Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 80 Complete Novel

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

_Ga duk mai son karanta littafin Abban sojoji,kai tsaye ya tuntu6eni ta numbar wayata 08103884440_

Special thanks to hafsat Usman Abubakar🥰,

“Koda ace baka samu zuwa ba,xamu zo nan damaturun,dama mu ya dace ace mun je can gaba ɗayan mu bayan komai ya lafa,ko don saboda ƴan ukun abusufyan,zamu je dasu don suma suga danginsu dake acan da kuma na zariyya,dana sauran state,”acewar ammi,
Modibbo yace”hakan ma yayi,Allah yayi maku albarka gaba ɗayanku,”suka haɗa baki wurin amsa mashi da ameeeen,

Duk wannan abun dake faruwa Aunty babba da hayaam suna acikin ɗaki,kowannansu ya dafi waya sai danna yake yi,gaba ɗaya tunaninsu ya tafi akan cewa An kori su sehrish,hakan yasa hankalinsu ya kwanta luf,

miƙewa zaune aunty babba tayi daga kishingiɗen da take,fuskar nan a washe tace”Oh ni ƴasu,ko ina waɗannan ƴan ukun suka dosa yanzu?
Hayaam tace”Wama ya sanin masu,suna can suna gagari acikin gari,ƙarshenta ma a samu wata babbar mota zubin ɗan gotte tayi mana awon gaba da kawunansu,”
Fashewa su kayi da dariya,sai da suka tsagaita dayin dariyar Aunty babba tace”duba mun ƙarfe nawa yanzu,agogon wayata ba saiti,”
“kusan Ƙarfe tara fa yanzu,gashi ko abincin dare ma ba mu nema ba,”
Tsoki taja”mtsww,wannan wani irin gidane!A tunani na Azmee ya kamata ace ta kawo mana dinner ɗin mu har cikin ɗaki,ni bansan menene amfanin matar nan ba a cikin gidan nan,bata wani aiki,sae dae ta dafa masu abinci,ta zauna taci ta ƙoshi ta tara tumbi,ta mayar da gidan kamar na ubanta,”
Hayaam ta ɗaura da cewa”Ae kwanaki har magana taso ta gayamun,saboda waccen korarriyar yarinyar,Sehrish take da suna ko wa ma…….”dakatawa tayi da yin maganar sakamakon turo ƙopar da taji anyi,atare suka kai idanunsu wurin,
Azmee ce ta shigo hannunta ɗauke da tray,koda su kayi arba da ita,nan fa suka shiga yin ƴan kame kame na rashin gaskiya,
Basu amsa mata sallamar da tayi masu ba,ƙarasawa tayi ta ajiye masu tray ɗin a ƙasa,sannan tace”abinci ne na kawo maku,bansan ko kuna buƙata ba,naga baku fito kun nema ba,shine nace bari na kawo maku a ɗaki,”
Washe baki suka shiga yi,hankalinsu harya kwanta,da alama bataji gossiping ɗinta da sukeyi ba,
“Mun gode sosae Azmee,wlh kina ƙoƙari sosai acikin gidan nan,ke kaɗae kike duk wasu aikace aikace na gidan nan,shekara da shekaru,baki ta6a gajiyawa ba,kin mayar da dangin nan tamkar naki,bansan meyasa har yanzu kike tare dasu ba,wahalar tayi yawa,yaci ace yanzu kin nemi miji kinyi aure,amma in kika cigaba da zama a haka,rayuwarki zata ƙare ne a matsayin baiwa kuma bazawara,ba wani cigaba,”
Tunda Aunty babba tafara magana azmee ta zuba mata ido tana kallonta,batare da ta ƙyafta idanunta ba,har sai da Aunty babba takai ƙarshen maganar,sannan tace”Bani da amsar da zan baki Laila,amma inaso ki sani dangin nan basu ɗaukeni kamar yadda kikayi tsammani ba,kuma ni bana gajiya da aiki a ƙarƙashinsu,saboda sunyi mun halarcin da bazan ta6a mantawa ba,”
Juyawa azmee tayi da sauri ta kama hanyar fita daga ɗakin,harta ruƙe handle ɗin ƙopar zata buɗe muryar aunty babba ta katse mata hanzarinta da cewa”har yaushe ne zaki cigaba da danne abunda ke zuciyarki?
“Mekenan”!azmee ta tambaya a yayin da ta juyo da kanta tana kallonta,
“Azmee nafa son komai!na son cewa akwai wanda kikeso acikin gidan nan!saboda kin ta6a sanar dani a lokacin baya,ko kin manta”?
Baza kunne hayaam tayi tana sauraronsu,
“Hakane,na ta6a sanar dake,amma yanzu babu wannan a zuciyata,kuma ko a lokacin dana so shi,saboda irin kyautatawar da yake yi mun ne,kuma da tausayin shi da nakeji,na rashin matarshi a kusa dashi,Amma yanzu Alhamdulillah,uwar ƴa’yanshi tana a kusa dashi,babu wata sauran damuwa,

Also Download>>> Mijin Malama Page 1 By Nimcy Sarauta

Murmushi aunty babba ta saki tare da miƙewa daga zaunen da take a gefen gadon,ta tunkari azmee tana cewa”Yanzu ke sai ki haƙura dashi?baki kwaɗayin ki aure shi,ki samu ƙaruwa dashi,ko don ki samu gado acikin gidan nan”? Da alama Aunty babba so take ta tunzura azmee,
Girgiza kai azmee tayi”ni bani da buri akan tara dukiya,bana kwaɗayin abun duniya,saboda sanin cewa komai na tara ƙarshe a gidan duniyar nan zan barshi!albashin da nake samu acikin gidan nan ya isheni in ƙarashe rayuwata dashi,”
Ta6e baki aunty babba tayi,fuskar nan ɗauke da shu’umin murmushin nan tace”Yanzu shikenan kin za6i ki ƙarashe rayuwarki a ƙarkashin wasu kenan?ke baki da ƴancin kanki?wlh azmee bakisan ciwon kanki ba,ban ta6a ganin ƴar wahala irin ki ba,kin ƙuntata rayuwarki,kin ƙasƙantar da kanki,duk don saboda ki faranta ma wasu!har yau babu wani cigaba a arayuwarki,yakamata ace yanxu kin mallaki katafaren gida naki na kanki,kin kuma mallaki mota,kinje hajji da umrah,kin kuma je yawon shaƙatawa dubai da sauran ƙasashe,haba azmee yakamata kiyima kanki adalci,wlh kina cutar kanki,Nidai shawara nake ba……”
Tsawar da azmee ta daka mata ne yasa ta kasa ƙarasa maganar,ba ƙaramin razana tayi da tsawar ba,tamkar ba abakin azmee ta fito ba,
“Ke baki isa ki tunzurani ba,laila!ki iya bakin ki,in ba so kike kija ma kanki ba,ki tsaya a iya matsayinki,nima in tsaya a nawa,idan ki kayi kuskuren shiga gonata wlh ranki zaiyi mugun 6aci,” tana ƙarasa maganar,ta janyo ƙopar da sauri ta fuce,
“Hmmmm Aunty laila,matar nan fa ba zaki ta6a iya canza mata ra’ayi ba,don na lura itama kaifi ɗaya ce,”
Jinjina kai aunty babba tayi aranta tana mai mamakin irin yadda azmee ta daka mata tsawa,sai kace batasan matsayinta agidan Ba,!
Komawa tayi cikin ɗakin ta zauna dirshan a gefen gadon,ranta ba ƙaramin 6aci yayi ba,taso ace taci nasara akan azmee ko don su sami haɗin kanta wurin Cimma burinsu,guntun tsoki taja tare da cewa”Ƴar wahala,sai kace tafi kowa tsoron Allah,kullum haka zaki ganta da cazbi a hannunta tana yawo,”
Ta ƙarasa maganar tare da mayar da idonta kan tray ɗin abincin da azmeen ta kawo masu,yatsina fuska tayi tare da kai hannu ta buɗe warmer ɗin,dambun shinkafa ne yaji kayan haɗi sai ƙamshi yake yi,a plate ta zuba masu nan suka zauna,suna ci ita da hayaam kamar wanda yunwa ta koro,

Azmee kuwa bayan fitarta daga ɗakin nasu,jiki a sanyaye ta wuce ɗakinta,kalaman aunty babba ba ƙaramin 6ata mata rai su kayi ba,zuciyarta ta sosu sosai,daure wa kawai takeyi,da ace bata kai zuciyarta nesa ba da ba abunda zai hana ta wanke fuskar laila da mari!

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

Sam ta manta da hafsat dake kwance a ɗakinta,baiwar Allah tun bayan fitarta daga ɗakin hayaam,ta wuce ɗakin azmee batare da sanin kowa ba azmee ce kaɗae tasan cewa tana a ɗakinta,anan tayi wanka,ta kuma ci abinci ta kwanta,saboda wani irin zazza6i daya saukar mata ajikinta,kwata kwata zuciyarta ba daɗi,tayi danasanin rayuwarta fiye da a ƙirga,idanunta na tsananin son ganin Su Jahad,amma tsoran tunkararsu takeyi,gashi har tsaraba tayi masu don ta basu hmmm,duk in ta tuna irin uƙubar da suka sha a hannunsu,sae ta fashe da matsanancin kuka,tun azmee na rarrashinta har ta gaji ta ƙyaleta,idanunta sun kumbura suntum haka la66anta ma,bakomai take yi ma fargaba ba,fa ce irin hukuncin da Mahaifinta zai yanke mata,don kuwa tasan muddin yaji abunda suka aikata masu jahad,Wlh ba zasu sha ba,su dukan su sae sun fuskanci mummunan hukunci a wurinsa,gaba ɗaya tayi nisa cikin zurfin tunani,taji shigowar azmee cikin ɗakin,buɗe idanunta tayi tana kallon azmee dake shigowa,yanayin yadda taga fuskar azmee ya tabbatar mata da cewar tana cikin damuwa,gefen gadon ta zauna zugudum yayin da idanunta ke cike tab da kwalla,
“AUNTY AZMEE” muryar hafsat ce ta dawo da ita cikin hayyacinta,juyawa tayi bayanta tare da kai idanunta kan fuskar hafsat dake kawance,ƙoƙarin 6oye damuwarta tayi kafin tace”har yanzu bakiyi bacci ba?
Miƙewa hafsat tayi daga zaune,sannan tace”Bazan iyayin bacci ba aunty azmee,inajin tsoron abunda zai biyo baya,nasan cewa daddy bazai ƙyaleni ba,”ta ƙarasa maganar tana faman matse kwallon dake gangarowa akan fuskarta,
“Kidaina sa damuwa aranki hafsat,a yadda kika bani labarin irin ruƙon da kuka yi masu jahad,da farko atare kuka azabtar da rayuwarsu ke da mahaifiyarki amma kuma daga baya kin nuna masu soyayya,ina mai tabbatar maki da cewar wannan soyayyar da kika nuna masu daga baya itace zata cece ki a hannun mahaifinki….”

Also Download Dr Eeshatt Romantic Hausa Novel Complete Document

“Taya kike tunanin hakan zai zame mun mafita aunty azmee?bayan ni ce dakaina,na ɗauki su jahad acikin mota ta,na fitar dasu daga cikin gidan,na damƙa su a hannun wannan mugun mutumin wanda mommy tasa ya zubar mata dasu a daji!”tana magana hawaye na zuba a fuskarta,
“Amma Ae kin sanar dani cewar,Mommynki yaudararki tayi akan cewar gidan marayu zaki kai su ashe zubar dasu take so ayi,”
“Hakane aunty azmee,amma ae su hosana basu son da haka ba!nasan cewa sun tsaneni yanzu,kallon mayaudariya suke yi mun,kuma ba kowa ne ya jawo mun haka ba,fa ce Mommy,”
Ta ƙarasa maganar tare da fashewa da wani sabon kukan,
“Ga shawara”! Cikin shessheƙar kuka Hafsat tace”Ina…sauraronki,koma wata irin shawarace inaso,”
“Gobe da safe tun kafin Abbanki ko Omar suyi yunƙurin tunkarar Su jahad akan maganar,ke ki fara yin hanzarin zuwa wurinsu ki nemi yafiyarsu sannan kiyi masu bayanin cewar bada saninki ba,wannan mutumin ya ɗauke su ya kaisu daji don ya zubar dasu ba,Mommynki ce ta yaudareki akan cewar gidan marayu zai kai su…..”
“Aunty azmee kina ganin in na faɗa masu hakan zasu yarda dani?hosana fa tana da ta6in hankali,daƙyar zata fahimce ni,”
..”kada ki damu,zasu fahimce ki,ki kwantar da hankalinki kawai,kamar kina acikin jirgi mai ya qare,”murmushi hafsat ta ɗan saki,har taji sanyi aranta,fatan ta Allah yasa gobe in taje wurin su Jahad,su fahimce ta,
Sun jima suna tattaunawa atsakaninsu kafin daga bisani,azmee tabar ɗakin hafsat kuwa bargo taja ta lullu6e kanta,sannu a hankali bacci ya ɗauke ta,

Acan falo kuwa bayan komi ya lafa,Ammi tace”Yakamata kowa yaje yayi sallah,ya kwanta ya huta,”amsa mata suka yi da toh,sannan kowannansu ya miƙe tare da nufar Bedrooms ɗinsu,atare Su jahad suka miƙe,saida suka fara yi ma su ammi sallama,ta amsa masu fuskarta asake tare da tunasar dasu akan in zasu kwanta kar su manta suyi addu’a,a ƙarshe dae falon ya rage babu kowa cikinsa,irfan shiya jagoranci Modibbo har zuwa ɗakin da zai zauna kafin gobe,Bayan ya kaishi ɗakin,Azmee ta shirya mashi kayan tea takai masa,kamar yadda ya buƙata,

*Boss Bature*

🤍❤🤍

A 6angarensu sehrish kuwa,bayan sun koma bedroom ɗinsu,alwala kowannansu yayi sannan su kayi salla atare,bayan sun kammala suka haye saman gadonsu,cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya ɗauki Jahad da Hosana,banda sehrish wadda bacci ya ƙaurace ma idanunta,tabbas ɗazu ta tsorata sosai da Ammi ta koresu,abun ya razanar da ita,ta kuma ji matuƙar tausayin Daddynsu,duk in tazo rufe ido,fuskarshi take gani a lokacin daya fashe da kuka yana faɗin cewa sai dai ta tsine mashi amma sai yabi ƴa’ƴan shi,bazai bari rayuwarsu ta wulaƙanta ba,tabbas ba ƙaramin so yake yi masu ba,yana tsananin ƙaunarsu fiye da tunaninsu,lokaci guda abunda ya faru a babban falo ya shiga dawo mata acikin kanta,mikewa tayi daga zaune,ta jingina bayanta a headboard din gadon,yayin da hannayenta ke rungume da pillow,a hankali tashiga tariyo abunda ammi tayi,na bijirema umarnin iyayenta,wanda hakan yasa ita ma ƴa’ƴanta suke bijire mata,Wannan abun ba ƙaramin tsoratar da sehrish yayi ba,saboda tunawa da Umarnin da mahaifinta ya bata na hana ta zuwa sashen sgr da sunan yi mashi aiki,amma taƙi bin umarninsa,hakanan ta dinga jin gabanta na faduwa,runtse idanunta tayi tare da buɗesu a hankali,wasu siraran hawaye ne suka shiga gangaro mata a fuskarta,a hankali la66anta suka soma motsi,ƙasa ƙasa take magana,matsar da kunne na nayi don inji me take cewa,

Also Download Wace ce ita (Who was she) Hausa Novel Complete Document

_Ya Allah ka yafemun!bani da hankali nayi kuskure,saboda kawai son wanda baisan inayi ba,saboda na faranta ma wanda nakeso,naƙi bin umarnin mahaifina,wlh bazan ƙara ba,inajin tsoron nima ƴa’ƴan da zan haifa suƙi bin umarni na,bana fatan hakan ya faru,zan daure nayi mashi biyayya_
Tafin hannunta tasa ta goge hawayen dake zuba a idanunta,bakomai idanunta ke hango mata ba,fa ce kyakkyawar fuskar SGR,tabbas yau yayi masu abunda ba zasu ta6a mantawa ba arayuwarsu,yana da matuƙar kirki sosai,bakowa ne zai gane hakan ba farat ɗaya,shi na musamman ne,samun mutun mai irin kyakkyawar zuciyarshi a wannan zamanin da muke ciki,zaiyi matuƙar wuya,
Zuro ƙafafunta tayi ƙasa daga saman gadon,ta miƙe tsaye,jikinta na sanye da riga da wando na bacci,milk colour,takawa tayi izuwa gaban door ɗin dakin,ta buɗe bayan ta fita ta janyo masu ƙopar ta rufe,
A hankali take tafiya,ga wani irin sanyi dake ɗan ratsa sassan jikinta,amma sam bata jin sanyin,saboda daɗinshi take ji,zura hannayenta tayi acikin aljihun wandon jikinta,kai tsaye ta wuce main palour din,wayaam taga babu kowa kamar yadda tayi tsammani,da alama ma mutanen gidan duk sunyi bacci,hakanan taji tana marmarin tasha Cornflakes acikin wannan daren,juyawa tayi da sauri ta nufi kitchen,within minutes ta fito hannunta ɗauke da Cup,ta cika shi da cornflakes haɗi na musamman tayi mashi,ta zuba uwar madara da bornvita duka ta sanya,ta kuma Tsula sugar,’
Dawowa tayi falon,ta zauna saman sofa tare da aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya,nace sannu ƴar masu gidan,
Motsa cornflakes ɗin ta shiga yi,da cokalin hannunta sae faman jujjuyashi takeyi aciki,kafin daga bisani ta shiga ɗebowa tana kaiwa abakinta tana sha,tana taunarsa kunnuwanta na motsi saboda daɗin da yayi,bakowa ne ya faɗo mata aranta ba fa ce junaid,abokin shiriritarta,murmushi tayi tare da cewa ɗan uwana rabin raina nasan yanzu haka yana can yana sharar baccinshi,da ace idonshi biyu da atare zamu sha wannan cornflakes din,i really missed u junaid,rashin kwanciyar hankali yasa,mun nisanta da juna,amma insha Allah tunda komai ya dai²ta,yanzu bamu da sauran wata damuwa,zamu dinga fita yawan shaƙatawa atare mu dukkan mu,

Also Download Nurul Kalb Hausa Novel Complete Document

Ita kaɗae abunta sai faman sambatu takeyi,kamar wata zautacciya,tana cikin shan cornflakes ɗinnan,ta wutsiyar idonta ta hango mutun a tsaye ƙiƙam,aikuwa hankalinta yayi mugun tashi,kasa juyawa tayi saboda tsoron kar ace dodo ne,tuni jikinta ya fara kerma,dama gata da shegen tsoro,zuciyarta ta shiga bugawa da ƙarfi da ƙarfi,tunaninta wanene mutumin data hango tsaye a upstairs,tsabar tsoro ya hana ta juyawa ta kalleshi da kyau,wani irin wahalallan yawu ta haɗiye,ajiye cup ɗin dake hannunta tayi,sannan ta lalla6e tare da saukowa daga saman sofa ɗin,ta durƙushe ƙasa tayi sujjada,kamar maiyin sallah,duk don saboda kar dodon ya ganta,a hankali ta shiga rarrafawa a ƙoƙarinta na tabar falon,ta koma ɗakinsu,
Shikuwa mutumin dake tsaye goye da hannayenshi asaman ƙirjinshi,zuba ma sarautar Allah ido yayi,abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba,tsoran yarinyar harya so yayi yawa,ko kallon inda ya ke bata yi ba,ta wutsiyar ido kawai taga inuwarsa amma ta sama ranta cewar wani mugun abunne,sam baiso ta tsorata ba,don bada niyar wannan yazo wurin ba,
Wani abune ya faɗo mashi aransa,cikin sauri ya koma cikin part ɗinsa,jimmm kaɗan sai gashi ya dawo hannunshi ɗauke da wayarsa,tsayawa yayi tare da saita wurin da take yana ɗaukarta video kasancewar akwai haske sosai a main falo din,
Ba ƙaramar wahala sehrish tasha ba,da wannan rarrafen ta ƙarasa har wurin da zata shiga corridor ɗin ɗakinsu,gaba ɗaya zufa ta wanke mata fuskarta,tana ƙokarin shiga,wani abu ya faɗo mata aranta,tsayawa tayi tana tunanin kodai ta juya taga wanene shi tunda dae ta iso wurin da zata shiga ɗakinsu,koma menene ai bai isa ya cutar da ita ba,da zarar ta juya taga dodo ne,sae ta watsa da gudu ta shige ɗakinsu,taja ƙopa ta rufe,fakat,
Jikinta na kerma,amma ahaka ta daure ta ɗan juyo da kanta,takai idanunta saman upstairs din,ae batasan lokacin da taƙarasa juyowa gaba ɗaya ba,ta baza idanunta donta tabbatarma kanta abunda take gani,ƙura ido tayi tana son gano wanene saboda yayi mata nisa,wannan hasken fatar nashi ne ya fara sa ta tunanin kamar sgr ne,ƙara zuba ido tayi anan ta hango wannan doguwar sunar kan tashi,tabbas kuwa shine,ajiyar zuciya ta shiga saukewa a fili tace”Ashe babban yaya ne,nasha wahalar banxa,Allah yasa dai ban zubar da cornflakes ɗina ba,
ganin tana kallonshi,yasa ya janye phone dinsa,ya kashe camera ɗin ya tura wayar a short pocket dinsa,da hannu yayi mata Alamar taxo,
Waro ido tayi tare da nuna kanta,don ta tabbatar in ita yake kira,nuna ta ya kuma yi da hannunshi,
Gabanta ba ƙaramin faɗuwa yayi ba rasss,tsoranta kar ya tuhumeta akan meya hanata zuwa part ɗinsa kai mashi Cofee don yau bata je ba,

Download>>> Bintu Diyar Bayi Ce Book 1 Complete Document

Miƙewa tayi kamar wata mara gaskiya,haka ta tunkaresa,kamar an zare mata lakar jikinta,a hankali take tattaka matattakalar stairs ɗin,harta ƙarasa ɗan nesa dashi tukunna ta tsaya,tunda ta saci kallonshi sau ɗaya,tayi arba da faffaɗan ƙirjin nan nashi,gashi babu shirt ajikinsa,Shorts ne kawai black colour ya sanya,kuma ma dai ba ƙaramin kyau yayi masa ba,
Ganin ta tsoge wuri guda,yasa shi moving ya ƙarasa inda take dab da ita,don har saida ta ɗan ja da baya,saboda ƙure matan da yayi,
Lokaci guda tarasa natsuwarta,sai ƴan kame kame take,a ƙarshe ma ta zura hannunta acikin sumar kanta,tana ɗan sosawa,ƙamshin turaren jikinshi ba ƙaramin illa yake yi mata ba,saboda wani yanayin da take tsintar kanta aciki,
gaba ɗaya idanunshi na akan lips ɗinta,mutsu mutsun da takeyi da bakinta,ba ƙaramin tafiya yake yi dashi ba,
Almost 5 mins suna a haka sannan ya buɗe baki da wannan Sexy voice ɗin tasa yace”Meyasa baki yi bacci ba”?
Muryarta na kerma tace”bana jin bacci ne,”
“Okey,that’s y You came out to disturb those who are sleeping”?

sunnar dakai ƙasa tayi tana girgiza mashi kai,alamar a’a,ganin ta dage sai faman sosa gashin kanta takeyi,yasa shi kai hannunsa ya damƙo wrist ɗin hannunta da ta zura acikin sumar kanta yace”ƙaiƙayi kike ji ne”?
A ruɗe tace”eh,”
Jinjina kanshi yayi tare da sakin hannun nata,
..”lemme help u…….’ɗagowa tayi a razane jin abunda yace,ko amsarta bai tsaya ji ba,ya sanya hannunshi tare da zagayo dashi ta gefen waist ɗinta ya tallabota sosai, ya janyota gaba ɗaya ta faɗa asaman wide chest ɗinsa,nan fa hankalinta yabi ya tashi,ta susuce ta zauce ta rasa uwar ubanta,a hankali ya ɗago da right hand dinsa,ya tsoma shi acikin lallausar sumar kanta,wani irin massage ya shiga yi mata,wanda ya haifar mata da wata irin matsananciyar kasala ajikinta,ita kanta batasan lokacin da ta zagaye waist ɗinshi ba da hannayenta duka,ta ƙankame shi sosai kamar zata koma cikin cikinshi,yana jin yadda numfashinta ke fita da zafi zafi,tausasan la66anta sai gogar masa fatarsa suke,sosai sehrish ke shaƙar daddaɗan ƙamshin jikinshi,tana jin kanta a wata irin duniya,wadda ba kalar tamu ba,just like in the dream haka take kallon lamarin,ta rasa gane wai shin SGR sosa mata kanta yake yi ko kuwa,saboda daɗin dake ratsa jikinta yafi ƙarfin a kirashi da daɗin susa kawai,tamkar zata zauce haka take ji,ga wani irin abu dake yi mata yawo a jikinta tamkar zufa,’

Duƙar da kansa ya ɗanyi tare da kai hancinsa ya cusa sa shi acikin sumar kanta,ƙamshin man da take shafama kanta ne ya daki hancinsa sosai ya shaƙe sa,lumshe idanunsa yayi tare da ɗan ware su a hankali ya buɗe su,kafin ya mayar da la66ansa asaman fatar kunnanta,tamkar mai yin whispering haka ya shiga yi mata magana”tell me What did you do in the kitchen when you entered”? Yayi maganar tare da raba jikinshi daga nata,idanunshi tamkar na mai jin bacci,
“Cornflakes na haɗa,saboda in sha,”ta bashi amsa a yayin da idanunta ke kallon yatsun hannunta data haɗesu wuri guda tana wasa dasu,.
“Okey,ɗaukomin cornflakes ɗin,inaso nasha nima,”
Batare da musu ba,ta juyawa da sauri da sauri ta sauka downstairs,a nan saman table,ta ɗauko cup ɗin da ta ajiye,sannan ta dawowa upstairs ɗin ta kawo mashi,miƙa mashi tayi,ya sanya hannu tare da kar6ar kofin,spoon ɗin ya ɗauka tare da ɗan jujjuya shi,kafin ya ciko cokalin yana ƙokarin kaiwa bakinsa yaji tace”Kamar yayi yawa,’ɗan ɗagowa yayi da idanunshi ya kalli fuskarta da sauri ta kawar da nata idanun gefe,saboda taga ya ɗebo da yawa ne kuma mouth ɗinsa is too small shiyasa tayi mashi magana,a ganinta cokalin bazai iya wuce wa ba,ta cikin bakinsa,amma sai gashi ya shanye abunsa,bayan ya tauna cornflakes din,ya ɗan dakata tare da cewa”Bana shan sugar sosai,sannan milk ɗin ma tayi yawa acikinsa,meyasa kika sanya da yawa har haka”?
. shiru tayi tana faman wurga ido,
Miƙa mata cup ɗin yayi tare da cewa”Kar6i kayan ki”hannu tasa ta kar6a,sannan tace”Zan iya tafiya,”?
Hanya ya nuna mata tare da cewa”na ruƙe ki ne”?
Ajiyar zuciya ta sauke,kafin ta juya da sauri da sauri ta sauka donwstairs,duk yana binta da kallo,kitchen ta shiga a tsaye ta ƙarasa shanye cornflakes din ta ajiye cup ɗin,sannan ta fito tare da kai idanunta Upstairs taga in yana nan,a tsaye ta same shi,idanunshi a lumshe,
Juyawa tayi ta kama hanyar zuwa bedroom ɗinsu,adai² corridor din ta kuma tsayawa tare da ɗan waiwayawa don taga in yana nan koya tafi,Again ta ƙara ganinshi a tsaye kuma da alama ita yake kallo,ranta ne ya bata cewar kodai tayi masa bye bye da hannunta,may be ya mayar mata da martani,
ɗaga hannunta tayi tare dayi mashi bye bye,abun mamaki sai gashi ya ɗaga mata hannu yana yi mata bye bye din shima,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta,har batasan lokacin da ta fashe da dariya ba,da gudu ta juya tare da faɗawa bedroom dinsu,
Ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa ya koma cikin part dinsa,bayan ya shiga bedroom ɗinsa,toilet ya fara shiga,bada jimawa ba,ya fito tare da hayewa saman shimfiɗeɗen gadonshi ya kwanta,tare da janyo pillow ya rungume shi asaman wide chest dinsa,yayin da blue eyes ɗinsa ke kallon haɗaɗɗen ceilling ɗin ɗakinsa,ya rasa gane meke damun shi,amma tabbas yana jin missing ɗin wani abu sosai atattare dashi,yana tsananin buƙatar wani abu,wanda baisan menene shi ba~~~~~~~

 

Back to top button