Hausa novels

Abban Sojoji Chapter 66 Book 2 Complete Novel

Abban Sojoji Boo 2

Father Of soldiers❤

Story and written by Hafsat Bature Mohamed Boss Lady_

Gagarumar Walima Abba ya shirya masu awashe garin ranar,na murnar dawowar Abusufyan Nigeria,tun da wuri aka soma shirye shiryen gudanar da ita,basu yi inviting ɗin kowa ba,anan cikin gidan kawai za’ayi ta,yasu yasu batare da wani bare ya shigo ba,don nasan halin sumayyer yanzu ta kwaso ƙafa tace zata,

Gaba ɗaya ko’ina na gidan ya karaɗe da ƙamshin dadɗaɗan girkin dasu azmee ke yi acikin kitchen ita da Hayaam,tun da sanyin safiya suka fara aikin girke girken,tun bayan da  Abbansu junaid ya sanar da ita game da walimar,suka soma gunadar da aikin batare da 6ata lokaci ba,

Matasan gidan kuwa wankan shadda zasu ɗauka gaba ɗayansu,kamar yarda Abbansu ya basu Umarnin su sanya shadda ajikinsu in kuma ba shadda ba kowane kalar kaya zasu iya sanyawa ajikinsu indai namu ne na hausawa,duk sun amince da hakan,

Karanta>>> Hanyoyin Magance Matsalolin Ma’aurata

“Azmee wai ita yarinyar can bazata fito ta tayamu aiki bane?tun safe muke ta faman aikace aikace ko leƙowa batayi ba,”Hayaam ce tayi maganar yayin da take ta faman kwa6a fulawa acikin roba,duk ta haɗa gumi a fuskarta,’

Azmee tace”kema ae ban matsa maki ba,naga kamar kina son aikin ne shiyasa ma nayi maki magana,amma idan kin gaji ko yanzu ma zaki iya tafiya,”

Rae a6ace tace”yanzu me ya kawo wannan maganar Aunty azmee?nifa ina magana ne akan waccen yarinyar sehrish ya kamata ta fito ayi aikin da ita,na lura kamar bakiso inayi maki magana akanta,kin gatanta yarinyar sosai,shiyasa bata da aikin yi sai dae ta zauna tayi ta sharar bacci kamar matacciya,bata tsinana uban komai acikin gidan nan hakanan take sunan yar aiki….”

Karanta>>> Yadda Zaki Kula Da Kanki Kafin Aure Da Kuma Bayan Aure

juyowa azmee tayi daga tsayen da take agaban gas cooker,ta kalli hayaam dake ta faman hura hanci ga uban gumi ta haɗa,

“Hayaam!sehrish ba tada lafiya,shiyasa ban tashe ta daga bacci ba,tun jiya da daddare take fama da raɗaɗin ciwon ciki daƙyar ma aka samu tayi bacci,wannan dalilin ne yasa banyi yunƙurin tashinta daga baccin ba,”

ta6e baki hayaam tayi tare da cigaba da aikin da takeyi cikin ranta tana fadin”ta dai gama iskancinta tayi bacci,

Marshal Omar

Tun yana cikin toilet wayar shi ke ta faman ringing,cikin sauri ya fito daga cikin toilet ɗin,jikinshi ɗaure da towel,ƙarasawa yayi inda ya ajiye wayar asaman pillow,ya miƙa hannunshi ya ɗauki wayar yana duba mai kiran nashi,murmushi yayi aranshi yace”Allah yasa jiya sun samu bacci,don na lura da yadda suke ta faman ɗokin son ganin ƴar uwar nan tasu,nima kaina a ƙagare nake dana haɗasu wuri guda,don su cigaba da rayuwa atare,

Picking call ɗin yayi ya kara wayar a kunnanshi,

Tun kafin yayi sallama muryar hosana ta katse  mashi hanzarinshi da cewa”Ya omar!yaushe zaka zo ne!kai muke ta jira,jiya fa ko bacci ba muyi ba,

Tana kai ƙarshen maganarta Jahad ta kar6e da cewa”ya Omar dan Allah ka tausaya mana,wlh ko breakfast ba muyi ba,kuma muna jin yunwa amma mun fi so muci abinci atare da ƴar uwarmu,”

Jin wannan maganar ta Jahad,yasa jikin shi yin sanyi,da alama ba ƙaramin so suke yi ma junansu ba,

“Ya omar kayi shiru,”muryar hosana ce tayi maganar a ƙagare,

cikin natsuwa ya soma magana”kuyi haƙuri kunji,insha Allah yau zaku ga ƴar uwarku,bazan samu zuwa ba,amma zan turo major ya ɗauko ku,abunda nake so daku yanzu,ku ci abinci ku ƙoshi,sannan kuyi wanka ku shirya ku sanya kaya masu kyau,a kowane lokaci zaku iya ganinshi yazo,”

Yana jiyo muryoyinsu ta cikin wayar suna ta faman fadin Wayyo daɗi yau zasu ga rishi ɗinsu,’

Sallama yayi masu bayan ya ajiye wayar,ya juya tare da wuce wa wurin closet ɗinshi,tsaf ya shiga shirya kanshi acikin rantsattsiyar shaddar shi.

 

SEHRISH,

Kwankwasa ƙopar ɗakin da akayi mata ne da ƙarfi,yasa ta tashi a firgice tana faman zazzare ido,ƙankame bargon jikinta tayi tana ƙara lullu6e jikinta dashi,fuskarta duk a yamutse saboda kukan da tasha jiya,amma yanzu Alhamdulillah tun da tafarka babu wannan ciwon cikin atare da ita,tamkar bata ta6a yin ciwo ba haka ta farka,taji sauƙi sosai,

“Reesh,baby junaid ne fa,in shigo daga ciki”?

Muryar junaid ce taji yana magana daga waje,

akasalance tace”eh,ka shigo,”

. tura ƙopar yayi tare da sanya kafa ya shigo cikin ɗakin hannunshi ɗauke da cup sae tiriri ke fitowa daga ciki,bakomai bane aciki face Corn flakes daya haɗo mata,yaji Uwar madara acikinshi,

Sae faman murmushi yake sakar mata,wuri ya samu daga gefen gadonta ya zauna,sannan yace”reesh ya jikin naki?jiya ko bacci banyi ba saboda damuwa da halin da kike ciki,’

“da sauƙi junaid,yanzu bana jin ciwo atare dani,na wartsake sosai,amma ina fata kaima kana cikin ƙoshin lafiya ko?naga fuskarka kamar ta canza kamanni,kayi haske sosai kuma fuskar ta ɗan sauya haka,Lips ɗinka sun ɗan kumbura kaɗan kalarsu ta ƙara cizawa sosai’tayi maganar yayin da take ƙare ma fuskar tashi kallo kamar wata malamar duba

Karanta>>> Ga Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah

Junaid yace”farin cikin da kika bani jiya shine ya canza mun kamannin fuskata,ko kin manta abunda mu kayi jiya acikin Mota tare da ke?fuskarshi ɗauke da murmushi yayi maganar,

Cike da mamaki sehrish tace”wane abu kenan?yaushe muka haɗu acikin mota?bayan bakazo ka ɗauke ni daga school ba,ni da ka manta dani junaid,nasha wahala jiya sosai,kamar bazan rayuwa ba,na neme ka na rasa…….’muryarta tamkar zatayi kuka tayi maganar,

“Sehrish!me kike nufi da banzo na ɗauke ki ba?ko raɗaɗin ciwo yasa kin manta da abunda ya faru jiya atsakaninmu”?

girgiza kai tayi alamar a’a tace”Nifa bakazo ka ɗauke ni ba,jiya da aka tashi daga school ciwon ciki ya kamani,shine na shiga toilet anan na yanke jiki na faɗi saboda azabar ciwon da nasha,gaba daya nafita hayyaci na…….’gaba ɗaya sehrish ta bashi labarin abunda ya faru da ita tun daga A har zuwa Z,abu ɗaya ne bata sanar dashi ba,shine zuwan waɗan nan matasan guda huɗu da suka ɗauketa a mota,

Tun da ta soma kora mashi bayani,hankalinshi yayi mugun tashi,jikin shi har kerma yakeyi wurin cewa”reesh dagaske ne duk abunda kika faɗamun”!.

ɗaga mashi kai tayi alamar eh,sannan tace”ka faɗamun me ya hana ka zuwa ka ɗauke ni junaid?nayi tunanin zaka dawo ka ɗauke ni,in kaji shiru ban dawo gida ba,amma bakazo ba,’

Gaba daya ta gama rikitar dashi duk yabi ya ruɗe,muryarshi har rawa takeyi wurin cewa”wlh nazo jiya school ɗinku,kuma naɗauke ki dakaina acikin motata…….’gaba daya junaid ya kwashe duk abunda ya faru tsakanin shi da jahad ya sanar ma Sehrish,

Zuba mashi ido tayi tana kallonshi ita kanta hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba da jin labarin da junaid ya bata,

“Junaid!ban karyata ka ba!amma anya ba gamo kayi ba?zai iya yiyuwa fa aljana ce in ba haka ba,taya za’a ce tana kama dani komai da komai har ka gaza gane cewa ni ce ko bani bace,”?a ruɗe tayi maganar tana kallon junaid,

Junaid sarkin tsoro tuni idanunshi sun cicciko da kwalla tsoranshi kar ace lokacin mutuwar tashi ne yayi shiyasa ya fara ƴan gane gane,zai iya yiyuwa ma mutuwarce tafara kawo mashi ziyara kafin tayi wuff dashi,

tuna wannan yasa shi fashe mata da kuka yana cewa”innalillahi wa’inna ilaihir raji’un shikenan lokacina yayi sehrish,dama nasan daƙyar zan wuce yau araye,….’

Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,ganin yarda junaid ya fashe mata da kuka,da alama ya tsorata sosai’

“Junaid ya isa haka,ka daina kuka kaji,insha Allah ba yanzu zaka mutu ba,har sai mun yi aure mun haifi ƴa’ƴa,in ma zamu mutu atare mutuwar zatazo ta ɗauke mu,’

Jin wannan zancen na sehrish yasa shi yin tsit yana faman sauke ajiyar zuciya,ga dariya na cinta amma tana tsoran karya kuma fashe mata da wani kukan,aranta tace”Tabɗijancan su junaid ansha soyayya da al’jana,da sauƙi ma tunda iya kiss suka tsaya,”

Miƙa mata cup ɗin hannunshi yayi tare da cewa”gashi kisha,corn flakes ne ni na haɗa maki da kai na,”wani irin tausayinshi ne taji ya kamata,musamman yarda ya nuna damuwarshi akanta,har ya haɗo mata cornflakes dakanshi don tasha,’

zuba mashi ido tayi tana kallonshi,fuskarshi duk a yamutse babu alamun natsuwa atattare dashi,duk ya firgice da jin cewa ba ita bace ya ɗauko a school ba,kuma hankalinshi bazai ta6a kwanciya ba har sae ya tabbatar da cewa ba aljanu bane suka fara kawo mashi ziyara,

Cikin sanyin murya tace”Junaid,dan Allah ka share hawayenka kaji?ko ka manta da alƙawarin da ka ta6a yi mun na cewa ba zaka ƙara yin kuka ba”?

Muryarshi akasalance yace”nadaina,kiyi haƙuri bazan ƙara ba,” yayi maganar yayin da yake miƙe mata cup din,

“Ba zaka ban abaki nasha ba”?

ɗagowa yayi yana kallonta jin abunda tace,tayi mashi hakan ne don ta kawar da damuwar dake a fuskarshi,

Matsawa yayi kusa da ita sosai,sannan ya zura hannunshi tare da dauko cokalin ciki,ya ɗebo cornflakes ɗin ya miƙa mata abakinta,

Buɗe bakinta tayi ya zuba mata aciki,a hankali take murzar shi abakinta tana haɗiyar shi,yayi mata daɗi sosai saboda madarar daya zuba aciki,

Haka yaci gaba da bata abakinta tana sha,tun fuskarshi na aɗaure harya fara sakin wannan murmushin nashi,ganin ya washe daga damuwar da yake ciki yasa sehrish cewa”junaid,Wai jiya Uncle ɗin nan naku ya ƙaraso ne”?

“Eh,yanzu haka yana acikin gidan nan ma,ya kamata kije ki gaishe su,hada aunty azeema kanwar Abbanmu itama tazo jiya,”

wani irin farin ciki ne ya lullu6eta cike da zumuɗi tace”inaso naje na gaishe shi,amma ina jin fargabar zuwa wurin shi,”

Junaid yace”meyasa toh?na gaya maki cewa basu da matsala,uncle dinmu mutun ne mai sauƙin kai fiye da tunaninki,haka Aunty azeemarmu ma tana da mutunci sosai,baki ga gift ɗin da takawo mun ba,zan nuna maki anjima,zaki sha mamaki,”

murmushi sehrish tayi a lokacin harya kammala bata corn flakes ɗin,

“Bari nashiga toilet nayi wanka,idan na kammala shiryawa sai mu tafi tare da kai ka rakani wurinshi in gaishe dashi,’

Amsa mata yayi da toh,sannan ya miƙe tare da ɗaukar cup ɗin daya ajiye asaman side drawer dinta,ya fuce dashi,

Download>>> Bintu Ɗiyar Bayi Ce Book 1 Complete Document

Ajiyar zuciya ta sauke,bayan fitar shi ta sauko daga saman gadon tare da nufar dressing mirrow dinta ta tsaya tana kallon kanta ta cikin madubin,hannu tasa ta shafo sumar kanta da sgr ya datse mata shi,nan take ta tuna da abunda ya faru jiya lokacin daya shigo yi mata allura,wannan kallon da yayi mata ya tsaya mata aranta,da kuma kalaman da ya furta mata cikin sanyin murya,tabbas tana ji aranta cewa sgr ya fara jin abunda take ji agame dashi,duk da tasan cewa zaiyi wuya ya gane cewa akwai soyayya atattare dashi,kuma zaiyi wuya ya iya furta mata ita,

ta cikin mirror ta hango jacket din da sgr ya sanya mata,tana ajiye saman gadon,juyawa tayi cikin sauri tare da kai hannu ta ɗauko rigar sanyin tana kallonta,

tunani tashiga yi rigar wanene wannan?taya akai tazo bedroom ɗinta kuma asaman gadon nata!?

ƙamshin Turaren jikin jacket dinne ya bata amsar tambayar da take nema,

Matse rigar tayi a hancinta,anan ta dinga jin ƙamshin turaren Sgr sosai ajikin rigar wannan ya tabbatar mata da cewa tashi ce,a hankali tashiga tunanin ta yadda akai jacket dinshi tazo bedroom ɗinta,kodai jiya ne daya zo yi mata allura…..  ‘

kwankwasa kopar da akayi ne ya dawo da ita daga zurfin tunanin da tashiga,

“Wanene”?ta tambaya tana kallon kopar,

Turo kopar azmee tayi tare da shigowa ciki tana cewa”ni ce sehrish,ya jikin naki fatan kin tashi lafiya,tun ɗazu nake ta zarya wurin leƙowa ɗakinki inga ko kin farka daga baccin,amma duk in nazo sai in same ki,kina ta sharar bacci,’

murmushi sehrish tayi tana kallonta tace”ina kwana Aunty azmee?fatan kun tashi lafiya,ya aiki”?

“Alhamdulillah sehrish,jiya mun shiga damuwar rashinki,kuma sai gashi Allah yasa an gano ki,da ba’a ganki ba,da bansan inda zan sanya raina ba,”ta ƙarasa maganar yayin da take ƙarasa shigowa daga ciki,ta tsaya a kusa da sehrish suna fuskantar juna,

“Aunty azmee wai meya faru dani jiya?ya akai nadawo cikin gidan nan?waye ya ɗauko ni?kuma naga wannan jacket din asaman gadona,kamar ta babban yaya ce,”

Azmee tace”ae jiya,shi da kanshi ya dawo dake acikin gidan nan,gaba ɗayanmu munyi mamakin ganinshi ɗauke da ke a kafaɗarshi,duk da banji da kyau ba,amma naji yana ba Abbansu labarin cewa acan suka same ki cikin wani garden wasu matasa suna ƙoƙarin lalata maki rayuwarki ……….’tunkan azmee ta ƙarasa maganar sehrish ta tunano da abunda ya faru jiya,sai lokacin komai ya dawo cikin kanta,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta jin cewa Sgr ne da kanshi ya taimaki rayuwarta a hannun waɗannan miyagun da suka kai mata hari,kuma taji daɗin bugun da yayi masu,don akan idanunta ya naushi ɗaya daga cikinsu,har haƙoran shi guda biyu suka 6allo daga bakinshi,tun daga sannan ne bata ƙara sanin meya faru ba,amma tabbas taji lokacin daya ɗauke ta a hannunshi ya sanyata acikin motarshi,kuma tana da tabbacin cewa shine ya sanya mata rigar sanyinshi,kilan saboda yaga jikinta na kermar sanyi,

Cike da farin ciki tace”Aunty azmee lokacin da babban yaya ya shigo dani cikin gidan nan akwai wannan rigar ajiki ne ko”?

ɗaga mata kai tayi alamar eh,

Washe baki ta shiga yi kamar wadda akayi ma albishir da gidan al’janna,

Murmushi azmee tayi ganin yarda sehrish ke ta faman murnar jin cewa sgr ne ya taimake ta,

hannu tasa tare da dafa shoulders dinta tace”Ki shirya yau akwai walima acikin gidan nan,zuwa anjima wuraren ƙarfe huɗu za’a soma gudanar da ita,inaso kiyi kwalliya sosai yau,yanzun nan zan sanya junaid ya kar6o maki kayanki,wlh mantawa nakeyi,’

“Aunty azmee baki ga abunda babban yaya yayi mun ba?taya zan iya yin gayu da wannan guntun gashi dake akaina”tayi maganar tana damƙo wutsiyar gashin kan nata,

Sae lokacin azmee ta lura da kan nata,hankali atashe tace”garin yaya hakan ya faru?waye ya yanke maki gashi har haka”?

“Babban yaya mana,saboda laifin da bani na aikata ba,ya sanya almakashi ya datse mun gashin kaina,banji daɗi ba,saboda nasha wahala wurin tara shi da yawa yanzu bansan ya za’ae nadawo dashi ba,”cike da damuwa tayi maganar,abun har yanzu yana yi mata ciwo,

Download>>> Dr Bobby Hausa Novel Document

“Wani laifi kenan kika aikata”?

Sehrish tace”a cikin coffee ɗin da nakai mashi jiya da safe,yana cikin sha,gashi ya sarke mashi a makoshi,ran shi ya 6aci sosai har ya yanke mun gashin kaina,wlh aunty azmee ba gashin kaina bane,ni banta6a yin kuskuren barin kaina abuɗe ba,lokacin da nake acikin kitchen,”

shiru Azmee tayi na dan wani lokaci kafin tace”bakomai kawai,kiyi haƙuri nasan kowanene ya aikata hakan,amma banaso ki sanya damuwa aranki,”

“Shikenan,yanzu bari naje nayi wankan,”ta ambaci hakan tare da ajiye jacket ɗin asaman gadon,

“Kinason ƙunshi ne?idan kina ra’ayi zan zana maki da kaina na iya sosai,”

“Inaso sosai Aunty azmee,yaushe rabon dana ga lalle a hannu na har na manta wlh,”

Azmee tace”yanzu kije kiyi wankan,kafin dai zuwa ƙarfe huɗun zamu kammala komai,’

ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta fuce daga cikin ɗakin,

Wuce wa cikin toilet sehrish tayi domin yin wanka

 

💋Boss Bature💋

 

Zaune suke acikin mota su biyu,Ayaan ne ke driving ɗinsu yayin da jahan ke zaune gefen shi sae faman buga tsoki yake yi yana cewa”Ayaan wai ina zaka kaimu ne!ni fa gida nace maka mu koma,banaso afara shagalin walimar nan,bana a kusa,’

Murmushi ayaan yayi tare da cewa”kai dai kawai ka zuba ido ka gani,wani abun mamaki ne nakeso na gwada maka,nasan cewa zai girgiza ka sosai,’ya ƙarasa maganar yayin da yake shigar da motar tasu gate din gidan Yayansu Abbas,

Jahan yace”wai dama nan zaka kawo mu?muyi me kenan?Anya kuwa ayaan kasha maganinka na safe kuwa?

dariya Ayaan yayi tare da cewa”a’a ban kaiga sha ba,amma yanzun idan nakai ka cikin gidan nan,na nuna maka abunda nakeso ka gani,bayan mun fito zaka faɗamun ni dakai waye mai buƙatar shan magani acikin mu,”cike da zolaya Ayaan yayi maganar,

shiru jahan yayi bai ƙara cewa komai ba ya zuba ma sarautar Allah ido,

Bayan Ayaan yayi parking ɗin motar,ya fito tare da zagayawa ya buɗe ma jahan motar tare da nuna mashi hanya da hannunshi yace”mun ƙaraso yalla6ai,”

harara jahan ya watsa mashi tare da zura ƙafafunshi ya fito daga cikin motar,yana faman ɗaure fuska ya wuce gaba ayaan yabi bayanshi suka shiga cikin gidan,

Karanta>>> Yadda Zaki Kula Da Nonuwanki Lokacin Da Kike Shayarwa

Da sallama abakunansu suka shiga cikin babban falon gidan,a lokacin Amani na a cikin kitchen tana aikin breakfast,jin sallamarsu twins yasa ta fitowa da sauri don taga su wanene,

Ba ƙaramin mamaki tayi ba,ganin ayaan da jahan atsaye ruƙe da hannun juna,

Ƙarasawa wurinsu tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace”Sannunku da zuwa,ashe kune sam banyi tsammanin ganinku ba,”

Kawar da kai gefe jahan yayi batare da yace komai ba,.

Ayaan yace”yawwa Aunty amani,kun tashi lafiya,fatan mun same ku lafiya?

Ta amsa mashi da cewa”Lafiya lou Alhamdulillah,nayi farin cikin ganinku,ku ƙaraso daga ciki mana,”

Jahan yace”sauri muke zamu wuce,Ayaan ka shiga daga ciki ku gaisa ni zan jiraka a mota,’yayi maganar tare da juyawa zai fuce,

Cikin sauri Ayaan ya ruƙo hannunshi tare da cewa”haba jahan wai menene haka?just 15 mins zamuyi fa kafin mu wuce gida,’

ɗaure fuska jahan yayi alamar an takura mashi,

Amani kuwa murmushi kawai tayi,tana mamakin yarda suka kasance twins komai nasu iri daya,amma hali ba iri ɗaya ba,Ayaan ta 6angaren Abbansu yake,shi kuma jahan sak mommynsu ce,

daƙyar Ayaan ya samu jahan ya bisu suka shiga cikin falon,atare suka zauna saman 3 seater,ita kuma ta zauna saman 2 seater tana fuskantar su,yarda jahan ke ta faman yatsina fuska,ba karamin dariya yaso ya bata ba,ji yake kamar ya ɗosana ass ɗinshi asaman ƙayoyi haka yake ji,

 

Ayaan ne ya soma magana”Aunty amani kinji mu shiru ko?ba mu sake zuwa mun duba jikin Amal ba,ban ji daɗi ba wlh abubuwa ne sunyi mana yawa,amma tana aran mu,shiyasa ma muka yanke shawarar zuwa yau mu duba ta,’

taji daɗin kalaman ayaan sosai,fuskarta ɗauke da murmushi tace”Amal taji sauƙi sosai,kullum sai ta tambayeni ina twins ɗin nan suke,musamman kai Ayaan tafi tambayarka saboda kaine ka kawota wurina,yanzu bari naje na kawo maku abun ta6awa,kafin na kira maku Amal ɗin ku gaisa,”

Ta ƙarasa maganar tare da mikewa ta wuce cikin kitchen,

Tana barin wurin jahan ya buga tsoki tare da cewa”Wlh ayaan ka bani haushi!ka zauna ka gama tsara mata ƙaryar cewa mun zo duba jikin wannan ƙarmasasshiyar yarinyar ne,yarinyar da nama manta da zancen ta ni,mtswwww,’ya kawar da kanshi gefe yana hura hanci,

Ayaan yace”Am sorry bro,nasan ban kyauta ba,amma kayi hakuri kasan banason 6acin ranka,ni aganina bamu kyauta ba,tun ranar da nakawo yarinyar nan,ba mu ƙara zuwa mun dubata ba,kuma abunda ya dace ace munyi ne,”

ta6e baki jahan yayi tare da kallonshi yace”sannu ko?sarkin tausayi,”

Jin takun tafiyar Amani ne yasa su kayi shiru,ƙarasowa ciki tayi hannunta ɗauke da tray,cups ne guda biyu,sae lemu masu sanyi acikin roba tare da plate na snacks,asaman table ta ajiye masu sannan ta juya tana cewa”bari na kira Amal din ku gaisa,”

ɗaukar lemun ayaaan yayi tare da buɗe shi ya tsiyaya masu acikin cup,ya dauki ɗaya ya miƙa ma Jahan,ya kar6a sannan shi kuma ya ɗauki ɗayan,yana sha,

 

Saukowa amani tayi daga upstairs,ta dawo wurinsu ta zauna saman sofa din tana cewa”gata nan zuwa,”

Ayaan yace”Allah ya kawota lafiya,”

Karanta>>> Tusar Gaba Da Abinda Ya Kamata Ki Sani Game Da Ita

Gaba daya sun mayar da hankalinsu wurin shan Lemun dake hannunsu,su ka jiyo takon takalminta,kwas kwas,

Ayaan ne ya fara ɗago da ido yana hangen yarinyar dake saukowa daga saman benen,juyawa yayi ya kalli amani tare da yin ƙasa da murya yace”ita ce ko”?

.murmushi amani tayi tare da daga mashi kai alamar eh,

Satar kallon jahan yayi wanda hankalinshi ba a kansu yake ba,

A hankali Amal ta ƙarasa saukowa daga saman benen ta nufo inda suke,lokacin da ta ƙaraso wurinsu fuskarta ɗauke da murmushi tace”sannunku da zuwa,”

Kai tsaye muryarta ta daki dodon kunan Jahan,daɗin muryarta ne yasa Jahan juyowa cikin sauri don yaga wacece,ai yanayin arba da wannan kyakkyawar fuskar ta Amal nan take ya saki Cup ɗin dake hannunshi ƙasa,ya tarwatse lemun ciki ya zube,

A gigice ya miƙe tsaye yana kallonta yayin da zuciyarshi ke bugawa da ƙarfi da karfi,yarda kasan hurool aini awurin kyau haka yarinyar ta koma mashi,

fara ce tass,har ma tafi Amanin haske,fatar jikinta har wani ƙyalli takeyi saboda gyaran da tasha,tabarakallah masha Allah ta ko’ina amal ta haɗa,ga manyan idanun nan nata dara dara dasu,ga dogon hancin nan nata kamar zaiyi sujjada,la66anta kuwa sunyi red colour sosai tamkar ta shafa janbaki,idan tayi murmushi kamar gonar auduga saboda hasken haƙoranta,lallai ba ƙaramin gyara Amani tayi ma ƙanwarta ba,ta canza mata kamanni sosai,ta fito a balarabiyarta,sleeping dress ne ajikinta pink colour riga da wando,ta yafa gyale fari asaman kanta,

dare ɗaya Allah kanyi bature,acewar ayaan,

Ina labarin Jahan daya miƙe tsaye ya zuba mata ido yana kallonta ko ƙyaftawa baiyi,abun tamkar a mafarki yake kallonshi,gaba daya ya gama ruɗewa,muryarshi na rawa yace”ke!kece!’cike da mamaki yayi maganar,

Amal kuwa aɗan tsorace taja baya,tana faman zazzare mashi kyawawan idanunta,ganin yarda ya harzuƙo kamar zai rufe ta da bugu,

murmushi kawai Amani ke saki ita da ayaan suna kallonshi,dama wannan duk shirin Ayaan ne,

“Aunty amani!surgery akayi mata ne?if not taya akai tayi transforming haka”? A ruɗe jahan ke tambayarta,

miƙewa tsaye amani tayi tare da takawa zuwa inda suke ta ruƙo hannun Amal tana cewa”ikon Allah ne jahan,babu wani surgery da akayi mata,gyarane kawai tasha,dama can Amal kyakkyawa ce,wannan asalin kamannin fuskarta ne ya dawo,’

Jiki asanyaye Jahan ya koma tare da zaunawa saman sofa din,har lokacin bai janye idanunshi daga kallon fuskar Amal da yake yi ba,kamar ya haɗiyeta haka yake ji,ya jima yana mamakin wannan ikon Allahn,

Miƙewa Ayaan yayi tare da cewa”mu zamu wuce gida,ana can anata shirye-shiryen haɗa walimar murnar dawowar uncle abusufyan,ina fata zaki zo mana tare da Amal,’yayi maganar yana kallon Amani,

Tace”mai zai hana,ae muna nan zuwa anjima insha Allah,tare da mu za’a buɗe taron walimar,”

“Allah ya kawo ku lafiya,’yayi maganar tare da mayar da idanunshi kan JAHAN daya ƙurawa Amal ido kamar mazuru yace”bro,tashi mu tafi mana,kada time ya ƙure mana,”

jiki amace jahan ya miƙe tare da ruƙo hannun ayaan cikin nashi,su kayi mata sallama tare da kama hanyar fita daga falon,

Suna tafiya Jahan na waiwayon Amal kamar zaiyi tuntu6e,hakan ba ƙaramin dariya yaba shi ba,saida suka fito daga cikin falon,bayan sun shiga cikin motarsu,Ayaan ya ɗan kallo shi cikin zolaya yace”Jahan ya kaga ƙarmasasshiyar ne?ko nace kingin rami ko?ya ma kace mun ran nan a asibiti daka ganta”?

Mene Ne Yakesa Nono Su Zama Ƙanana

A tsiwace jahan yace”bansani ba!dallah ni ka tashi motar mu tafi gida,”

dariya sosae Ayaan yayi yayin da yake tashin motar,ya ja ta suka bar gidan,yana driving yana kumshe dariya abakinshi,jin yarda Jahan ke ta faman buga tsoki,duk yabi ya susuce tunda yayi arba da Amal acikin idanunshi,ya nemi natsuwarshi ya rasa,a haka har suka ƙaraso cikin gidan,

 

wuraren ƙarfe sha biyu,sgr ya fito daga cikin toilet jikinshi sanye da bathrobe,yayin da hannunshi ke ruƙe da guntun towel wanda yake goge Sumar kanshi dashi,agaban dressing mirror ya tsaya yana ƙarasa goge sumar kan nashi,koda ya ɗago da idanunshi da niyyar ya kalli fuskarshi acikin madubin,sae ya dinga ganin fuskar sehrish acikin mirror ɗin amaimakon tashi,lokaci guda ya shiga tariyo duk abunda ya faru jiya atsakaninsu,tun daga lokacin daya je taimakonta,har izuwa lokacin da yaje yi mata allura,tana faman cizon la66anta,hakanan yaji yana marmarin son ganinta acikin idanunshi,tambayoyi ya shiga yi aranshi yana cewa meyasa batazo ta kawo min breakfast ba?ko har yanzu jikin nata ne?

Jin takun tafiyar mutun abayanshi yasa shi kai idanunshi wurin ta cikin madubin ya hange ta tsaye duk a tunaninsa yarinyar ce tazo,koda yayi arba da fuskar hayaam sai ya kawar da fuskarshi cike da mamakin wacece wannan?meya kawota bedroom ɗinshi,

ƙarasawa ciki hayaam tayi tana tafiya cike da kwarkwasa,wankan atampa ta ɗauka ajikinta,riga da skirt ne,kayan sun matse ta sosai,sun bayyana surar jikinta soaai,musamman saman rigarta boobs ɗinta sun fito waje kamar zasu ciro daga cikin rigar,akwai mayafi a jikinta lokacin da ta fito daga bedroom ɗinta,tana ƙarasowa ɗakin nashi ta cire mayafin tare da ruƙe shi a hannunta don taja hankalin shi,cike da ƙwarin guiwa tazo ɗakin nashi,saboda kwallin data shafa ma idanunta,wanda bokansu ya bata don tayi amfani dashi,ya tabbatar masu da cewa muddin sgr ya sanya idanunshi acikin nata,shikenan sun gama dashi,zai haukace akanta,ya rasa natsuwarshi,

Maganin Hips Cikin Sauki ga Mata:

Tsayawa tayi daga bayanshi,tare da kashe murya tace”ya kake ranka shi daɗe,ka tashi lafiya,”

Shiru Sgr yayi bai amsa mata ba,gaba daya lamarin ya gama ɗaure mashi kai,ƙarfin halinta ya bashi mamaki,

daƙyar ya iya buɗe baki yace”Ke!wacece ke!what are u doing in my room?yayi maganar batare daya sanya idanunshi acikin nata ba

zagayowa hayaam tayi ta gabanshi tamkar zata manna ƙirjinta asaman nasa,

Cike da rangwaɗa tace”Zuwa nayi don na gyara maka bedroom ɗinka,tunda ita yarinyar dake kula da part ɗin naka,bata jin ɗaɗi bazata iya yin aikin ba,idan ba damuwa inaso ka bani damar na ci gaba da kula dakai kanka,ina mai tabbatar maka da cewar zaka ji daɗin kasancewa tare dani,saboda ni ina da komai da komai,ba gyara ɗaki kaɗai ba,hatta ɗebe maka kewa zan dinga yi,nasan dole ka buƙaci mace akusa dakae especially da daddare haka.

 

Tashin hankalin da ba’a sa mashi date,yau hayaam tazo yi ma Sgr kwartanci acikin ɗakinshi,ita ga kwararriyar ƴar bariki,tana magana tana ƙara kusanta jikinta da nashi,

Just speechless gaba daya ta gama rufe mashi bakinsa,ya rasa abun cewa,shiru kawai yayi yana jira yaga me take ƙokarin yi mashi,daga nan zai san wane irin hukunci ya dace da ita,don ya lura cewa giya tasha,tana bukatar adawo da ita cikin hayyacinta,kuma har lokacin bai kalli cikin idanunta ba,

Wannan shurun da yayi ne yasa hayaam ta fara tunanin cewa kodae ya amince mata ne?shu’umin murmushin nan nata ta shiga saki tana bin surar jikinshi da kallo sae faman haɗiyar yawu takeyi kamar zata lashe shi,aranta tana cewa”dama nasani,muddin yayi arba da sura ta,dole ya kwaɗaitu,yanzun nan zan canza mashi alƙibla,zanja hankalin shi sosai,har nasamu abunda nakeso,

Kafin Sgr yayi wani yunƙuri gaba daya hayaam ta afka mashi tai hugging nashi sosae,tashin hankali saboda tsabar mamakin daya shiga ne yasa bai janyeta Ba,kanshi ya gama ɗaure wa,domin kuwa tunda ya ke arayuwarshi wata ƴa’ mace bata ta6a kuskuren ta6a wani sashe na jikinshi ba koda gigin wasa,sae wannan mai rabon shan dukan,

 

ita kuwa hayaam jin bai yi yunkurin yi mata wani abu ba yasa ta fara kokarin tura hannunta cikin Bathrobe din dake a jikinshi don tasan takan yadda zata ida kashe mashi jikinshi,aikuwa a zafafe ya finciko ta,ya ware faffaɗan tafin hannunshi da ƙarfin gaske ya kifa mata mari zazzafan gaske gami da hankadata ta daki dressing mirrorn,agigice hayamm ta fasa wata irin razananniyar ƙara,wani irin jiri ne ya ɗebe ta,nan take ta yanke jiki ta faɗi ƙasa tana birgima,taji ƙamshin mutuwa wlh,ihu ta shiga saki tana fadin Wayyo Allanta,

Adai dai lokacin Sehrish ta shigo part dinshi hannunta ɗauke da tray,na breakfast dinshi data kawo mashi,ganin bashi a parlourn yasa ta nufi bedroom din bakinta dauke da sallama, tana sanya ƙafarta acikin bedroom ɗin,ta jiyo sautin wannan ƙarar da hayaam ta saki,a firgice ta saki tray ɗin hannunta ya faɗi ƙasa kayan abincin suka tarwatse ƙasa,hankali a matuƙar tashe take kallonsu,sautin faɗuwar tray ɗin hannunta ne yasa sgr juyowa karaf idanunshi suka shiga cikin na sehrish,zuba mashi ido tayi tana kallonshi yayin da shima yake kallonta sae faman huci yake yi yarda kasan mayunwacin zaki,da ace sehrish bata faɗo ɗakin nan ba,da ba ƙaramin illata Hayaam zaiyi ba,so yayi ya nakasata,yarda bazata ƙara yin gigin takowa tazo bedroom ɗinshi balle har tayi yunƙuri ta6a wani sashe na jikinshi ba,

atsorace sehrish ta mayar da idanunta kan Hayaam dake a baje ƙasa,magashiyyan sae faman Birgima takeyi har lokacin bata dawo cikin hayyacinta ba,wato taji tafin hannun maza,dama zafin hannu gare shi,shiyasa bai cika son yakai bugu ba,saboda za’a iya samun matsala,da mari kaɗae zai iya sumar da mutun,

A zafafe Sgr ya juya ya tunkari hayaam dake baje kasa,da alama yau fa hayaam sai dai

buzun ta,ganin hakan yasa hayaam da kyar ta rinka jan jiki tana ja baya gami da yi masa magiyar yayi hkr kar ya kasheta hannunta guda dafe da kuncin,gaba daya sautin jin kunanta ya ɗauke ɗuff ta 6arin da daya mare ta,cikin husky voice yace”who the hell are u? da sauri cikin shesshekar kuka la66anta na kerma tace”ni…ni..ƙanwarku ce….au ƙanwar matar yayyen kuce ishaq da abbas” tsayawa Sgr yayi lokaci guda ya gane itace yarinyar da tazo rannan har aka faɗa masa”to waye ya shigo da ita gidan? Ya jefa ma kansa tambaya,

 

Ganin abunda ke faruwa yasa Sehrish ja da baya zata watsa aguje saboda tsoran kar itama laifin da hayaam ta aikata ya shafe ta,

da wata irin murya taji yace”ke!zonan,”

Jiki na rawa sehrish ta shigo cikin ɗakin nashi,sae faman kerma take yi kamar yace zai buge ta,

ƙarasawa kusa dashi tayi tana faman zazzare idanu hankali atashe take kallonshi,tana jiran jin me zaice mata,

daidaita natsuwarshi yayi tare da sassauto da muryarshi calmly yace”ya jikin naki!’?

Tsananin mamaki ne ya kama sehrish,jin abunda yace mata,kuma da irin muryar da yayi mata maganar,hakan yasa taji hankalinta ya kwanta,

muryarta na rawa tace”naji sauƙi sosai,yanzu bana jin ciwo atare dani,”

https://aihausanovels.com.ng/sirrin-rike-miji/gyaran-nono-gare-ku-yan-mata-masu-kananan-nonuwa-ga-yadda-zaku-yi/

Jinjina kanshi yayi kafin ya kuma cewa”Okey,Allah ya ƙara lfy,’

“Ameen,”ta amsa mashi,

shiru suka ɗanyi na wani lokaci,kafin ya mayar da idonshi kan hayaam dake ta faman yi mashi tsuwa acikin dakinshi duk ta cika masu kunnuwansu,

A fusace yace”get out from my bedroom!’

Jiki na rawa hayaam ta miƙe da gudu zata fuce a tsawace sgr ya tsaidata ta hanyar cewa” hey! juyowa tayi har lokacin hannunta na akan kumatunta ya cigaba da cewa “make sure u pack all ur shit and leave this house! A kausashe yayi maganar, idasa fucewa daga cikin ɗakin tayi tana cigaba da shar6ar kukan nata,

 

Lumshe idanunshi yayi tare da buɗesu akan fuskar sehrish da tai tsuru² jin ance hayaam ta tattara kayanta ta bar gidan, yace”yanzu ya za’ae da breakfast ɗina da kika zubar mun a ƙasa?

cikin sauri tace”bari naje na haɗo maka wani” juyawa tayi da niyyar ta tafi,kwatsam taji ya ruƙo hannunta acikin nashi,a ɗan tsorace ta juyo tana kallonshi,gabanta ne taji yana faɗuwa ganin yarda Sgr yake kallonta,nan fa ta shiga taitayinta,

“Meyasa jiya,baki dawo gida ba?ko saboda na datse maki gashin kanki ne”?

Girgiza kai sehrish tashiga yi tana cewa”a’a ba haka bane,bani da lafiya ne,bacci ya ɗauke ni a school bansamu wanda ya tashe ni ba lokacin da aka tashi har junaid yazo dauka na bai ganni ba,shiyasa bansamu nadawo gida ba,’

Kallon bakinta dake bayanin kawae yake har ta gama,a hankali ya furta Okey,sannan ya saki hannunta daga ruƙon da yayi mashi,

juyawa tayi da sauri ta ƙarasa bakin kopar dakin nashi,zukunnawa tayi ta kwashe kayan abincin data zubar mashi aƙasa,duka ta tattara su acikin tray din,sannan ta fuce daga ɗakin nashi,

Gaba daya ta rasa natsuwarta,wani irin yanayi ta dinga ji atare da ita,kallon nan da yake yi mata ba ƙaramin kashe mata jiki yakeyi ba,kamar wadda aka cire ma lakar jikinta haka ta dinga jin kasala,

 

A kitchen ta samu azmee tana wanke kayan abincin da sukayi amfani dashi na breakfast,

Ganin ta ɗauke da tray a hannunta yasa azmee cewa”Har ya kammala yin breakfast ɗinne”?

girgiza kai tayi alamar a’a tace”matsala aka samu,ni ce na 6arar da kayan abincin,shine yace na sake kawo mashi wani,’

Azmee tace”wasa wasa sehrish kema kin iya shiririta wlh,kina sake da baki har kika zubar mashi da kayan abincin ko?

“Ae bada sanina,hakan ya faru ba,”ta yi maganar yayin da take ƙarasawa cikin kitchen ɗin,

“Shikenan bari na sake haɗa maki wani breakfast din ki kai mashi,Amma kada ki jima a part din nashi fa,da zarar na kammala gyara kitchen din,zanyi maki ƙunshin,ko baki so ne’?

“Inaso mana,”tayi maganar fuskarta ɗauke da murmushi,

Batare da 6ata lokaci ba,Azmee ta kammala shirya mata wani kayan abincin acikin tray,ta bata takai mashi,sae da ta ja mata kunne akan karta kuskura ta ƙara zubarwa,’

fitowa daga cikin kitchen din sehrish tayi,fuskar nan ɗauke da annuri,wani irin daɗi takeji aranta,kamar anyi mata albishir da gidan aljana,

A hankali take taka stairs din,yayin da Zuciyarta ke tariyo mata abunda ya faru aɗakin sgr,batasan meya faru tsakaninshi da hayaam ba,da har ya kwashe ta da mari,amma koma meye dae tana da tabbacin cewa wani abu tayi mashi ba dae dae ba,

Ta6e baki tayi tana cewa”to ni ina ruwana?meye damuwata da ita?koma meye ita taja ma kanta,nasan cewa babban yaya bazai ta6a ɗaga hannu ya mari mace ba hakanan batare da wani dalilin ba,na yarda dashi sosai,kuma baiyi mun kama da irin mazan dake dukan mace ba,Yau dae hayaam take kowa ma,tasha mari wlh ko a ha6ar zani na,ba ƙaramin daɗi naji ba wlh,babban yaya ya burgeni sosai daya kwashe ta da mari,gobe ma in halinta ne ta ƙara yi mun shisshigi a aikina,angaya mata cewa sauƙi ne kula da babban yaya?nikaina kullum cikin fargabar kada nayi mashi kuskure nake,shiyasa nake lalla6ashi kamar kwai acikin cokali,Allah sarki yau hajia hayaam taji tafin hannun babban yaya koya raɗaɗin yake?tabb dole ma akwae mugun radadi tunda ta kasa cire hannu daga kan kuncinta, gwara ni Almakashi yasa ya datse mun gashin kaina,nan da wani lokaci gashin zai fito,ita kuwa marinta fa yayi? nasan har abada bazata manta da wannan ranar ba,

ashema hakanan take ma mutane kankanba ko sanin wacece ita bai yi ba”

 

Dariya sosai sehrish takeyi kamar wata zautacciya,sae faman sambatu takeyi,da alama taji daɗin Marin da Sgr yayi ma Hayaam,abun ko ajikinta,

Lokacin da ta shiga part ɗin Sgr,a kishingiɗe ta same shi saman doguwar kujera,ya miƙe kafafunshi,bai kaiga shiryawa ba,Vest ce kawai ajikinshi sae shorts farare,

Karasawa ciki tayi tare da ajiye mashi tray din asaman table,sannan tace”ga wani breakfast ɗin na kawo maka,”

sauko da ƙafafunshi yayi ƙasa ya miƙe daga zaune,ya jingina bayanshi a jikin sofan yana jira tayi serving ɗinshi,

Sehrish ta jima awurin sgr tana mashi ɗawainiya har sai da ya kammala yin break fast din nashi,sannan ta koma ta gyara bedroom ɗinshi,bayan ta gama ta dawo ta gyara falon sannan ta ɗauko kayan abincin da yayi amfani dasu,ta wuce dasu kitchen,sae da ta wanke komai ta mayar dashi a ma’ajiyar shi,sannan ta wuce ɗakin azmee don suyi maganar zanen lallen da zatayi mata,

 

Wuraren ƙarfe biyu na rana,Junaid ya kar6o mata kayanta,akwati guda ne na atampha da lace,da kuma shadda,hada materials,duk an ɗinka mata su,

acikin bedroom ɗinta ya ajiye mata akwatin kayan,

sae da suka kammala sallar azhar,tukunna suka zauna zaman yin ƙunshi,anan corridor din ɗakunan nasu azmee tayi masu shimfiɗa suka zauna sama,tunda suka fara ƙunshin junaid keta zarya awurin sae faman santin kunshin sehrish yake yi,tun kafin a wanke mata ƙunshin ma,cikin nishaɗi suke yin firar su,tana yi mata ƙunshin suna fira tare da junaid,don ya kasa ya tsare sae anyi tare dashi,

 

A6angaren Hayaam kuwa tunda ta faɗa cikin bedroom ɗinta saman gado,take ta faman shessheƙar kuka,fuskarta tayi jawur saboda kukan da tasha,gefen fuskarta dauke da sahun yatsun sgr ruɗu ruɗu sun fito wurin ya kumbura sosai gashi kunnanta daya dumm take jin shi,tunda take arayuwarta wani ɗa namiji bai ta6a gigin ta6a lafiyar jikinta ba,sae akan Sgr ta fara shan mari,ta jima tana mamakin yarda ya ɗaga hannu ya kwasa mata mari,duk irin yarda ta ɗau wanka,ta bayyana surar jikinta don taja hankalinshi amma hakan baiyi tasiri akanshi ba,kwallin data shafa kuma ya tashi abanza saboda bai kalli cikin idonta ba bare asirin ya kamashi,

ɗagowa tayi daƙyar take iya buɗe idanunta,wayarta ta ɗauko dake ajiye saman side drawer na gadonta,layin Aunty babba ta kira,wayar ta shiga ringing,

Cikin sa’a ta ɗaga kiran,Aunty babba nayin sallama,hayaam ta 6are baki ta fashe da wani sabon kukan,

Tunda Aunty laila taji kukan hayaam hankalinta yayi mugun tashi,daga zaune take saman kujera amma tana jin kukan hayaam ta miƙe tsaye tana tambayar lafiya!

Cikin shessheƙar kuka hayaam tace”Aunty lailai,yau Sgr ya gama dani,ya wulakantani kuma ya tozarta ni,yayi mun abunda wani ɗa namiji bai ta6a yi mun ba!’

Hankali tashe Aunty babba tace”Me yayi maki ne!kiyi mun bayani yarda zangane,kuma kidaina wannan kukan da kikeyi,”

dakatawa da yin kukan hayaam tayi sannan taci gaba da magana tana cewa”Mari na fa yayi,banyi mashi komai ba ya ɗaga hannu ya kwasa mun mari agaban waccen ƙaskantacciyar yarinyar ya mare ni….’

Tunkan ta ƙarasa maganar Aunty babba tace”Ƙarya kike hayaam!Sgr bazai ta6a marinki ba batare da kinyi mashi laifi ba!dole akwai dalilin dabyasa ya mare ki,don nasan halinki baki da hankali,kuma baki da kamun kai,halan ƙoƙarin kai mashi hari kikayi saboda gajen hkr!!”

Cikin en ena hayaam tace”nifa banyi mashi komai ba,kawai da safe ne nashiga ɗakin shi lokacin ya fito daga wanka,nayi ƙoƙarin jan hankalinshi ne da surar jikina,amma ko kallo ban ishe shi ba,shine nayi hugging nasa nayi ƙoƙarin ta6a short ɗin jikinshi don in tayar mashi da sha’awar shi,amma shine kawai ya kwashe ni da wani mahaukacin mari…..’

dafe kai Aunty babba tayi tana cewa”ka ji tsiyar!wlh kin ban kunya hayaam!bansan ke wata irin mace bace!sam baki da kamun kai,idan jarabarki ta motsa, me yasa bazaki iya control din kanki bane agabanshi!wannan mutumin fa da kaina nayi maki alƙwarin cewa mijinki ne shi,idan kikayi haƙuri nan da ɗan wani lokaci zaki mallake shi duka,sae kiyi yarda kika ga dama dashi,amma tun yanzu saboda gajan haƙuri irin naki kin gaza jurewa,kina ƙokarin lalata mun shiri na!bazaki ta6a burge Sgr ba,saboda shi irin mazan nan ne da basa ra’ayin mace mara kamun kai ballagaza,wadda bata iya 6oye zalamarta akansu……’

 

Ɗaure fuska hayaam tayi jin yarda Aunty babba ke ta zaginta a fakaice,

Rai a6ace tace”Aunty laila nifa ban kiraki don kici mun mutunci ba,sae faman gaya mun magana kikeyi ta inda kike shiga bata nan kike fita ba,ni da na kawo maki kukana maimakon ki share mun hawaye na,Amma shine kike ta zazzaga mun masifa!wannan abun fa ba laifina bane,ko kece kika ganshi a yanayin dana same shi dole ki kai mashi attack balle ni da nake budurwa……..’

Waro ido waje Aunty babba tayi rae a6ace tace”Hayaam don ubanki ni kike gayama wannan maganar!ashe ke daƙiƙiyace baki da hankali!an gaya maki ko wace mace irin ki ce mara aji da zata dinga kai kanta wurin namiji har tana ƙokarin ta6a jikinshi!ni tunda nake arayuwata ban ta6a kusantar mijin da banawa ba,duk irin mugun halin da nake dashi kuwa,a iya miji na natsaya ban zarce nan ba!amma ke fa?kullum kina yawon biɗiɗi wurin raba jikinki ga kowane ƙazamin namiji yayi amfani dake,don ki samu kuɗi,ki faɗamun wace riba kika ta6a samu a yawon barikancin naki!acikin mazan da kikayi mu’amala dasu akwai shegen daya ta6a cewa zai aure ki ne!!saboda baki da wani amfani awurinsu,tamkar totuwar masara kike da zarar sun cinye masarar jikinshi ya gama amfani sae su jefar dashi ƙasa,ni kuwa kinga ina da daraja tunda ina da aure kuma a ƙarkashin kulawar mijina nake,shiyake amfani dani kuma shi yake bani kuɗin da zanyi abunda nake so,riba biyu ga kuma lada ina samu……’

Wani irin huci hayaam ta shiga fitarwa saboda tsabar 6acin ran kalaman da Aunty babba ta gaggaya mata,

Muryarta har shaƙewa takeyi wurin cewa”Aunty Laila!!ni kike faɗama waɗannan munanan kalaman!yau da kanki kike yi mun gori?Ya salam!wlh bazan ƙyale ki ba,kamar yarda kikayi mun gorin aure,nima zan raba auran ki Da Ishaq,ki dawo bazawara,”

fashewa da dariya Aunty babba tayi tana girgiza kai kafin tace”ni zan aje waya,kada ki manta kisha maganinki na rana,don da alama kin manta jawabin da  likitan mahaukatan nan  yayi maki,akan kula da shan magungunan ki akai akai,”ta ƙarasa maganar tare da kashe wayar,

Wani irin ihu hayaam ta zabga tare da aza hannunta saman kanta,tana fadin innalillahi wa’inna ilaihirraji’un….”

 

Zafi biyu,gana marin da Sgr yayi mata ga kuma na zafafan kalaman da Aunty babba ta gaggaya mata,zuciyarta tamkar ana rura mata garwashin wuta haka ta dinga ji,wani irin zazza6i ne ya lullu6eta,nan ta baje saman gadon tana ta faman birgima a ranta tana cin alwashin ba zata bar gidan ba har sai taga bayan Sehrish don ita taja mata duk wadannan abubuwan da suka faru da ita.

Back to top button