Hausa novels

Mijin Malama Page 3 By Nimcy Sarauta

*🌈MIJIN MALAMA🌈*

Nimcyluv Sarauta
*_Arewabooks@Nimcylub_*

 

*3…..*
Maganganun Aliyu suka kusan tarwatsa mata zuciya, idanunta ya rufe kafin tayi magana ya ce “Ko a lokacin da nake yaro, ban taÉ“a kuka saboda wahala ba, ba kuma zan yi kuka saboda abin da zaki aikata ba, ki sawa ranki ba a haifi Aliyu domin sadaukarwa ba, amma an haifi ni domin bautawa Ubangiji da kuma cimma burukana, bana da burin daya shige zama da Malama Majeederh Abdul’aziz Khan!” Ya fesar da numfashi ya ce
“Ban taÉ“a neman abu na rasa ba, kin san yadda nake zama mahaukaci akan abin da nake so….,” Da Æ™arfi Latifa ta ce “And so what Aliyu? Ni kuma zan tabbatar a wannan karan na zama sanadin da zaka rasa abin da ka ke nema, ka yi ta farauta wacce bata da amfani har zaki ya yi gaba da abin farautar taka, zaka san kuma kaci amanar matarka ni Latifa Omar zaka sani” tayi hanging off na kiran.
Tsakanin ita da Aliyu ba a san wanda ya fi wani shiga damuwa da baƙin ciki ba, shi yana jin baƙin ciki idan ta shegenta ɗan gidan Jeederh, yana jin tamkar gudan jininsa ta shegenta. Latifa Omar tana ganin Majeederh ta munafurceta tayi mata kyakkyawan zato ta ci amanarta, Allah kaɗai ya san lokacin data ɗauka tana bin baza, ko komai nata zai ƙare ba zata taɓa barin Bar Aliyu Sufyan Alhassan ya kasan inuwa guda da Jeederh ba.
Ta dunƙule hannu tare da kaiwa iska naushi cikin zafi ya juya yana faɗin.
“I can’t take it any longer Majeederh, dole kiyi haÆ™uri mu zama abu guda” shiru not respond.

Also Download>>> Mijin Malama Page 1 By Nimcy Sarauta

Ya riÆ™e Æ™ugu cikin sauke numfashi yana son ya saisaita kan shi ya kasa ya ce. “Ina son na je wajan Dr Jamal, i have something to discuss with him” nan ma shiru sai a lokacin ya juya zai sake kiran sunanta yaga wayam! sai gado da drip yana É—iga a Æ™asa.
Baki buɗe ya tsaya cak yana ƙarewa room ɗin kallo kamar ƙungi.
“What?” Cikin sauri ya buÉ—e Æ™ofa ya fita suka ci karo da wata nurse ya ce
“Heee Nurse” “Yes, Sir how can i help you?”
Ya juya idanunsa ya yi ta kallon wajan yana son yaga ta ina zai gano Jeederh. “Sir!” Kiran ya dawo da shi hankalinsa ya ce “Kinga wata yanzu da baby a hannu ta fita?” Ta shiru alamar tunani sai kuma ta ce.
“Yanayinta?” Ya ce “She’s beautiful, fara tas yar yellow take tana da jiki zata kai 35 yrs going to 36” Ta kalli hanya ta ce
“Oh Malama Majeederh Abdul’aziz Khan?” Ya É—aga ya ce “Exlty, where she’s?” Ta ce “She Left, alright”
Ya yi baya a fili ya ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un, why? why Jeederh mun shiga uku daga ni har ke” da gudu kuma yabar world É—in ya nufi reception har zuwa parking lot na hospital É—in amma babu ko mai kama da ita.
Motarshi ya shiga tare da yi mata key kamar zai tashi sama haka yabar cikin asibitin bakiÉ—aya wanda ya yi kwana Uku ciff a cikinsa.
Dr Jamal na zaune a office É—insa yana operating system sai gumi yake duk da sanyin A.cn dake office É—in. Bell aka danna ya ce “Come in” buÉ—e Ƙofar akai tare da shigowa.
“Dr Jamal wai meke faruwa da kai ne, kwana uku baka cikin hayyacinka” ya share zufa ya ce “Tajju ina cikin damuwa”
“Problem?” Tajju ya maimaita. Dr Jamal ya gyara zama ya ce “Ka san Malama Majeederh Abdul’aziz Khan?” Gaban Tajju ya faÉ—i hakan ya tuna masa da wasu memories ya ce “Uhm, ina jinka” kai tsaye Dr Jamal ya ce “Ta haihuwa, kuma yanzu an nemeta an rasa, kwana kenan bana barci kullum sai na duba all scanning da na taÉ“a yi mata, wallahi tsayin shekara biyu result bai taÉ“a nuna mini Majeederh nada ciki ba ko da wasa, infact results É—in na nuna she’s Good, sai a satin nan dana sake mata wani ya nuna mini Æ™ari ne a cikinta shi ne ya haddasa kumburin Cikin, sai gashi kuma wai ta haihu harta gudu” cikin wata kalar hausa Tajju ya ce

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

“Innalillahi, subuhana”
Ya yi ta maimaita wa kafin ya ce “Amma tayi aure?” Dr Jamal ya ce
“Ko engagement ba tayi ba balle aure, bata taÉ“a aure a zahiri ma babu wani É—a namiji daya taÉ“a cewa yana son ta”
Tajju ya miÆ™e ya shiga kai kawo cikin office É—in da sauri kuma ya fice yana cewa “ina zuwa”
Yana fita mota ya shiga ya nufi gidan shi dake cikin Nassarawa. Tun da ya shiga bedroom yake tunani,akwai muhimmin abu da yake son tunawa amma ya rasa mene? Dr Jamal abokin Tajju ne gabaÉ—ayansu likitoci ne.
A hankali ya ce “Malama Majeederh Abdul’aziz Khan? Ya Allah!”
Kwanciya ya yi nan take barci kuma ya É—auke shi.
Can cikin barcinsa ya ci wasu maganganu na tashi a kunnenshi a firgice ya farka yana haÉ—a zufa jikinsa na rawa ya ce.
“Gang” ya miÆ™e ya ce “Gang team!” a haukace Tajju ya dinga fito da kayan wardrobe nasa cikin sa a wata envelope ta faÉ—o ya É—auka da sauri yana dubawa, har yanzu wani sassan yan Æ™amshi ke tashi jikin envelope É—in, ya duba da kyau idan har ba zai manta ba shekaru biyu kenan da bashi saÆ™on ya bawa Majeederh, shi kansa ba zai iya tuna abin da ya mantar da shi ba. A hankali ya duba jikin envelope da aka rubuta.

*_No words to explain, no words to describe, no words to as your forgiveness, Wait for me, I’ll be back sooner or later, Please Jee_*

Tajju na gama karantawa ko gyara bedroom É—in bai ba ya zari key É—in mota tare ficewa daga cikin gidan, tana ina zai fara? Ina zai ga Malama Majeederh har ya bata wannan saÆ™on? A fili ya ce “Allah na tuba, ban san me ya mantar dani ba” haka yaci gaba da driving.
Tun safe Majeederh take tafiya fuska rufe babyn ya yi shiru a jikinta, kamar mahaukaciya haka ta zama bata gane komai bata bambance komai, kiran sallar Magriba ya yi daidai da tsayuwarta a gefen wani shago a lokacin kuma babyn ya kama kukan yunwa, ta samu waje ta zauna ta shiga kallon fuskar jaririn ko Allah zai sanya ta gane dawa yake kama, amma abin mamaki komai nata ne, kamarsa É—aya sak da ita idanunsa ne kawai da bai fiya buÉ—ewa ba yasa bata gama gane Æ™wayar tawa ba, ganin kukansa zai sanya hankalin jama’a ya dawo kanta ya sa ta zura shi cikin hijabi bata san me zatai masa ya daina kuka ba can ta tuna abincinsa yana jikinta ta É—aga rigar asibitin dake jikinta tare da sanya masa nono a baki, babu ruwa ko kaÉ—an zai azabar zafi, haka ya dinga jan fata jin baya shan komai ya cika ya dinga tsala ihu. Sai a lokacin ta fashe da kuka take rungume shi ta ce.
“Asstagafirullah Ya Allah, ba san komai, na yarda da Æ™addara, Allah ka kawo mini É—auki albarkacin Annabin rahama” a hankali ta dinga tattaro yawun bakinta tana bawa jaririn yana sha, tun tana bashi har yawun ya Æ™afe bai kuma daina kuka ba. Ta miÆ™e riÆ™e da shi tare da Æ™ara sawa wajan shagon tayi sallama can Æ™asa kafin tayi magana ta ji saukar muryar Abbu a kunnenta ta juya da sauri ta kalli T.v dake shagon, fuskar mahaifinta tar a t.v yana yi wa Æ´an jarida bayani ya ce.
“Me kuke son sani?” ÆŠan jaridar ya ce “Shin da gaske ne Æ´arka Malama Majeederh Abdul’aziz Khan kan ta haihu? bayan duniya ta san bata da aure? Ko dai tayi aure a É“oye ne, ko kuma zargin da ake a kanta ya tabbata?” Abbu ya yi dariya sosai yana kallon ÆŠan jaridan ya ce.

Also Download Dr Eeshatt Romantic Hausa Novel Complete Document

“Ina da Æ´a Majeederh, amma tawa yarinyar ta zama gawa tun tuni bata raye, ban kuma san yarinyar dake amfani da sunana da kuma sunan familyna ba, zan yi amfani da wannan damar wajan yi mata Allah ya isa har abada, zan kuma shaidawa duniya duk inda suka samu yarinyar nan mai amfani da sunana su jefe ta ko kuma suyi mata bulala akan laifin aikata zina, su kuma É—auki mataki akan amfani da rigar Muslunci tana aikata alfasha”
ÆŠan jaridar ya kalli Abbu sosai, da alama ya firgita da maganganun shi ya ce. “Kenan Malama Majeederh ba Æ´arka ba ce wacce muke tunani?”
Cikin tsawa Abbu ya ce
“Yara biyar ne kaf duniya, tawa Majeederh ta zama gawa tun da jimawa bana son wata tambaya bayan wannan” a firgice Majeederh ta dafe Æ™irjinta da yake wani bugawa jajirin ya nemi suÉ“ucewa ta shiga kokawa da numfashinta, wani abu mai nauyi ya tsaya mata a Æ™irji Idanunta suka tsaya Æ™am akan fuskar mahaifinta tunani take ko dai da gaske bashi ya haifeta ba? Mai shagon ya girgiza kai ya ce.
“Kai duniya, kai duniya wai yanzu aikata zina ya zama ruwan dare? Matan aure su aikata zina, Æ´an mata su aikata zina, zawarawa su aikata zina, mijin aure ya nemi matar wani, matar aure ta nemi mijin wani? ga FyaÉ—e daya ya waita, ga matsalar tsadar abin duniya, ga rashin nefa ga rashin ruwan sha, albashi wannan sai a shige wata ba a biya, wani lokacin ma a rage albashin, ga yawan aibata Musulunci yanzu Fisabilillahi a kaf garin nan waye bai san Malama Majeederh Abdul’aziz Khan babbar malamar musulunci ba ce? waye bai san irin tallafin da take bawa Muslunci ba, waye bai san wa’azin da ta kewa masu aikata alfasha ba, sai gashi ana zaton wuta maÆ™era sai gata a masaÆ™a, shi ya sa ake cewa kayi amfani da faÉ—ar Malam kada kayi amfani da abin da yake aikatawa, wallahi ko ki aka bani dama sai na jefe wannan shaiÉ—aniyyar” Lawan ya girgiza kai ya ce “A’a Bala, amma dai Allah ya kyauta!” Bala ya ce “Amin, shi ya sa taÆ™i aure tana ta zuba alfasha, kasan daman duk wani mai aikata zina aure bai dame shi ba, kuma ko ya yi aure ba zai daina yin abinda ya saba ba”

Also Download Dr Eeshatt Romantic Hausa Novel Complete Document

Malama Majeederh bata tsaya neman ruwan ba, ta juya da sauri tare da barin wajan a lokacin ji take kamar ta shiga duniya, kamar ta zama ƙaruwar da suke danganta ta da ita, ji take kamar ta zama sanadin lalata sunan mahaifinta dana familyn da yake nesa ta da shi gudun kada ya ɓaci, zuciyarta ta ƙe ƙashe duk damuwarta ta tsaya, lokaci zuwa lokaci take jan numfashi ta sauke sbd abinda ya tsaya mata a saitin zuciya da maƙo shinta. Tayi tafiya mai nisa sosai kafin ta samu wani waje kusa da wata bola ta zauna ta rungume yaron wanda ya yi shiru, jikinsa ya ɗauki zafi. Ji take kamar ta rataye kanta, ga jinin haihuwa daya gaba ɓata mata jiki a haka barci ya ɗauketa.
Tsaye suke gabaÉ—aya a parlour Hajia ta girgiza kai ta ce “Me kayi haka Zaki? Me ka aikatawa kan ka haka Aliyu?”
Almustapha ya kalli news paper É—in ya Æ™ara ware idanunsa akan photon Bar Aliyu Sufyan Alhassan da kuma photon Malama Majeederh Abdul’aziz Khan dake zaune fuskarta rufe da liÆ™ab. Almustapha ya shiga karanta headline É—in jaridar. “Bar Aliyu Sufyan Alhassan shi ne ya aikata zina da Malama Majeederh Abdul’aziz Khan, tare da saninta domin su wulaÆ™anta matar Aliyu wato Latifa Omar kasancewarta aminiyar Jeederh” ya karanta a fili cikin zafin nama da faÉ—a Almustapha ya ce “Wanne shirme da hauka ne haka Aliyu? Zina? ÆŠan shege?” Aliyu ya kalli yayan nasa ya ce..
“Ba shege bane” “To uban mene? Aurenta kayi?” Aliyu ya ce “Ko É—aya, ina son ta am ready to marry her, É—a kuma ba shege ba ne” Almustapha ya É—auke Aliyu da mari ya ce
“Mahaukaci, to kayi gaggawar zuwa gidan jaridar nan ka Æ™aryata rubutun su, ina da tabbacin kuma matarka Latifa Omar ce tayi wannan aikin ai a gidan jaridar take aiki”
“Tayi dubun su, ba zai sauya mini ra’ayi ba”
Cewar Aliyu. Almustapha ya ƙara ɗaga hannu zai mari Aliyu,cikin sauri Aliyu ya riƙe hannu ya ce
“Kasan Allah ka Æ™ara marina zan karya hannunka,ka bar ganin kai yaya na ne, idan kun shirya korata kamar yadda Mahaifin Majeederh ya koreta fine I’ll leave the house” abu kamar wasa dambe ya sarÆ™e tsakanin wa da Æ™ani cikin É“acin rai Hajia ta zabgawa Aliyu mari ta Æ™ara zabga masa mari ta ce “Ka nutsu Zaki, ka nutsu” Aliyu ya fashe da kuka ya rungume Mahaifiyarshi ya ce
“What should I do Hajia? Dame zan ji ne? Wallahi idan kuka matsa mini zan iya aikata komai, Hajia I love Majeederh don Allah ki nemo mini ita, hajia hajia….,”
Da Hajia da Almustapha su kayi kan Bar Aliyu Sufyan Alhassan wanda ya faÉ—i a Æ™asa sumamme…

Also Download Wace ce ita (Who was she) Hausa Novel Complete Document

Government House
Labarai ake ta ko’ina gabaÉ—aya kuma akan Malama Majeederh Abdul’aziz Khan ne, Human rights sun shiga maganar, Æ™ungiyar mata ta shiga maganar, shugaban Æ´an hisba. Ya sauke É“oyayyiyan numfashin tare da juyawa kaÉ—an ya kalli tulin jaridun da aka wallafa, gefe guda kuma yana mamakin gidan Jaridar Hausa lastest News, domin sun fi ko wanne gidan jarida É—aukan zafi da kuma aibata Malama Majeederh. Sama sama yake kallon photon ta, bai taÉ“a ganinta ba amma muryarta kullum tana yi masa amsa kuwwa a kunne. “Ham…mad” Hammad ya yi sauri ya rusuna ya ce
“Your excellency” “Waye me wannan Shirman?” Hammad ya Æ™ara yin Æ™asa ya ce “Wata Æ´ar Jarida ce, Latifa Omar”
Abu-turab ya ce.
“A dakatar da gidan jaridar” with so much respect Hammad ya ce
“With pleasure Your excellency” ya jinjina kai kawai, Hammad ya juya cikin sauri. Kai tsaye akai sanarwar da yawun Gwamna tare da bada umarnin rufe gidan Jaridar. Abu-turab ya kasa komawa gida, tun safiyar yake jiran ya ji ance an samu Malama Majeederh Abdul’aziz Khan amma shiru har biyar na yamma ya yi. Tajju ne ke driving hannunsa riÆ™e da Envelope yana ta yawo amma bai samu Majeederh ba, gashi har an kwana wani daren na shirin yi kamar ance masa ya juya idanunsa ya sauka akanta tana nan zaune bakin bolar ta Æ™anÆ™ame jaririn kamar za a kwace mata shi, ta fita hayyacinta duk jini ya É“ata jikinta, cikin sauri Tajju ya gangara gefen titi tare da yin parking yana Hammadala a ransa ya fito,bai san mene a envelope É—in ba amma yasan dole yana da alaÆ™a da wannan jaririn babu ko tabbata musamman yanzu daya tuna wata rana. Yazo daidai tsakiyar titin yana Æ™oÆ™arin tsallakawa wata Æ™atuwar tifa tayi awon gaba da shi….

 

Continue To Page 4

 

#Bar Aliyu Sufyan Alhassan
#Dr Jamal
#Abu-turab

Na’ima Sulaiman Shu’aibu
08119237616
Not

editing

 

Back to top button