa deen knocking yazo ya bude kofa suje suyi sallah amma yaji shiru kamar babu mutum a ciki, kuma yasan yana ciki, da farko yayi tinanin ko rashin mutuncin nasa ne ya motsa sai kuma yaga deen baya wasa da sallah musamman ta asuba in ba da wani dalili me karfi ba, knocking ya cigaba dayi yana addu’ar Allah yasa lafiya yake, amma yafi one hour yanayi shiru, dole ya hakura yayi sallah a parlourn ya nemi guri ya zauna yana zaman jiran fitowarsa…..
Sai karfe takwas yaji ya bude kofar, da sauri ya mike ya isa ga dakin, shiga yayi ya gansa a zaune akan sallaya, hakan ya tabbatar masa da lokacin ya idar da sallah, zama yayi a bakin gadon yana jiransa ya gama lazimi……
“Sudais!”….
Deen ya ambaci sunansa….
“Yes bro”…..
“Inaji a jikina yau zan mutu”…..
Cikin tashin hankali sudais yace;
“Bangane yau zaka mutu ba, Allah kar yasa muga hakan”…..
Murmushin dayafi kuka ciwo yayi yace;
“Bazan iya rayuwa da tinanin tana gidan wani ba”……
Tashi sudais yayi ya koma ta gefen da yake ya dafa kafadarsa yace;
“Look saif you have to do this, dole ka cireta a ranka and face your life, ka dau hakan a matsayin kaddara kawai dan kai da kanka haryanzu baka amince sonta kake ba”….
“Sudais ba iya sonta nake ba, bugun numfashina ne ya rataya a wuyanta, my life completely depend on her!”…..
Ba karamin shock sudais yayi ba, be taba tinanin deen zeyi accepting yana sonta ba, atleast tinda ya daure har aka kai wannan lokacin yayi tinanin ya hakura ne, irin wannan ranar ya dinga guje masa amma yaki jin shawara, sai yanzu ranar da za’a daura mata aure sannan zece itace rayuwarsa, ai kuwa ya makara dan babu taimakon da ze iya basa a yanzu……
“Saif it’s too late, ka riga kayi wasa da damarka, irin wannan ranar na dinga guje maka amma kaki daukan shawara, yanzu ya kakeso muyi?”……
“Dama bance maka ga abinda zamuyi ba, I only said you should get ready to lose me”…..

Karanta>>> Hadin Karawa Mace Ni’ima, Sha’awa Da Kuma Karin Dandano

Daga nan be kara cewa komai ba ya juya yayi kwanciyarsa akan sallaya…..
Kasa cewa komai sudais shima yayi saidai hankalinsa yayi mummunan tashi da furucin deen, yasan sa da mugun zuciya tsoro yake kar a daura auren ya cutar da kansa, gashi sai maimaita kalmar mutuwa yakeyi, dafe kansa yayi ya shiga tinanin mafita kafin lokacin da za’a daura auren yayi which is 10am….
Har karfe tara be samu solution ba, duk inda yabi sai yaga ba zasu billa ba, idan yaje ya samu su mami da maganarnan yasan ba lallai su saurareshi ba because it’s absolutely late, shi baze ma iya tunkararsu ba saboda da kunya ranar daurin aure bayan angama shirin komai ace a fasa a daura da wani……
Dan dukan kafadarsa ya farayi da zummar su samo mafita tare amma deen yaki tashi, mamaki ne ya kamasa saboda yasan deen bashida nauyin bacci sai in beyi niyar kula mutum ba, hannun shi ya dan ja yaga hannu yabishi ya koma, and it occurred to him that deen passed out, da gudu ya fita daga part din ya tafi nasu, luckily enough ya hango mami da umm a gaban part din, sunci ado sosai ga mutane sai kaikawo suke, karasawa yayi yana nishi yace;
“Umm kuzo ku gani saif is unconscious”…..
“What?!”…
Suka hada baki gurin fada….
“Eh kuzo ku gani dan Allah”….
Bin bayansa sukayi kirjinsu na dukan uku uku…..

Suna tafiya khaleel ya karaso gidan saboda ya takura sai sun hadu da baby tee kafin ya tafi daurin aure, yau satinsa biyu kenan be sata a ido ba shiyasa duk a damu, a boye hussy ta fito da ita batareda kowa ya gane ba, a mota ta sameshi tacewa hussy ta jirata su gaisa ta fito sannan ta bude inda yake a bayan motan tashiga saboda bashi yake driving ba, fita drivern yayi ya basu waje, lumshe ido khaleel yayi saboda yanda kamshinta ya cika motar, kura mata ido yayi yaga ta kara kyau sosai kamar ya saceta ya gudu, itama kasa kasa take kallonsa saboda wani mugun kyau daya kara, fuskarsa tasha gyara kamar me, gashi sai tashin kamshi yake me dadi, ya dade yana kallonta kafin ya kamo hannunta yace;
“Kinyi kyau sosai kamar na gudu dake yanzu, I love you so much wifey”…
Murmushi tayi tace;
“I love you too hubby, you’re looking very handsome too”……
“Wow I love the name, wifey you have no idea how I’m longing to see you in my custody”…
Murmushi tayi ta rufe fuska…..
Shima murmushin yayi yace;
“Can I hug you?”…..
Batasan meyasa ba haka kawai ranar taji batasan hanashi, gyada kai tayi tana rufe ido….
A hankali ya matsa kusa da ita ya rungumeta na tsawan mintina sannan yayi pecking dinta a kumatu ya saketa…
Bude motar tayi batareda ta juyo ba tace;
“I will miss you! Until then!”…..
Gyada kai yayi fuskarshi wadace da fara’a yace;
“I will miss you more wifey!”….

Suna shiga parlourn mamaki ya cikasu ganin yanda ko ina ya zama very scanty, har tv babu saidai yanzu ba lokacin wannan bane, suna shiga bedroom dinsa suka ganshi shima empty, har mirror babu komai akai, kanshi sukayi da sauri umm ta fara kokarin ceto numfashinsa, sunfi minti goma tana mishi duk dabarun da tasan zesa ya tashi amma ina ko motsi beyi ba, hankali tashe ta kalli sudais tace;
“Get the securities, we have to take him to the hospital”…..
A gigice sudais ya tafi kiransu zuciyarsa duk babu dadi…
A nearest hospital dake street din suka tsaya, nan da nan akayi emergency dashi, umm har zata bisu taji zuciyarta ta karaya, karo na farko da taji bazata iya handling patient a rayuwarta ba….
Around 9:30 suka samu nasarar ceto numfashinsa bayan sunsha gumurzu, chanza masa daki sukayi sannan su umm suka shiga ganinsa, suna ciki abby, dad da mahaifin eesha suka shigo, dama daurin aure zasu wuce su mami suka kirasu…
A hankali ya bude idonsa tar akansu, sai kuma ya maida idon ya rufe saboda dishi dishin da yake gani, umm na ganin haka ta matso bakin gadon dama tafi kusa dashi, hannunta ta dora a jikinsa taji yayi mugun daukan zafi, janye hannun tayi yayi saurin ruko hannun nata, girgiza kai tayi cikin tausayawa tace;
“Sannu son, ubangiji Allah ya baka lafiya”…..
Hannunta ya sake rikewa gam bece komai ba, sai ga hawaye ya silalo a saman fuskarsa, zaro ido tayi dan bazata iya tina when last taga hawaye a idon deen ba tun yana yaro kuwa, komi girman abu tsap yake shanyesa, sai yaso ka gane ma, a rikice tace;
“Saif hawaye fa kakeyi, ya ilahil alameen lafiya kake kuwa”……
Rintse ido yayi wani sabon hawaye yana sauko masa, shi kansa he can’t believe kuka yake abinda baze iya tina yaushe yayi last ba, sannan be taba tinanin wata halitta zata iya sashi kuka a duniya ba sai yau, kokarin tsaida kukan yake amma hawayen kamar ana dadasu, su kansu sauran mutane dake dakin babu wanda ya iya cewa komai saboda mamaki, a bazata sukaji yace;
“Umm ina sonta!”…..
Shiru dakin ya dauka saida mami tayi karfin halin cewa;
“Wa kake so?”……
Kai tsaye a raunace yace;
“Fatima..Zahrah..Baby tee”….
Tsit dakin ya sake daukan wani mugun shiru kowa na sake saken da yakeyi, sudais na ganin haka ya fita daga dakin saboda zuciyarsa bazata iya daukan abinda ze biyo baya ba dan yasan ba me dadi bane, saidai yayi matukar murna da deen ya fadi abinda ke ransa koda be sameta ba…..
“Wace irin magana kakeyi haka saifuddeen?”….
Cewar mahaifinsa…..
“Yes dad, wallahi ina sonta bazan iya rayuwa babu ita ba, idan kuka aura mata wani mutuwa zanyi”…..
“Ba zaka mutu ba sai lokacinka yayi saboda haka ina baka shawara da ka dau dangana dan bazamu zama kananun mutane ba,lokaci ya ja ku mu tafi gurin daurin auren dan Allah”…..
Juyawa sukayi suka tafi badan zuciyarsu da dadi ba, sosai abby yayi matukar tausayawa deen abinda yasa ya kasa magana kenan, shi dama ya dade da gano saif son baby tee yake shiyasa har yayiwa boddi magana amma ta nuna masa yace bayaso, shi kuma mahaifin eesha jikinsa ne yayi sanyi ganin wanda ze zama sirikinsa yana kuka akan wata, toh ya matsayin rayuwar yarsa yake?”…….

Karanta>>> Amfanin Hulba A Jikin Yan Mata Dama Matan Aure.

Suna fita hawayensa suka kara gudu yana jin zuciyarsa kamar zata fito, saukowa kasa yayi ya tsuguna har kasa ya fashe da kuka yace;
“Dan Allah dan annabi badan halina ba ku taimaka kuce su fasa aura mata wanchan, wallahi mutuwa zanyi idan ta auri wani bani ba”…..
Wani irin kallo mami ta masa tace;
“Da meya samu bakinka all this while? So nawa muna tambayarka kana mai damu kamar wanda basu san me sukeyi ba”…..
“Mami ban taba soyayya ba, bansan menene soyayya ba sai akan zahrah, shiyasa ya daukeni lokaci me tsawo kafin na gane sonta nake, daga ranar dana fara ganinta a school zuciyata bata kara nitsuwa ba, nayita bibiyarta har Allah yasa na ganota, daga wannan lokacin zuciyata bata kara hutawa ba saboda yanda ko karamin abu tayi yake matukar tasiri araina, nasha cewa na fita daga sabgarta amma sai na kasa, ashe sonta nake bansani ba, mami na kasa cin abinci na kasa komai amma wallahi bansan soyayyarta ce ta mun lahani ba, a duk lokacin dana tuno aure za’a mata sai naji zuciyata kamar zata fita daga gangar jikina amma wallahi bangane so bane, idan ta aureshi bazan iya kara minti daya a duniya da tinanin gidan wani za’a kaita ba, ku taimaki rayuwata kuce a fasa aurennan”……
“Hmmm ai kuwa bakin alkalami ya riga ya bushe saifuddeen, duk wannan surutan basu da amfani yanzu, idan zaka dau dangana gwara ka dauka, bazan iya sauraron wayennan shirmammun zantukan ba, kunga tafiyata……
“Mami please please”….
Ya fada da karfi yana rarrafawa gabanta amma ko kafin ya karasa tayi ficewarta ta samu gurin da babu kowa ta zauna tana masa addu’a Allah ya kawo masa sassauci ya zaba masa mafi alkhairi…..
Yana ganin mami ta fita yadawo gaban umm, kafafuwanta ya rike yana kuka yace;
“Umm ke kadai kika ragemin, dan Allah karki juyamin baya kema”….
Hawayen dake kokarin zubo mata ta maida sannan ta kamo hannunsa ta mayar dashi kan gado, hannu tasa tana share masa hawayen fuskarsa tace;
“Stop crying son ina tare dakai, babu inda zan tafi in barka”….
Be iya ya tsaida hawayen ba yace;
“Dagaske umm? Dan Allah ki bani aurenta toh”…..
“Saif ai bani zan bada aurenta ba, saif mun dade da gane kana son baby tee shiyasa muka dinga tambayarka amma kace a’a, ka dauka zamuso bare ne fiye dakai? Lokuta da dama nakan zauna inji kamar inyi forcing dinka ka aureta sai kuma naga itama bata kai take ba kamar yanda kaima kake denying dinta, wallahi babu yanda za’ayi kace kanaso a basa kome ze faru kuwa, sannan kuma munki pushing abun ne saboda kanada wani hali saif, abu in bakai kace kanaso ba ko an tilastaka bijirewa zakayi”…..
“I accept all that umm and I really regret doing that amma dan Allah ki taimaka kiyi wani abu, umm ki taimaka a auramin ita, I promise you I’ll take very good care of her, na miki alkawari ko tsawa bazan mata ba, kuma ko harara baze shiga tsakanina da ita, na miki alkawari bazan kara takura mata ba, zan bita sau da kafa yanda takeso, I can be the cook, the dishwasher and everything for her, I will do absolutely everything for her, zan mata biyayya kuma bazan taba tsallake umarninta ba, I’ll make sure I be the person she wants, umm idan tanaso kullum in kwanta akan titi tana takani wallahi zanyi, umm I’m madly in love with your daughter, ku auramin ita or I run mad!!!”……
Tinda ya fara wannan sambatun umm take kallonsa, gabadaya sai surutu yake kamar wani zararre, lallai ta yarda shi so babu ruwansa da wanene kai, duk kamewarka sai ya ita burkita ka, she can’t believe deen ne yake yima baby tee irin son da ze kalleta ido cikin ido ya fadamata yana son yarta, har dasu ze mata biyayya sai kace wata uwarsa, wannan wani kalan mugun so ne da yasashi ya fita hayyacinsa haka?….
Wayarta ce ta fara ringing ta kalli screen din taga abby ne, dauka tayi gabanta na faduwa, saboda tsabar rikicewa ashe a speaker tasa wayar bata sani ba…..
“Boddi an daura auren!”….
Shine iya abinda taji ta yanke wayar, a take numfashin deen ya yanke ya zube a gurin!!!……

 

Back to top button