Hausa novels

Abban Sojoji Chapter 69 Book 2 Complete Novel

Abban Sojoji Chapter 69 Book 2

The Father Of Soldier

Written By: Boss Bature

Duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za’a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata  zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari*,

 

 

Bayan wani lokaci

 

 

Tafiya takeyi tamkar batason taka ƙasa,jikinta na sanye da uniform na islamiyya,dogon hijab Brown colour har wuce guiwarta,wandon kuma milk colour,ta rufe fuskarta da nikab,yayin da hannayenta ke ruƙe da jakar makarantarta,da gudun gaske wata danƙareriyar mota ash colour ta faɗo cikin layin da take tafiya,gadan gadan mai motar ya tunkari inda Abu taja ta tsaya,waro ido waje tayi tare da ja da baya jikinta na kerma,koda mai motar nan ya ƙaraso inda take,sai ya shiga zagaye ta da motar gaba ɗaya ya tada mata ƙura,

Ƙanƙame jikinta tayi gabanta ya faɗi rass,tsoronta kar ace sace ta aka zo yi,

Sai da ya tabbatar da cewa ta gama tsorata sannan ya tsayar da motar wuri guda ta tsaya cak,

A ɗan tsorace abu ta buɗe idanunta tana kallon motar cikin ranta tana tunanin wanene wannan bawan Allahn daya firgitar da ita haka,

Bata ƙarasa zancen zucin nata ba taga ya zuge glass ɗin motar,lokacin da tayi arba da kyakkyawar fuskarshi sae da gabanta ya faɗi rasss!matashi ne wanda bazai gaza shekara 20 ba zuwa ashirin da daya,kana kallonshi zaka ga ƙuruciya atare dashi,jikinshi na sanye da crazy jeans sae farar t shirt agaban rigar an rubuta Am crazy,’da alama bashi kaɗae bane acikin motar,akwai wani agefen shi,

 

Muryar mace tajiyo daga cikin motar tashi tana cewa”Hey,ƴan mata,mun tsorata ki ko?ki yi haƙuri Babyn nawa ne sae a hankali,wai kin burge shi ne,shiyasa yayi maki wannan wasan,’.

rai atsananin 6ace take kallon fuskokinsu ta cikin niqab din fuskarta,bakowa yafi bata haushi ba face shi saurayin daya yi mata wannan ɗanyen aikin,arayuwarta ta tsani mutane masu wayewa irin tasu,kallo guda tayi masu ta gane cewa ba mata da miji bane,amma sun manne ma juna acikin motar kamar zasu haɗe su zama ɗaya,

jinjina kai kawai tayi tare da zuƙunnawa ta ɗauki jakar islamiyyarta da ta fadi,cikin sauri ta kama hanyar zuwa gida,biyo ta sukayi da motarsu,hakan yasa hankalinta ya tashi,saboda gudun kada Abbanta ya ga motar dake biye da ita,don kullum yana ja mata kunne akan karta kuskura wani ya tsaidata akan hanya ta tsaya,yanzu in ya ganta  tare da wannan jibgegiyar motar dake bin bayanta batasan wane hukunci zaiyi mata ba,dole ya tuhume ta akan ina ta samo su,

“Baby,kana ganin zata faɗa mana address ɗinta kuwa?da alama yarinyar kamar za tayi ji da kai nake gani,kasan ƴan islamiyyan nan,ji su keyi kamar sunfi kowa tsoran Allah,suyi ta kame kansu acikin hijabi,suna yi ma mutane kallon shaiɗanu,’matashiyar dake acikin motar ce tayi wannan maganar,kuma duk akan kunnan Abu,

Saurayin yace”ae ko bata faɗa mana address ɗinta ba,zamuyi ta bin bayanta ne har mu gano gidansu,”

Jin wannan maganar yasa,yarinyar zuƙunnawa tare da kwale takalman ƙafafunta,kafin su ankara ta watsa da gudun gaske kamar zata tashi sama,ko waiwayensu batayi,har ta 6ace ma ganinsu,,

 

Tun daga nesa Baba buzu mai gadin dake a zaune saman benchi yana sauraron radiyo dake ruke a hannunshi,ya hango ta sai faman tsala gudu takeyi,hankali tashe ya miƙe tsaye yana jiran ƙarasowarta,koda ta ƙaraso a galabaice ta zube agabanshi,saman guiwowinta tana faman haki,

 

“Abu meya faru ne naga kina gudu haka?waye ya biyo ki”?

Muryar mahaifin nata ne ta dawo da ita cikin hayyacinta,

daƙyar ta iya cewa”wasu ne a mota,bansan kosu wanene ba,sae faman bibiyata sukeyi,shine na watso da gudu don karsu gane gidan da nake,”

Jin wannan maganar yasa ran buzun mai gadin ya 6aci sosai nan fa yashiga zazzaga masifa yana cewa”da kin bari sun ƙaraso don ubansu dana koya masu hankali,shikenan ba dama yarinya ta ɗan fita ɗauko karatu sae an samu wanda ya takura rayuwarta!zan yi maganin koma wane ɗan ja’irin ne yake son cutar mun dake…..’ta inda yake shiga batanan yake fita ba, a ƙarshe dae yace”tashi ki shiga ciki,kiyi wanka kici abinci ki kwanta ki huta kafin akira sallar magariba,ki kwantar da hankalinki kinji Abunah,ina nan ina jiran Koma wane ɗan iskan ne,saina koya masu hankali,’

Ajiyar zuciya abu ta sauke tare da miƙewa tayi mashi sallama,sannan ta shiga cikin gidan ta ƙopar gate ɗinsa,

Lokacin da ta shiga cikin main palour ɗin gidan babu kowa,alamar suna can upstairs bedrooms ɗinsu,don haka ta wuce nata ɗakin kai tsaye,

 

Bayan ta ajiye jakar islamiyyarta,ta cire hijab ɗin jikinta,ta ninketa tare da turata cikin wardrobe na kayanta,shaf shaf ta kammala cire kayan islamiyan nata ta wuce cikin toilet don tayi wanka,

 

After some minutes,ta fito daga cikin toilet ɗin jikinta ɗaure da farin towel,jikin nan nata har wani ƙalli yakeyi saboda hasken fatarta ga gyaran da take sha,agaban mirror ta tsaya tana ɗaure sumar kanta mai tsayi da yawan gaske,tana da yalwataccen gashin kai wanda yakai har qugunta,tana cikin ɗaure gashin kan nan nata kwatsam taji anyi mata gyaran murya abayanta,a firgice tajiyo don ta ga kowanene,lokacin da tayi arba da mutumin da yayi mata gyaran muryar acikin ɗakinta nan take ta zazzaro ido amatuƙar tsorace take kallonshi,

kwance yake asaman gadonta,ya miƙe ƙafafunshi yayin da hannunshi ke ruƙe da brazier ɗinta da ta cire kafin tashiga toilet,sae faman latsa breast curve ɗin yakeyi cike da tsokana,

Hankali a matukar tashe abu tace”innalillahi wa’inna ilaihirraji’un…Nashiga uku….!’gaba daya taba ma ranta cewa al’jani ne shi,ba kowa bane wannan face saurayin nan daya tsoratar da ita da motarshi akan hanyarta ta dawowa daga islamiyya,shi da budurwarshi,

Muryarta na rawa tace”wa..wanene…kai dan Allah!me kakeso a wurina ne!taya akai kasan gidan mu har ka biyoni ɗakina”?

Ƙayataccen murmushi ya saki tare da cewa”bani da amsar tambayoyinki,ni dai kawai nagani inaso,in kika yi mun biyayya mu rabu lafiya,koda yake bazama mu ta6a rabuwa ba,saboda kinyi mun wlh,” ya ƙarasa maganar tare da kai bakinsa ya manna ma bra ɗinta kiss

Runtse ido abu tayi agigice ta fasa ihu tana neman ɗauki,akan azo a fidda mata aljanin dake aɗakinta,

Da gudu ta watsa waje babban falon jikinta na kerma ta shiga cewa”Mommy!!mommy!!ya haris!daddy!!dan Allah kuzo ku taimake ni,Aljani aɗakina saman gadona….’

Jin sautin kukan Abu yasa hankalin Hajiya ameena tashi,da saurin gaske ta sauko downstairs ta nufi wurinta tana cewa”Abu meya faru ne kike ta kwaɗa ihu?

Cikin shessheƙar kuka tace”Wani ne acikin ɗakina saman gadona,bansan ko wanene shi ba,a kan hanyar dawowata daga islamiyya ya tsoratar dani da motarshi,shine yanzu kuma bayan na fito daga wanka na ganshi kwance saman gadona,’

Cike da mamaki hajiya Ameena tace”Wani kuma!acikin gidan nan saman gadonki?taya akai har ya samu damar shigowa cikin gidan nan….’

Ba ta kaiga ƙarasa maganar ba,sae ga Abusufyan ya fito daga cikin ɗakin abun,fuskarshi ɗauke da murmushi,

Ganin shi yasa abu yin saurin nuna shi da hannu tace”Ga shi nan mommy….wlh shine ..Aljani ne,”

murmushi hajiya Ameenatu tayi tana kallon Abusufyan tace”Son sai yau kaga damar dawowa gidan?irin wannan zuwan bazata haka?ka tafi kabarmu da kewarka ko?ko tunanin makaranta bakayi ba,ka kama hanya ka tafi kan abunda bai kai ya kawo ba,’

Langwa6e kai abusufyan yayi yana tsuke bakinshi alamar an 6ata mashi rai,

…zuru abu tayi tana kallon ikon Allah,aranta tana cewa”Ashe ɗan masu gidan nan ne,ni duk atunanina aljani ne shi,amma dae da alama baijin magana sosai,’

“Pls mom just forget about it,komai ya wuce tunda dae nadawo,”

Jinjina kai hajiya ameenatu tayi,kafin ta mayar da idanunta kan Abu dake tsaye sototo tana kallonsu tace”Calm down ur mind Abuna,wannan da kike gani ɗan yayata ne,sunan shi Abusufyan,bai jin magana amma kada wannan ya hanaki sakewa dashi,shima ki ɗauke shi tamkar Yayanki Haris,’

Jiki asanyaye tace”insha Allah mommy,”kafin ta ɗan wurga ido ta kallo shi har lokacin kashe mata ido yakeyi,hakan ba ƙaramin haushi yake bata ba,har tafara jin tsanarshi,

 

Tun daga ranar da Abusufyan ya dawo cikin gidan abu ta shiga uku dashi,ya hana rayuwarta sakat,duk inda ta sanya ƙafarta yana biye da ita,toilet ne kawai bai binta shi dai kawai burinshi ta sake dashi kamar yarda take shiri da haris,ita kuma tace bazata ta6a ɗaukarshi yayanta ba,saboda bai da kamun kai,bakomai yaja mashi hakan ba face Abubuwan da yake yi mata na rashin kunya,da kuma ƴan mata da take ganinshi tare dasu manne da juna,hakan ba ƙaramin ƙona mata rae yake yi ba,duk a tunaninta Abusufyan ɗan iska ne kamar yana bin mata,saboda ita tayi believing da abunda idanuwanta ke nuna mata,

 

Ana haka wata rana malamin nan nasu Sayyadi ya ɗaukota daga islamiyya asaman machine dinsa super cub,tun suna akan hanya motar abusufyan ke bin bayansu saboda ya hangota abayan mashin ɗin malamin,ranshi yayi mugun 6aci wani irin kashi ne ya lullu6e shi,saboda ya lura akwai soyayya tsakaninta da malamin nan nasu,babu yarda abusufyan baiyi da ita ba akan ta bari ya dinga kaita school amma taƙiya,da yake tana da kafiya sosai,mace ce mai wuyar sha’ani,

 

A bakin gate ɗin gidan sayyadi ya tsayar da mashine ɗinsa,abu ta sauko hannunta ruƙe da jakarta,tsayawa tayi suna ƙara gaisawa dashi,

“Abu har yanzu baki bani amsa ta ba”?

Sunnar da kai ta ɗanyi tana murmushi tace”amsar me kenan”?

sayyadi yace”oh har kin manta kenan?abu kinfa san ina sonki sosai,kuma kema kina sona,bana buƙatar mu 6ata lokaci atare da juna batare da munyi aure ba,banda burin daya wuce wannan, in ganki amatsayin matar aure na,’

Cike da jin kunyarshi abu tace”dan Allah ka ƙara mun lokaci,zanyi tunani akan hakan,’

Kafin sayyadi ya buɗe baki ya ƙara yin wata maganar,suka ji dirar motar Abusufyan agefensu,tun daga kan yarda yayi parking ɗin motar ya tabbatar masu da cewar ba’a hayyacinshi yake ba,

.zuba ma motar ido sayyadi yayi kafin ya mayar da idonshi kan abu yace”wanene acikin motar nan”?

Muryarta na rawa tace”yayana ne Abusufyan,’

ɗan ta6e bakinshi yayi yana jinjina kai,

Atsiyace abusufyan ya buɗe murfin motar ya fito,jikinshi sai faman rawa yake yi,kai tsaye wurinsu ya nufo sai faman huci yake yi,

Wani irin mugun kallo ya jefa mata tare da nuna mata hanyar gida yace”Ke wuce ciki!tun kafin ranki ya 6aci shashasha kawai wadda batasan ciwon kanta ba!ki rasa da wa zakiyi mu’amala sae wannan ƙarmasasshen mutumin,ko uban miye abun so ajikinshi!mutumin da ya kusa tsaran ubanki!”

Hankalin abu ba ƙaramin tashi yayi ba jiki na rawa ta kama hanyar shiga gida,

Muryar sayyadi ce ta dakatar da ita”Abu kada ki tafi!bangama magana dake ba,”

Zuba ido abusufyan yayi yana kallon ikon Allah,tsayawa abu tayi saboda umarnin da sayyadi ya bata akan karta tafi,

Rai amatuƙar 6ace Abusufyan ya daka mata tsawa tare da cewa”ke!har ni zan baki umarni kiƙiyi mun biyayya saboda wannan munafukin mutumin malamin ƙarya!”

Waro ido waje sayyadi yayi yana kallonshi,

Abu kuwa jin an ta6a masoyinta yasa tace”Abusufyan ya isa haka!karka ƙara zagar mun malamina,wannan mutumin da kake gani yafi mun kai so dubu,saboda yana da ilimin addini kuma shi yake koyamun karatu,mutum ne shi mai kamun kai ba kamar kai ba….’jin kalaman abu akan shi yasa sayyadi ya shiga sakin murmushi yana kallon Abusufyan dake tsaye zuciyarshi na tafarfasa,

Tuni idanunshi sun ciko tab da kwalla saboda bai iya jurar 6acin rai ba,Zainab ta bada shi awurin malaminsu,

daƙyar yake iya haɗiyar yawun bakinshi da ya gama ƙafewa,jinjina kanshi ya shiga yi kafin daga bisani ya soma magana cikin sanyin murya”Naji duk abunda kika ce abu,amma inaso ki sani bakowane malami bane yake zama mutumin kirki,don kawai ya ruɗe ki da karatun kur’ani yana jawo miki aya da hadisi yana fassara maki su,shine yasa kike tunanin cewa shi mutumin kirki ne?mutun nawa kika sani yana da haddar al’qur’ani akanshi amma hakan bai hana shi aikata zunubin daya ga dama ba…..”?

ɗaure fuska sayyadi yayi yace”Kaga ɗan saurayi yarinyar nan ta nuna cewa bata sonka,dan Allah karabu da rayuwarta mana haba,ita malami takeso mahaddacin al’qur’ani ba ɗan tasha ba mai yawo da mata acikin gari,’

Wannan maganar ba ƙaramin fusata Abusufyan yayi ba,har baisan lokacin da ya ware tafin hannunshi ba ya kifa ma sayyadi mari asaman kuncinshi,kafin abusufyan ya zame hannunshi daga kan fuskar Sayyadi yaji saukar mari ɗauuuu a kan fuskarshi agigice ya juya yana kallonta hankalinshi amatuƙar tashe bai ta6a tunanin cewa abu zata iya ɗaga hannu ta mareshi ba,tunda yake arayuwarshi ko dunguri wannan wani bai ta6a gigin yi mashi ba,sai yau da Abu ta mare shi saboda ya mari sayyadinta,

Hawaye ne suka soma gangarowa daga cikin idanuwanshi,muryarshi har kerma takeyi wurin cewa”A..ab..bu..ni kika mara saboda na mari wannan ƙasƙantaccen mutumin mai fuska biyu!?

ɗaga hannu tayi zata ƙara kwasa mashi mari,kamar daga sama taji an ruke hannunta kafin tayi wani aune kuma taji saukar mari zazzafan gaske akuncinta,

A firgice ta juya tana kallon shi,bakowa bane ya mare ta ba,face mahaifinta shi da kanshi baba buzu,

Fashewa tayi da matsanancin kuka tana cewa”baba…yau kai da kanka ka mare ni?”

A faɗace yace”idan kika sake buɗe baki kikayi magana saina kikkifa maki wasu marukan,sakarya kawai wadda batasan halacci ba,yanzu saboda wannan mutumin kika mari abusufyan ko?

wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarshi jin yarda mahaifinta ya goya mashi baya,sayyadi kuwa ranshi ba ƙaramin 6aci yayi ba,sae faman mazurai yake yi,

Kafin yace”haba baba buzu,ni kake kira da wannan mutumin?ka manta matsayin da nake dashi awurin ƴarka?nifa ne malamin dake koya mata karatun addini,ya kamata ka darajani,kuma abunda abu tayi ba kuskure bane,yaron nan rashin kunya yayi mani dole ranta ya 6aci,dan Allah kaja mashi kunne ya daina yi mana shisshigi saboda ni da abu son juna mukeyi kuma aure zamuyi……’

Tunkan ya ƙarasa maganar baba buzu ya daka mashi tsawa tare da cewa”ubanwa zai auraka maka ita!ko ita take da ikon aurar da kanta ne!Ni ne mahaifinta kuma ni nake da ikon na aurar da ita ga wanda naso,kuma naga ya dace da rayuwarta,don haka tun yau inaso ka cire ta aranka,abu nayi mata miji,kuma ba kowa bane mijin nata ba face ABUSUFYAN!muddin ina numfashi abu bazata ta6a auran wani ba in ba shi ba!!!

Hankali tashe abu ke kallon mahaifinta da idanuwanta da sukayi jawur saboda kukan da tasha,mayar da idonta tayi kan Abusufyan dake ta faman sakin murmushi,girgiza kai tashiga yi tana cewa”baba…ni banason abusufyan,bai dace da rayuwata ba,ba mutumin kirki bane shi,bai da kamun kai,kuma baida ilmin addini,boko kawai yasa agaba,wayewarshi tayi yawa baba…..’

Ganin yarda mahaifinta ya harzuƙo zai rufe ta da duka yasa ta watsa aguje cikin gidan tana kuka,

“Yanzu abunda kayi ya dace baba buzu?yarinyar nan ta nuna tana son malamin addini mahaddaccin al’qur’ani saboda ya tarbiyantar da ƴa’ƴanta,ta san cewa idan ta aure ni zan bata kyakkyawar kulawa kuma zan ilmantar da ita da kuma ƴa’ƴan mu saboda me zaka hana ta aure ni!?kafi son ta auri wannan sangartaccen da baisan komai ba sai yawo da ƴan mata acikin gari?ahaka kake tunanin zai bama ƴarka tarbiyya in ya aure ta?

sayyadi nakai ƙarshen maganarshi baba buzu yace”Ka gama sambatun naka?to kama hanya kabar ƙopar gidan nan tun kafin raina ya 6aci,banason ganinka tare da abu,don ban yarda dakai ba,akwai wata mummunar manufa atare dakai na son cutar da ƴa ta,shiyasa naji baka kwanta mun araina ba,amma abusufyan ya kwantamin araina,duk da ya kasance yana da ƙananun shekaru amma ina da tabbacin cewa yafi ka hankali da tunani……..’

Jin wannan maganar ta baba buzu yasa hawaye sauka a idon sayyadi muryarshi a kasalance yace”Wai me nayi maka ne ka tsane ni?me na tsare maka ne?dama tunda na fara zuwa gidan nan ina koya ma abu karatu na lura da irin kallon da kakeyi mun,meyasa baba buzu?ko don na kasance malamin makaranta banda arziƙin da zan iya siyen zuciyarka ne?saboda banda kuɗin da zan dinga baka cin hanci don ka auramun ƴarka zainab,sae shi daya taso gidan naira,kasan cewa idan ka aura mashi abu tattalin arziƙinka zai bunƙasa,baba buzu ka tabka babban kuskure arayuwarka muddin ka aura ma abu wannan sangartaccen yaron……..’

Yana kai ƙarshen maganar shi ya tada rugwagwar mashin dinshi yabar wurin,

matsawa baba buzu yayi tare da dafa kafadar Abusufyan cikin rarrashi yace”kayi haƙuri abusufyan,duk sai naji na tsani kaina da abu ta ɗaga hannu ta mare ka,ni ina da tabbacin cewa wannan malamin dake bibiyar rayuwarta ba mutumin kirki bane,ba don Allah yake son abu ba,tabbas akwai wani abu dayake son cimmawa atare da ita,’

Abusufyan yace”baba kada ka damu komai ya wuce,kuma ina baka haƙuri game da kalaman da sayyadi yayi maka,banji daɗinsu ba,’

Baba buzu yace”babu komai yaje don kanshi,Allah na gani ba don komai yasa nakeson ka auri abu ba,sai don saboda in saka ma mahaifiyarku da irin ɗawainiyar da take damu ni da ƴa ta abu,wlh bani da burin daya wuce wani acikin ƴa’ƴanta ya nuna yana son abu ni kuma in aura mashi ita,wannan ce kawai hanyar da nake da ita da zan iya sakamata,’

Murmushi abusufyan yayi tare da cewa”Baba yanzu in na nemi auran abu a wurinka zaka aura mun ita?a yadda nake da ƙananun shekarun nan”?

baba buzu yace”mai zai hana?ni lokacin da iyaye na sukayi mun aure ban kai shekarunka ba,kuma muka zauna da matata lafiya har Allah ya al’barkace mu da samun zainab,abusufyan in har dagaske kana son abu,kuma zaka ruƙe mun ita amana,na amince kayi ma Abbanku magana ya nema maka auranta awurina nikuma zan baka ita,kai tun ma yanzu inaso ka sama ranka cewa abu ta zama matarka,saboda na mallaka maka ita,sadaki kawai zaku biya a aura maka ita,’

wani iri farin cikine ya lullu6e abusufyan,saboda tsabar farin ciki baisan lokacin daya ɗauki baba buzu ba ya daga shi sama yana jujjuya shi,dariya sosai baba buzu yayi yana cewa”Abusufyan ka sauke ni mana!ko nauyi na baka ji!duk murnar na mallaka maka abu ne yasa ka ɗauke ni haka kamar diyar roba,

Sosai sukayi nishaɗi atsakaninsu,

 

Lokacin da abu ta shiga falon gidan tana faman zabga kuka,hajiya Ameena na ganinta ta tashi daga zaunen da take saman kujera ta tunkareta tana tambayarta lafiya,

adai dai lokacin Mijinta Alhaji nuraddeen yana kan saukowa ƙasa daga saman bene,tun kan yaƙaraso yake tambayarsu me akayi ma abu take kuka,

cikin shessheƙar kuka tace”Baba ne yace zai auramun abusufyan kuma ni bashi nakeso ba sayyadi nakeso in aura……’

Jin wannan maganar ta abu yasa hajiya ameena ta ɗaure fuskarta tace”Abu yanzu saboda mahaifinki ya za6a maki abusufyan amatsayin mijin da zaki aura shine kike kuka!meyasa bakya son shi ne?

Muryar daddy ce ta katse mata hanzarinta”Wannan abun bazai ta6a yiyuwa ba!babu yarda za’ae abu ta auri Abusufyan yaron da bai gama mallakar hankalinshi ba!ban goyi bayan wannan maganarba,zanje na samu mahaifin naki muyi magana dashi,indai aure yakeson yi maki sai dae ya aura maki sayyadi saboda shi ya mallaki hankalinshi zai iya kula dake amma ba abusufyan ba,’

Wurga mashi wani kallo mai kama da harara hajiya Ameenatu tayi tare da cewa”Wannan abun bai shafeka ba alhaji!babu ruwanka da shiga shirgin Abusufyan,tunda ubanta da kanshi ya mallaka mashi ita,babu wanda ya isa ya dakatar dashi daga auranta!aure kamar anyi an gama ne’

murmushi kawai alhaji nuraddenn yayi yana girgiza kai yace”oh kema kin goyi bayan Abu ta auri abusufyan?bayan kinsan halin shi sarai bai jin magana,kuma yarinyar nan ta nuna cewa bata son shi,dan Allah karku takura rayuwarta,ku bari ta auri za6in ranta karku tilasta mata!kuma sannan ke kin manta da cewa Yayarki hajiya Aishat bazata bari abusufyan yayi aure da ƙuruciyarshi ba!kuma kin manta da tsarinta na ƙin auren bare”?

ta6e baki hajiya ameenatu tayi kafin tace”ni wannan bai dame ni ba,ba’a auran bare ita ta auri amininka salahuddeen?ko tana da alaƙa dashi ne?ba haɗuwar barikin sojoji bace,’tayi tambayar tana kallonshi,

Cigaba da magana tayi,”idan kuma kuruciyarshi kake magana,kai kamanta kana da shekara nawa na aure ka?wasan ƴar 6urun 6urun muka dinga yi dakai adaren farkon mu ko ka manta da wannan”?

Bakin Alhaji fa ya mutu shiru yayi bai tanka mata ba,don bai da amsar da zai bata,

guntun tsoki taja kasa² tare da mayar da idanunta kan abu dake tsaye hankali tashe tana kallon mommyn jin ta goyi bayan auranta da abusufyan,

“Abu,kiyi hakuri ki bi za6in da mahaifinki yayi maki,ni ina da tabbacin cewa bazaki ta6a dana sanin auran abusufyan ba!nasan kina yi mashi kallon mutumin banza ne saboda son mu’amalarshi da mata,amma inaso ki sani abusufyan ɗina ba ɗan iska bane,kuma shima yana da ilmin addini fiye da tunaninki,shigar ƙananun kaya da yake yi da kuma yawan manne ma matan da yakeyi hakan ba yana nufin cewa shi mutumin banza bane,zainab abunda nakeso ki sani,bata suttura kota kalaman baki ake gane mutumin kirki kona banza ba,wannan azuciya yake,zaki iya ganin mutum malamin addini mai haddar al’qur’ani kanshi kullum sanye cikin jallabiya yana wa’azi bainar nasi,alhalin zuciyarshi baƙa ce yana aikata wasu muna nan abubuwan a6oye batare da sanin kowa ba sai mahalincinshi ,haka zalika zaki iya samun mutumin da kullum yake ɗabi’u irin na turai,sanya ƙananun kaya,hulɗa da mata rashin jin magana da sauransu amma kuma zaki samu zuciyarshi kyakkyawa ce tsarkakakkiya bai sa6ama ubangijinshi,ki daina yarda da abunda idanuwanki suke nuna maki abu,tun farko kinyi ma abusufyan mummunan zato shiyasa kika tsane shi,amma ni nasan cewa kina sonshi kamar yarda yake sonki,bansan me malamin can ya faɗa maki agame dashi ba,dayasa har kika za6e shi akan jini na,to inaso ki sani muddin kinason ganin farin cikina,tun daga rana irin ta yau ki cire soyayyar wancan mutumin aranki,ki fara koyama kanki soyayyar Abusufyan,kafin aɗaura auranku.,…….’

Murya na rawa abu tace”..mo..mommy..ke ma kin amince in auri abusufyan in rabu da sayyadina?

Jinjina mata kai hajiya Ameenatu tayi alamar Eh,

Fashewa da kuka Abu tayi tare da watsa wa da gudu ta shige ɗakinta saman gado tana kuka tana faɗin”Ni bani sonshi bana son abusufyan bazan aure shi ba,sayyadi nakeso,’kamar zautacciya haka tashiga sambatu har bacci ya ɗauketa,

 

Alhaji dae bai ƙara tanka masu ba saboda baisan 6acin ran matarshi,ya zuba ma sarautar Allah ido,yana kallon ikon Allah,

 

Batare da 6ata lokaci ba,hajiya Ameenatu ta biya sadakin abu dubu ɗari ta damƙa ma mahaifinta,shi kuma ya damka ma zainab kuɗin a hannunta,daƙyar ta kar6i kuɗin,ko da ta koma ɗakinta dasu,wurgi tayi dasu asaman gadonta,ta koma tana sharar kwalla,

 

Duk wannan budurin da akeyi,iyayen Abusufyan basu son da zancen auren abusufyan ba,tun lokacin da Hajiya ameenatu ta kira Ammi awaya take sanar da ita cewa Abusufyan yaga yarinyar mai gadin gidansu yana so,tun kafin ta rufe bakinta ammi ta katseta a fadace tace”Kar na sake jin wannan zancen,ki rabashi da yarinyar don karya sama ranshi ita,ni bazan ta6a aura mashi yar mai gadi ba mara asali,ƴa’ƴana bazasu auri bare ba,auran zumunci zanyi masu,”tun da hajiya Ameenatu taji wannan zancen na yayarta ta tabbatar da cewar bafa zata amince abusufyan ya auri abu ba,saboda ita kaifi ɗaya ce in ta furta abu babu wanda ya isa ya dakatar dashi!

 

Koda Hajiya ameenatu ta sanar ma Abusufyan abunda mahaifiyarshi tace na ƙin amincewa da aurenshi da abu,ranar har zazza6i yayi yaƙi cin abinci kuma,duk yabi ya hargitse ya shiga damuwa sosai,hakan yasa hankalin hajiya yayi mugun tashi saboda ta mutu akan son Abusufyan,batason ganin damuwarshi,shiyasa ta yanke shawarar aura mashi abu batare da sanin iyayenshi ba,ko wani daga cikin danginsu don kar Ammi ta samu labari,a wata ranar juma’a ne bayan an kammala salla,aka ɗaura igiyoyin auransu dubban jama’a suka shaida,daga ciki hada ni hafsat bature muhammad,da kuma makaranta wannan littafin,

 

Tun lokacin da labarin auren Abu da abusufyan yaje kunnan sayyadi,tun daga ranar bai ƙara takawa yaje gidan ba,abun ya ɗaure mashi kai,yarda suka shirya komai batare da saninshi ba,suka aurar da yarinyar da yake mutuwar so,har gadon asibiti sai da ya kwanta yayi jinya,

 

Bayan aurensu da sati guda hajiya Ameenatu ta ware masu katafaren ɗakin da zasu zauna anan cikin gidansu,ta zuba masu duk wani abu na more rayuwa acikinshi,duk don ta faranta ma abusufyan dinta,hatta lefen kayan abu duk ita ta siya mata komai da kayan ɗakinsu,

Duk yadda abusufyan yaso ya shawo kanta ta amince suyi rayuwar aurensu amma abu taƙi amincewa dashi,har yau ganinshi takeyi tamkar ba mijinta ba,saboda bata son shi ita sayyadi takeso,kullum Abusufyan yayi yunƙurin ta6a ta,hana shi takeyi tana cewa ba tayi tanadin kanta  saboda shi ba sai don sayyadinta,’wannan maganar ba ƙaramin ƙona mashi rai takeyi ba,gashi Allah ya jarabce shi da tsananin sonta,duk wulaƙancin da abu keyi mashi,bai ta6a sanarma kowa ba,jurewa kawai yake yi donnya rufa mata asiri,yasan muddin ya sanar ma mommyn shi aminatu ko mahaifinta baba buzu sae ranta yayi mugun 6aci don mahaifinta har bugunta zai iyayi,saboda ya tsani yaji tana maganar sayyadin nan,

 

 

Wuraren ƙarfe sha biyu na dare,tana kwance saman gadonsu tana bacci,ta dinga jin shessheƙar kukan mutum akusa da ita,buɗe idanunta tayi masu ɗauke da bacci,tare da miƙewa daga zaune tana kallonshi,

Ya tasa ta gaba ya zabga uban tagumi yana ta faman zubda hawaye,gabanta ne taji ya faɗi rass ganin abusufyan na kuka da idanunshi,zuba mashi ido tayi tana kallonshi batare da tace mashi komai ba,

Cikin shesshekar kuka yace”Abu dagaske baki sona?meyasa kika tsane ni ne?

buɗe baki tayi tare da cewa”ba kaine ke bana so ba,ɗabi’unka da halayanka ne ke bana so,na tsani naganka kana mu’amala da wasu matan da sunan abokantaka,kuma natsani naganka kana sanya irin waɗannan kayan ajikinka,kuma baka da kunya abusufyan agaban kowa kake faɗin duk abunda yazo bakin ka,ni nafison kamilin mutun natsastse mai ilimin addini,’

cikin sanyin murya yace”zan canza halaye na saboda son da nake yi maki ne kawai,’

“Kayi mun alƙawarin bazaka ƙara kula wata mace ba in ba ni ba?

ɗaga mata kai yayi alamar eh yace”Nayi maki alƙawari abu,zan daina,daga rana irin ta yau bazan ƙara hulɗa da mata ba,zan kame kaina kamar yarda kikeso,zan zama irin mutumin da kikeso,’ya ƙarasa maganar yana kallon cikin idanunta,

Jinjina kai tayi tace”idan kuma ka sa6a fa?ka yadda na yanke duk hukuncin dana ga dama akanka”?

“Na amince”ya bata amsa,

Ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙa hannunta ta ɗauko al’qur’anin dake ajiye asaman side drawer dinta ta miƙa mashi,yasa hannu biyu ya kar6a cike da mamakin me zaiyi da al’qur’anin da ta bashi,gabanshi ne ya shiga faɗuwa tsoranshi kar tace ya rantse da al’qur’ani don bazai iya rantsuwa dashi ba,

“Me kike nufi da wannan qur’anin da kika bani,”

Murmushi ta saki kafin tace”so nake ka rantse dashi cewa ba zaka ƙara hulɗa da wata ƴa mace ba aduniyar nan in ba ni ba,babu ruwanka da mace indai ba ƴar uwarka bace sai kuma ni da nake matarka,in kuma harka sa6a hakan na kama ka tare da wata ƴa mace zaka sake ni saki ukku!ka amince da hakan!!”

Shiru abusufyan yayi gabanshi na faɗuwa,aranshi yana zullumin amincewa da maganarta,saboda baisan halin da zai tsinci kanshi ba anan gaba,tsautsayi zai iya afkawa dashi a lokacin da baiyi tsammani ba,

 

“Dan Allah abu ki janye maganar rantsuwa da qur’ani,banaso kuma ma babu kyau yin rantsuwa dashi,kiyi haƙuri pls,wlh nayi maki alƙawarin bazan ƙara kula mata ba,komai zan daina,”cikin sanyin murya yayi maganar yana kallonta,

ɗaure mashi fuska tayi tare da cewa”Abusufyan dole fa sai ka rantse mun da qur_’anin nan sannan zan yarda dakai!ƙin amincewa da hakan zaici gaba da haddasa rashin zaman lafiya atsakaninmu!”

babu yarda ya iya da ita,saboda aƙagare yake da su fara kasancewa amatsayin ma’aurata tare da ita,baison 6acin ranta ko kadan,baida burin daya wuce yaga suna zaman lafiya da ita,wannan dalilin ne yasa shi yin rantsuwar da har yau yake danasaninta,

 

Hannu tasa tare da kar6ar qur’anin ta maida shi saman drawer ta ajiye shi,

“Yanzu zaki bani haƙƙina kenan”?ya tambaya yana kallonta,

jinjina mashi kai tayi alamar eh,kafin ta sanya hannunta tare da cire rigar jikinta,ya rage daga ita sae bra,nan fa hankalin Abusufyan ya tashi haikam da ganin surar ƙirjinta,gaba daya ya afka mata,suka manne ma juna,gaba daya suka zautar da junansu,sosai Abusufyan ya biya bukatarshi da ita,sai lokacin ta gane ba ƙaramin cutar kanta takeyi ba,na ƙin amincewa dashi tun ranar farko da aka ɗaura masu aurensu,ba ƙaramin so ya nuna mata ba awannan daren,kuka sosai abusufyan yayi mata saboda tsantsar farin cikin da yaji na kasancewarshi mutun na farko daya fara kar6ar budurcinta,

 

Tun daga wannan lokacin soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninta dashi,saboda irin tarairayar da yake yi mata,da kuma irin kulawar da yake nuna mata,kullum yana tare da ita yana faranta mata,da kanshi yake kaita school sannan ya wuce tashi makarantar,idan an tashe su shi yake zuwa yaje ya ɗaukota ya kaita gida,tamkar romeo da juliet haka suka koma,har acikin mota soyayya suke sha,idan tana aiki a kitchen haka zai bita yana tayata aiki,gyaran ɗakinsu duk shi ke yi in yana gida,hatta gugar kayan makarantarta shi ke zama ya goge mata su,duk wannan soyayyar da suke sha akan idon Hajiya Ameenatu,dama itace ta bama soyayyar tasu wurin zama,in taga sunyi kwana biyu basu fita yawon shakatawa ba,da kanta take ɗauko kudi tabasu tace su tafi shan ice cream,ko suje suyi siyayyar abunda suke so,shi dai Alhaji nuraddeen har lokacin zuba masu ido kawai yake yi,mahaifin abu kuwa baba buzu mai gadi,hankalinshi ba ƙaramin kwanciya yayi ba,ganin yadda Abusufyan ke kular mashi da yarinyarshi,yanzu baida sauran damuwa sae fatan cikawa da kyau da IMANI,

 

Bayan wata guda da sati uku da yin auransu………………

 

Suna zaune a cikin class ɗinsu na islamiyya,ƙawayenta na kewaye da ita,tana basu labarin irin soyayyar da suke sha ita da abusufyan ɗinta,dama bata da wata magana sai ta Abusufyan,suna cikin firar nan sai ga malamin nan nasu sayyadi ya faɗo cikin ajin a fujajen yana ta faman huci,suna haɗa ido da abu ya kwaɗa mata kira”Zo nan zainab,”

 

ƙin zuwa tayi sai da wata ƙawarta tace mata”Abu kije ya sayyadi na kira,”ba don taso ba ta miƙe tare da zuwa inda yake,waje suka fita daga gefen ajin nasu,

“Yanzu abu kin kyauta abunda kikayi mun?kawai sae dai naji agari an ɗaura auranki da abusufyan”? Muryar shi tamkar zaiyi kuka yayi maganar,

 

“Dama Allah ya ƙaddara cewa kai ba mijina bane Sayyad,Abusufyan shine mijina,don haka ina baka haƙuri kuma ina yi maka fatan Allah ya baka mace tagari wadda ta fini,”tana faɗin hakan ta juya zaka koma class cikin sauri yasha gabanta tamkar zai rungumeta,ɗan ja da baya tayi tana kallonshi a tsorace,

Rai amatuƙar 6ace yace”Zainab!kada kiyi mun haka kin manta alƙawarin da mukayi ma juna,zamu yi aure mu haifi ƴa’ƴa mu tarbiyantar dasu atare?abu ni fa kikeso ba Abusufyan ba?me zakiyi da namiji mai bin mata?ke da kanki kika sanar dani cewa Abusufyan mutumin banza ne mai hulɗa da mata,kuma bai da tarbiyya sannan baida ilmin addini rayuwar turae yasa agaba bai damu da addinin shi ba….’

Abu tace”hakane ni na faɗa maka haka da bakina,tabbas munyi alƙawari dakai sai gashi Allah bai nufa ba,tunda bani ke iko dakaina ba,mahaifina shiya za6amun Abusufyan kaga dole nayi masa biyayya,malam kaida kanka kake yi mana nasiha akan mubi iyayenmu muyi musu biyayya,don haka bai kamata kaga laifina ba,don nabi umarnin mahaifina ba,sannan zancen cewa abusufyan na bin mata,rashin sani ne yasa nayi mashi mummmunar fahimtar nan,amma ni mijina baya bin mata,abusufyan mutumin kirki ne,yana mu’amala da mata amma bai ta6a kusantar su da sunan aikata zina ba,iya friendship yake yi dasu,maganar ilmin addini kuwa abusufyan shima malami ne mai zaman kanshi,da farko na dauka boko ya sanya agaba,amma yanzu nagane cewa yana da ilmin addini sosai,bai cika bayyanawa bane agaban mutane,amma shi da kanshi yake ƙara mun karatun hadda in aka bani a makaranta,kuma yana tashi na muyi sallar dare dashi,kuma muyi karatun alƙur’ani atare…….’

Tunda tasoma magana sayyadi ke ta faman huci kamar ya rufe ta da bugu haka ya dinga ji,sae da ta kai ƙarshen maganarta sannan yace”yanzu kin haƙura da duk wasu munanan dabi’u nasa kin amince zaki cigaba da zama dashi yana hulɗa da mata,”

ɗaga mashi kai tayi alamar eh tace”Abusufyan yayi mun rantsuwa da alƙur’ani cewa bazai ƙara mu’amala da wata ƴa mace ba in bani ba,in kuma har yayi hakan zai sake ni ne mu rabu,” tun daga kan yarda abu ke magana zakasan cewa akwai ƙuruciya sosae atare da ita,

Jin maganarta yasa sayyadi jinjina kai tare da matsa mata hanya yace”ki koma aji,”

sallama tayi mashi sannan ta wuce cikin class,

Bayan shigarta aji,murmushi ya shiga saki yana cewa”ta kwana gidan sauƙi,”yana fadin hakan ya ƙara gaba.

 

 

*Zuwa gobe insha allah zamu kammala labarinsu sehrish ataƙaice sannan mu ɗaura daga inda muka tsaya*

Back to top button