Hausa novels

Abban Sojoji Book 3 Takun Karshe Chapter 76 Complete Novel

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*jiki

Sai faman safa da marwa takeyi acikin bedroom ɗinta,gaba ɗaya ta rasa samun natsuwa,hakanan ta dinga jin fargabar zuwa abuja,ga zumuɗin zuwan da takeyi amma kuma tana zullumin abunda zai biyo baya,hakanan ta dinga jin kamar wani abu mara daɗi zai faru,ƙafafunta har sun fara ciwo saboda zaryar da take ta faman yi,tun bayan da ta kammala sallar asuba bata koma bacci ba,Jikinta na sanye da Zumbuleliyar riga doguwa brown,sae guntun hijabin da ta kammala sallah dashi,hannunta na ruƙe da wayarta,wani tunani ne ya fado mata aranta,cikin sauri ta shiga danna wayar dake hannunta,Hayaam ta buga ma waya,nan take kiran ya shiga,batare da 6ata lokaci ba hayaam ta ɗaga kiran,daƙyar take magana saboda ta katse mata baccinta,rai a6ace tace”Lafiya kika kira Ni?bayan kin gama kwashe mun albarka”!
Cikin lallami Aunty babba tace”Dan Allah hayaam komai ya wuce kinji ƙanwata?nasan ban kyauta ba,amma kiyi haƙuri,”
Tsoki hayaam taja tare da cewa”hmmm,halan yanzu kin gasgata maganata ne?shiyasa kika kira don jin ƙarin bayani?
Aunty babba tace”EH,hakane,na yadda da abunda kika faɗamun,tuntuni shiyasa ma na kira ki,”
Hayaam tace”Yanzu ya kenan?ya zamuyi?don gaskiya akwai matsala aunty laila,burin mu bazai ta6a cika ba,muddin yaran nan suna nan!”
Jinjina kai Aunty babba tayi tana cewa”babban takaicina yaran da suka kasance mata ne!har ƴan uku,gaskiya abusufyan bai kyauta mana ba tsakani da Allah,haka ake?kawai sai yaje yayi aure a 6oye batare da sanin kowa ba?wai kuma da sanin ammi kuwa”?
Hayamm tace”Anya,gaskiya ina tunanin Ammi bata sani ba,’
Jin haka yasa Aunty babba cewa”Allah yasa in tazo tace bata amince da yaran ba,kinsanta Jarababbiyace,musamman ma da yayi auren bada saninta ba,Wai shin su yaran ina mahaifiyarsu take ne?tana da asali kuwa”?tayi tambayar cike da son jin ƙarin bayani,
Hayamm tace”Ina fa,ae rannan na tambayi azmee game da mahaifiyarsu,shine take sanar dani cewa mahaifiyar yaran Ƴar fa mai gadin gidan gwaggon katsina ne!basu da wani asali,buzaye ne ƴan niger,”
Aunty babba tace”tabɗijancan aikuwa Ammi bazata ta6a yarda dasu ba,kinsanta ta tsani mutun mara asali,gata ita kaifi ɗaya ce muddin tace bata yarda dasu ba amatsayin ƴa’ƴan Abusufyan to fa korasu zatayi daga gidan,yakamata muyi wani abu akai,tun kafin takai ga zuwa,”
Hayaam tace”meke nan zamuyi?kinsan fa gobene walimar kuma gobe zata zo,”
“Abunda zamuyi shine,Ae ina da numbar Ammin a wayata,zanyi amfani da sabon sim ɗina,wanda ban fara amfani dashi ba,zan kirata na sanar da ita game dasu tunkan taji a wurin wani,”acewar Aunty babba
dariya hayaam tayi tare da cewa”Gaskiya aunty laila kin iya haɗa tuggu,ni sam banyi tunanin hakan ba,wannan ce hanyar da zamu bi wurin tarwatsasu,idan kika kirata awayar ki tunzurata sosai,ki ɗaurata akan network har sai ta amince da kalamanki,ki sanar da ita cewa yaran shaggu ne,abusufyan yayi ma mahaifiyarsu ciki a 6oye,shine suka so su 6oye mata,don karta sani,”
Murmushi Aunty babba ta saki tana cewa”hakan yayi sosai,zan tsara komai yanzu………”tana cikin maganar taji alamar dirar motar ishaq,
Cikin sauri tace”Hayaam inaso ki ɗauko min hoton yaran kafin muzo gobe,zan kashe wayar yanzu ishaq ya dawo,
“Toh aunty laila,zanyi ƙoƙarin ɗauko maki hoton nasu,”

Daga haka sukayi sallama da juna,
Ajiyar zuciya aunty babba ta sauke,har taji wani sanyi a ranta saboda ta samu mafita,

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

Bayan sun kammala wayar hayaam ta buɗe ƙopar ɗakinta tare da fitowa,cikin sanɗa hayam take tafiya don kar wani ya ganta,a haka har ta ƙarasa bedroom ɗinsu sehrish,tura ƙopar tayi cikin sa’a ta samu ƙopar ɗakin a buɗe,leƙa kanta ta fara yi anan ta same su,suna ta sharar bacci wanda tun bayan sallar Asuba da suka tashi suka koma suna yin baccin,

Murmushi ta saki tare da sa kai ta shige ciki,adai dai bakin gadon nasu ta tsaya tare da ɗago da wayarta dama already a cikin camera take,Saita fuskarsu tayi dama kuma duk suna facing ɗin ceilling,kyakkyawan hoton fuskokinsu ta ɗauka,bayan ta kammala ɗaukar hoton,ta lalla6a batare da kowa ya ganta ba,ta koma bedroom ɗinta,cikin sauri ta tura ma Aunty babba hoton ta whatsapp ɗinta,

❤🤍❤

Wuraren karfe takwas,suka farka daga bacci,sehrish ce ta fara shiga toilet tayi wanka,bayan ta fito daga wankan jahad ta shiga ciki,gaban dressing mirror ta zauna ta gama shafe jikinta,ta feshe shi da turare,sannan ta koma ta ɗauko Jallabiya fara ta zura ajikinta,ba ƙaramin kyau tayi mata ba,musamman adon dake jikin rigar na stones,shiya ƙara ƙawata rigar,bayan tayi rolling kanta da mayafin rigar,ta fito daga cikin bedroom ɗin nasu ta wuce kitchen,cike da zumuɗin kaima babban yaya breakfast ɗinshi gaba ɗaya ta manta da abunda Uncle abusufyan ya faɗa mata,

A kitchen ta samu azmee,har ta kusa kammala girkin,ganin yadda take ta aiki ita kaɗae yasa sehrish taji duk ba daɗi,muryarta a sanyaye tace”Ina kwana Aunty azmee,”
Juyowa tayi daga tsayen da take gaban gas cooker,fuskar nan ɗauke da murmushi tace”Lafiya lou ƴan matan abusufyan,fatan kun tashi lafiya”
“Lafiya lou,amma aunty azmee gaskiya banajin daɗi in naga kina aiki ke kaɗae,meyasa baki tashe mu ba,munzo mun tayaki aikin”?tayi maganar yayin da take ƙarasa shiga cikin kitchen ɗin,
Azmee tace”kada ki damu,na riga na saba da aiki,wannan ba wani abu bane,Abba ma ya nemi daya ƙaro masu aiki amma nace mashi ya barshi kawai,saboda na saba da yin aiki ni kadae,”
Girgiza kai sehrish tayi tare da cewa”that’s impossible,gaskiya in har ba zaki amince a ƙaro masu aiki ba,to daga yau Ni dasu jahad zamu dinga tayaki aiki,don bazaiyiwu ba kiyi ta wahala ke kaɗai,”
murmushi kawai azmee tayi batare da tace Komai ba,
“Aunty azmee idan akwai abunda kika kammala inaso zan fara kaiwa dining in jera,kinga na rage maki wani aikin,”
“Ban kaiga shiryasu ba,amma sai dai idan zaki kaima Sgr nashi,sae na haɗa maki,ki kai mashi,”
Murmushi ta saki tare da cewa”Toh,”

Download>>> Bintu Diyar Bayi Ce Book 1 Complete Document

Shirya mata breakfast azmee tayi acikin ƙayataccen tray,bayan ta kammala,sehrish ta ɗauki tray ɗin tare da fucewa daga kitchen ɗin,

tana cikin tafiya harta kusa hayewa upstairs taji anyi mata gyaran murya abayanta,cikin sauri ta juya don taga Wanene,ganin Uncle abusufyan yasa gabanta faɗuwa,saboda tana kallonshi ta tunano da abunda ya faɗa mata a daren jiya,

Muryarta na rawa ta furta”Daddy,”ƙarasawa yayi wurinta tare da tsayawa dab da ita fuskarshi a ɗaure yace”Me na faɗa maki jiya?tun yanzu zaki fara sa6amun”?
Hankali tashe sehrish tace”a’a daddy,wlh mantawa nayi,bazan ƙara ba,dan Allah kayi haƙuri,”
“Zo ki wuce ki mayar da kayan abincin kitchen,inyaso azmee taje takai masa,”
Jiki asanyaye Sehrish ta juya tare da kama hanyar komawa kitchen,duk wannan abun daya faru akan idon,Mommynsu junaid alexandra,tana tsaye abakin part ɗinsu na downstairs tana kallonsu,

Haka ta koma kitchen da kayan abincin idonta cike tab da hawaye,taci burin ta ganshi yau,amma Uncle abusufyan yayi mata tsiya,
Tamkar wadda aka zarewa laka haka ta shiga kitchen ɗin,Azmee na ganinta dauke da tray a hannu tace”Lafiya naga kin dawo da kayan abincin”?tuni hawaye sun wanke mata fuskarta,muryarta tamkar zatayi kuka tace”Uncle ne ya hanani zuwa part dinsa da sunan aiki,tun jiya da daddare ya gargaɗeni akan Karna kuskura na ƙara yin aiki a ƙarkashinsa,bansan meyasa ya hanani ba,”
Cike da mamaki azmee tace”to fa!ko meyasa yayi hakan?kuma kin tabbata bakiyi wani laifin ba wanda yajawo har ya hanaki aiki a part ɗinsa”?
“Aunty azmee ni banyi laifin komai ba,”ta ƙarasa maganar a yayin da take ajiye tray ɗin hannunta,
Shiru azmee tayi aranta tana mai mamakin hukuncin da Abusufyan ya yanke ma sehrish,to kodai don saboda basa shiri da Alexandra ne?tabbas zai iya yiyuwa hakane!tunda akwai gaba atsakaninsu,dole kuwa ya hana Sehrish tayi ma Sgr aiki,don bazai ta6a yarda ƴarsa tazama baiwarsa ba,
“Aunty azmee ko zaki iya nema mun alfarma a wurinsa yabarni in cigaba da aiki acikin gidan nan kamar yadda na saba,”muryar Sehrish ce ta katse mata tunaninta,
zaro ido azmee tayi tare da cewa”Ni ƴar ubanwa?na isa in shiga tsakaninki da mahaifinki?bazaiyiwu ba sehrish,shawarar da zan baki shine kawai ki bi Umarnin mahaifinki ki xauna lafiya,Shi kaɗae yasan dalilinshi na yin hakan,kuma in har kika yi mashi biyayya zakiga ribar yin hakan,”
ɗakyar ta iya haɗiye yawun bakinta,ga hawaye sae faman zarya sukeyi a fuskarta,
“Wannan hukuncin da mahaifinki ya yanke,yayi mun dai dai,don koda bai dakatar dake daga yi mashi aiki ba,to ni dakaina zan hanaki!”
Gaban Sehrish ne ya faɗi rass jin muryar Mommynsu junaid abayanta,Azmee kuwa na ganinta tasha jinin jikinta don tasanta sarai bata da mutunci ta wani 6angaren,
Juyawa sehrish tayi da sauri tana kallonta,
A hankali take tunkararsu yayin da take ci gaba da magana”Banason kusancinki dashi ko kaɗan!just maintain a good distance between u and him,In ba haka ba,You will see the trouble!!”Jikin sehrish har kerma yake yi don ba ƙaramin tsoranta takeyi ba,koƙarin 6oyewa a bayan Azmee takeyi,don gani take tamkar Alexandra zata bugeta ne,
Koda ta ƙaraso dab dasu,harara ta wurga ma azmee tare da cewa”Matsa daga gabana,da ita nakeson magana,”jiki na rawa azmee ta janye jikinta gefe guda,aranta tace”tashin hankali ashe har yanzu matar nan,bata canza ba,lallai akwai matsala,”
goya hannayenta tayi asaman ƙirjinta,yayin da suke fuskantar juna ita da Sehrish,saboda tsabar tsoro ƙiris ya rage sehrish ta saki fitsari,ko idonta bata iya dagawa ta kalleta saboda yadda tayi mata tsaye aka,
Wani irin kallo Alexandra ke bin Sehrish dashi,tun daga ƙasa har sama,yatsina fuska tayi tare da cewa”Ur name”?
Murya na kerma tace”Sehrish,”
Jinjina kai alexandra tayi tare da cewa”saboda daddynki ya hanaki aiki a part ɗin rafayet shine kike kuka?why?
..girgiza kai sehrish tashiga yi tana cewa”a’a..ba saboda haka nake kuka ba….”
“Kukan menene toh”?ta sake jefa mata tambaya a karo na biyu,
“Babu komai,”ta bata amsa tana faman zazzare idanu,
Murmushin gefen fuska alexandra ta saki kafin ta kuma cewa”dama ana kuka ne just without any reason?ki faɗamun gaskiya mana,kodai kin faɗa tarkon shi ne”?

Download>>> Bintu Diyar Bayi Ce Book 2 Complete Document

Waro ido waje Sehrish tayi hankali tashe tace”a’a ba haka bane,kawai ina kuka ne saboda tsoron hukuncin da babban yaya zai yanke mun in ya gane cewa na daina yi masa aiki,”
Ta6e baki alex tayi tare da cewa”Just calm down ur mind,Bama zai ta6a damuwa akan hakan ba,kiyi ma mahaifinki biyayya,kuma ki nisanta kanki dashi kamar yadda nace,hakan zaifi maki kwanciyar hankali,”tana kai ƙarshen maganarta,ta juya cike da isa tare da fucewa daga kitchen ɗin,

Fitarta keda wuya Azmee ta mayar da idonta kan sehrish saboda ta lallashe ta,amma ina,tuni sehrish ta watsa da gudu tabar kitchen ɗin,

A bakin ƙopar dakinsu ta tsaya tana faman shessheƙar kuka,zuciyarta har wani tafarfasa takeyi mata,dole tayi kuka saboda tasan cewa ta rasa Sgr na har abada,tunda mahaifiyarshi ta nuna bata sonta,zuƙunnawa tayi a ƙopar ɗakin tana cigaba da kukan nata,ta jima zuƙunne a wurin cikin wani irin yanayi mara daɗin ji,tana jiyo muryarsu jahad acikin bedroom ɗin,suna tattaunawa kan wankan da zasu ɗauka gobe ranar walima,hada zancen saloon ɗin da daddynsu yace zai kaisu ayau,
gaba ɗaya taji komai ya fita ranta,don har wani zazza6i taji ya saukar mata ajikinta,ita kaɗae tasan raɗaɗin da takeji acikin zuciyarta,hannu tasa tare da share hawayenta sosai don karsu hosana su gane cewa tayi kuka,bayan ta kammala goge hawayen ta miƙe,tare da buɗe ƙopar ɗakin tashiga ciki,
Jahad na zaune gaban mirror tana shafa powder a fuskarta,hosana kuma na tsaye gaban wardrobe tana cewa”Nama rasa wani kaya zansa yau,saboda inaso in na kammala shiryawa inje in tashi Ya Omar daga bacci don nasan cewa bai kaiga tashi daga bacci ba,”ta ƙarasa maganar tare da ɗan juyawa ta kalli jahad tace”daddy yace yau zai kaimu Saloon ko?to da yaushe zamu fita?donni hada ƙunshi za’ayimun a hannuna,yanzu ma in naje ɗakin ya Omar zan tambayeshi wani kalar ƙunshi yakeso ayimun baƙi ko ja,” jahad tace”Soyayya daɗi,kunshin ma sai an tambayi ya omar wani kala yakeso kenan?to gyaran gashin fa?shi bazaki tambayeshi wani kala yakeso ba?
murmushi hosana tasaki tare da cewa”dole ma in tambayeshi wani kalar gyaran gashi yakeso ayi mun,”_
Suna cikin magana muryar Sehrish ta katse su da cewa”Ƴan uwana rabin raina,me kuke tattaunawa akai ne?naji kamar ana gulmar ƴa omar,ko kunnena ne,’tayi maganar tana ƙoƙarin danne damuwarta,gefen gadon ta samu ta zauna,tana faman sauke ajiyar zuciya,
.juyowa sukayi suna kallonta,hosana tace”Sehrish ina kika je,na tashi ban ganki ba,har naji tsoran kada ace wannan halittarce mai ƴan idanu ta ɗauke mana ke”
Dariya sehrish tayi tare da cewa”ni harna manta da wannan abun,koda na tashi daga bacci ban iya tuna abunda ya faru jiya ba,sae naji kamar duk a mafarki ne,”
Hosana tace”Ae taji tsoro ta gudu,yau da daddare in tadawo,zan aro bindigar yaya Omar in harba mata bullet acikin idanunta,”atare suka fashe da dariya jin abinda hosana tace,hada kwatantawa da hannunta yadda zatayi shooting din guguwar,
Jahad tace”Cika baki kawai,kin manta kukan da ki kayi mana ajiya?kinfi kowa tsorata,ba don nayi maki addu’ar ɗaukewar fitsari ba,da ba’asan me zai biyo baya ba….’dakyar ta ƙarasa maganar saboda dariyar da tazo mata,
cike da nishaɗi suke yin firar tasu,kafin lokacin yin breakfast yayi atare suka fita,Hosana ta wuce part ɗin Omar,yayin da su kuma suka wuce dining,Sehrish dae jurewa kawai takeyi,suk ta gaza sakewa saboda rashin sanya sgr a idanunta,gashi bai sauko downstairs ba,saboda Azmee takai mashi nashi a part ɗinsu,kuma sam bai tambayeta akan Sehrish ba,Hakan na nufin cewa Sgr bai damu da ita ba ko kaɗan,dama haroon yace Iskace ke wahalar da mai kayan kara,

Yana kwance yana sharar bacci,hosana ta shiga bedroom ɗin nashi,lalla6awa tayi ta haye saman gadon har wurinshi ta ƙarasa,saitin fuskarshi tana kallon zunzurutun kyawunsa,

Hura mashi iska tayi a fuskarshi,nan take ya ɗan motsa tare da yatsina fuskarshi,murmushi hosana ta saki tare da kai hannu ta toshe mashi hancin shi,aikuwa a gigice ya farka batare da ya sani ba ya tattara dukkanin ƙarfinshi ya cakumi hosana tare da yin wurgi da ita,gaba daya ta tafi yaraf ta kife ƙasan tiles ɗin daga gefen gadon,nan take ta fashe da kuka saboda hancinta daya daki ƙasa,shi duk atunaninshi wani ne ya kawo mashi hari shiyasa yayi mata haka,kuma yana yin wurgin da ita,yaci gaba da baccinsa,dama duk a cikin magagin bacci ne yayi mata hakan,

Cikin baccinshi ya jiyo sautin kukanta tana cewa”Wayyo Allah,hanci na ya fashe,ya Omar ka kashe ni,”

A firgice ya ware idanunshi tare da miƙewa daga zaune yakai idanunshi wurin da sautin kukan ke fita,anan ya samu hosana dafe da hancinta a zaune dirshan tana kuka,

Hankali atashe ya sauko daga saman gadon ya zukunna agabanta yana tambayarta lafiya?garin yaya taji ciwo a hancinta,

Cikin shessheƙar kuka tace”bakaine ka cakume ni ba,kayi wurgi dani daga saman gado na faɗo ƙasa har hancina ya bugu,”

Waro ido waje yayi tare da cewa”Ni kuma dakaina”?
Jinjina kanta tayi tare da cewa”Eh mana,saboda kawai na toshe maka hanci,

Hannu yasa tare da tallabo fuskarta yace”Hosana bada sani na nayi maki hakan ba,laifin ki ne,meyasa zaki toshe mun hancina?so kike na mutu’?
Girgiza kai tayi”a’a,banso ka mutu,ae ni wasa nayi maka ko,”tayi maganar tana satar kallon fuskarshi,
“Faɗa mun me ya kawoki bedroom ɗina har saman gadona”?
A ƙule tace”nifa nazo ne na tashe ka don kaje ka ci abinci,naga kowa ya fito banda kai,kuma zasu iya cinye abincin duka,”
fuskarshi ɗauke da murmushi yace”Waya faɗa maki za’a cinye abincin,ae ko ban fita ba Azmee zata kawo mun ne har cikin part ɗina,”
Shiru tayi tana faman sauke ajiyar zuciya,ɗagowa ta ƙara yi zata saci kallonshi suka haɗa ido,ganin yadda yake kallonta ko ƙyaftawa baiyi hakan yasa ta ɗaure fuska cikin shagwa6a tace”Ya omar wannan kallon fa,ka wani tsare ni da ido,”
yadda tayi maganar ba ƙaramin burgeshi tayi ba,ya jima yana kallonta batare da yace wani abu ba,har sai da ta hasala rai a6ace tace”shikenan tunda ba zaka mun magana ba,bari na tashi na tafi,dama ko abincina banci ba,saboda kawai inzo in tashe ka daga bacci,amma ko farin ciki ba kayi ba,’
Ajiyar zuciya ya sauke tare da ruƙo hannunta cikin nashi”Hosana,so nake ki faɗa mun gaskiya,kina sona da gaske?kuma zaki aure ni? Waro ido waje hosana tayi tana kyakkyaftasu kamar na ƴar tsana jin abunda yace,a ruɗe tace”Ya Omar!aure fa!”_
Jinjina mata kai yayi tare da cewa”eh,aure hosana ko baki shirya ba,”
Turo baki ta ɗanyi tana ƙunƙuni ƙasa ƙasa,hankalinsa kam harya ɗan tashi saboda ganin yadda ta tsorata don yayi mata zancen aure,dama fargabarsa kada sai anje wurin nema mashi auranta tace bata shirya ba,don yasan ba cikakken hankali gare ta ba,

Karanta>>> Abban Sojoji Book 2 Complete

Lalla6ata ya shiga yi”pls hosana,ki faɗamun gaskiya,zaki aure ni”?
daƙyar ta iya buɗe baki tace”Ni yanzu tashi zanyi in tafi,dama zuwa nayi fa don in tambayeka,wani kalar ƙunshi kake so ayimun baƙi ko ja,”
ya lura cewa batason zancen auren shiyasa ta kawo maganar ƙunshin,cikin sanyin murya yace”Nafison jan lalle zai fi yi maki kyau,kuma ba mai yawa ba ƙunshin,ƴar flower kawai za’a zana maki mai kyau,”
Yana kai ƙarshen maganar,hosana ta miƙe tana faman shan ƙamshi,da sauri ta juya ta bar bedroom ɗin nashi,bin bayanta yayi da kallo har ta fuce,jiki asanyaye ya miƙe tare da nufar toilet ya shige,
Hosana na fita daga cikin bedroom ɗin nashi,a falonsa ta tsaya tana faman zabga murmushi,tsabar farin ciki kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha,Yau ya Omar ya nuna yana sonta harma yanayi mata zancen aure,ta rasa ma wa zata fara faɗamawa,sai faman zagaye zagaye takeyi a cikin falon,

Wuraren ƙarfe biyu da rabi na rana,Abusufyan ya ɗaukesu acikin motarshi kamar yadda yayi masu alƙwarin kaisu wurin saloon da kanshi,hosana da jahad suna a bayan motar duk sun ɗau wankan jallabiya sun laga mayafi,Sehrish na agaban motar kusa da driver seat inda Uncle abusufyan ke zaune yana driving ɗinsu anatse,Su jahad da hosana sae fira sukeyi tare dashi,amma ita ko uffan bata tanka masu ba,dama tunda ta shigo cikin motar Abusufyan ya lura da yanayinta,

gyaran murya yayi mata hakan yasa ta ɗan dago da kanta ta kalle shi,
“Meyake damunki ne Daughter?tunda kika shigo cikin motar nan baki tanka mana ba,ga ƴan uwanki suna ta fira a tsakaninsu amma ban dake”.
Muryarta asanyaye tace”Babu komai,”
“ko don saboda na hana ki kai ma Sgr abinci ne”? Yayi maganar batare daya kalleta,
Cikin sauri tace”a’a ba haka bane,kawai bana jin daɗin jikina ne,”
“Ban yarda ba daughter,saboda shi ne yasa kika shiga damuwa,”_
Shiru tayi bata ce komai ba,murmushi abusufyan yayi kafin yace”banyi hakan don na takura maki ba,face don na ɗaukaka darajarki,nasan ba zaki fahimce ni ba a yanzu amma nan gaba da kanki zakiyi mun godiya akan hakan,idan kuma hakan ya 6ata maki rai,kiyi haƙuri,’ya ƙarasa maganar adai dai lokacin da suka ƙaraso wurin Saloon ɗin,parking ɗin motar yayi jahad da hosana suka fita waje,tana ƙoƙarin buɗe motar ta fita ya ambaci sunanta”Sehrish,”juyowa tayi tare da kallon fuskar daddyn nasu tace”Na’am daddy,”
“Murmushi kawai nakeso kiyi mun kafin ki fita,”
fashewa tayi da dariya har fararen hakoranta suka bayyana,duk a tunaninta wani abu mai muhimmanci ne yasa ya kirata,ashe kawai don ya tambayi murmushinta ne,shima dariyar yakeyi,kafin su fita daga cikin motar atare,

**************
Fitowarshi kenan daga wanka,yana cikin shirya kanshi cikin riga da wandon jeans,yaji an kwankwasa ƙopar ɗakinshi,daga muryarshi yayi tare da cewa”ƙopar a buɗe take,”yayi maganar tare da juyawa yana kallon mai shigowar,
Cike da mamaki yace”Ya HAROON!kaine!dama kana nan,”
Shu’umin murmushin nan nashi ya saki tare da ƙarasa shiga cikin bedroom ɗin nashi yana cewa”Ina nan mana junaid,kaine ka manta dani,kowa ma ya manta dani,”
“Ya haroon ba haka bane,wlh ni ban manta dakai ba,kana araina,”
ta6e baki haroon yayi alokacin da yake tsayawa agaban junaid suna fuskantar juna yace”Ka ƙara kyau da haske,hankalinka kwance baka da wata damuwa,ba kamar ni ba,kullum cikin damuwa nake,zuciyata har nauyi takeyi mun saboda halin da nake ciki amma babu wanda ya damu dani,yau ko mutuwa nayi babu wanda zai damu,sae ma farin ciki da za’ayi,”
Jin wannan maganar ta haroon yasa jikin junaid yin sanyi,wani irin tausayin shi ya kamashi,muryarshi tamkar zaiyi kuka yace”pls Ya haroon dan Allah kadaina faɗin wannan maganganun,wlh bana jin daɗi,”
“Junaid ƙarya nayi ne?an damu dani acikin gidan nan ne?kowa yayi watsi dani,babu wanda ke damuwa dani,tamkar bare haka nakeyin rayuwata,hatta azmee da take ƴar aiki acikin gidan nan ta fi ni muhimmanci tunda ita ana damuwa da ita,ni kuwa fa?
Hawaye ne suka cicciko a idanun junaid,dama shi akwai tausayi,gaba ɗaya tausayin haroon ya kamashi,saboda duk abunda ya faɗi gaskiya ne,ba’a damu dashi ba,ko zancen shi ma babu maiyi acikin gidan,idan zai share wata a waje babu mai tambayar ina yaje,
“Tamkar maraya ni fa haka nake acikin gidan nan,kalli kaga yadda na koma duk na rame saboda damuwa,gaskiya ni bazan iya cigaba da rayuwa ba junaid,zan kashe kaina ne kowa ya huta,” yana kai ƙarshen maganarshi ya juya da sauri zai bar ɗakin,
Da gudun gaske junaid ya rungumoshi ta baya tare da fashewa da matsanancin kuka yana cewa”Meyasa ya Haroon!pls stop saying that,banason jin kana zancen mutuwa,ko kowa bai damu dakai ba,Ni nadamu dakai,ko don saboda ni ya haroon kada ka aikata hakan,idan ka kashe kanka,nima bazan rayuwa ba,zan bi ka mu tafi tare,”
Wannan kalaman na junaid ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya su kayi ba,cire hannunshi yayi daga ruƙon da yayi ma waist dinshi,sannan ya juya suna fuskantar juna yace”Junaid dagaske ne ka damu dani?kuma bakaso in mutu”?
cikin shessheƙar kuka junaid yace”Eh ya haroon bana so pls,”
Hannu haroon yasa yana share mashi hawayenshi,kafin daga bisani ya janyo shi ajikinshi tare da rungume shi sosai ajikinshi,kamar zai mayar dashi cikin shi,saitin kunnanshi yakai bakinshi tare da cewa”I love u so much junaid,cos you’re so special,in dai zan kasance tare dakai bazan ta6a shiga wani ƙunci na rayuwa ba,kallon ka kawai zai iya sanya farin ciki a cikin zuciyata,daga yanzu inason ka zama abokina junaid,saboda ka dinga ɗebe mun kewa,muna fita yawo atare,don bani da aboki,nifa kowa gudu na yake yi,bansan meyasa ba,’ya ƙarasa maganar tare da janye junaid daga jikinshi,

Karanta>>> Yadda Zaki Kula Da Nonuwanki Lokacin Da Kike Shayarwa 

“Junaid!ka amince zaka zama abokina”?
Jinjia kai junaid yayi tare da cewa”Eh,na amince,amma dan Allah ya haroon kadaina zancen zaka kashe kanka,banjin daɗi banso pls,”
“Shikenan na daina,daga yau kome kakeso ma zanyi,am sorry na sanyaka zubar da hawayenka,”
“Ya haroon ni zanje nayi ma Abba magana akanka,nasan abba zai fahimce ni,”
cikin sauri haroon ya ruƙo hannun shi tare da cewa”A’a junaid,just leave it,banason kowa yasan meke tsakanina dakai,kada kayi ma kowa maganata don ba lalle su fahimce ni kaman yadda kai ka fahimce ni ba,”
“Shikenan bazan faɗa ba,”
“Yawwa junaid ɗina,Yanzu zan barka ka ƙarasa shiryawa,”
Yana faɗin hakan ya juya tare da fucewa daga ɗakin junaid,ya koma bedroom ɗinsa,agaban dressing mirror ɗinshi ya tsaya yana ƙarewa fuskarshi kallo,
A hankali wannan mugun murmushin nashi ya soma bayyana akan fuskarshi,fashewa yayi da dariya kafin daga bisani ya ɗaure fuskarshi,kalaman junaid ya shiga tariyowa,tuni jikinshi yayi sanyi,ta wani 6angaren ji yake tamkar bazai iya ba,amma bai da wata mafita daya wuce wannan!
“Junaid kada ka damu zamu mutu atare,”ya faɗi hakan tare da komawa ya zauna daga gefen gadonshi,

Bayan junaid ya kammala shiryawa,saukowa downstairs yayi har lokacin jikinshi ba kwari,haroon ba ƙaramin tausayi ya bashi ba,A main palor ya samu Abbansu tare da Momnynsu dasu Twins suna fira atsakaninsu,tunkararsu yayi fuskarshi ɗauke da murmushi,suna haɗa ido da Abbansu ya watsa mashi harara,sunnar da kai ƙasa junaid yayi da wurin Abban yaso ya fara zuwa amma wannan hararar da yayi mashi ce tasa ya fasa zuwa ya wuce wurin mommynsu,dukawa yayi tare da manna mata kiss kafin ya rungumeta,fuskarta asake tace”My romeo,”Amsa mata yayi da mommy,a lokacin daya koma wurinsu twins suna gaisawa,Jahan yace”Ina zuwa naga key ɗin mota a hannunka,”
“Zanbi su uncle ne,” ayaan yace”Kada ka bari Mommy taji to,in ba haka ba bazata bari kabi su ba,”
“Saboda me”?ya tambaya yana kallonshi,Jahan ne ya bashi amsa da cewa”Saboda bazata barka ba,idan ta tambayeka ina zaka je,sae kace mata gidan abokinka zakaje,”duk wannan maganar da sukeyi a kunnan abbansu saboda yana kusa dasu,kallonsu kawai yakeyi,juyawa junaid ya ɗanyi tare da satar kallon mommyn,idonta na akanshi hakan ya tabbatar mashi da cewar so take taji me suke cewa,’
“Ka tafi kawai,”acewar ayaan,
harya juya zai tafi ya tuna da Abbansu,dawowa yayi tare da zuƙunnawa agabanshi yace”Abba,”ɗaure fuska abba yayi batare da ya tanka mashi ba,
“dan Allah kayi haƙuri abba in na 6ata maka rai,bazan ƙara ba,”
Ta6e baki abba yayi tare da cewa”Junaid kenan,ae ni yanzu babu ruwana dakai,kafi ƙarfi na,”_
Ashagwa6e ya kuma cewa”pls abba,kayi hakuri,ka manta da abunda ya faru jiya,bazan ƙara ba,”
“Naji,tashi ka tafi,ka kulamun da kanka,”
Murmushi junaid ya saki tare da mikewa ya manna mashi kiss a fuskarshi,sannan cikin sauri ya kama hanyar fita,
“Junaid ina zuwa”? Jin muryar Momnynsu yasa shi dakatawa da tafiyar da yake yi,

Karanta>>> Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata

tsayawa yayi tare da juyawo ya kalleta,
“Mommy gidansu abokina zani je,”
“Kai da wa?waye zai kai ka?
Nuna mata key ɗin motarshi yayi kafin yace”Ni zan kai kaina,”
Jinjina kai tayi tare da cewa”Okey,u can go,” da sauri ya fuce daga cikin gidan,
Mayar da idanunta tayi akan abbansu tace”Dama inaso inyi magana dakai,wai meyasa kuka bar romeo yana Driving da kanshi?Also babu wani security guard dake tsaronsa,Shi kadae yake yawonshi,”
Abba yace”Allah xai tsare mana shi,”
Alexandra tace”Nasan da wannan,Amma wannan babban ganganci ne,koda ace kowanne daga cikinsu zaiyi yawonshi batare da security guards ba,amma bai kamata ace kamar junaid ƙaramin yaro yana yawo shi kaɗae ba,ba wani tsaro atare dashi,Especially yadda kowa ya sanya mashi ido,gaskiya ni hakan bai kwanta mun araina ba!!”
shiru abbansu yayi yana nazarin maganarta,
Jahan yace”Gaskiya Abba,maganar mommy gaskiya ne,yakamata ace junaid akwai security guards dake tsaronsa duk inda zaije,musamman a wannan yanayin da muke ciki,bibiyar rayuwarmu akeyi don kawai acutar damu,junaid kuma yafi kowa ƙaranta acikinmu,yana buƙatar security,”
“Abunda nake ƙoƙarin fahimtar dashi kenan,”acewar mommnynsu,
jinjina kai Abba yayi tare da cewa”hakane,zanyi wani abu akai’,
daga nan suka cigaba da tattauna a tsakaninsu,

*Boss Bature*

Tun bayan da Hayaam ta tura ma Aunty babba hotonsu hosana,bata samu damar duba hoton nasu ba,ko whatsapp ɗinta bata shiga ba,wayarma tana ajiye cikin bedroom ɗinta,Shirye shiryen zuwa walima kawai sukeyi,atare da hafsat suka fita saloon daga nan za’ayi masu ƙunshi,bayan nan kuma zasu biya Shopping mall,saboda siyayyar da tace zatayi ma Ƴa’ƴan uncle ɗinsu,basu suka dawo gidan ba sai wuraren karfe shida na yamma agajiye suka dawo,kowa ya wuce bedroom ɗinshi,Aunty babba na shiga ɗakinta,kai tsaye ta faɗa saman gadonta ta shiga sharar bacci,Hafsa kuwa saida ta fara yin wanka,ta canza kayan jikinta izuwa riga da skirt marasa nauyi,sannan ta fito falo ta kwashe shopping bags ɗin da suka bari a falo,takaisu ɗakinta,tana cikin dudduba kayan wayarta dake ajiye gaban mirror ta shiga ringing,hannu takai tare da ɗaukar wayar tana kallon screen ɗinta,ganin Sunan Aunty Hayaam ya bayyana akan secreen ɗin wayar,yasa ta ɗaga kiran tare da karawa a kunnanta,
“Assalamu Alaikum aunty hayaam,’
Ko amsa mata sallamar batayi ba tace”Hafsat ina Aunty laila take ne?tun da sassafe na tura mata hoton bata duba ba,har nagaji da jira,”

Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam

Hafsat tace”yanzu muka dawo daga kasuwa agajiye,tana a bedroom ɗinta ina jin bacci ne ya dauketa,ko inyi mata magana ne”?
Hayaam tace”A’a,kawai idan ta tashi ki sanar da ita cewa na tura mata hoton ƴa’ƴan abusufyan ɗin,ta duba ta whatsapp ɗinta,”
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e hafsat,muryarta na rawa tace”hoton ƴa’ƴan Abusufyan dinmu!zan sanar mata kuwa,”
Rejecting call ɗin tayi,da gudu ta fito daga bedroom ɗinta,kai tsaye ta haye upstairs ɗakin aunty babba,tura kopar ɗakin tayi tare da shigewa ciki,a kwance ta samu aunty babba saman gadonta sai sharar bacci takeyi,ga wayarta ajiye agefenta,
Cikin sanɗa takai hannu tare da ɗaukar wayar,ta danna power ɗinta ta kawo haske,ganin akwai password yasa ta ɗan bubbuga kafarta tana cewa”Kai mommy,yanzu dole sae kin tashi sannan zan samu damar ganin hoton babies ɗinmu!gaskiya ni a ƙagare nake,”
Tana cikin maganar,ta tuna da finger print ɗin dake akwai ajikin wayar,nan take zuciyarta ta bata shawarar cewar me zai hana,ta lalla6a ta hau saman gadon,ta dangwalo yatsan aunty babba,kota samu wayar ta buɗe,Good idea,ta furta hakan tare da lalla6awa ta hau saman gadon,cikin sanɗa ta ƙarasa inda aunty babbar take,hannunta ta ruƙo tare da sanya yatsan hannunta a wurin,ya rubuta mata wrong,haka ta dinga bin yatsun hannun aunty babba tana jarabawa,har sai da taci nasarar buɗe wayar,saukowa tayi daga saman gadon,ta tsaya atsaye,hannunta har kerma sukeyi wurin daddana wayar,tsoranta kar Aunty babba tafarka saboda tasan halin Mommyn nata,ta tsani wani ya ɗaukar mata wayarta,kamar mara gaskiya,
Tana shiga whatsapp ɗinta,sai ga wani security ɗin,rai a6ace tace”Mommy kamar mara gaskiya,duk tabi waya ta garƙame da security,”
Allah yaso shima finger print ne,komawa tayi tare da dangwalo yatsan aunty babba,whatsapp ɗin ya buɗe,
Kaitsaye ta shiga chat ɗinsu da Hayaam,anan taga hoton da Hayaam ta tura mata,bai buɗe ba hoton saboda data a kashe take,cikin sauri hafsat ta kunna data ɗin,nan take yashiga loading yana ƙoƙarin budewa,a hankali hoton ya soma bayyana,ƙura ido hafsat tayi tana jiran hoton ya kammala buɗewa,
Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu ji kake Daram!!Dararam!!tamkar ana buga ganga,Waro ido waje hafsat tayi agigice a matukar razane,tamkar wadda taga Zombie,hankali a matuƙar tashe tace”Kai!!!”
Hannunta har kerma yakeyi wurin yin zooming ɗin hoton nasu ta matso dashi kusa don tagani dakyau,gaba ɗaya tagama kiɗima,wata irin zufa ce  ta soma tsattsafo mata agefen fuskarta,daƙyar take iya haɗiye yawun bakinta saboda maƙoshinta daya bushe ƙamas,juyawa tayi ta kalli Aunty baba dake ta faman mutsu-mutsu alamar zata farka daga baccin da takeyi,aikuwa cikin sauri tayi deleting ɗin hoton gaba daya,sannan ta rufe wayar,tayi wurgi da ita asaman gadon,jikinta na kerma ta fuce daga dakin,gudu gudu sauri sauri haka take tattaka stairs ɗin ƙiris ya rage ma tayi tuntu6e saboda yadda jikinta ke rawa kafkaf kamar wadda sanyi ya kama,
Bedroom ɗinta ta koma,tana shiga ta aza hannu akai tana faɗin”Tashin hankali!In har dagaske ne abunda idanuna suka gane mun acikin hoton nan kenan hakan na nufin cewa HOSANA DA JAHAD Suna araye kuma suna a gidansu daddy!taya hakan ya faru?Kenan Ya Omar shine ya ɗaukesu?Ina wannan tsohon mutumin da mommy tasa ya kwashe su da nufin ya zubar dasu?Taya akai hosana da jahad suka kasance ƴa’ƴan uncle ɗinmu!?wacece ita ɗayar yarinyar mai kama dasu sak!dama su ƴan uku ne?Tabɗijancan,akwai matsala,

Karanta>>> Hadin Karawa Mace Ni’ima, Sha’awa Da Kuma Karin Dandano

Komawa tayi gefen gadonta ta zauna tare da kifa hannunta asaman fuskarta,hosana da jahad suna raye,suna gidan abban mu,wayyo Allah na,ina farin ciki sosai,duk da ina tsoran abunda zai biyo baya,Ashe jinina ne su!shiyasa akace rashin sani yafi dare duhu,mun cutar dasu sosai,mun zalunce su bayin Allah,mutuwa ce kawai batazo ta daukesu ba acikin gidan nan amma sunsha wahala,sun ƙuntata,tabbas Mommy mun shiga uku,idan Abba yaji,daga ni harke ba wanda zai tsira,kwara ni hukuncina mai sauƙi ne tunda na nuna masu soyayya daga baya amma ita mommy itace silar fitar dasu daga gidan nan don azubar dasu,Wayyo Allah na!,
Yatsun hannunta sae faman kerma sukeyi,jiki na rawa ta ɗauki wayarta tare da lalubar numbar junaid ta danna mashi kira,
A lokacin junaid yana tare dasu Uncle abusufyan,dama sai daya fara kiranshi a waya ya tambayi address ɗin inda suke ya bashi,har an kammala yi masu saloon tuntuni,anyi masu ƙunshin jan lalle a hannuwansu,daga can suka wuce shoprite siyayya,bayan sun kammala siyayyar,suka biya gidan Uncle ɗin nasu wuraren 6,saboda su kwaso wasu daga cikin kayansu Jahad da hosana wanda zasuyi kwalliyar walima dasu,
A bayan motar junaid aka sanya trolley ɗin kayan nasu,sannan Sehrish da hosana suka shige motar abusufyan,jahad kuma ta shiga motar junaid,atare motocinsu suka fita daga cikin gidan,
Tunda jahad ta shiga motarshi,ya ɗaure fuskarshi,dama tun wurin siyayyar yake ta shan mur yana murtuke mata fuska,amma hakan bai hana tayi masa magana ba,duk in ta ɗauko abu sai ta gwada mashi ta tambayeshi zaiyi mata kyau,daƙyar yake amsa mata da eh,ko a’a,sai dae kawai tayi murmushi ta girgiza kai,
Kiran Hafsat na shigowa a wayarshi,yace”ki ɗauki wayar,ki amsa wayar sai ki sanyata a handsfree,”
hannu jahad tasa tare da ciro wayar daga aljihun gaban rigarshi,picking call ɗin tayi bayan ta sanyata handsfree sannan tayi Mata sallama,
Muryar hafsat ce ta karaɗe kunnansu”Junaid!kana ina ne”? Gaban jahad ne ya faɗi rass saboda jin muryar hafsat,duk da bata tabbatar da cewar ita bace,amma muryar tayi mata kama da ta sister hafsat,
“Ina akan hanyar komawa gida ne yanzu hakan,”
Hafsat tace”junaid dan Allah so nake in tambayeka,waɗannan yaran ƴa’ƴan uncle abusufyan Ƴan uku ne”?
“Of course they are triplet,”ya bata amsa a yayin da yake ƙoƙarin juya sitiyarin motar,ya karya kwana,
Hafsat tace”Ya sunan su”!
Juyowa yayi ya ɗan kalli jahad da idanunta ke akan shi,kafin ya mayar da idanunshi kan driving din da yakeyi,a jere ya ambaci sunayensu”Hosana Sehrish Jahad”!hafsat na jin haka,a gigice ta kashe wayar,
“kiran ya katse,”Jahad ta faɗi tana ƙare ma wayar kallo,
“May be network ne,idan na koma gidan zan kirata,”
“In mayar maka da wayar”?
“A’a ki ruƙe a wurinki,idan mun isa gida zan kar6a,”

ta amsa mashi da toh,
Gallery ɗinshi ta shiga tana kallon kyawawan hotunanshi da yayi,tare da videos,yawanci duk na ban dariya ne,wasu yana a kwance,wasu ya zullo harshe waje,wasu hotunan ya kashe idanunshi,
Dariya ta dinga yi a yayin da take kallon videos ɗinshi na tiktok,duk yana sauraron sautin dariyarta,wani lokacin har satar kallon fuskarta yakeyi,ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,musamman inta tuntsire da dariya,wani sa’in hada kifa kanta saman laps dinta saboda tsabar dariya,murmushi kawai yayi tare da mayar da hankalinshi akan driving ɗin da yake yi,a haka har suka ƙarasa gida,

Karanta>>> Amfanin Hulba A Jikin Yan Mata Dama Matan Aure.

Bayan hafsat ta katse kiran,ta Kifa kanta asaman pillow ɗinta,tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka,dama ance dana sani ƙeya ce,

Farkawa Aunty babba tayi da wata irin matsiyaciyar yunwa,sae faman hamma takeyi,tashi tayi daga zaune tare da kai hannu ta ɗauki wayarta tana cewa”Ko hayam ta tura mun da hoton?bari na duba na gani,Allah yasa dai bata manta ba,”
shiga cikin whatsapp ɗinta tayi tare da duba chat ɗinsu da hayaam,rai a6ace taja dogon tsoki tare da cewa”Wai dama bata turamun hoton ba!harfa ƙara nanata mata nayi akan ta tura mun hoton amma bata turo ba,” ta ƙarasa maganar tare da yin wurgi da wayar saman gadon,
Saukowa tayi daga saman gadon,fita tayi daga cikin bedroom din ta sauko ƙasa,kai tsaye ta nufi kitchen,
Batare da 6ata lokaci ba,ta shiga harhaɗa kayan da zatayi amfani dasu,bayan ta ɗaura girkin,ta ɗebo snacks a plate ta haɗo da coke mai sanyi ta dawo falo,ta zauna,tana ci tana kallo a plasma hankalinta kwance,

jin motsin mutun a gefenta yasa tayi firgit tare da juyawa don taga wanene,ashe hafsat ce atsaye yanayinta kamar na wadda tayi amai da zawo,fuskar nan tayi gwanin ban tausayi,idanunta sun ƙankance saboda kukan da tasha,
“Hafsat!lafiya naga fuskarki tayi jawur?kinyi kuka ne”?
Girgiza kai hafsat tayi tare da cewa”Babu komai mommy,wani film nake kallo acikin wayata,shine ya sanya ni kuka,”
Tsoki Aunty babba taja”shirmen banza,kawai daga kallon film saiki kama kuka kamar wata sakarya,”
murmushin takaici hafsat tayi tare da samun wuri daga gefen aunty babba ta zauna,batare da tace komai ba,
Aunty babba taci gaba da cewa”gaskiya kowane film ne wannan ya ciri tuta tunda har ya iya sanyaki zubar da hawayenki,yadda kike da shegen taurin kai,
“Mommy ba zaki gane bane,”
“Taya za’ae in gane?tunda bakiyi mun bayanin meya faru ,acikin film ɗin ba,ki ɗan bani labari mana,”
Gyara zama hafsat tayi kafin ta soma bata labarin kamar haka”wata matace fa,mijinta ya kawo mata wasu marayun yara donta rainesu a wurinta,tun ranar da mijin ya kawosu gidan shi kuma yayi tafiya,ae kuwa matar nan,ta shiga gana masu azaba,ta hanasu abinci yunwa kamar zata kashesu,har bugunsu takeyi,sannan kuma ta dinga sanyasu aikin wahala,har saida suka kusa rasa rayuwarsu,mommy kinsan meya faru”?
Dakatawa Aunty babba tayi daga shan lemun hannunta da takeyi tace”a’a saikin faɗa,”
“Hmmm,Mommy ƙarshe fa matar nan,tasa aka kwashe yaran nan,aka 6atar dasu saboda kawai kar asirinta ya tonu a wurin mijinta…’
“Hakan da tayi yayi mun dai dai,”Acewar aunty babba,
Murmushi hafsa tayi kamin tace”Ae ban ƙarasa maki labarin film ɗin ba,bayan tasa an zubar da yaran nan,ita duk a tunaninta sun mutu ma,Ashe can wurin gararin rayuwar da sukeyi a daji Allah ya haɗasu da kanin mijinta har ya taimakesu ya kaisu gidansu mijin,da akayi bincike aka gano cewar yaran ƴa’ƴan kawunsu ne wato ƙanin mahaifinsu,”
Aunty babba tace”tashin hankali!ita ko wannan ya zatayi da kanta?
Dariya hafsat tayi tare da cewa”Nima abunda nake tunani kenan!amma Mommy idan kece ya zakiyi,”
shiru Aunty babba tayi tana tunani kafin daga bisani tace”Ae kawai tunkan asirina ya tonu zan gudu ne,a neme ni arasa,amma nikam hafsat wai ya sunan Film ɗin nan ne?tayi tambayar tare da kallon hafsat ɗin wadda itama kallonta takeyi,mikewa hafsat tayi tsaye tare da cewa”An fara kiran sallar magriba,bari naje nayi salla,”
“Amma baki faɗamun sunan film ɗin ba!”Aunty babba ce ta sake nanata mata tambayar da tayi mata,
*AN YANKA TA TASHI* shine sunan film ɗin mommy,yanzu na kalleshi a tashar youtube,tana kai ƙarshen maganarta,ta juya da sauri ta wuce bedroom ɗinta,
Zugudum Aunty babba tayi tana maimaita sunan film ɗin da hafsat ta faɗa mata,wato An yanka ta tashi,
Aranta tace”gaskiya ya kamata in kalli film ɗin nan,Inaso inga yadda matar nan zata ƙare,ko ya mijinta zaiyi da ita?tabɗijancan,akwai badaƙala,”tayi maganar tare da mikewa ta wuce kitchen domin ta duba girkin da ta ɗaura,

Karanta>>> Amfanin Zogale Guda 18 A Jikin Dan adam

Bayan ta kuma fitowa daga kitchen ɗin,upstairs ta wuce bedroom ɗinta,gefen gadon ta zauna tare da miƙa hannunta ajikin drawer chest ta janyo gidan farko,sabon sim ne ta ɗauko tare da daukar wayarta dake ajiye saman gadon,zura sim card ɗin tayi aciki,sannan ta lalubo lambar wayar Ammi wadda tayi copying kan phone,danna mata kira tayi,nan take kiran ya shiga,kusan sau uku kiran na katsewa batare da anyi picking ɗinsa ba,tana kira a karo na hutu Ammi ta ɗaga kiran 😳

ɗan zaro ido Aunty babba tayi kafin ta gyara natsuwarta tare da zabga sallama”Assalamu Alaikum Ammi barka da warhaka,”ta maƙe muryarta yadda ammi bazata iya gane muryar wacece ba,
on the other hand Ammi ta amsa mata da cewa”Wa’alaikumus salam,barkanki dai,zan iya sanin dawa nake magana”a dake take magana,
Aunty babba tace”Nasan bakisan dawa kike magana ba,saboda baki sanni ba,Ni matar abokin Abusufyan ce,wadda ke zaune a ƙasar turkey,”
Shiru ammi tayi tana sauraran me magana,
Aunty babba taci gaba da cewa”akwai wani mummunan abu da abusufyan ya aikata a 6oye baison kowa ya sani,shiyasa na kira don in sanar dake,don banason abunda zai ta6a mutuncin family ɗinku,wannan abun kunya ne,muddin ya fita waje mutane sukaji to fa,zaku rasa duk wata ƙima da martaba da kuke da ita….’
tana cikin magana Ammi ta dakatar da ita”Ya isa haka!banason wata kwanana,ki faɗamun abunda kikeson sanar dani!me Abusufyan ya aikata?wani laifi ne wannan da har kike ikirarin zai ta6a ƙimar family ɗinmu a idon jama’a,”?
Wani irin wahalallen yawu aunty babba ta haɗiye kafin daƙyar ta soma kora mata jawabi kamar haka
“Shekarun baya da dadewa,Abusufyan yayi ma wata fyaɗe,harta samu ciki…..”
Wata irin tsawa da Ammi ta daka mata har sae da takusa sakin fitsari a wando,a tsiwace tace”Dakata!ki iya bakinki!kinaso ki shiga tsakanina da ɗana ne!wacece ke,kada kiyi tunanin kin kirani da 6oyayyiyar number,zan iya sa agano munke duk inda kike,”
Muryar Aunty babba na kerma tashiga faɗin”wlh dagaske nake ammi ba ƙarya nake ba,gobe idan kinzo abuja wurin walima,zaki ga yaran,ae suna nan gidan Abba,Sun jima suna 6oye maki gaskiya,saboda tsoron hukuncin da zaki yanke ma Abusufyan,yanzu haka maganar da nake maki,sun gama shirya yi maki ƙaryar cewar yaran ba shaggu bane ta hanyar aure aka haife su bayan ba haka bane,suna nan yaran ƴan uku ne mata,sun girma sosai,’ tana kai ƙarshen maganar Ammi tace”Kin gama”?
Shiru Aunty babba tayi tana faman mazurai aranta tace”Wannan tsohuwa badae taurin kai ba,bansan ya zanyi na fahimtar da ita ba,ta cika jaraba,”
tana cikin wannan zancen zucin Ammi ta katse kiran,
Wurgi Aunty babba tayi da wayarta,tare da mikewa tana cewa”Ae shikenan,nasan cewa gobe tana ganin yaran zata tuna da kalamai na,daga nan saita ɗauki hukuncin daya dace,”

❤🤍❤

*Boss Bature*

Zaune yake asaman Sofa mai mazaunin mutun uku,gaba ɗaya ya tattara hankalinshi akan Laptop ɗinshi da yake daddawana anatse,jikin shi na sanye da linen tank top,blue colour tabi shape din jikinsa,sick pack din nan nasa ya bayyana ajikin rigar,trouser ɗin jikinsa kuma white colour ne,wani irin daddaɗan ƙamshi ne ke fitowa daga kowani sashe na jikinsa,

Shigowa Azmee tayi part ɗin nasa da sallama a bakinta,yayin da hannunta ke ruke da tray,amsa mata sallamar yayi batare daya ɗago ya kalleta ba,ƙarasawa azmee tayi tare da ajiye mashi tray ɗin asaman empty table din dake a gefenshi,hannu takai tare da ciro plate ta daukko serving spoon tana ƙokarin buɗe warmer,muryarshi ta katse mata hanzarinta da cewa”ɗazu da safe meyasa kika kawomin breakfast?kuma kika gyaramun bedroom ɗina,dama kece ke gyara mun part ɗina ne”?
gabanta ne taji ya faɗi rass,muryarta na kerma tace”A’a bani bace,Sehrish ce,”
“Meya hanata yi mun aiki,”?yana magana yana danna laptop dinsa har time ɗin bai ɗago da idonshi ba ya kalle ta,
Azmee tace”Am…um…dama…”bata ƙarasa maganar ba,ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannunshi,cikin sauri ta shiga taitayinta,
Cike da bada Umarni yace”Call her right now,”
Jiki na rawa azmee ta juya tare da fucewa daga part dinsa,downstairs ta saukko,babu kowa a falon duk suna a bedroom ɗinsu,wasu ma sunyi bacci,
Kai tsaye ɗakinsu Sehrish taje,tsayawa tayi abakin ƙopar ɗakin tana kwankwasawa,sai faman knocking takeyi amma ba’a buɗe mata kopar ba,da alama sun jima da yin bacci,
Har sae da ta fidda rai da za’a buɗe mata kopar,tana kokarin juyawa tabar wurin,taji alamun za’a buɗe kopar,Jahad ce ta buɗe ɗakin tana tambayar wanene,
Ganin azmee yasa tayi saurin gaishe da ita cikin girmamawa,
Azmee da nan take ta gane ba sehrish bace tace”kiyi hakuri na tashe ki kina bacci,Sehrish nake nema,dan Allah ki sanar da ita cewa SGR yana nemanta a part ɗinsa,”
Jahad tace”tayi bacci,bari na tashe ta,”tayi maganar tare da juyawa cikin sauri ta shiga cikin ɗakin,
Wucewa azmee tayi ta koma kitchen,cike da zullumin mai zai biyo ba idan Sehrish ta sanar ma Sgr cewa Uncle abusufyan ne ya hanata yin aiki a part ɗinsa,tabbas za’a kwashi ƴan kwallo,

“Sehrish!ki tashi babban yaya yana son ganinki a part ɗinsa,dan Allah ki tashi kije,”jahad ce keta kokarin tashinta daga bacci,sehrish kuwa sai faman mutsu mutsu takeyi,daƙyar ta iya cewa”Wanene ke nema ne’?
Jahad tace”babban yaya,”
Jin sunanshi yasa Sehrish buɗe idanunta ta wurgasu kan jahad dake tsaye,yatsina fuska tayi tare da maimaita sunan nashi”babban yaya?shike nema na,waya faɗa maki”?
“Aunty azmee,yanzun nan bata jima da tafiya ba,naga kamar ma bata acikin natsuwarta,”
Jin hakan yasa gaban sehrish faɗuwa rass,yunkurawa tayi tare da mikewa zaune,ta saukko da ƙafafunta ƙasa,kafin ta miƙe tsaye,saboda tsabar saurin ta fita ko Mayafi bata ɗauka ba,gashi kanta ko kallabi babu,sumar kanta ce da tasha gyara,an mayar mata da gashin mai gazar gazar ya sauko har kafaɗarta,a hankali gashin kan nata ke toho yana fitowa,har ta launin gashin anyi mata dying dinsa ya koma 2 colour,Kayan bacci ne ajikinta riga da wando sharara suke,farare masu laushin gaske,irin waɗanda kana sanyasu ajikinka,Ko baka jin bacci nan take zai zo maka,
Tunkan ta ƙarasa shiga falon nashi take jin ɗar ɗar acikin zuciyarta,tun jiya rabon da ta sanyashi acikin idanunta,daƙyar ta iya yi mashi sallama tare da kutsa kai cikin falon nashi,bai amsa sallamarta ba,har ta ƙarasa inda yake,atsaye muryarta na rawa tace”Gani,”bai dago ba kuma bai tanka mata ba,sae ma cigaba da danna system ɗinshi da yake yi,lokaci bayan lokaci yakan kai hannunshi ya dauki Coffee ya kur6a,zuba mashi ido tayi tana kallon kyakkyawar fuskarshi,ba ƙaramin kewarshi tayi ba,sam batayi tunanin ma zai nemeta ba,
sai da ta ƙara cewa”babban yaya gani,Aunty azmee tace kana kira na,”sannan ya soma magana anatse”yau da safe,meya hanaki zuwa part ɗina”?
Shiru tayi gabanta na faɗuwa,batasan amsar da zata bashi ba,saboda tsoran abunda zai biyo baya,
“Kinsan bana maimaita magana,amsarki nake jira,”
Runtse idanunta tayi aranta tana fadin”nashiga uku,!Allah ka kawomin ɗauki,bansan me zan faɗa masa ba,”shirun da tayi mashi ne ya fusata shi,aikuwa a zafafe ya daka mata tsawa,har sai da ta zura da gudu saboda yarda ta tsorata,kama hanyar fita tayi saboda ruɗewar da tayi,hakan yasa ya miƙe tsaye tare da bin bayanta,ruƙo hannunta yayi tare da fusgota ta dawo saitin shi,Waro ido waje tayi tare da ja da baya da baya,har suka ƙure ma bangon,runtse idonta tayi muryarta na kerma tashiga faɗin”Am so sorry babban yaya,I can explain,zan faɗa maka,”
A hankali ya ware blue eyes ɗinshi akan fuskarta,sumar kanta yabi da kallo,yayi mamakin ganin yadda gashin yayi tsayi cikin ƙankanin lokaci har ya kamo kafaɗarta,gyaran gashin da akayi mata ya ƙara fiddo da kyawun fuskarta,mayar da idanunshi yayi akan La66anta dake ta faman kerma duk tabi ta gigice,lokaci guda ya tsinci kanshi cikin wani irin yanayi mara misaltuwa,moving ya ƙarayi gaba ɗaya yayi mata rumfa da faffaɗan ƙirjinshi,lokacin da taji tsinin hancinshi na gogar nata,nan take gabanta ya kuma bugawa daramm,jikinta ya shiga yin kerma ta ko’ina,gaba ɗaya duk tabi ta susuce har lokacin ta gaza buɗe idanunta saboda tsabar tsoro,jin saukar hannunshi asaman ƙirjinta yasa ta yin saurin ware idanunta arazane,kai tsaye suka sauka cikin nashi,face to face,Eyes to eyes,nose to nose,mouth to mouth!!,
A firgice ta janye idanunta daga kan fuskarshi ta mayar dasu akan ƙirjinta,Ashe gaban rigarta ne ta bari a buɗe ta manta bata sanya links ɗin rigar ba,Shine ya sanya hannunshi a wurin yana manne mata su,jurewa kawai takeyi amma ba ƙaramin yanayi Sgr ya jefa mata ba,musamman yadda hannunshi ke nutsewa a cikin boobs ɗinta,ba ita kaɗae ba,hatta shi kanshi daya kai hannunshi wurin saida yayi regretting,saboda wani abu daya dinga jin yana fisgarshi yadda kasan magnet,mayen karfe ba,
daƙyar ya iya zame hannunshi daga saman ƙirjin nata,bayan ya kammala sanya mata links ɗin,Sannan cikin sanyin murya yace”tell me the reason why baki zo yi mun aiki da safe ba!bakisan bana son sharing a aiki na ba!?
Magana yakeyi amma idanunshi sae ƙokarin lumshewa sukeyi tamkar mai jin bacci,wanda kuma ba kowa ne yajawo hakan ba face Sehrish,
Cikin en ena tace”Kayi haƙuri ba laifina bane,Daddy ne ya hanani zuwa”
Cike da mamaki yace”Kina nufin Uncle ne ya hanaki zuwa,”
Jinjina mashi kai tayi alamar eh,yayin da take ta faman haɗiyar yawu,
. “just without any reason ya hanaki aiki a ƙarƙashi na”?
daga mashi kai tayi alamar eh,
Cije pink lips ɗinsa yayi tare da tsoma hannunshi acikin sumar kanshi yana cakuɗata,ranshi a matuƙar 6ace yace”hakan bazai ta6a yiyuwa ba,dole kiyi aiki a ƙarƙashina!ban damu da matsayinshi a wurinki ba,dole ne ayimun biyayya!!!!!!!!*

*Tashin hankalin da ba’a sama shi date!*

Gobe walima,suwa suka shirya zuwa💃💃💃💃

 

Back to top button