Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 78 Complete Hausa Novel

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

Ƙarasa fitowa tayi daga cikin motar,jikinta na sanye da wani jigunannan lace,anyi mata riga da zani,rigar takai har guiwarta,ta coge É—aurin É—ankwalin nan ture kaga tsiya,tun daga kan wuyanta zuwa hannayenta,duk zinari ne,tsohuwa mai ran Æ™arfe,hajiya Ammi kenan Ummu Hossein,Ummu Azeema,Ummu Abusufyan,kaka ga su junaidu da kuma sehrish,fara ce tass bafullatanar asali doguwa kuma siririya,tsufanta bai hanata yin gayu ba,tsohuwar soja ce wadda tasha gwagwarmaya,kuma itace mace ta farko a lokacinsu data fara ruÆ™e muÆ™amin Major General,kaifi É—aya ce ita,mace mai wuyar sha’ani,mutum mai tsananin haÆ™uri ne kawai zai iya jurar zama da ita,hannunta É—aya na ruke da sandar karfe ta alfarma,yayin da É—ayan kuma yake ruÆ™e da sigari,tana tafiya tana busa ta,har ta hanci hayaÆ™in ke fitowa,

Babu wanda yayi tunanin cewar zatazo da wuri,bata sanarma kowa Æ™arfe nawa zata zo ba,duk sunyi tunanin sae wuraren marece zata Æ™araso,Atare da MG Osman da Captain Adam suka zo,sae Hajiya Sarah Æ´ar wurin yayanta Modibbo,tare da ya’yanta mata su biyu Yasmeen da noor,dukkansu ba zasu wuce shekara ashirin da biyu ba,tunda matasan gidan sukaji zuwan ammi nan fa kowa yasha jinin jikinshi don sun san zuwanta bai cika zama alkhairi ba,duk in tazo sai wani abu ya faru,wannan karan basu san dame tazo ba,gaba É—ayansu sun hallara a main palour É—in suna jiran Æ™arasowarta ciki,mutun É—aya ne bai fito wurin tarbarta ba,bakowa bane face Abusufyan,tun da yaji zuwanta ya kasa samun sukuni,sae faman safa da marwa yakeyi acikin bedroom É—inshi,jikinshi nata kerma ba don komai ba sai don zullumin abunda zai biyo baya,idan tayi arba da triplet É—inshi,duk da yayi ma kanshi alÆ™awarin cewar,koda ace ta koresu to tabbas Æ™afarsu Æ™afarshi,bazai Æ™ara barin rayuwarsu ta wulaÆ™anta ba,duk inda zasu je zai kasance atare dasu,

hayamm kuwa tana la6e jikin window tana leƙen Ammi,tun fitowarta daga mota,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta saboda tana sa ran cewar tuggun da suka shirya,zaiyi aiki,

Lokacin da suka shiga falon,nan fa kowa ya shiga miƙa gaisuwa,abun da zai baka mamaki,ko amsawa wannan batayi kamar mai fama da ciwon baki,sai dae ta ɗaga masu hannu,Azmee ce ta kaisu ɗakunan da aka gyara masu,domin su sauke gajiyar da suka kwaso,kafin zuwa anjima,kowa sai da ya kara zuwa gaishe ta ɗaya bayan ɗaya har ɗakin data sauka,mutun uku ne kawai basuje gaishe ta ba,Sgr,Abusufyan sae junaid wanda bai kaiga fitowa ba daga bedroom ɗinshi,

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

Mg Osman kuwa a nan falon suka zauna tare da Marshal Omar,suna gaggaisawa,saboda anjima ba’a haÉ—u ba sunyi kewar junansu sosai,

Hayaam tana ƙoƙarin zuge glass ɗin windon da take leƙe sai ga Motar Abbas tayi parking cikin gidan,tsayawa tayi tana jiran ganin su wanene kuma suka ƙara zuwa,kodai Aunty laila ce ta ƙaraso ne,bata ƙarasa zancen zucin nata ba,Abbas ya fito daga cikin motar,daga bisani kuma Amani da Amal suka fito atare daga cikin motar,
Ƙura ido Hayaam tayi tana ƙare ma Amal kallo,cike da mamakin wacece wannan Kyakkyawar yarinyar da Amani tazo da ita,A iya saninta dae Amani bata ta6a haihuwa ba,balle harta haifi ƴa kamar wannan,duk yadda taso ta gane wacece yarinyar nan amma hakan ya gagara,kwakwalwarta a toshe take,saboda tsabar mugunta irin tasu tun Amal na ƙarama suka canza mata kamanni saboda uƙubar da take sha a hannunsa,dole hayamm ta kasa gane wacece ita,
“Hayam!”muryar Azmee ce ta karaÉ—e kunnanta,da sauri ta rufe glass É—in windown tare da juyowa tana kallon Azmee,shigowarta kenan É—akin jikinta na Sanye da jallabiya baÆ™a,anyi mata kwalliyar zanen flower blue,veil É—in data yafa ma blue ne,ba Æ™aramin kyau azmee tayi ba,ta wanku sosai,
Ƙarasawa hayaam tayi wurinta tana faÉ—in”Aunty Azmee sae yanzu za’a tuna dani?yunwa kamar zata kashe ni,kowa yana rayuwarshi acikin gidan nan sai ni duk a Æ™untace,”

 

“Ke kika so ki Æ™untata kanki hayam,Sgr yanzu haka ya manta da cewar ya koreki daga gidan nan,zai iya yiwuwa ma ya manta dake gaba É—aya,kuma kinga yau ranar Walima ne mutane duk sunzo,ba dole bane ya ankara dake ba,bama haka ba mutumin da kafin ya É—aga ido ya kalli wani aiki ne a wurinsa,don haka ina baki shawarar ki daina kullan kanki,”
Tun kan azmee ta Æ™arasa maganar hayaam ta soma washe baki,la66anta har rawa sukeyi wurin cewa”An..aunty Azmee kina nufin sgr ya manta da laifin da nayi mashi kuma zan iya fita inyi yawo na acikin gidan nan kamar kowa,’
Jinjina kai azmee tayi tare da cewa”Of course,amma fa hayaam koda gigin wasa kada ki kuskura ki Æ™ara yunÆ™urin zuwa sashen shi!duk yawon da zakiyi ki tsaya a downstairs babu ruwanki da abunda ya shafi upstairs ina fata kin gane”?
yatsina fuska tayi tana fadin”dama ni Aunty azmee me zai kai ni,waccen karan ma tsautsayi ne da Æ™addara,”
“Sannan kuma,kada ki kuskura ki Æ™ara shiga shirgin Sehrish!kinsan dai yanzu tafi Æ™arfinki nesa ba kusa ba,Æ´ar masu gida ce ita,kuma shalelen daddynsu,ga kuma yayyanta maza muddin kikace zaki ta6ata wlh zaki ta6o ma kanki ne,akanta sae abaki Red card na barin gidan nan,”
ta6e baki hayaam tayi,tana faman hura hanci,maganar ba ƙaramin ƙona mata rai tayi ba,don bata da yadda zatayi ne,
Murmushi azmee tasaki tare da juyawa ta kama hanyar fita tana faÉ—in”Yakamata kiyi wanka,ki shirya saiki fito ayi shagalin dake,”
Cikin sauri ta ruÆ™o rigar Azmee tace”Aunty Azmee don Allah ki taimakamun wlh yunwa nake ji,tun jiya da daddare rabona da Abinci,”
“Its Okey,zan kawo maki yanzu,”
Komawa ciki hayaam tayi tana jiran azmee ta kawo mata abinci taci,kafin tayi wanka ta kimtsa,
bayan su Amani sun shigo cikin main palour É—in,anan suka zauna suna gaisawa dasu kanal yousouf,kafin tabar wurin tare da Amal,wurin Azmee taje suka gaisa tayi masu kwatancen É—akin Hajiya Azeema da kuma na gwaggo,duk saida tabisu ta gaishe su,hatta É—akin Abusufyan saida suka je,sukayi mashi Allah sanya Alkhairi,daga nan suka dawo kitchen,lokacin Azmee tana haÉ—a ma Hayaam lunch É—in da zata kai mata,
Juyowa tayi jin sallamarsu tace”har kun dawo”?
Amani tace”Eh,duk naje nayi masu Allah sanya alkhairi,yanzu abunda ya rage mun inason zuwa wurin dasu yaran suke,bansan a wani É—aki suke ba,’
Azmee tace”Ae suna nan É—akin da Sehrish take,ae kinsan É—akinta wanda ke a kusa da namu,yakamata kuje wurinsu,’
Murmushi Amani ta saki aranta tace”ba dole inje ba,ni da nakeson na gyara tsakanina da Sehrish,”
A fili kuma tace”okey,nagane É—akin bari muje wurinsu,”
Juyawa sukayi atare da Amal suka nufi ɗakinsu sehrish,abakin ƙopar ɗakin suka tsaya,Amani ta kwankwasa ƙopar,jahad ce ta buɗe kopar,ba ƙaramin kyau tayi ba,wankan swiss lace ne ajikinta wanda aka haɗa da bazin shadda,stones work ne ajikin kayan wanda ya ƙara fito da ɗinkin sosai,
Murmushi Amani ta sakar mata tare da cewa”Sehrish ce ko”?ta tambaya ne saboda Abbas ya sanar da ita cewar kamanninsu É—aya sak,
Martanin murmushin jahad ta mayar mata kafin tace”A’a,ba ita bace,tana ciki in kira maki ita ne,”ta Æ™arasa maganar tana kallon Amal wadda itama jahad É—in take ta kallo,

Also Download Dr Eeshatt Romantic Hausa Novel Complete Document

Amani tace”bari mu shiga daga ciki,sai mu gaisa,”
Matsa mata hanya jahad tayi suka shiga cikin É—akin,
A lokacin Sehrish na kwance saman gadon ta É—an kishingiÉ—a,tana hutawa,saboda ba Æ™aramin gajiya tayi ba,sun sha zurga zurga,gashi Anjima za’a fara walimar bayan Sallar la’asar,shiyasa ta dawo É—aki don ta huta,kafin lokaci yayi,ganin Amani yasa ta miÆ™ewa daga zaune tana kallonsu,
Wuri Amani ta samu daga gefen gadon ta zauna,Amal ma ta zauna,tun kafin ma Amanin tace wani abu sehrish tace”Sannunku da zuwa,”hakan ba Æ™aramin daÉ—i yayi ma Amani ba,tayi tunanin zata ga akasin haka ne,
“Yawwa,fatan mun same ku cikin koshin lafiya”?
Sehrish tace”Lafiya lou Alhmdllh,”
Amani tace”kin gane ni ko”?murmushi kawai sehrish ta saki,taya za’ae ta manta da matar da tace zata iya rasa ranta idan ta cigaba da shisshige ma matasan gidan,
“Ina fata dai baki ruÆ™e ni aranki ba?dan Allah ki manta da komai dana ta6a faÉ—a maki,komai ya wuce,yanzu zumunci ya Æ™ullu atsakaninmu,ko wancen karon ma da nayi maki wannan maganar,wlh bada wata manufa na faÉ—a maki hakan ba,”
Jinjina kai Sehrish tayi tare da cewa”babu komai,ae ya riga ya wuce,”
Ba Æ™aramin daÉ—i Amani taji ba,juyawa tayi tare da kallon jahad dake tsaye tace”zo ki zauna mana,inaso muyi fira tare daku,”zagayawa jahad tayi ta 6angaren hannun hagu ta zauna daga gefen gadon,
Amani tace”ina cikon ta ukun take ne?Abbas ya faÉ—amun cewa ku Æ´an uku ne,”
Jahad tace”hakane,hosana ce babu,taje wurin yaya Omar ne” shiru Amani ta É—an yi tana maimaita sunan hosana a cikin zuciyarta,kamar ta ta6a jin sunan abakin wani,”ke ya sunanki”?
“Ni sunana jahad,” jinjina kai amani tayi tare da cewa”Suna mai daÉ—i,amma nifa bansan komai ba,agame daku,sehrish kawai nasani tana aiki a gidan nan,”
Jahad tace”ae mu muna a wurin ya Omar ne,shi ya taimake mu a lokacin da muke cikin mawuyacin hali,bayan Æ™addara ta rabamu da Æ´ar uwarmu,”
..A ruÉ—e Amani tace”Hannun Ya Omar”
Jahad tace”eh,”
Cike da son jin Æ™arin bayani Amani ta kuma cewa”Kun zauna a kaduna ne”?
Ita kanta jahad sai da gabanta ya faÉ—i jin Amani ta ambaci kaduna kai tsaye,taya akai tasan cewa sun zauna a kaduna,
DaÆ™yar ta iya bata amsa da cewa”Eh,mun zauna acan,daga baya ne Ya Omar ya dawo damu Abuja,gidan daddynmu,”
Tashin hankali,miÆ™ewa amani tayi da sauri jikinta na rawa tace”Ga Amal nan Æ™anwata ce,in ba damuwa ta zauna a wurinku,”
Amsa mata sukayi da toh,cikin sauri ta fuce daga É—akin,kallon juna jahad da Sehrish suka yi atare,duk sun lura da yadda Amani ta ruÉ—e,

Also Download Wace ce ita (Who was she) Hausa Novel Complete Document

“Wacece wannan Sehrish”?jahad ce tayi mata tambayar,sehrish tace”matar yaya Abbas ce,Aunty Amani,”
Taso ta Æ™ara tambayarta,amma saboda Amal dake zaune a wurin yasa tayi shiru,tabbas ta so taga kamannin Aunty babba kaÉ—an a fuskar Amani,duk da Amani tafi kyau sosai,kuma ita bata da jiki irin na Aunty Babba,miÆ™ewa jahad tayi tare da cewa”Zan fita yanzu zan dawo,”
Sehrish tace”adawo lafiya,”
Bayan jahad ta fita,Sehrish ta kalli Amal dake zaune,rashin sabo yasa ta kame kanta wuri guda,
Murmushi tasakar mata tare da cewa”ki saki jikinki mana,naga duk kin gaza samun natsuwa,ko dan bamu ta6a haÉ—uwa bane?”
Sunnar da kai Amal tayi tana murmushi,wata irin kunyace da ita,daÆ™yar ta iya cewa”banta6a zuwa nan ba,yau nafara zuwa,bazan iya sakin jikina ba,tunda bansan kowa anan ba,”
Sehrish tace”Ae kuwa yanzun nan zansa ki saba dani,da farko dai ki dinga kirana da Aunty Sehrish,saboda ina kallon Æ™aramar fuskar nan taki nasan cewa na girme ki,tsawo ne kawai gare ki,amma a shekaru ba zaki wuce sha huÉ—u ba,ko nayi Æ™arya”?
dariya Amal tayi tana girgixa kai tace”A’a bakiyi Æ™arya ba,shekarata sha huÉ—u amma na kusa kai shekara goma sha biyar,nan bada jimawa ba,”
“Kice zamu zo yanka cake ko”?acewar sehrish,
Amal tace”Eh,zan gayyace ku idan lokacin yayi,”
Sehrish tace”Nima na kusa cika shekara sha takwas,banma sani ba ko na kai shekara sha takwas ko ban kai ba,nifa banma son ranar da aka jefo ni duniya ba,ni dai kawai na ganni ina yawo na ne….’kasa Æ™arasa maganar tayi saboda dariyar da Amal ta kwashe da ita,abu kamar wasa sai gashi cikin lokaci Æ™ankani sun saba da juna,nan suka zauna suna ta fira atsakaninsu,

Amani kuwa tun bayan da ta fita daga ɗakinsu sehrish,tarasa inda zata tsoma kanta,abun ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,Aunty babba ta sanar da ita cewar tasa an zubar da yaran da Omar ya kawo mata,kuma tace mata ƴan biyu ne yaran,hakan na nufin cewar jahad ne da hosana a wurinshi?kamar yadda jahad ta sanar da ita cewa su A wurin yaya Omar suke,indae dagaske hakane to taya akai Yaran suka dawo wajen Marshal Omar bayan tasa an zubar dasu!?kodai Omar ya sanya ɗan leƙen asiri ne acikin gidan?tabbas hakan zai iya faruwa,indai kuwa hakane Watan cin uban Aunty laila ya tsaya,Zuwa maiduguri ba fashi,
Acewar Amani wadda ke ta faman yin safa da Marwa a tsakanin corridor É—in É—akunansu sehrish,daga bisani tace”Allah yaso ni ban tsoma hannu na ba,a wurin cutar dasu ba,ashe da rabon aure na yayi lasting,Aunty babba kam ta shiga uku,taja ma kanta bala’e,kwara ma da hakan ya faru,da nayi niyyar É—aukar ma Amal fansa,amma yanzu na fasa,zan zuba idone kawai inga yadda dramar nan zata kaya,”ta Æ™arasa zancen zucin nata,fuskarta É—auke da murmushi,ba komai take hangowa ba face yadda rayuwar Aunty babba zata Æ™are,……..’

Bayan fitar jahad,kitchen ta wuce ta shirya lunch acikin tray,kamar ita zata ci,upstairs ta wuce dashi,adai dai Æ™opar É—akin junaid ta tsaya tare da sanya hannunta É—aya,ta É—an bubbuga Æ™opar É—akin,wata murya taji daga cikin É—akin ta amsa mata da cewa”Wanene”?muryar kuma bata junaid bace,
“Ni ce,” ta bashi amsa ataikace
“Kece wa”?
“Jahad,”shiru taji anyi mata kafin,harta fidda rai da za’a buÉ—e mata,tana Æ™oÆ™arin barin wurin taji alamun ana buÉ—e Æ™opar,tsayawa tayi har ya kammala bude kopar,ganin fuskar wani daban bata junaid ba yasa tasha jinin jikinta,musamman yadda taga fuskar mutumin a murtuke babu fara’a ko misÆ™ala zarratin,
“Wa kike nema”?
Muryarta na rawa tace”Wurin junaid nazo,naga ban ganshi ba duk yau,”
“Shine kika zo kawo mashi abinci?yace maki yana jin yunwa ne”?shiru jahad tayi masa batace komai ba,da alama dae wannan ba Æ™aramin masifaffe bane,
“Wuce ki shiga,”ya faÉ—i hakan tare da matsa mata hanya ta wuce ciki,shi kuma ya fuce daga É—akin,

Also Download Nurul Kalb Hausa Novel Complete Document

jikinta sai kerma yakeyi saboda tsoran mutumin da tayi arba dashi,hakanan taji tsanarshi aranta,kuma sam baiyi mata kama da mutanen kirki ba,
Lokacin da ta Æ™arasa shiga É—akin a kwance ta samu junaid,daga shi sai farar shirt da short fari a jikinshi,ya kwantar da kanshi asaman pillow,idanunshi na arufe,ajiye mashi tray É—in tayi asaman front table É—in gadon nasa,sannan ta samu wuri daga gefen gadon ta zauna tare da ambaton sunanshi”junaid,”
A hankali ya buÉ—e idanunshi tare da azasu akan fuskar jahad,yanayin shi ya nuna tamkar baijin daÉ—in jikinshi,idanunshi kansu sun marairaice,
Bai tanka mata ba sae da ya gama Æ™are mata kallo sosai,saboda ya tantance wacece acikinsu,tashi yayi daga zaune sannan yace”Jahad ko”?
É—aga mashi kai tayi alamar eh,sannan ta Æ™ara da cewa”duk yau ban ganka ba,shiyasa nace bari nazo na duba ka,hada abinci ma nazo maka dashi,duk da bansan ko kana jin yunwa ba,”
“Thanks for your caring,duk yau babu wanda ya damu dani,sai ke kawai,naji daÉ—i sosai,”yayi maganar tare da sauko da Æ™afafunshi Æ™asa,hannu yakai zai É—auki jug,ta riga shi É—aukar jug É—in tare da cewa”bari na zuba maka,”dakatawa yayi ta tsiyaya mashi lemu mai sanyi acikin cup,sannan ta miÆ™a mashi,yasa hannu ya kar6a,tare da kai cup É—in saitin bakinshi yana kur6a,
binshi tayi da kallo,yayi wani irin haske fari fat,kamar mara jini a jiki,hakanan ta dinga jin wani irin tausayinshi na shigarta,ga tsananin ƙaunarshi da takeyi kamar kamar me,
Har ya kammala shan lemun bata sani ba,juyawar da zaiyi suka haÉ—a ido dashi,kawar da idonta tayi gefe guda tare da yin saurin cewa”Kamar baka lafiya ko”?
“Me kika gani”?
“Kawai yanayinka na gani,kamar na wanda bashi da Æ™oshin lafiya,”
“Lafiyata Æ™alou,don inajin yunwa ne shiyasa kika ganni haka,amma da zarar naci na Æ™oshi,zan dawo dai dai,”
“Kasan kana jin yunwa amma meyasa baka tashi ka nemi abinci ba”?tayi maganar a yayin da take janyo plate ta shiga zuba mashi fried rice aciki,
“Tun safe fa naketa yin bacci,ni kaina bansan ya akai nayi bacci mai tsayi ba,kuma dana tashi jikina duk ba Æ™wari,shiyasa bansamu na sauko downstairs ba,saboda kasalar data baibaye ni,
“Kuma baka sha wani abu ba?kamar maganin bacci”?
Shiru junaid ya É—anyi yana tunani kafin yace”a’a bansha komai ba,amma ya haroon ya kawo mun wani tea a cup wuraren Æ™arfe takwas yace mun insha,kuma saida na tambayeshi maganin menene yace mun maganin Æ™ara kuzari ne,shine nasha,tun daga lokacin nidai ban Æ™ara sanin meke wakana ba,yanzu ma da kika ganni a kwance tashi na kenan,kuma shi ya tashe ni,yace mun in tashi inyi wanka in shirya,lokacin walima ya kusa,”
É—agowa jahad tayi tare da kallon fuskarshi tace”Wannan mutumin daya fita yanzu shine Ya haroon”!?
É—aga mata kai yayi alamar eh,
ta kuma cewa”Wanene shi?don ban ta6a ganinshi ba a gidan,”
Junaid yace”Shima yayan mu ne,bai cika zama gida bane shiyasa baki ta6a ganinshi ba,”
“Kada na cika ka da surutu,ka fara cin abincin,”
MaÆ™e hannayensa yayi tare da cewa”Hannu na ciwo yakeyi mun,”murmushi ta saki tare da kai hannu ta É—auki cokali tana faÉ—in”bari na baka abaki to,”

Also Download ABBAN SOJOJI BOOK 2 Hausa Novel Complete Document

É—ebowa ta dinga yi tana tura mashi abakinshi yana Ci suna fira,gwanin ban sha’awa,a haka harta samu yaci abincin sosai,sannan ya tashi ya shiga toilet wanka,zama tayi tana jiran fitowarshi saboda yace ta jira shi,su fita atare,hakan ba Æ™aramin daÉ—i yayi mata ba,a sannu a sannu dai junaid ya fara sakewa da ita,Allah sarki

*Boss Bature*

Bayan Sallar la’asar,kowa ya É—auki wani sabon wankan,Amani da kanta tayi masu Jahad makeup ita da Hosana da Sehrish,gaba É—ayansu suka sanya Swiss lace ajikinsu,wanda aka É—inka masu shi domin su sanya a aranar walimar,riga da skirt ne ba Æ™aramin kyau kayan sukayi masu ba,sun wanku iya wankuwa,yadda kasan dollar wurin kyau haka suka koma,Suna acikin É—akin nasu Su huÉ—u hada Amal,in aka haÉ—a da Amani sun zama su biyar kenan,zama tayi tana Æ™arasa gyara masu É—aurin É—an kwalin da tayi masu,

A Can ciki kuwa Matasan gidan duk sun hallara,Azmee da Saude ne suke ta ɗawainiyar bin kowani table dake a wurin suna Jejjera abinci kala kala,daga bayane hayaam ta samu damar fitowa daƙyar,tun tana ƴan kame kame kamar mara gaskiya har dae ta fara sakewa,tashiga tayasu Azmee kai ma baƙi lemu,

A hankali Motarsu Aunty Babba,ta shararo izuwa cikin gidan,a dai dai parking space,hafsat ta tsayar da motar,tare da juyawa ta kalli fuskar Mommyn nata dake ta faman jan minshari,tunda suka taho ta kama bacci acikin motar,hannu hafsat tasa tare da bubbuga kafadarta,a firgice Aunty babba ta farka tana fadin”Har mun Æ™araso ne,”
Hafsat tace”eh mana,gamu acikin gidan ma,kin barni da driving kina ta sharar bacci,’
Yamutsa fuska Aunty babba tayi tare da buÉ—e motar tana faÉ—in,wlh agajiye nake,ga baccin ma bai isheni ba,kuma yunwa ma nake ji,’
Bayan motar ta tsaya tare da buɗe Boot ɗin motar,ta curo trolley ɗin kayansu,tare da saukko dashi ƙasa,
Sai da hafsat ta sanya niqabin da ta siya a hanya sannan ta buÉ—e motar ta fito,hannunta ruÆ™e da Æ´ar purse É—inta,ganinta da niqabi yasa Aunty babba jan guntun tsoki tare da fadin”Yau naga ikon Allah,kamar wata Munafuka,kin nace dae yau sai kin sanya wannan baÆ™in abun a fuskarki,kamar wata Æ´ar shi’a”
“Mommy ba zaki gane bane,”
Tayi maganar tare da kama hanyar shiga cikin gidan,bin bayanta aunty baba tayi tana fadin”ba zaki zo ki kar6i trolley É—in ba”
“Haba Mommy,Duk aikin driving É—in da nayi,kuma sai na wani É—auki trolley,ae ke yakamata ki janyoshi,tun fa da muka kamo hanya kike ta bacci,kika barni da aiki,nima agajiye nake bazan iya É—aukar shi ba,”
“Kar Allah yasa ki É—auka toh,”suna tafe suna magana har suka shiga cikin Main palour É—in,Hayaam najin sallamar Aunty babba,ta wani saki ihu har saida hankalin kowa ya dawo kanta,da gudu taje ta rungumota tana faÉ—in”Wayyo Allah aunty laila,tun dazu nake ta baza ido inga zuwanku amma shiru,har na fara fidda rai da zuwanku ashe kuna hanya,”tayi maganar tare da raba jikinta daga na aunty babba,fuskar nan awashe Aunty babba tace”Mezai hana mu zuwa,naso na sanar maki wlh mantawa nayi,koda yake bacci fa nayi a mota,hada Æ™arin haka yasa ban samu na kira ki awaya ba,’
“Gaskiya nayi kewar ku sosai,”acewar hayaam tayi maganar a yayin da take mayar da idanunta akan Hafsat dake sanye da niqabi,a ruÉ—e tace”Kai!wai hafsat ce sanye da niqabi,”
Hannu hafsat ta sanya tare da É—an É—age niqabin tace”Nice mana,gaba É—aya hankalinki na akan mommy dayake kinfi damuwa da ita,”
Washe baki hayaam ta kuma yi tare da rungumo hafsat ajikinta tana faÉ—in”Sorry bangane ki bane wlh,kema ce kin sanya niqabi kamar wata mara gaskiya,”
Suna cikin magana muryar Azmee ta katse su da cewa”maraba da manyan baÆ™i,Yau su hajiya laila ne a gidan namu,wata sabon gani,yau za’ayi ruwa da Æ™anÆ™ara,”
Dariya sukayi gaba É—ayansu,kafin daga bisani Aunty babba tace”Ae wannan zuwan na musamman ne,Har sai kun gaji damu Allah,”tana magana hafsat na zungurinta alamar ta daina faÉ—in zasu jima,amma zafin É—umi yasa ko lura batayi ba balle ta ankare,
“Ae tunda na ganku da trolley É—in kayan nan nasan cewa zaku jima mana anan,wataÆ™il ma har sai an aurar da Æ´a’Æ´an namu tukunna,kunga sai ayi agabanku,’
Gaban aunty babba ne ya faÉ—i rass,a razane tace”Auren wasu Æ´a’Æ´a kenan”?
dariya azmee tayi tare da cewa”Ƴa’Æ´anku mana na wurin Abusufyan,”
É—aure fuska Aunty babba tayi tana fadin”haba dae,wani aure kuma ana zaman lafiya,daga ganin yaran kuma sai ki fara yi masu fatan yin aure,duka nawa suke,bana ji ance Æ´an shekara sha bane,’
kafin azmee ta kuma cewa wani abu hafsat tace”Dan Allah mu shiga ciki mu zauna,wlh agajiye nake,gashi ko salla ma ba muyi ba,”
Atare suka Æ™arasa shiga ciki,bayan sun kammala gaisawa da mutanen dake zaune a babban falon,daga bisani hayaam takaisu bedroom É—inta,suna shiga ciki hafsat ta cire niqabin data sanya,tai wurgi dashi saman gadon,tashige toilet don ta É—auro alwala,a Æ™agare take da tayi arba dasu jahad,duk da tsoran karsu canza mata,musamman in suka tuna abubuwan da sukayi masu a gidansu,tana cikin toilet tajiyo muryar hayaam tana fadin”Tun jiya fa na tura maki hotunan nasu,baki gani bane,kuma har hafsat saida na kira a waya na sanar da ita don ta tunasar dake,’
Aunty babba tace”Gaskiya ni banga wani hoto ba da kika turamun a whatsapp É—ina,mu barma zancen tunda dae gani acikin gidan zan gansu da ido,batare da nasha wata wahala ba,’
Hayaam tace”Ae yanzu haka suna can cikin É—akinsu tare da Amani…’
Cike da mamaki Aunty babba tace”Amani kuma?Ubanme ya haÉ—ata dasu da har take shiga É—akinsu?Oh ni yau naji ikon Allah,wannan shisshigi da kutsu irin na Amani,”

Also Download FARRAH Hausa Novel Complete Document By Maman Shuraim

“Nima azmee ce ke sanar dani cewa tana a É—akinsu wai tanayi masu kwalliya,ni duk bama wannan bane damuwata ba,Akwai wata kyakkyawar yarinya fara da Amani tazo da ita,na rasa gane wacece yarinyar nan,kuma fuskar yarinyar sak irinta amanin ce,”
Aunty babba tace”To fa,ko ina tasamu yarinya,zai iya yuwuwa fa daga gidan marayu Abbas ya É—aukko masu ita don su raina,kinfa son cewa basu ta6a haihuwa ba,’
“Bari naje ciki,kada azmee taji ni shiru,ina É—an tayata aiki ne,’acewar hayaam
Harara Aunty babba ta watsa mata tare da cewa”dama aiki na turoki kiyi acikin gidan?shiyasa naga duk kin zabge,nida zanzo inga ko’ina na jikinki ya cicciko,amma sai uban Æ™asusuwan wuya,kamar wadda tayi jinya,’
Tsuke fuska hayaam tayi tana faÉ—in”Bakisan halin dana shiga bane,shiyasa zaki ce haka,tunfa da Sgr ya kore ni daga gidan nan,ban Æ™ara samun kwanciyar hankali ba,kullum ina Æ™umshe acikin É—aki saboda tsoran kar muyi arba dashi,ga ciwon yunwa dake damuna,ba don azmee ba ae da tuni na jima da sheÆ™awa,itafa ce take kawomun abinci har É—akina,wani lokacin in ta manta bata kawo mun ba,sae dai fa in dare yayi kowa yayi bacci in saci hanya inje kitchen in É—ebo abinci,gaskiya nasha wahala sosai,
“Laifinki ne hayaam,kina zaman zaman lafiyarki acikin gidan nan,Amma kika toÆ™ano masifa,kirasa wa zaki kaima hari sai Sgr,ae wlh ki godema Allah dabai kakkaryaki ba,nikaina nayi mamaki da kikace iya korarki yayi kawai,’
Tur6une fuska hayaam tayi tare da juyawa tana fadin”Ni dae mu bar maganar ae yariga da ya wuce,kuma ma ae ya yafe mun,bakiga yanzu ina yawo na hankali kwance acikin gidan ba,”
Aunty babba tace”Allah yasa dagaske ne cewar ya yafe maki É—in,sai kiyi taka tsantsan kafin mu samu Allah ya cika mana burin mu,don wannan karon da shirina nazo,Bazan bar gidan nan ba,har sai naga an shafa fatihar aurenki,keda Sgr,”
Cike da farin ciki hayaam ta sanya tafin hannunta tare da rufe fuskarta tana sakin dariyar farin ciki,
“Aunty laila kina ganin hakan zai yiwu kuwa?ga Yaran nan Æ´a’Æ´an abusufyan,wlh ba Æ™ananu bane balle ace basu isa aure ba,Sun kaifa sha Takwas inaji,kuma wlh bakiga surar jikinsu ba,matane sosai,ni tunda nagansu ma duk sai naji na tsani kaina,kuma kinga su Æ´an gidane za’a iya tunanin haÉ—asu auren Zumunci…’
Tunkan ta Æ™arasa maganar aunty babba tace”Impossible!wlh bazai ta6a yiwuwa ba!Muddin ina numfashi É—aya daga cikinsu bazata ta6a auren Sgr ba,kwara ma Omar abra saita haÆ™ura amma Allah sgr ya Haramta agaresu na haramta masu shi,da bala’e sai ya aureki,ko anaso ko ba’aso,babu wani shege daya isa ya hana wlh,babu shi,”yadda Aunty babba ke cika baki tana magana ba Æ™aramin dariya ya so yaba hafsat ba dake acikin toilet tana sauraronsu,ita batasan halin da suke ciki ba,sae faman kuri take tana cika baki,
Ita kuwa hayaam sae faman washe baki takeyi,gaba daya ta miƙa yardar ta ga Aunty babba,ae gani takeyi zata iya aikata komai don ta mallaka mata Sgr,
Bayan fitar hayaam daga É—akin Hafsat ta fito daga cikin toilet din,idonta na akan Aunty babba data É—an kishingiÉ—a asaman gadon,
“Mommy yakamata kije kiyi sallah,kinsan fa yanzu za’a hallara gaba É—aya wurin waleemar yakamata ki hanzarta yin sallar,”
yatsina fuska tayi tare da cewa”Anya zan iya yin sallar nan kuwa,nagaji sosai,zuwa anjima dai nayi sai in haÉ—a da magriba duka inyi,”
girgiza kai kawai hafsat tayi batare da ta ƙara cewa komai ba,don ba yau ta saba yin haka ba,ita kanta hafsat ɗin zamanta dasu jahad ne ta fara yin sallah cikin lokacinta,

Zaune yake agefen gadonshi ya zabga uban tagumi,tun bayan da suka dawo daga sallar la’asar,yadawo É—akinshi atakure,turo kopar É—akin nashi Abba yayi tare da shigowa ciki,ba Æ™aramin tausayi abusufyan ya bashi ba,wuri ya samu tare da zama daga gefenshi sannan yace”Bana faÉ—a maka cewa ka kwantar da hankalinka ba?jibi yadda duk kabi ka tukura kanka,”
É—agowa yayi tare da kai idanunshi kan abba,muryarshi asanyaye yace”bansan ya zanyi bane,hankalina yaÆ™i kwanciya wlh,bansan wane hukunci Ammi zata yanke mun ba,ni tsorona kada tace bata yarda cewar da aure na samu su jahad ba,kasan halinta yaya hossein,tana da wuyar sha’ani,”
Abba yace”hakane,amma insha Allah zanyi iyakar bakin Æ™oÆ™arina wurin ganin na fahimtar da ita,kaima kasan cewa bazan ta6a bari yaran nan su tozarta ba akan idon kowa,Ammi tana buÆ™atar hujjoji masu Æ™arfi kafin ta gasgata abu,zamuyi kokari wurin ganin cewa munyi amfani da hujjojin da muke dasu a hannu wurin fahimtar da ita,abunda nakeso dakai yanzu ka saki jikinka,nasan cewa da anjima kaÉ—an idan ta farka daga bacci zata fito nan babban falon,so nake kazo da Æ™warin guiwarka ka gaishe da ita,kasan kun jima baku haÉ—u ba,kuma dama can kai mai laifi ne a wurinta,’
fuskar Abusufyan cike da damuwa yace”Hada Æ™arin hakan yasa nake fargabar haÉ—uwa da ita,Ni kullum mai laifi ne a wurinta,ko kirana ma bata É—agawa,tunda nabar nigeria shekara goma sha,amma mommy bata ta6a É—aukar waya da sunan zata kira ni ba,kuma ko na kirata bata É—agawa,ni ina ganin kamar bata so na ne,shiyasa takeyi mun haka,’
ruÆ™e hannunshi abba yayi acikin nashi”abunda kake tunani ba haka bane,zanma iya cewa tafi sonka fiye da kowa,kuma ta damu da kai sosai,babban laifin da kayi mata shine naÆ™in sanar da ita dalilin da yasa kabar Nigeria,ammi batasan komai game da tafiyarka ba,tayi kewarka sosai,don akwai lokacin da ta kirani a waya,kuka ne kawai batayi ba a lokacin,saboda ka tafi batare da saninta ba,wannan dalilin ne yasa take fushi dakai,amma yanzu ina da tabbacin cewar in har muka sanar da ita dalilin tafiyarka,zata fahimce mu,kuma zata kar6i yaran nan hannu bibbiyu,kuma zata yafe maka”
Jiki asanyaye abusufyan yace”Allah yasa,dana fi kowa farin ciki,”
Murmushi abba yayi tare da miÆ™ewa tsaye ruke da hannun abusufyan yana cewa”Tashi muje ciki,nasan yanzu haka triplet É—inka suna nan,sun É—au wanka suna jiran daddynsu don suyi hoto tare dashi,”

Also Download Idan Ba Ke Hausa Novel Complete Document By Na’ima Sarauta

Jin haka yasa Abusufyan sakin fara’a a fuskarshi nan take yaji damuwarshi ta ragu saboda an ambaci Æ´an ukunshi,
atare da abba suka fito daga cikin É—akin,adai dai lokacin Hajiya Azeema da gwaggon katsina da saude suma duk sun fito,kowa yasha kwalliya a fuskarshi,ga harris shima tare da Marshal Omar duk sun hallara anan falon,A jere su Sehrish suka fito su uku Ita dasu jahad hosana,sae Amal dake abayansu tare da Amani,
Ae tunda suka shigo cikin falon hankalin kowa ya dawo kansu,yadda kasan wasu taurari haka suka bayyana,kai tsaye wurin abusufyan suka nufa,haÉ—asu yayi su duka ya rungumesu sosai,bayan ya sakesu,suka gaishe da Abba tare dasu Marshal Omar dake tsaitsaye a wurin,Hannu abba yasa tare da jan kumatun hosana yace”Amaryar Omar,irin wannan kyau haka,”da sauri tasa hannu tare da rufe fuskarta,tana dariya,kawar da kai gefe Omar yayi yana É—an sakin Murmushi,da zasu bashi dama da ba abunda zai hana ya rungumota don ba Æ™aramin kyau tayi mashi ba,matsowa kanal yousouf yayi kusa dasu yana fadin”Uncle ni wacce za’a bani acikinsu tunda ya Omar yayi kamun tashi,kada su Æ™are ni in rasa,”dariya sukayi gaba dayan su,Uncle abusufyan yace”Layi zaka bi,don mutun ko da kuÉ—inshi saida rabonshi,” Abba ya kar6e da cewa”kwarai kuwa,sae wanda ya dage da sallar dare zamu bamawa,”
daga bayansu suka jiyo muryar junaid yana cewa”Kamar ni kenan,duk gidan nan babu wanda yakai ni tashi yin sallar dare,”ya Æ™arasa maganar tare da ruÆ™e qugunshi,fuskar nan É—auke da wannan kyakkyawan murmushin nashi,yayin da idanunshi ke akan jahad,
fashewa suka kumayi da dariya,kanal yousouf yace”haba junaid,cewa zakayi duk gidan nan babu wanda yakai ka,sharar bacci idan dare yayi,mutumin da daÆ™yar ake tashin shi sallar asuba shine yake cika baki yana faÉ—in yafi kowa sallar dare,”
bubbuga Æ™afa junaid yayi cike da shagwa6a yace”Kai yaya yousouf dan Allah ka daina faÉ—in haka,kada kasa araina ni,”
“Raini kuma na yaushe junaid!agabansu fa kake bubbuga Æ™afa kamar Æ™aramin yaro kana shagwa6a,a haka kake cewa kar araina ka,wace mace ce zata so ta auri shagwa6a66an namiji irinka?acewar kanal yousouf,
Tur6une fuska junaid yayi yana faman zumbura baki,juyawa yayi tare da kai idanunshi kan abusufyan yace”Uncle,ae dai zaka bani kyautar É—aya ko”?
Abusufyan yace”mezai hana junaid?ko sisi bana buÆ™ata,duk wacce kakeso acikinsu,zan baka ita kyauta,basai ka biya sadaki ba,” gwalo yayi ma kanal yousouf yana fadin”ae dae Uncle yace zai bani,kuma a kyauta ma,”
Hakan ba Æ™aramin dariya ya basu ba,duk wannan rashin wayon da Junaid ke yi akan idon jahad,zubama sarautar Allah ido tayi,aranta tace wai dama haka yake?saboda ita bata ta6a ganin junaid na shagwa6a agabanta ba,hada su gwalo É—abi’unsa kamar na yaron goye,kaÉ—an kika gani

Cike da nishaÉ—i sukeyin firar tasu,adai dai lokacin General ishaq da Abbas suka shigo cikin main palour É—in,sae faman sakin fara’a suke yi,Æ™arasa shigowa sukayi kai tsaye suka nufi inda su Abba ke tsaye,gaishe da abba sukayi,kafin su jahad suka haÉ—a baki wurin gaisar dasu,

Fuskar ishaq É—auke da murmushi yace”Masha Allah,nama rasa abunda zance,yanzu wannan duk namu ne”?yayi maganar yana nuna su hosana,Abba ne ya bashi amsar cewa”Naku ne ishaq,halak malak Allah ya mallaka maku,gasu nan harsu uku,”
Abbas yace”kamar yadda Allah ya nuna mana wannan ranar da ranmu kuma da lafiyarmu,ina fata Allah ya Æ™ara haÉ—amu a ranar auransu kamar haka dae……..’ haÉ—a baki su Abba suka yi wurin cewa”Ameen,”banda abusufyan wanda ya sunnar da kanshi Æ™asa yana murmushi,Sehrish da jahad kuwa duk kunya ta gama rufesu,
Abba yace”ko baku son auren ne”? Shiru su kayi suna faman Æ™umshe dariya,

“Sun ma isa suce basa so?ga yayyansu nan duk tazurai,ae dole su bada hadin Kai asamu a rufa ma juna asiri,” cike da zolaya ishaq yayi maganar,yayi matuÆ™ar basu dariya.

Adai dai lokacin Aunty babba ta shigo cikin falon ita da Hafsat😲

 

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Danna Inda Aka Saka Download Now


Back to top button