Hausa novels

Abban Sojoji Chapter 68 Book 2 Complete Novel

Abban Sojoji Book 2

The Father Of Soldier

Written By Boss Bature

*Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za’a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata  zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari*,

“Meya faru Abba”? Marshal Omar ne yayi mashi tambayar yayin da yake kallonshi kafin ya mayar da idanunshi kan Abusufyan dake tsaye duk a rikice,tsayawa Sgr yayi tare da goya hannayenshi asaman wide chest ɗinshi,tunda ya ƙaraso wurin idonshi na akan Sehrish da abusufyan dake atsaye cikin wani yanayi ita Sehrish a tsorace shi kuma Uncle abusufyan duk a firgice,

 

Fuskar Abbansu aruɗe yace”nikaina bansan meke faruwa ba,uncle ɗinku ne tun da yayi arba da yarinyar nan duk yabi ya rikice,ya rasa natsuwarshi,”ya ƙarasa maganar yana yi mashi nuni da Sehrish,

Matsawa Omar yayi tare da dafa kafaɗar Abusufyan yace”Uncle meya faru ne?ko kasanta ne”?

Shiru Uncle sufyan yayi batare da yace komai ba amma duk yanayin shi ya canza sosai,idanunshi har lokacin suna akan Sehrish kamar yarda itama take kallonshi,

Suna cikin wannan yanayin kowa ya miƙe tsaye,

Major yayi sallama,Omar ya bashi iznin shigowa daga ciki,

6oyewa jahad da hosana su kayi a bayan major saboda fargabar haɗuwa da dangin ya Omar ɗinsu,

..murmushi Marshal ya saki yana hangen ƙafafuwansu,

Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel – Aihausanovels

Zuba ido kowa yayi yana jira yaga su wanene waɗannan dake ta 6oyewa,kowa ya mayar da hankalinshi akan Major dake tunkaro su,

Koda major ya ƙaraso wurinsu,sae yace”Jahad hosana ku fito ga ƴar uwarku nan,”

Jin haka yasa su yin hanzarin fitowa daga bayanshi,

Tashin hankalin da ba’a sama shi date,

Waro ido waje su fawan su kayi suna kallonsu,tun daga Ayaan jahan,irfan khaleed da jabeer da kuma kanal yousouf kowannansu ya gama kiɗima da wannan abun al’ajabin,kowa ya gaza buɗe baki yayi magana,kallonsu kawai sukeyi,idan suka kalli Jahad da hosana sae su mayar da idanunsu kan Sehrish,

Tsayawa sukayi daga bayan sehrish,basu da tabbacin cewa itace amma ransu na basu hakan,

Atare suka haɗa baki wurin ambaton Sunanta,

“SEHRISH”

Gabanta ne taji ya faɗi rassss,a firgice ta juya bayanta don taga su wanene suka ambaci sunanta,zuba masu ido sehrish tayi tana kallonsu,lokacin da ta juyo suka tabbatar da cewar itace rishi ɗinsu,wani irin farin ciki ne ya cika su,jiki na rawa suka tunkareta zasu rungumeta,abun mamaki sae suka ga tana ja da baya baya fuskarta da alamun tsoro tace”su wanene ku!ni bansan ku ba,dan Allah kada ku matso kusa dani,”

gabansu ne suka ji ya faɗi rass,nan take kuma idanuwansu suka cika tab da kwalla,

Muryar jahad na rawa tace”sehrish,ashe zamu sake sanyaki acikin idanuwanmu?mun rasa ki a lokacin da muke tsananin buƙatarki,ba mu ta6a tunanin cewa zamu ƙara haɗuwa dake ba,sae gashi Allah ya ƙara haɗamu..,

Deen House (Romantic Story) By Oum Hairan

“Sehrish…….’hosana ce ta ambaci sunanta,

Zuba ido kowa yayi yana kallon Wannan ikon Allah,

Girgiza kai sehrish ta shiga yi jikinta na rawa tace”Ni…ban..sanku ba..dan Allah ku daina kiran sunana,banason ji,”

Fashewa da kuka sukayi su biyun jin abunda tace masu,

“Omar kun barmu acikin duhu,!dan Allah ku sanar damu ina aka samu waɗannan twins ɗin!”Abbansu ne yayi maganar yana kallon Marshal,

 

Abusufyan kuwa tunda yayi arba da Jahad da hosana ga kuma sehrish,batare da sanin kowa ba,yabar wurin izuwa bedroom ɗin da ya sauka,wani irin matsanancin ciwon kaine ya taso mashi,ga wani zazza6i daya lullu6e shi lokaci guda ya rasa in da zai tsoma ranshi,abun ya gama gigita shi,

 

Gyaran Murya Omar yayi kafin ya soma magana anatse yace”Abba waɗannan twins ɗin da kake gani,sune yaran da nake baka labari,mun haɗu dasu a asibiti cikin mawuyacin hali,na taimakesu a wannan lokacin har na kawosu gidan Uncle abusufyan don su cigaba da rayuwa acikinshi,tun da nake dasu ba mu ta6a tattaunawa agame da danginsu ba,saboda tun lokacin da na fara haduwa da su sun sanar dani su basu da kowa,bayan nakawo su gidan uncle abusufyan aranar dana fara ganin Yarinyar nan sehrish,abun ya ɗaure mun kai ganin kamanninsu iri ɗaya sak da yaran da nake ruƙo a wurina,nasha tambayar sehrish ko tana da ƴan uwa don in bugi cikinta inji ko tana da alaƙa da yaran dake wurina,amma sae tace mun ita bata da kowa,daga baya na dinga tunanin cewa kodai son da nake ma Jahad da hosana ne yasa nake ganin fuskarsu akan ta yarinyar,amma abun da ya faru jiya ne ya tabbatar mun da cewa Bani kaɗae ke ganin kamanninsu ba,junaid yaje ɗaukar sehrish lokacin da aka tashe su daga school,cikin rashin sani ya ɗauko Jahad!amaimakonta ya kawota cikin gidan nan….!

Tunda Omar ya soma magana kowannansu ya kasa kunne yana sauraronshi,fuskokinsu da alamun mamaki sosai,

“Jahad hosana da kuma sehrish,uwarsu ɗaya ubansu ɗaya,su ƴan Uku ne!na jima ina mamakin Yarda Allah ya haɗasu dukkansu a ƙarƙashin kulawar family dinmu,ni na haɗu dasu hosana a wani hali na rayuwa na taimakesu na kawosu gidan Uncle abusufyan,yayin da Sehrish aiki ne ya kawota cikin gidan nan…..’

Yana kai ƙarshen maganar Abbansu yace”Amma Omar abun ya ɗaure mun kai wlh!taya akai duk hakan ya faru?

matsawa Omar yayi wurin da su hosana suke tsaye suna faman sharar kwalla saboda ganin yarda sehrish ɗinsu ta nuna batasan su ba,duk murnar da suke tayi ta koma ciki,

Ruƙo hannun Jahad yayi cikin sanyin murya yace”Jahad,ki faɗa masu yarda akai kuka rabu da ƴar uwarku,har tsawon wannan lokacin baku atare,”

Daƙyar jahad ta Iya bayyana masu dukkan abunda ya faru,tun kafin zuwan sehrish aiki,har abunda yayi silar rabuwarsu da ita,da kuma wahalar da suka sha kafin Allah ya haɗasu da Marshal Omar,

Wani irin tausayinsu ne ya kama matasan gidan,jikin kowa yayi mugun sanyi,hatta Sgr dake tsaye yana kallonsu ba ƙaramin tausayi suka bashi ba,yaran sun sha wahala sosai,

Hanyoyin Magance Matsalolin Ma’aurata

“Amma Omar meyasa tun farko baka faɗamun komai agame dasu ba?ae da tuni mun haɗasu da ƴar uwarsu wuri guda sunyi rayuwarsu,”acewar Abbansu muryarshi tamkar zaiyi kuka yayi maganar,dama shi akwai tausayi

 

Omar yace”Abba,nima naso nayi hakan,kayi haƙuri da rashin sanar maka da banyi ba,amma yanzu gasu nan na kawo maku su,kuma ina fata zaku kar6esu hannu bibbiyu kamar yarda kuka kar6i ƴar uwarsu sehrish,!!!

Hankali tashe sehrish tace”Ni ba ƴan uwana bane ya Omar,wlh bansansu ba,bansan su wanene su ba,dan Allah kada ku haɗa ni dasu,bansan ganinsu,bazan iya rayuwa wuri ɗaya tare da su ba,’

Wannan kalaman na sehrish yasa kowannansu kallonta cike da mamaki,ƙiri ƙiri ga abu ya fito zahiri amma ta nuna cewa ba ƴan uwanta bane!bayan sunji cewa saboda su ne tazo aiki agidan don ta samu kudi,”

“Rishi mune ba ƴan uwanki ba!sehrish yau da kanki kike faɗin hakan!dan Allah kidaina cewa haka,wlh zuciyata zata iya bugawa na mutu….’jahad ce tayi maganar yayin da idanunta ke fitar da wasu zafafan hawaye masu ɗumin gaske,

..hosana tace”sehrish kin manta ni nima?kin manta hosanarki da kika bari kwance gadon asibiti bata acikin hayyacinta”?muryarta asanyaye tayi maganar,

gaba ɗaya sun rikita sehrish,ko son kallonsu bata yi,in su kayi magana ƙara mata ciwon kai sukeyi,kamar yarda suke kuka haka itama ta fashe da kuka tana rantsuwar cewar batasan su ba,

tashin hankali!

Sai lokacin kanal yousouf yace”Ina azmee take ne?fawan kaje ka kira mana ita,ina da tabbacin cewa tasan wani abu game da yarinyar nan,tunda tafi kusanci da ita,zai iya yiyuwa akwai wani abu da ta ta6a sanar mata,’

Fawan ya amsa mashi da toh,sannan cikin sauri ya wuce sashen su azmee don ya kira ta,

Ganin yadda su Hosana da jahad ke ta kuka yasa Abbansu junaid cewa”Ku zo nan,”

Hannunsu cikin na juna suka ƙarasa wurinshi,

bin fuskokinsu yayi da kallo na wani lokaci,kafin ya sanya tafin hannayenshi yana goge ma hosana hawayenta,cikin lallashi yace”kudaina kuka ya isa haka,kada ku sa damuwa aranku,yanzu lokacin farin ciki ne,tunda ƴar uwarku tana atare daku yanzu kuma insha Allah,babu wanda zai ƙara rabaku da ita,”

Yadda Zaki Kula Da Kanki Kafin Aure Da Kuma Bayan Aure

Cikin shessheƙar kuka jahad tace”Amma ta nuna batasan mu ba ai,”

Abba yace”kada ku damu da wannan,wasa take yi maku,zuwa anjima zata dawo dai dai ne,’

“Rishi ba wasa take mana ba,”acewar hosana,bayin Allah gaba ɗaya duk zazza6i ya lullu6esu,

Tunda fawan ya sami azmee aɗakinta,ya sanar da ita game da bayyanar ƴan uwan sehrish,farin ciki ya cikata ta shiga faɗin”Alhamdullillah,Alhamdulillah”

Jiki na rawa ta biyo bayan fawan suka nufo falon,

Tunkan su ƙarasa ciki take hangensu Jahad da hosana dake tsaye agaban Abbansu junaid,abun ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,yanzu ta ƙara tabbatar da cewar Dagaske ne!sehrish tana da ƴan uwa,kuma su ƴan ukune,hakan na nufin cewa Sehrish ba ƙarya tayi mata ba,

Tana ƙarasowa sehrish ta nufeta tare da faɗawa jikinta ta rungumeta tana kuka tana cewa”Aunty azmee ni bansan su wanene waɗannan ba masu kama dani,sunce wae sun san ni,bayan ba haka bane,ni bani da wasu ƴan uwa,’bubbuga bayanta azmee ta shiga yi tana lallashinta,

“Azmee muna sauraronki,ko akwai wani abu da kika sani game da ƴan ukun nan!kunfi kusanci da Sehrish nasan cewa dole akwai wani abu da ta ta6a sanar maki agame da rayuwarta,”

Marshal Omar ne yayi maganar,

Azmee tace”Sehrish bata ta6a sanar dani wani abu game da rayuwarsu ba,amma ina da masaniya akan Ƴan uwannan nata……..’gaba ɗaya azmee ta sanar dasu,yarda sukayi da sehrish tun farkon zuwanta,da kuɗin da ta nema awurinta na biyan kuɗin aikin hosana,duka kaf ta kwashe ta sanar dasu,

“A lokacin ni da kaina,na kar6i acct numbar likitan da yake kula da ƙanwar tasu,na tura mashi kuɗi dubu ɗari tara na aikin yarinyar,acikin kuɗaɗen dana jima ina tarasu na albashina da kuma wanda kuke bani don inyi hidimar kaina….’

Tunkan ta ƙarasa maganar Sgr ya dakatar da ita da hannunshi,

Sai lokacin ya samu damar buɗe bakinshi yace”Meyasa baki sanar da waninmu game da waɗannan yaran ba!bayan ta sanar dake halin da ƴan uwanta suke ciki?sannan waya baki iznin bata kuɗi har 90k batare da sanin kowa ba?kuma kika hana ta zuwa ganin ƴan uwanta saboda kunyi yarjejeniyar zatayi aiki acikin gidan nan harna tsawon shekara ɗaya da rabi,Why AZMEE!?

Hankalin azmee ba ƙaramin tashi yayi ba jin tuhumar da sgr yake yi mata,

“Ba laifina bane Rafayet!duk wani abu daya faru nayi ne saboda sehrish!bakomai ne yajawo hakan ba face

tsoron kar asirinta ya tonu ku gane cewa ita mace ce ba namiji ba,Abban ku ya nemi mai aiki namiji,amma sai ga sehrish tazo aiki amatsayin namiji,dagani harku babu wanda yasan cewa ita mace ce ba Namiji ba,Ni ce na fara gane cewa ita mace ce,akwai wata rana da naje kiranta don muyi aiki,anan na same ta akwance babu gashin bakin nan da take sanyawa ga kuma dogon gashi akanta hakan ya tabbatar mun da cewa ita mace ce ba namiji ba,koda na sanar mata cewa nagane ita mace ce,a lokacin ta dinga roƙona akan na rufa mata asiri batason kowa ya sani,saboda sanin halin matasan gidan nan da nayi na rashin son ganin mace acikinsu,kuma ga laifin ƙaryar da tayi na zuwa a matsayin namiji,wannan ne dalilin dayasa na rufa mata asiri ban sanar ma kowa ba,daga baya kuma bayan kowa ya gane cewa ita mace ce,naso nayi mata maganar ƴan uwanta amma sehrish sai ta nuna mun cewa ita bata da wasu ƴan uwa aduniyar nan ita kaɗaice……..’tun daga farko har ƙarshe azmee ta sanar dasu dukkan wani abu daya faru tsakaninta da sehrish akan maganar ƴan uwanta,da kuma abunda junaid ya sanar da ita na wayarshi da sehrish take ɗauka a 6oye tana kiran ƴan uwanta,komai ta sanar dasu,

Gaba daya sun gamsu da bayananta,duk da basu ji daɗin halin da ƴaran suka kasance aciki ba,sun so ace tuntuni sunsan da zancen,da tuni sun jima da kasancewa a wurinsu,

Jin takun tafiya yasa suka ɗan juya don ganin wanene,Hajiya azeema ce ta fito daga masaukin da ta sauka,ta ca6a ado,wurinsu ta nufo tana tambayar lafiya? mai ya faru ta gansu atsaitsaye cirko-cirko?

Koda ta ƙaraso cikin babban falon karaf idanunta suka sauka akan Jahad hosana da kuma sehrish dake manne da azmee taƙi sakinta,saboda halin da take ciki,

Cike da mamaki tace”Ya hossein!su wanene waɗannan ƴan ukun masu masifar kama?ƴa’ƴan wanene?

Abba yace”wannan wani case ne da muke tattaunawa akanshi,shiyasa kika ganmu atsaitsaye,zan sanar dake komai bayan mun dawo daga sallar magrib naga lokaci ya ƙarato,”

Ya ƙarasa maganar tare da kallon azmee yace”Ki wuce da sehrish ɗakinta,sannan waɗannan ƴan uwan nata ki sama masu ɗakin da zasu zauna kafin mu dawo daga sallah,”

Omar yace”a’a Abba banaso arabasu,yaran nan sun kwallafa rai akan ƴar uwarsu,jiya saboda murnar jin cewa tana a gidan nan,ko bacci basuyi ba,kuma basu ci abinci ba,saboda sunyi alƙawarin cewa atare da ƴar uwarsu zasu ci abinci,don haka inaso a haɗasu ɗaki ɗaya da ita,kuma ashirya masu lafiyayyen abinci suci tare da ita,ko tana so ko bataso,”

Jinjina kai Abba yayi tare da cewa”Shikenan,hakan ma yayi Azmee ki tabbatar da kin haɗasu wuri ɗaya tare da ƴar uwarsu,”

“Insha Allah zanyi hakan,”ta amsa mashi,sannan ta kalli su jahad da hosana tace”ku biyoni mu tafi,”

tayi maganar tare da ruƙe hannun sehrish dake ta faman faɗin bataso bataso a haɗata ɗaki ɗaya dasu,ahaka suka wuce bedroom ɗinta,

Tusa Gaba Abinda Ya Kamata Ki Sani Da Kuma Yadda Zaki Kare Kanki Daga Ita

Bayin Allah,duk sunji sun tsani kansu saboda juya masu bayan da sehrish tayi,duk irin ɗoki da murnar ganinta da sukeyi amma ta nuna batasan su ba,kamar wasu bare haka take kallonsu,haƙiƙa zuciyoyinsu ba ƙaramin karaya sukayi ba,

 

 

Bayan azmee ta tafi dasu Jahad,anan su abba suka tsaya suna ƙara tattaunawa atsakaninsu,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,lamarin ya rikirkitasu,bakomai yafi tsaya masu aransu ba,face yarda Sehrish ta nuna batasan ƴan uwanta ba,bayan ga shaidunan sun bayyana karara nacewar ƴan uwanta ne su,kome yasa haka!?

 

“Wai ni ina Uncle abusufyan yake ne!ko kun lura da yanayin da ya shiga lokacin da yayi tozali da Sehrish!”Khaleed ne yayi maganar yana kallon fuskar Abban nasu,

Fawan yace”Nima nayi mamakin razanar da naga yayi lokacin daya ganta,”

Jahan yace”ku ka sani ko kwalliyar da tayi ne,yasa ya tsorata da ganin kyawun fuskar…..’bai ƙarasa maganar ba saboda kallon da Sgr yayi mashi,tsit yayi da bakinshi,

“Gaskiya bana tunanin haka jahan,!sae dae wani abun na daban ne yasa shi firgita,”acewar Ayaan,kowa dae da abunda yake tunani acikin ranshi,

Marshal Omar yace”Kowa ya wuce yayi shirin sallah,kafin a fara kira,”

Amsa mashi sukayi da toh,sannan suka kama gabansu kowa ya nufi room dinshi,jikinsu duk a mace,sun jima basuji tausayin wani ɗan adam ba kamar yarda sukaji tausayin su sehrish,sun tausaya masu sosai ganin irin halin rayuwar da yaran suka shiga,

Bayan tafiyarsu,falon ya rage daga Abbansu sai Omar da Sgr sai kuma kanal yousouf,

“Ni fa ina zargin Uncle Abusufyan abba!kamanninshi da yaran nan yayi yawa abun is over,komai na fuskarsu irin nashi ne!kuma tun daga kan yarda ya firgita da ganin sehrish yasa na tabbatar da cewa akwai wani abu aƙasa,bayan wannan kuma akan idona uncle abusufyan yabar wurin nan agigice jikinshi na rawa ganin ƴan uwan yarinyar nan,ya kamata muje muga a wane hali yake ciki,sannan kuma muji dalilin dayasa ya razana da ganin yaran,”!

Jinjina kai Abbansu yayi jin abunda kanal yousouf yace,Tabbas ya yarda da maganarshi,don shi kanshi ya lura da halin da ƙanin nashi ya shiga,yana son jin meyasa shi firgita da ganin yaran!

Batare da 6ata lokaci ba,Suka nufi ɗakin Abusufyan atare,

Yar Harka Page 1-10 Hot Romantic Hausa Novel

Lokacin da suka tura ƙopar ɗakin nashi suka shiga ciki,samunshi sukayi zaune dirshen a ƙasa gefen gado yana ta faman sharar hawaye hannunshi dafe da kanshi,sae faman sambatu yakeyi shi kadae,

Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba,musamman Abbansu,da sauri ya ƙarasa wurinshi,tare da zubewa kasa daga gefenshi yace”abusufyan meya same ka ne!meya faru!me yasaka zubar da hawayenka har haka ne?dan Allah ka faɗamun wlh hankalina ya tashi sosai……..’gaba daya duk ya ruɗe ganin halin da abusufyan ke ciki,

Daga gefen gadon Sgr da Omar suka zauna suna kallonsu,yayin da kanal yousouf yake tsaye ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi,turo ƙopar aka kumayi,Hajiya azeema ce tabiyo bayansu,

“Subhanallahi Meya faru ne!naga Abusufyan na kuka?wani abu ya sameshi ne”?fuskarta ɗauke da damuwa tayi maganar ayayin da take ƙarasawa ciki ta samu wuri saman stool na gaban dressing mirror ɗinshi ta zauna tana fuskantar su,

gaba daya suka haɗu suna tambayarshi dalilin yin kukan nashi,

Sai faman share hawaye yake yi,ya gaza buɗe baki yayi magana,

“Uncle dan Allah kadaina kukan nan,duk ka sanyamu acikin damuwa,idan akwai wani abu dake damunka dan Allah ka sanar damu,koda bamu da maganin damuwar taka,zamu taya ka da addu’a akan Allah ya yaye maka ita,”Marshal omar ne yayi maganar cikin tausasa murya,

Hajiya azeema tace”Ƙanina dan Allah ka sanar damu mana,meyasa ka ware kanka anan kana kuka kai kaɗae kamar wani ƙaramin yaro?mu fa nan danginka ne wanda baka da kamarsu aduniyar nan,dan haka kada kaji komai ka faɗa mana damuwarka insha Allah,zamu nemi mafita atare,’

ɗagowa yayi da idanuwanshi wadanda sukayi jawur suka kumbura saboda kukan da yasha ya kalli yayan nashi la66ansa na kerma yace”ƴa’ƴana yaya,Su ne damuwata,saboda su ne nake zubar da hawayen nan,na cuci rayuwarsu akan idona rayuwarsu ta wulakanta batare da na ɗauki mataki ba………’

Hankali atashe Abba da Azeema suka haɗa baki wurin cewa”Ƴa’ƴa kuma!wasu ƴa’ƴa kake magana akai kenan!”

ganin yarda suka razana da jin maganarshi yasa jikinshi yin sanyi dama yasan dole suyi mamakin jin cewa yana da ƴa’ƴa,

Sgr da Omar kuwa shiru sukayi suna sauraran abunda Uncle ɗin nasu ke cewa,

Fassarar Mafarkin Ruwan Sama

Jin yayi masu shiru yasa ran Abban nasu 6aci a fadace yace”ba zaka buɗe baki kayimana magana ba!

 

Sam ya rasa ta yarda zai fara sanar dashi game da ƴa’ƴan da yake magana akai,tsoranshi karya ƙi amincewa da zancen shi,yana fargabar abunda zai biyo baya in ya sanar dasu cewa yaran nan ƴa’ƴanshi ne,

 

“Kai nake sauraro abusufyan!ka sanar mun akan wasu ƴa’ƴa ne kake magana!’wannan karan a rikice abba keyi mashi magana,

 

cikin sanyin murya Abusufyan yace”Yaya hossein,ina magana akan ƴa’ƴana ne,waɗanda na haifa,na haifi ƴa’ƴa batare da saninku ba………..’

A razane abbansu junaid ya miƙe tsaye yana kallonshi yace”What!!abusufyan kai da kanka kake faɗamun cewa kana da ƴa’ƴa naka na kanka!?Anya ba kunne na ne ke jiyomun ba dai dai ba,”yayi tambayar fuskarshi da alamun ruɗu acikinta, jiki na rawa abusufyan ya miƙe tare da

ruƙo hannun abban acikin nashi yace”dan Allah ka zauna yaya,zanyi maka bayanin komai,tabbas dagaske ne ina da ƴa’ƴa abba,kuma suna nan araye,jini na ne su,’

dafe kai Abba yayi saboda wani irin jiri daya ji yana niyar kwasar shi,dakyar ya iya buɗe baki yana ambaton”innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!abusufyan ka cuce mu Kuma ka yaudare mu ka zubda ƙimar family dinmu!ashe dama abunda ka aikata kenan shiyasa ka gudu kabar ƙasar nan!?saboda kayi ma wasu ciki kana tsoran asirinka ya tonu shine ka tattara kabar ƙasar nan!”ƙarasa maganar yayi yayin da hawaye ke gangarowa daga cikin idanunshi,abun ba ƙaramin gigita su yayi ba gaba dayansu,basu ta6a tunanin cewa abusufyan dinsu zai iya aikata wannan mummunan abun ba,

 

A faɗace yaci gaba da magana”ka faɗamun gaskiyar lamarin tun kafin ranka ya 6aci!tun yaushe wannan abun ya faru baka sanar mun ba!wacece ko kuma suwa kayi ma ciki har aka haifa maka ƴa’ƴa!kuma ina ƴa’ƴan suke,

gaba ɗaya abusufyan yasha jinin jikinshi ƙoƙari yake yayi mashi bayani amma  ya kasa,

 

Marshal Omar ne yace”Abba,pls mubi komai asannu har mu samu uncle  ya warware mana komai,Ni ina da tabbacin cewa Uncle abusufyan bazai ta6a aikata abunda muke zarginshi dashi ba,dole akwae wani dalilin.

Girgiza kai Abbansu ya shiga yi ranshi atsananin 6ace yace”Kabarni Kawai Omar,abusufyan ya gama da mu,bansan iya zunubin da ya aikata ba,da yasa harya gudu yabar ƙasar nan tsawon lokaci,

 

Amman tunda ni bazai sanar dani gaskiyar Lamarin ba, bari na kira Ammi a waya na sanar da ita abunda ya aikata,may be ita zai iya yi mata bayani tunda ni bazaka faɗamun ba!”

Yana ƙarasa maganar ya zura hannu acikin aljihun wandon shi yana ƙoƙarin curo wayarshi don ya kira ammi,

Cikin sauri abusufyan ya ruƙo hannunshi muryar shi har kerma takeyi wurin cewa”ya..ya hossein ka saurareni dan Allah,ina ƙoƙarin na fahimtar dakai ne,muddin ka sanar ma ammi wannan maganar zan tattara kayana nabar gidan nan ne!saboda bazata ta6a fahimtata ba,kamar yarda kai zaka fahimceni…….’

jikin Abbane yayi sanyi ganin yarda Abusufyan ke ta faman zubar da hawayenshi,

Sassauta muryarshi yayi cikin lallami yace”ka sanar dani Abusufyan!taya akai ka samu ƴa’ƴa”?

Hannuwanshi duka biyun yasa ya rike kanshi da yake jin kamar zai fashe,ga wata uwar zufa da ke zubo mashi har ta jika wuyan shaddar jikinshi,sai faman girgiza kanshi yake ya rasa ta ina zai fara komae ya dagule masa,da ka kalle shi zaka fahimci bai cikin hayyacin shi,

Kanal yousouf ne ya dan yi gyaran murya kafin yace”Abba ni ina ganin muje muyi sallah kilan uncle zai samu natsuwa yayi cikakken bayani don na fahimci kaman bai acikin hayyacin shi ma” jinjina kai Abban yayi don shima ya fahimci hakan,ya mika masa hannu tare da cewa”taso muje muyi sallah amman in muka dawo dole kayi mana cikakken bayani” daga masa kai Uncle Abusufyan yayi alamar ya amince daga haka suka fito gaba dayansu suka nufi masallaci kowa da abunda yake sakawa a ransa.

 

Zamu so muji yarda wannan al’amarin ya faru,taya akai abusufyan da bai ta6a aure ba ya samu ƴa’ƴa’,taya akai yayi aure batare da sanin Danginshi ba?suwaye ƴa’ƴan nashi da yake magana akai,amsoshin duka wadannan tambayoyin na a bakin Abusufyan,batare da 6ata lokaci ba zamu nutsa cikin labarin da Abusufyan zai ba yayan nashi hossein da zarar sun dawo daga masallacin.

Maganin Rage Tumbi Sadidan Ga Yan Mata Da Matan Aure

A6angaren su Sehrish kuwa,tunda azmee ta shigar dasu hosana da jahad a ɗakinta,gaba ɗaya ta takure kanta saman gado,jikinta sae kerma yakeyi ko son ganinsu bata yi,hakan ba ƙaramin raunata zuciyoyinsu yayi ba,zuba mata ido kawai sukayi suna kallonta yayin da hawaye ke zuba a fuskokinsu,a gefen gadon nata suka zauna,

Jahad tace”banta6a tunanin cewa zakiyi mana haka ba sehrish,nayi tunanin zakiyi murnar ganinmu bayan tsawon lokaci da bamu haɗu ba,amman sae gashi kin juya mana baya,agaban mutane kika nuna cewa baki san mu b….!”

Tunkan takai ƙarshen maganar Sehrish ta kwatsa mata tsawa tana cewa”Karki ƙara yi mun magana!ni ko muryoyinku bana son ji wlh,bansan su wanene ku ba,kawai kunzo don ku takura ma rayuwata ne..,…’

Cikin shessheƙar kuka hosana tace”dan Allah sehrish ki daina faɗin hakan!bana jin daɗi,meyasa zakiyi mana haka?Yanzu kin manta da hosanarki?ga kuma jahad?rishi dan Allah kidaina yi mana wannan wasan,’

Hannu sehrish tasa tare da toshe kunnuwanta alamar bata jin ma abunda suke cewa……..’

 

Duk wannan budurin da akeyi Hayaam na kumshe aɗakinta batasan meke wakana ba,tsoranta karta fito su haɗu da Babban yaya awaje,don tasan muddin yaganta acikin gidan sai yasa an wurgar mashi da ita waje,wannan dalilin ya hana ta fitowa,

 

Amani kuwa har sun kammala kimtsawa ita da Amal zasu zo gidan,sai ga Abbas ya shigo gidan,a lokacin suna tsaye ita da Amal acikin falon gidan,

tarar shi tayi tare da cewa”Kai fa muke ta jira tun ɗazu mun kammala shiryawa,”

Abbas yace”sai dai kuyi haƙuri,yanzun nan Abba ya kira ni awaya ya sanar dani cewa wani babban al’amari na faruwa agidan,inyi sauri inxo Suna jira na,bana tunanin cewa suna yin wannan walimar ma,”

Jiki asanyaye tace”Allah yasa dae ba wani abunne ya faru ba,bari mu hakura to in komai ya dai dai ta munje,”daga haka Abbas ya shige ciki yayi abunda zai yi ya fice.

Wannan ne abunda ya hana su Amani zuwa gidan,

 

Bayan sun kammala Sallar magrib,atare suka dawo a nan babban falon suka Hallara gaba ɗayansu banda Azmee da Hayaam da kuma su Sehrish,a lokacin Shima C.g Abbas ya ƙaraso gidan,kowa ya samu wuri ya zauna,Su fawan jabeer da kuma Irfan suna zaune a 3 seater,Abbansu tare da Uncle abusufyan suna zaune asaman 2 seater,Omar kuma tare da Sgr da Kanal yousouf suna xaune ne aɗayar 3 seater ɗin,Abbas da khaleed suma suna zaune asaman 2 seater,sai Aunty azeema dasu jahan kowanne na akan one seater,

 

Gyaran murya Abba yayi tare da kallon Abusufyan dake zaune zugudum agefenshi yace”kamar yarda ka buƙaci mu hallara gaba ɗayanmu a falo,gashi nan duk mun haɗu a wuri ɗaya kai muke sauraro,”

Nannauyar Ajiyar zuciya Abusufyan ya sauke kafin ya soma magana calmy yace”abunda yasa nace ku haɗu ku dukan ku wuri ɗaya,saboda inaso in bayyana maku cewa ina da ƴa’ƴa,kuma ƴa’ƴan nan na same su ne ta hanyar daya dace,Banaso wani ya zargeni ne da laifin aikata zina,wlh ni tunda nake arayuwata ban ta6a kusantar zina ba,ban ta6a kasancewa tare da matar da ba muharramata ba ina nufin ba matata ba…….’

Shiru yayi na ɗan wani lokaci alamar yana nazarin wani abu,duk suka kasa kunne suna sauraron shi,kowa burinshi yaji taya akai Abusufyan ɗinsu ya samu ƴa’ƴa,kuma suwaye ƴa’ƴan nashi!?

 

“Shekara ashirin da ƴan kai da suka gabata,mun samu sa6ani da Ammi saboda rashin jin maganata,babu jituwa atsakanina da ita,bakomai yake haɗani da ita ba,face irin rayuwar dana taso inayi,abota da mata,na maidasu tamkar maza awurina yarda nake friendship da mata ko maza bana kulawa haka,wannan abunne ke 6ata mata rai,saboda ta tsani ta ganni tare da ƴan mata,ko in aka bata labarin cewa anganni tare da mace acikin mota,nan fa hankalinta zai tashi,a ƙarshe data rasa yarda za tayi dani shine,ta tattara mun kayana gaba ɗaya tace in koma Kano wurin ƙanwarta Hajiya Ameena inci gaba da zama acan,saboda nafi ƙarfinta ba zata iya dani ba don ta lura kaina rawa yakeyi,amma tana da tabbacin cewa in na koma wurin ƙanwarta zan shiryu in dawo dai dai,

 

Wannan ne farkon abunda ya rabani da gidanmu na koma wurin goggon mu da zama gaba daya,don ta gyaramun tarbiyyata kamar yadda ku su yaya hossein kuka sani,maimakon hakan sai ta sangarta ni saboda tsananin son da takeyi mun wanda ko ɗanta a wannan lokacin bata nuna mashi irin son da takeyi mun,komai nakeso shi takeyi mun,wankane kawai ba tayi mun,idan nayi laifi kuwa ko na janyo faɗa awaje rufe ido takeyi taita zazzaga masifa kuma tana sane cewa ni ne mai laifin,in mun shiga gida tayi ta lallashina tana bani haƙuri,

 

TUSHEN LABARIN,

Alhaji nuraddeen mai dala,hamshaƙin mai kuɗi ne kuma attajirin gaske,na bugawa a jarida,babban ɗan kasuwa ne wanda yayi kaurin suna a harkar kasuwancin saye da siyarwa  atsakanin ƙasashe daban daban,haifaffen garin zariya ne,kuma yana ɗaya daga cikin Aminnan Salahuddeen,aiki ne ya kawo shi katsina kafin daga baya lokacin daya fara kasuwanci ya yanke shawarar komawa garin kano da zama saboda kasuwancinshi yafi ƙarfi acan,wannan dalilin ne yasa shi tattarawa ya dawo gaba ɗaya da zama anan kano tare da iyalanshi a katafaren gidanshi dake a unguwar Nasarawa g.r.a anan jihar kano,farkon haɗuwarshi da hajiya Amina kanwar Ammi wato goggon katsina,tun lokacin da suka je ɗaurin auren Salahuddeen da Ammi a jihar yobe damaturu,acan ya ganota ya ƙyasa,basu baro wurin ɗaurin auren ba sae da aka shafa fatiharsu su duka biyun a lokaci guda,

 

Yaronsu ɗaya wanda sai da sukayi aure da jimawa kafin Allah ya albarkace su dashi,ba kowa bane wannan face Dr haris babban likita,shine ɗa ɗaya tilo da suke dashi,kafin Ammi ta mallaka mata Abusufyan don tagyara mata tarbiyarshi,sae suka kasance su biyu ne ƴa’ƴan dake a wurinta,ɗanta da kuma ɗan yayarta abusufyan,tom da kuma jerry,don gaba ɗayansu basa jin magana a wannan lokacin,ƴan abi yarima asha kiɗane,atare suke fita yawon dare,sun iya zuwa club a haɗu da ƴan mata ayita rawa,zuwa wurin party kuwa koba a gayyace su ba sai sunje,wannan shine rashin jin da ammi ta tsana na abusufyan,shi dae haka rayuwarshi take baida burin daya wuce afita yawo tare da ƴan mata akashe masu kuɗi,kullum yana manne dasu,shi dai kawai yaji mace akusa dashi ba namiji ba,kuma bawai don yayi wani abu da ita ba,sam shi wannan bai agabansa,

 

Ana haka su Abusufyan suka samu hutun makaranta,atare da dr haris suka je kai ziyara zariya wurin danginsu,

 

Bayan tafiyarsu ne,Hajiya Amina da Mijinta alhaji nuraddeen suka tafi umra,dama tun kafin su tafi alhaji ya sallami mai gadin gidansu baba buzu don yaje ƙasarsu niger ya gano danginshi kafin su dawo,

 

Ba ƙaramin daɗi yaji ba,saboda dama atakure yake na rashin ganin ƴar shi tilo da yake da ita,kullum yana cikin damuwar rashin yarinyar a kusa dashi,saboda halin da ya barota acan,basu da kowa danginsu duk sun tarwatse ba haɗin kai,ga talauci dake damun kowannansu,ita kanta yarinyar ya barta ne a hannun matar babanshi,tunda baida kowa iyayenshi duk sun rasu,matar nan ta tsani yarinyar ta takurama rayuwarta gata irin tsoffin nan ne masu mitar tsiya,duk wani aiki yarinyar take ɗauramawa,girki,sharar gida,wanki,ɗebo ruwa,kuma ƙarama ce alokacin bazata wuce 16 years ba,

 

Koda baba buzu yazo niger ganin gida,zuwan bazata yayi masu bai sanar ma kowa da maganar zuwan nashi ba,saboda yana so yaba Abu mamaki kuma yaga irin farin cikin da zatayi idan ta ganshi,kwatsam yana shiga gidan ya samu matar baban nan tashi zaune saman abu ta danneta a tsakar gida,yarinyar sai ihu takeyi tana wutsil wutsil da ƙafafunta,ita kuma matar sae sambatu takeyi tana cewa”Babu abunda zai hana inƙi kasheki acikin gidan nan Abu,dan ubanki ni zakiyi ma asarar tsintsiya?kin barta a ƙasa har ruwan sama ya jiƙata baki ɗauketa ba!ko don kina taƙamar ubanki ne ke turo mana da kuɗi muna siyan kayan abinci….’

Hankalin baba buzu ba ƙaramin tashi yayi ba a wannan lokacin,ganin zai rasa ƴarshi ɗaya tilo akan tsintsiyar shara da bata wuce naira hamsin ba,ba ƙaramin fusata yayi ba,a ranar ko zama gidan baiyi ba ya ɗauki ƴarshi ya tafi da ita gidan wani amininshi,tamkar ya zubar mata da hawaye haka yaji a wannan lokacin,yarinyar duk ta rame ta fige ta ƙanjame kamar ba mutun ba,yarinyar da duk garinsu babu wanda ya kama ƙafarta a wurin kyau,tun lokacin da mahaifiyarta ta haifa mashi ita,Allah yayi mata rasuwa tabar mashi ita ƴar jinjira da ita,shi yaci gaba da kula da yarinyar,mutane sunsha zuwa suna nuna mashi kuɗi don ya bar musu yarinyar su ruƙe awurinsu amma yaƙi amincewa da hakan,saboda son da yake yi mata,

 

Bayan hajiya Amina sun dawo nigeria ita da mijinta,Baba buzu ya shirya tafiya tare da ƴarsa abu,babu yarda abokinshi baiyi dashi ba akan ya bar mashi Abu suci gaba da kular mashi da yarinyar a hannunsu,amma ina yace ae ƙafarshi kafar abu,bazai ƙara gangancin barinta a wurin wani ba,kwara ta kasance atare dashi,yana jin motsinta a kusa dashi,zaifi samun kwanciyar hankali,

 

Da daddare suka ƙaraso nigeria bayan uwar tafiyar da suka sha agalabaice suka iso cikin gidan,ruƙe da hannun Abu ya shigo cikin falon gidan,lokacin hajiya ameena na zaune saman kujera mai mazaunin mutun uku tana kallo a tv,tun da sukayi sallama ta dago ta kellesu ganin baba buzu yasa ta saki fara’a tana cewa”marhabun lale ƙaraso ciki mutumina,ashe kana kan hanya banyi tsammanin zuwan…..’bata ƙarasa maganar ba,saboda ganin yarinyar dake ruke da hannunshi,

.mikewa tayi tare da zame farin glass ɗin dake a fuskarta tace”baba buzu wannan yarinyar fa?yar waye kazo da ita,”

bai bata amsa ba,sae da suka ƙarasa wurin kujerar da take tsaye,suka zauna kasa saman carpet,sannan ya soma magana”hajiya shannunku da dawowa,ya gajiyar tafiya,’

“Lafiyalou Alhmdulillah,”

Taƙarasa maganar har lokacin idanunta na akan abu,komawa tayi tare da zama saman kujerar sannan tace”bakayi mun bayani game da yarinyar nan ba,”Tayi maganar tana nuna Abu dake ƙankame jikin abbanta

 

Fargabarsa kada ya sanar dasu cewa ƴarshi ce,suƙi kar6arta baisan inda zai kai yarinyar ba,ya kwaso yarinya ya kawo masu batare da ya sanar dasu ba,

 

dakyar ya iya buɗe baki muryarshi kamar zaiyi kuka yace”yarinyar wurina ce hajiya sunanta Abu,ina neman alfarmar ku taimaka mun ta zauna awurina,saboda bata da kowa acan niger,dama a hannun kishiyar babata take zaune,matar bata da imani naje na shame ta tana gallazama yarinyar nan,ban ta6a sanin abunda ke faruwa ba,sai da nayi masu zuwan bazatan nan…….’komai ya kawashe ya sanar ma hajiya ameena,

Kamar jira takeyi ya kai ƙarshen maganar tashi,nan ta rufe shi da faɗa tana cewa”Amma baba buzu ka bani mamaki wlh,yanzu duk irin shaƙuwar dake tsakaninmu dakai,duk irin yarda muka ɗaukeka tamkar ɗanuwanmu,hakan baisa ka sanar damu cewa kana da ƴa ba,meyasa tun lokacin daka fara aiki agidan nan baka ɗauko yarinyar ka kawota gidan nan ba!….’ta inda take shiga bata nan take fita ba,

Jin waɗannan kalaman na Hajiya ameena yasa baba buzu fashewa da kuka yana cewa”na cuci kaina da ban sanar maku ba,ban ta6a tunanin cewa zaku kar6i yarinyar nan hannu bibbiyu ba hajia,da tuni na jima da kawo maku ita,kullum ina cikin takaicin rashinta a kusa dani,saboda itace kaɗai nake gani inji dadi aduniyar nan……’sosai baba buzu ke zubda hawayenshi,

Abu kuwa ganin mahaifinta na kuka yasa itama ta fashe da kukan,jikin hajiya ameena ne yayi sanyi,tausayinsu duk ya kamata,

tausasa muryarta tayi tace”baba buzu kukan ya isa hakanan,naji daɗin dawowarka musamman daka kawo mana wannan ƴar kyakkyawar yarinyar taka,kuma insha Allahu zamu bata kyakkyawar kulawa,zata zama tamkar ƴar cikina,dama kuma banda ƴa’ mace,gashi inason ƴa mace,Ashe da rabon zan samu……’

Share hawayen shi ya shiga yi yana yi mata godiya,

“Yanzu abunda nakeso dakai,ka wuce ɗakinka kayi wanka zansa akawo maka abinci,nasan kun kwaso gajiya sosai kuna bukatar hutu,ita abu kabarta awurina,zan gyara maka ita sosai da anjima zata zo ta gaishe ka,”

Cikin shesshekar kuka baba buzu yace”hajiya bansan da wani irin kalamai zan gode maku ba,kunyi mun abinda bazan iya saka maku ba,kun jima kuna ɗawainiya dani kuma yanzu gashi zaku ɗauki ɗawainiyar yarinyata,Allah yasa ka maku da mafifincin alkhairinsa…..’sosai baba buzu ya shiga yi masu addu’o’i hakan ba ƙaramin dadi yayi ma Hajiya ameena ba,

 

Tun daga wannan lokacin Abu tazama tamkar ƴa awurin hajiya Ameena,baka ta6a gane cewa ba ƴar cikinta bace saboda yadda suke ruƙe ta hannu bibbiyu duk wata ɗawainiyarta tadawo kansu,hatta makarantar islamiyya dana boko babu wanda basu sakata ba,dama yarinyar akwai hazaƙa sosai,akwai son karatun addini,kullum zaka ganta rungume da kur’ani a hannunta tana karatu,ko aiki takeyi zaka ji tana ta rero karatun haddar da aka basu,bata ta6a zama bakinta shiru batare da tana karatu ba,wannan abun ba ƙaramin burge hajiya ameena yake ba,shiyasa batajin wuyar kashe mata kuɗi,saboda ita ta ɗauko malamin da zai dinga zuwa gida yanayi mata karatu,malamin makarantar islamiyyarsu wanda suke kira da Ya sayyadi,tun da zainab tafara zuwa makarantar islamiyyar asatin farko kullum sai yazo gaishe da hajiya ameenatu,idan yazo yayi ta zuzuta zainab awurinta yana yaba irin ƙoƙarin dake gare ta,hajiya Ameenatu najin daɗin hakan,Amma mahaifin Abu,baba buzu mai gadi mutumin bai kwanta mashi araiba,ya tsani yaga malamin nan yazo wurin Abu zai koya mata karatu,shisshigin da yake yi ma yarinyar yayi yawa,kullum sai yazo da ɗan rugwagwar mashin ɗinshi ƙopar gate din gidan wurinta,hakan ba ƙaramin ƙona ma Baba buzu rai yake ba,shiru kawai yake yi don bai da yadda zaiyi ya hana shi zuwa gidan,tunda hajiya ameenatu ta ɗauke shi amatsayin malamin da zai dinga koyama Abu karatu,tun Abu na da wata daya acikin gidan haris ya dawo batare da Abusufyan ba,saboda shi yace bazai dawo ba sai daddy mijin Aunty ameenatu ya bashi haƙuri,saboda yace shi yake 6ata tarbiyyar Haris,rashin jin maganar shi yayi yawa,koda haris ya hadu da Abu acikin gidan saiya mayar da ita tamkar ƙanwarshi,idan aka bata assignment na school shike zama ya fidda mata shi,harma ya koya mata karatu.

Back to top button